QANIN MIJI 11

Advertisement

11
Rungume take a jikinsa bayan sun idar da sallar, zaune suke akan darduma sai kalamai yake raɗa mata ido cikin ido cikin wani irin salo mai ɗaukar hankali, ita kuwa sai wani narke masa take sake yi tare da shagwaɓe masa, domin duk da hafeez qanin mijinta ne amma ya

girmeta sosai

Hancinsu ya haɗa guri guda yana gogawa yana wani lumshe idanu, ya fara cewa
“my swampy, ko a mafarki cikin mafarkai kar ki gujeni, ina roqon alfarmarki da kasancewar tare da ni cikin wannan sabuwar duniyar da kika kai ni a yau da ban taɓa shigarta ba, ki min alqawarin hakan my reedah, idan ba haka ba zan zauce, zan zauce reedah….”
Ya qarashe maganarsa cikin sake tausasa muryarsa mai kama da yana yin raɗa sannan ya fara kissing ɗin lips ɗinta yana binta da sheɗanin kallo
Irin waɗannan abubuwan fareedah take buqata daga fa’eez tun farko, tana matuqar son a nuna mata tana da muhimmanci amma ta rasa hakan daga gurinsa, sai ga shi cikin sauqi ta samesu a gurin hafeez, dan haka cikin jin daɗi ta sake narkewa a jikinsa ta qanqameshi ta sanya hanunta a kanshi tana shafawa a hankali idanunta a lumshe ta ce
“Hafeez ni ma zan so ɗorewar alaqarmu, ba zan so nisantarka ba”
“da gaske Swampy”? Yace yana mai ɗago fuskarta kamar zai haɗa da tashi, idanunta ta zuba masa tana murmushi sannan ta lumshesu ta gyaɗa kai
Kamar zai mayar da ita ciki haka ya ruqunqumeta yana mai tsantsan farinciki tamkar zai lasheta sai maimaita mata kalmar I love you my reedah yake yi, ita kuwa tun tana murmushi ganin haukar murna da sambatun sun yi yawa sai ta fara masa dariya qasa qasa
Shi ko bai yi qasa a gwiwa ba ya ɗagata daga jikinsa ya miqe tsaye ya kinkimeta suka koma bakin gadon da suka baro ya zaunar da ita sannan ya je ya ɗauko ɗaya cikin ledojin da ya shigo da su ya dawo bakin gadon ya zauna, tana kallonshi ya ciro wani akwai mai ɗan girma daga ciki ya buɗe, saidai abin mamaki duk girman akwatin nan, qaramin zobene a cikinsa mai ɗan banzan kyau da qyalli
Zoben ya ciro daga cikin akwatin ya kama hanunta ya sanya mata zoben, ita kuwa sai binshi take yi da kallo
Kan zoben ya sumbata sannan ya kalleta yana mata murmushi yace “wannan zoben na alqawarine tsakaninmu, ki min alqawarin zaki aureni, bayan kin karɓi takardar sakinki daga hanun wancan mutumin, sannan ba za ki sake kusantarshi ba, sai ni kawai”
Dammm ta ji zuciyarta ta buga, wani irin alqawarine wannan?, cikin zare idanu tace
“Hafeeez….”
Saurin dakatar da ita yayi da cewa
“ki cire wancan banzan tunanin a ranki, ki ɗauka kawai nine mijinki a yanzu, duk wasu hakkokinki sun dawo kaina, na rantse miki da Allah da qani zai iya sakin matar yayansa da a yanzu ba sai anjima ba zan sake masa ke, daga nan sai ki zama mallakina, reedah ki sani wallahi tallahi, da zan iya gane namijin quda to wlh idan ya sauka a jikinki kwanansa ya qare, balle wani qaton banza, numfashina barin gangan jikina zai yi, haɗiyar zuciya zan yi in mutu, pls Reedah, kar yarda da shi, ni kaɗai zan iya gamsar da buqatarki”
Cikin qanqanin lokaci har idanunsa sun yi jajir tare da rawar murya
