QANIN MIJI 12

Advertisement

12
Cikin zaro idanu tare da dafe qirji  Fareedah tace
“what”?

Shi ko gogan naku yalwataccen murmushi yayi wa likitan tare da furta alhamdulillah sannan ya miqa wa likitan hanu suka yi musabiha haqoransa waje yace
“lallai wannan babban albishirne, zan kuwa baka tukuicin da kaima za kayi farinciki kamar yadda nayi, ka turo min account number ɗinka, ko yanzu a nan gurin zan tura maka da kyautar farinciki”
Dariya likitan yayi cikin jin daɗi da kwaɗayin abun da za a bashi yace
“Allah ya qara arziqi yallaɓai, na gode, na gode”
“kar ka damu, ka cancanci hakan daga gareni”
Fareedah da ta ga babu wanda ya damu da damuwarta cikinsu, hafeez sai murna yake yi abinsa kamar wanda aka masa kyakkyawan albishir, sai kawai ta fashe da kuka mai matuqar taɓa zuciya
Daga likitan har hafeez kallonsu suka mayar kanta yayin da likitan yace cikin sakin fuska da barkwanci
“hajiya kukan mene ne kuma, ko na tsoron haihuwarne”??
Janyota Hafeez yayi jikinsa ya rungumeta yana ɗan bubbuga bayanta sannan ya mayar da kallonsa ga likitan yace yana murmushi
“ka san su mata da raki, musamman wannan tawan shagwaɓaɓɓiya, abin kuka tayi kuka, abinda bai kai kuka ba tayi kuka”
Dariya likitan yayi yace “oh!, ashe hakane?, toh sai ka rarrashi kayanka, ka faɗa mata haihuwa ba zafi ko kaɗan, tana bacci ma za ta iya haihuwar”
Tare suka qyalqyale da dari da Hafeez suka sake yin musabiha, Hafeez yace
“toh mun gode likita, sai na jika”
“toh angon madam, godiya nake”
Miqewa yayi tare da ɗago Fareedah da take rusar kuka ya sake rungumeta a jikinsa ya ajiye wa likitan card ɗinsa a kan table ya ja fareedah suka fice
A rungume a gefensa tana kukan ya kaita mota, mutane sai kallonsu suke yi suna faɗin
“ayyah sannu, jikin ne ke damunta”?
Godiya kawai Hafeez yake musu, daga nan ba ya sake cewa komai
Tana rungume a jikinsa a cikin motar yana shafa mata baya tare da hura mata kunne cikin salo na rarrashi har sai da ya ji ta fara rage kukan sannan yayi magana cikin tausasa murya
“my swampy wai mene ne na kukan?, kina son ɗaga min hankali ko?, haba my reedah, yaya kike so ki rabani da nutsuwata”?
ɗagowa tayi daga qirjinsa tana tsiyayar hawaye tana kallonsa tace
“Hafeez ciki fa?, cikin wata ɗaya da kwanaki yayin da Faeez yake da wata kusan biyar ba ya gida, wayyo Allahna na shiga uku ni Fareedah”
Take fuskarsa ta rikiɗe da ɓacin rai, cikin haɗe fuska yace
“akan cikin ne kike kira wa kanki shiga uku?, ko dan ba cikin wancan jakin bane azzalumi”
Cikin matuqar mamaki bakinta na rawa tace “Hafeez…ka…ka fahim….”
Dakatar da ita yayi da cewa
“No Fareedah, na fi kowa fahimtarki da gano matsalarki ko ba ki faɗa ba, ni a gurina kukanki da shiga damuwarki sune masifa da tashin hankali, ba wai wannan cikin ba, wai shin ba ki san ubanshi bane”?
Hawayene ya sake zubo mata ta sake cewa
“Hafeez na san cikinkane, amma yaya zan yi in fuskanci Faeez da shi balle idan al’umma suka sani”
Hawayen ya sanya hanu yana share mata ya ce
“tamkar ruwan dalma ake ɗiga min a zuciyata a dalilin zubar waɗannan hawayen, Fareedah ko na minti ɗaya kar ki sake ɗaga hankalinki, dole abu biyune za su faru akan wannan cikin, na farko, idan daqiqancinsa da rashin kularsa ba su barshi ya gano cikin ba a dawowarshi shikenan, hankali kwance zaki cigaba da rainar min kayana, idan kuma ya san da cikin toh shi ma zan yi farinciki domin zai sakeki in aureki kuma shi zai qunshi baqin cikinsa shi kaɗai dan ba zai iya faɗa ma wani ba, kin ga nan ma hankali kwance zamu cigaba da more rayuwarmu qarqashin inuwar aure, sai me kuma daga nan”?
Ya qarashe yana mata murmushin nuna zallar qauna
