QANIN MIJI 10

Advertisement

Ina matuqar godiya ga ɗaukacin masoya ma su bin wannan littafi na qanin miji, ba sai na ce group kaza da kaza ba, matuqar kika ga wannan page kawai kiyi murmushi, ka yi murmushi domin da ke nake, da kai nake, gaba ɗaya wannan page sadaukarwane gareku, ina yinku guys, 143 forever and ever💕

10
Sake turo qofar yayi a karo na biyu bayan dawowarshi daga masallaci ya sake rufo qofar
Har yanzu fareedah baccinta take tayi hankalinta kwance sai sauke numfashinta take yi a hankali
Zama yayi a bakin gadon ya qura mata idanu tsawon lokaci, yalwataccen  murmushine ya bayyana a kan fuskarsa saboda wata iriyar zazzafar qaunarta da ya ji tana dabaibaye masa dukkan sassan jikinsa, ajiyar zuciya ya sauke tare da jingina da jikin gadon ya lumshe idanu yana tunano abubuwa da dama, buɗe idanun yayi ya sake kafe kyakkyawar fuskarta da su yana cigaba da murmushi, ji yake kamar ya ɗauketa ya sanyata cikin zuciyarshi ya adanata saboda tsabar qauna
Kasa jure wa hakan yayi, a hankali ya kwanta a kan gadon ya sanya hannayensa ya rungumota ya janyota kan cikinsa tare da matseta cikin hannayen nasa, ita kuwa ko daɗin bacci ko son zuciya oho, sai ta wani lafe masa a jiki tare da qanqameshi ita ma ta cigaba da baccinta
Ganin irin cacumar da ta masa, ya gane matuqar bai tasheta ba toh ba ta shirya tashi yanzu ba, kuma ba ya so ta rasa sallah a kan lokaci
Agogo ya kalla sannan ya dawo da idanunsa kan fuskarta ya fara hura mata iska a kan fuskarta a hankali, fuskar ta janye ta mayar wani side ɗin ta cigaba da baccinta, murmushi yayi mai sauti sannan ya saita bakinsa daidai kunnenta ya fara hura mata iska nan ma yana yi yana murmushi, maimakon ta tashi sai ture bakinsa tayi tare da shagwaɓe fuska cikin baccin
Da ya ga dai lamarin nata da gaskene sai kawai ya zameta daga jikinsa ya tashi ya cire kayan jikinsa ya wuce toilet ya haɗa musu ruwan wanka a karo na biyu sannan ya dawo ya sunkuyo gadon ya cicciɓeta sai toilet, sai a lokacin ta buɗe idanu dan ta ga me yayi sama da ita dan sai take ji kamar a mafarkine ake yin saman da ita
Ba ta gama farfaɗowa daga magagin barcin ba ta ji ta a cikin ruwa, ai tarwar ta buɗe idanunta tana rarrabasu
Hafeez da ta gani yana qoqarin shiga bathtube ɗin ta shagwaɓe wa fuska, shi ko wawa jiki na rawa ya qarasa shiga cikin bathtube ɗin ya rungumota yana dariya yace
“yi haquri my swampy, lokacin sallah zai fita ba tare da kin yi ba, shi ya sa na aikata hakan, amma in kin ji haushi kiyi hakuri kin ji tawan”?
Ya wani marairaice mata, murmushi kawai tayi tana binsa da kallo, shi ko ya kai bakinsa jikin na ta ya sumbaci lips ɗinta tare da tallafo haɓarta yana mata wani sheɗanin kallo yace
“na gode matar, zan miki wankan da kaina, na san ma kin amince ko”?
Yadda yayi maganar ya ɗauke mata hankali, dan haka sai ta tsaya kawai tana binsa da kallo mai cike da yanayin kana burgeni, hakan da ya gani ne ya bashi qarfin zuciyar fara mata wanka yana yi yana abin da ransa yake so, lallai ba dan sallah ba da wata tsiyar za a kuma,
Tsab ya wanketa ya ɗauraye musu jiki suka fito tare kowanne ya ja towel ya ɗaura sannan tayi alola suka fito
Kai matasa ku ji tsoron Allah, ku kiyaye da dokokinsa, wai wacce tsiyar kuke tsinta a zinane?, me zai sa ku jefa kanku cikin najasar zina duk da tana gadar da talauci wa duk al’ummar da ta yi riqo da ita?, me yasa ba za ku dinga zuwa ga halalinku ba, yanzu kai mai zina ba ka karanta qur’ani ka ji illar zina da baqin duhunta, wallahi ni a gurina ya zama abin qyama da neman tsarin da ya kamata a nemi tsari da shi, je ka qur’ani cikin suratul baqara in da Allah ya qulla alaqa tsakanin zina da yin shirka wa Allah, me nake nufi shi ne, ayar nan da Allah yake cewa “Azzani la yankihu illa zaniyatan au musrikatun, wazzaniyatu la yankihuha illah zanin au mushrik, wa hurrima zalika alal mu’minun”
Ma’ana, mazinaci ba ya aure sai mazinaciya ko mushrika, haka mazinaciya ba ta aure sai mazinaci ko mushriki, Allah yace an haramta hakan wa mu’minai