Cike da damuwa ta fara magana “Hafeez ni a karan kaina ba zan taɓa neman hakkina a gurin faeez ba, amma yaya zan yi idan shi ya nemi hakan”?
Cikin zafin rai da ɗaga murya tare da tsabar baqin kishi yace
“ko shi ne ya nemeki kar ki kuskura ki yarda, wallahi idan na san ya kusanceki sai na illatashi”
A tsorace fareedah take binsa da kallo ganin yadda ya haukace mata, ganin yadda ya tsoratata ya sanyashi rungumota qamqam a jikinsa ya fashe mata da kuka, yayin da zuciyarshi take wani irin bugawa tamkar wacce take neman hanyar fasowa daga qirjinsa ta fito
Qanqameshi tayi ita ma cikin tausayawa tare da jin wani baqon  yanayi ya daki zuciyarta, saboda fahimtar da tayi cewa ba qaramin so hafeez yake mata ba, ba ta taɓa tsammanin hakan daga gareshi ba, cikin tausasa murya da rarrashi tace
“Hafeez dan Allah kar ka cutar da kanka, na maka alqawari zan kiyaye duk wani abu da zai sanyashi kusantata, hakan ba za ta faru ba ma inshaa Allah, ka ji, dan Allah”
Bai iya magana ba, sai shiru da sauke ajiyar zuciya yayin da ita kuma take ta rarrashinsa ta hanyar masa waɗansu abubuwan na musamman, a haka ta samu ya sauko ya ɗago daga jikinta ya zuba mata idanu yace cikin marairaice murya “ina sonki my swampy”
Murmushi ta masa ta kashe masa idanu tace “me too my Hafeez”
“ina godiya” yace tare da lumshe idanu, bin sa take da kallo sai can ta ja yatsun hanunsa tace “my hafeez in tambayeka”?
Buɗe idanun yayi ya zubasu a kanta yace “girmankine, mene ne tambayarki my swampy”?
Sai da ta luguiguita maganar sannan cikin jin kunya tana aika masa da wani irin kallo tace
“ka taɓa kusantar wata mace”?
Yalwataccen murmushine ya faɗaɗa a kan fuskarsa sannan yace
“kafin swampy ban taɓa kusantar wata qazama ba, kuma a bayanta na haramta kaina wa mata”
Yadda take kallonsa sai ya ga kamar ba ta yarda ba, dan haka ya dafa kafaɗarta yace
“na rantse da Allah, ban taɓa kusantar wata mace ba kafin yau, wallahi, tallahi, ke kin san halina, ba zan iya faɗin qarya ba”
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ba ta san me yasa ba, amma maganar ta mata daɗi matuqa
***
Tun daga ranar Hafeez da Fareedah suka buɗe sabon babin rayuwa tamkar mata da miji, har sun fi wasu ma’auratan ma, tare suke kwana suna aikata mashaarsu, ko su kwana a ɗakinta ko kuma a ɗakinsa, duk yadda dai suka so, haka suke aikatawa, cikin qanqanin lokaci kowannensu ya canza, Hafeez sai  wani haske yake yi da qiba yayin da Fareedah take qara cikowa tare da sheqi da walwali, kowa ya ganta sai ya furta, sannan walwalarta ta wuce na baya tare da kazar kazar ɗinta
Haka Faeez a can qasar ya cigaba da holewarsa da Tina, duk da ya kammala abin da ya kaishi can tun a wata ukun amma ya qi dawowa, sai online meeting da yake kiran ma’aikatansa daga can ya isar musu da duk abinda yake da buqatar sanar musu, daga qarshe ma ɗaukar Tina yayi suka fara bin qasashe hutawa da jin daɗi, yayin da ya daina waya da su fareedah sai an yi sati ya kira sama sama yace aikine ya masa yawa, su ko dama babu mai nemanshi cikinsu, rayuwarsu suma suke yi ba tare da suna tunashi ba, ko hirarsa ba sa yi, idan ma ya kirasu kowanne cikin nuna rashin kulawa yake amsa masa wayar, wani lokacin kafin ya ajiye wayar sun ajiye, musamman Hafeez, dan ko fareedah ya kira matuqar suna tare idan ya fahinci maganar za ta yi nisa sai kawai ya karɓe wayar ya kashe ya haɗe fuskarsa, ita kuwa farinciki hakan yake sakata sai tayi ta rarrashinsa da daɗaɗan kalamai masu tafiyar masa da zafin kishin daga qirjinsa