Turo baki tayi tana hararansa still wasu hawayen suna sake zubowa tace “kai jin daɗin rayuwane damuwarka ko?, ni dai wallahi ina cikin tashin hankali, bana son  cikin nan mu zubar kawai”
Cikin haɗe fuska yace
“mu zubar?, cikin nawa?, wallahi ba za a zubar da shi ba, yadda shi ma ɗansa ya tako qasa ni ma sai nawa ya taka”
Ita ma cikin fusata da faɗa tace
“wallahi sai na zubar da cikin nan, dan ba zan iya ganin tashin hankalin da zan shiga ba idan mijina ya san da cikin nan, ba zan iya ba”!!!
Da qarfi ya rungumo kafaɗarta cikin kishi da masifa yace “kar ki sake cewa wani banza mijinki, kar ki sake nace”!!
Tureshi tayi ta ce “na faɗa mijina, mijinane, cikine dai sai na zubar da shi, ba zan haifeshi ba”!!
Yadda ya ga take masa masifa da kalaman da suke dukan zuciyarshi sosai, sai kawai ya rintse idanu ya jingina bayanshi da seat, ya ɗau tsawon minti biyu a haka zuciyarsa tana tafasa saboda kishin ɗan uwansa, hawayene suka fara bin kumatunsa yayin da ya fara cewa
“ka cuceni Faeez, ka cuci rayuwata, me yasa ka fara aurenta?, me yasa ka auri matata?, me yasa?
Yana kaiwa nan ya kifa kanshi a kan steery ya fashe da kuka tamkar qaramin yaro, dan maganar gaskiya Hafeez ya kamu da zazzafar qaunar Fareedah da kishinta da suke tafasa masa zuciya
Jikin fareedah ne yayi sanyi, dan ita ma har cikin zuciyarta yanzu take jin son Hafeez na mamayeta ba wai kawai ta ɗaukeshi a matsayin mai kore mata sha’awarta bane, bayan hakan akwai qauna da take masa
Rasa abin ƴyi tayi, kawai sai ta fashe da kuka ta kifa kanta ita ma
Kukan ta da ya ji ne ya sakashi dakatar da nashi ya ɗago da kansa ya rungumota jikinsa ya haɗe musu baki da nufin hana ta kukan
Tsawon lokaci suna a haka sannan ya sake mata bakin ya qanqameta a jikinsa ya fara raɗa mata magana a kunne
“kiyi hakuri my swampy, ina sonki, ina qaunarki, bana buqatar kukanki, zuciyata za tayi bindiga, zafi nake ji a qirjina swampy”
Ba ta ce komai ba sai ajiyar zuciyar da take yi a hankali
“mu je gida kiyi bacci ki huta, bana son zazzaɓin nan ya cigaba, kin ji”
Yana gama faɗin haka ya ɗagota daga qirjinsa ya fara share mata hawaye, sai da ya  gyara mata fuska tas sannan ya gyara mata zama zuwa kwanciya  tare da kanta a cinyarsa sannan ya tayar da motar suka bar asibitin
A hanya ya shiga wani guri na sayar da kayan qwalama ya faka motar sannan ya juyo ya kalleta yana murmushi, ganin ta fara lumshe idanu sai ya shafi fuskarta yace “my reedah me kike so in shiga in sayo miki”?
Cikin muryar jin bacci tare da shagwaɓe murya tace “ina muke”?
Yana murmushi ya sunkuyo ya ja hancinta yace
“qwalam da maqulashe store, na san zaki buqaci wani abu ko”?
Murmushi tayi wanda bai kai zuci ba tace “cake kawai”
“toh madam, an gama, ko za a min uzirin tafiya”?
Sake murmusawa tayi ta yunqura za ta tashi ya taimaka mata ta zauna sannan ya fice bayan ya raɗa mata I love you
Bin bayansa tayi da kallo tana jin tausayinsa a cikin ranta sosai, dan ɗawainiyar da ta fahimci yana yi da qaunarta
Mintunan da ya ɗauka ba yawa ya fito riqe da leda a hannunsa, murmushi tayi da ta hangoshi domin haka kawai ta ji daɗin ganin fitowarshi, shi ko sai sauri yake yi yana dumfaro gurin motar
Wata budurwace ta tareshi a daf da motarshi tace “Hafeez”!
Kallonta yayi sannan ya ɗaure fuskarshi ya buɗe mota zai shiga
“Haba Hafeez, wai me na maka a rayuwane?, masoyi ba zai taɓa zama maqiyi ba, ba fa ni na ɗora wa zuciyata qaunarka ba, ya kamata ka tausaya min” cewar budurwar tare da riqe qofar motar, ita tsabar makancewa a So ba ta ga Fareedah ba
Fisge murfin motar yayi yana cewa