Kun ga da ayar nan, da cewar da Annabi yayi duk lokacin da masu zina suke yin zina akan cire musu rigar imani, na fahimci cewa ita zina abace da tayi kusa da shirka, domin wannan ayar ta cikin suratul baqara ta nuna bayan mazinacin babu wanda ya dace ya auri mazinaciya sai mushriki, kenan bayan mazinaci Allah ya nuna mushriki ma ɗan uwan mazinaciyace, ke mazinaciya ki ji tsoron Allah, kar ki cutar da ‘ya’yanki ta hanyar musu shimfiɗa a cikin mahaifarki da datti da najasar zina, domin wallahi gubace a garesu fiye da hayaqin bama baman nuclear, ke gwara su zama dukkansu nakasassu da su kwanta cikin dauɗar zinar da kika tara a cikin mahaifarki, abinda baki sani ba yara a halaye sun fi gadon uwa, wallahi yadda kika yaudari iyayenki kika zubar musu da mutunci kika je kika yi zina da wani qato, toh dole sai kin samu wannan baragurbin cikin yaranki, sai sun gadoki wallahi saboda shayar da su, da dafa musu abinci da kike yi, da wannan alaqar da ubangiji ya sanya tsakani uwa da abin haihuwarta tun cikin mahaifa, ‘yar uwa ba a wayo wa Allah, duk tsaronki matuqar kin taɓa yi toh ki jira kawai kika ta inda abin zai ɓillo miki, amma za a yi hakan, in faɗa miki mafita?, toh ki koma gurin iyayenki ki roqi gafararsu akan laifuffukanki da kika taɓa musu tun tasowarki, ba wai lallai sai kin faɗi sunan lafin ba, na biyu, mijinki da ya aureki a matsayin budurwa sai ya samu kin taɓa kwanciya da wani, toh wallahi yana da wannan hakkin, dole sai kin koma kin roqi gafararsa, ba tare da kin faɗi laifin ba, ya yafe miki dukkan laifukanki kawai a gareshi, sannan ki zaunar da yaranki cikin hikima da basira da iya sarrafa harshe irin na uwa ki ninkesu baibai ki ce musu su yafe miki duk wani cutarwar da kika taɓa musu cikin sani ko akasin hakan, domin kin cutar da su matuqar cutarwa domin kin shafa musu gubar zinar tunda sun kwanta a mahaifanki, daga nan sai ki koma ga mai tausayinki, wato ubangijinki Allah kenan, ki yi ta kai masa kukanki kina roqon yafiyarsa, sannan kina neman tsari wa zurriyarki da kada su aikata zina, toh inshaa Allahu yaranki ba za su aikata zina ba matuqar tuba kika yi irin wacce Allah ya kira da nasuha
Ku mazinata maza ku ji tsoron Allah, ku ji tsoron gamuwarku da shi, musamman waɗan da suke zina da matan aure, ku sani manzon Allah ya ce, duk wanda yayi zina da matar wani, idan kiyama ta tsaya a filin hisabi za a kawo aikin alherin  wanda yayi zina da matar wanin, a kira wanda kayi zina da matarshin, a ce masa ya ɗebi iya yadda ya masa, kai shashasha mai zina da matan mutane, manzon Allah yace kana gani zai rage maka saura?, wallahi ko ni in za a ban izini zan ce ya kwashe tas, a gungura banza cikin wuta, ku matasa ku ji tsoron Allah, ku sani zina ba alheri ba ce, za ta hallakaka ta hallaka al’ummarka, kai yanzu ba za ka yi tunani ba, matar wani ta tsaya a gabanka cikin tsaraici kuma ka iya kallonta ka ji daɗi?, me za ka ce wa ‘ya’yanta idan sun sani, me zaka ce wa ubangijinta da yake tsananin kishinta ta fiye da mijinta?ƙdan Allah mu haɗu mu gyara al’ummarmu👏🏼😭
A cikin kwanciyar hankali hafeez ya zage yayi ta ba wa fareedah abinci a baki yana kalallameta da riritata, ita kuwa sai narke masa take yi tana jin daɗin gwaɗata da yake yi, tun a gurin cin abincin suka sake tsokano kansu dan haka sai da aka je round two, suka sake gangarawa cikin fushin Allah da tsinuwarsa, a nan kam sai da sallar la’asar ta kubce musu, dole sai bayan an daɗe da yinta kafin suka samu damar gabatar da ita
Wayyo Allah, lallai ubangiji yayi gaskiya da yace “kalla bal, rana ala qulubihim ma kanu ya’amaluun”
Allah kar ka ɗiga mana Ran a zuciyarmu saboda ka qawatar mana da wani laifinmu, ka yafe mana domin kai mai gafarane😭
Ran tsatsace da take dabaibaye zuciyar mutum bayan Allah ya masa ɗigo akan zuciyar sakamakon laifin da yake ta aikatawa, haka za a yi ta ɗiga masa har sai ya daina ganin munin laifin da yake aikatawa
swampy kamar yadda inbox ɗina ya kusa amai saboda yawan tambaya a kansa, wato a Agriculture, qarqashin types of land akwai swampy, to abin nufi gurin da qasar gurin take da yawan ruwa, like fadama, toh sai ku haɗa da maganar hafeez a nan zaku gane me yake nufi, dan Allah a bar ni in huta, tambayoyin sun isa haka pls😍👏🏼
ISLAM IS MY IDENTITY

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

QANIN MIJI 1

Advertisement QANIN MIJI Daga alqalamin marubuciyar zamani✍🏼 MARYAM A.I GITAL @ Meerahgee pure moment of life writers👌🏻  SADAUKARWA GA…

QANIN MIJI 14

Advertisement  Ina matuqar ba da hakuri wa masoyana masu bin littafin JININANE hakuri saboda tsaikon da aka samu…

QANIN MIJI 9

Advertisement IYAYE KU JI TSORON ALLAH, ‘YA’YANKU SUN FARA KAWO MIN QARARKU, KUKAN HANASU AURE AKAN KARATUN GABA…