**
Kwance suke da safe a kan gado, yau watansu guda da kwana ashirin da shiga duniyar jin daɗinsu, duk da yau Hafeez yana da makaranta amma ya kasa tafiya saboda damuwa na Zazzaɓin da fareedah ta tashi da shi mai zafi, duk da an fi sati zazzaɓin na damunta amma bai yi zafi irin na yau ba, hankalin Hafeez a matuqar tashe yake gaskiya, ji yake kamar ya zubar da hawayen tausayin Swampyn tashi
Cike da damuwa da rarrashi ya fara magana
“my love dan Allah ki yarda in kaiki asibiti, ba zan iya samun nutsuwa ba sai na tabbatar da cewa zazzaɓin nan ya bar jikinki, ke kanki kin  sani”
Jikinta na rawa ta yi magana a shagwaɓe
“ni dai ka barni kawai a gida ka je ka sayo min magani”
“a a Reedah, dole in kaiki hospital, ba zan yarda da self medication ba, mu je in miki wanka ki ji qarfin jikinki sai ina samar miki abin da za ki ci kafin mu tafi”
Bai jira amsarta ba ya tashi ya ɗagota tana masa kukan shagwaɓa haka ya qyaleta ya je ya mata wanka shima yayi sannan  ya je ya haɗa mata abinci mai sauqi ya zo ya ba ta ta ci sannan ya shiryasu suka fito yana riqe da ita, sai da ta ga sun zo falo ta qwace kanta daga gareshi tana turo baki, dariya kawai ya mata ya wuce ɓangaren mai aikin da ba ta cika shigo musu ɓangarensu ba saidai in su suka nemeta, abinci ma ita take yin nata a can
Umurnin gyara gidan ya bata yana hararanta dan a ganinshi tana barin fareedarsa da aiki da yawa, cikin tsoronsa ta amsa tare da miqewa tsaye, shi ko yayi tafiyarsa abinsa ya dawo gurin fareeda ya sakar mata murmushi sannan suka fice
*
Zaune suke a gaban likitan da ya sa aka wa fareedah gwaji daban daban dan gano ainahin matsalarta, sun nutsu sosai suna sauraronsa yayin da yake karanta result ɗin, ɗago kansa yayi yana murmushi ya fara magana cikin baiwa irin tasu ta likitoci
“sakamakon farko ya nuna akwai typoid amma ba mai yawa ba, sakamako na biyu kuma sai ka ban goron albishir” ya qarashe yana sake yalwata murmushinsa
Dam dam qirjin fareedah ya buga amma hafeez yalwataccen murmushi yayi yace “Dr name your price, ko nawane zan baka a matsayin goron albishir, faɗa min kawai, mene ne”?
Murmushi likitan ya sake yi ya ce “yanzu haka, matarka tana ɗauke da cikin wata ɗaya da sati biyu, gaskiya congratulation, zaku haifo zallar kyau matuqar zai gaje siffofinku”
😳khutmelesee fans idan kune a matsayin Hafeez da Fareedah yaya za ku yi?
ISLAM IS MY IDENTITY

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

QANIN MIJI 1

Advertisement QANIN MIJI Daga alqalamin marubuciyar zamani✍🏼 MARYAM A.I GITAL @ Meerahgee pure moment of life writers👌🏻  SADAUKARWA GA…

QANIN MIJI 12

Advertisement 12 Cikin zaro idanu tare da dafe qirji  Fareedah tace “what”? Shi ko gogan naku yalwataccen murmushi…

QANIN MIJI 6

Advertisement QANIN MIJI🤵🏻  6  Da mugun qarfi ya rintse idanunsa yayin da zuciyarsa take luguden duka saboda tsabar…