“keh wai wacce irin mahaukaciyace Nazeefah, na faɗa miki bana sonki, bana sonki, wai dolene?, kar ki kuskura ki ga fushina, dan in kika cigaba da bibiyata zan miki rashin mutunci, zuciyata da wacce ta mallake, ki bi wani sarkin”
Yana gama faɗin haka ya shige motar ya rufeta da qarfi sannan ya fisgeta da gudu ya buɗe Nazeefah da qura
Fareedah da take cikin motar tana jiyosu, wani irin kishine ya taso mata mai zafi a qirji, tuni fuskarta ta haɗe, kamar ba ta taɓa dariya ba
“mene ne swampy”? Yace yana kallonta ganin yadda take fushi
Harara ta banka masa ta ɗaukè kai tana cika tana batsewa
Hanu ya kai zai taɓata ta buge masa hanu ta sake banka masa harara
Murmushi yayi ya shafa sajensa yana binta da wani irin kallo sannan ya cigaba da tuqinsa yana murmushi jifa jifa
**
Kwance suke da misalin qarfe 8:00 na dare, har yanzu fareedah fushi take yi da Hafeez, tun dawowarsu yake ta bin ta amma ta qi kulashi, kishine kawai yake nuqurqusar zuciyarta, shi kuwa sai nace mata yake yi yana lallaɓata, dan ko maganin da ya sake komawa asibiti tambayar likitan kasancewar sun manta, da qyar ya lallaɓata ta sha
“haba my TILO, dan Allah ki rufa min asiri ki bar fushin nan, wallahi tallahi bani da budurwa a waje, ke kaɗai nake so Fareedah, ni naki ne ke ɗaya tal”
A shagwaɓe tace “toh ya aka yi ka san sunanta”?
“makarantarmu ɗaya fa Swampy, irin ‘yan matan nan ne marasa kamun kai, ai ni ba zan taɓa kula macen da ta ce tana sona ba, me zan yi da ita, Allah ya sauwaqe, ita ce wahalalliya da take qin sauraran samarukanta a kaina”
“Allah”? Ta sake cewa a shagwaɓe
Qanqameta yayi a jikinsa yace “Allah my Swampy, ke kaɗaice tilo”
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta lafe sosai a jikinsa tana lumshe idanu ta sake cewa
“Hafeez ni fa har yanzu hankalina a tashe yake akan cikin nan”
Tsawon lokaci ya ɗauka shiru sannan ya fara magana a hankali
“ki kwantar da hankalinki, zan jefa rayuwata cikin matsala domin in samo miki kwanciyar hankali”
“kamar yaya Hafeez”?
Cike da damuwa yace “ki yi duk yadda za ki yi Faeez ya kusanceki idan ya dawo, a kuma  ranar da ya dawo, zan san duk yadda zan yi ya dawo qasar nan a cikin sati me zuwa, sauran tsarin kuma ni zan shirya da kaina, amma kar ya wuce sau ɗaya, dan idan ya kusanceki fiye da ɗaya zan iya rasa hankalina, ko yana nan, babu ke babu shi, zan tsara yadda zamu dinga kasancewa tare,  pls my swampy”
Kafin ta ba shi amsa wayarta ta fara ringing, shi ya ɗauko wayar, saidai ganin faeez ne sai kawai ya ajiye ya haɗe fuska, musamman da ya ga sunan da tayi saving nambarshi da ita, ita ma da ta ga haka sai ta yi lif a jikinsa tayi shiru, haka faeez yayi ta kira, sai da ya ga dama sannan ya ja tsaki ya ɗaga kiran a zuciye
Bai amsa sallamar faeez ba yace “ta bar wayar a falone, tana ɗakinta”
Bai damu da yadda ya ji muryar hafeez ba yace “ok, Hafeez ne?, yah school”?
“lau”
“mashaa Allah, toh ka sanar mata cikin satin nan zan dawo inshaa Allah, idan na wuce ma toh next week zan dawo, bari in barka, na ga kamar kana jin bacci, sai anjima”
Ba tare da hafeez ya jira faeez ya kashe wayar ba, ya rigashi kashewa ya ja doguwar tsaki ya jefar da wayar a jikin bango cikin zafin rai ta tarwatse
ISLAM IS MY IDENTITY

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

QANIN MIJI 6

Advertisement QANIN MIJI🤵🏻  6  Da mugun qarfi ya rintse idanunsa yayin da zuciyarsa take luguden duka saboda tsabar…

QANIN MIJI 14

Advertisement  Ina matuqar ba da hakuri wa masoyana masu bin littafin JININANE hakuri saboda tsaikon da aka samu…

QANIN MIJI 1

Advertisement QANIN MIJI Daga alqalamin marubuciyar zamani✍🏼 MARYAM A.I GITAL @ Meerahgee pure moment of life writers👌🏻  SADAUKARWA GA…