QANIN MIJI 13

Advertisement

13
Qarar buguwar wayar ta razana fareedah, da sauri ta bar jikinsa tana waro idanu tare da bin gurin da ta jiyo qarar da kallo
Wayarta da ta gani ta damage yasa ta juyo da sauri ta kalli Hafeez, shi ko huci ma yake yi kamar wanda yayi tsere da zaki

“Hafeez lafiya”?
Tace tana riqo hanunsa, qin magana yayi sai da duk ya ga ta shiga damuwa tace
“wani mummunan abu ya samu Faeez ne”?
Sai a lokacin yayi magana a zafafe cikin faɗa da buɗe idanu
“idan wani abu ya sameshi ina da asarane, ni murna ma zan yi idan hakan ta faru”!!
Zaro idanu tayi waje tare da dafe baki da tafin hanunta tace
“ɗan uwankan”?
Zabura yayi ya riqota da qarfi yana zaro mata jajayen idanunsa yace
“a kanki ban san kowa a matsayin ɗan uwana ba, ina da kishi nace miki!!!, na tsaneshi”!!
A tsorace murya na rawa tace
“innalillahi wa inna ilaihirrajiun, haba Hafeez, dan Allah ka daina irin waɗannan maganganun, ba ka isa ka yanke alaqar da ta ke tsakaninka da Faeez ba, dole ka kirashi ɗan uwanka”
“saboda shi kike so ba, na ce saboda kina sonshi ko”?!!!
Ya qarasa a faɗace yana mata ihu
Rintse idanunta tayi saboda ihun yana shiga mata har qwaqwalwa, hanunta ta ɗora a goshinta ta dafe tace “wasshhh… “
Kallonta ya fara yi yana mai nazarin yanayin da ta shiga, yadda ya ga tana yatsina fuskane tana ɗan jujjuya kan, sai ya ji tsoro kar wani abin ne ya sameta
Cikin nuna damuwa yace bayan ya sassauta murya
“me ya sameki Reedah, mene ne??”
Ba ta amsa ba sai ma cigaba da tayi da jujjuya kai, janyota yayi jikinsa cikin rawar jiki yace
“yi hakuri dan Allah, na bar maganar, wallahi rainane yake tafasa, Faeez yana nan dawowa cikin satin nan, ko satin sama”
A tsorace ta bar jikinsa, kamar ba ita ce mai ciwon kai yanzu ba, tsabar tsorata ko magana ta kasa yi sai kallonsa da take yi kamar ta ga abin tsoro
Janyota yayi ya sake mai da ita jikinsa cikin lallashi ya fara magana domin da gaske har cikin zuciyarsa ba ya son tashin hankalinta
“mene ne abin tashin hankali Swampy?, ba mun gama magana a kan wannan ba, babu abin da zai faru, ki kwantar da hankalinki dan Allah, just for me my Reedah”
Cikin muryar kuka tace “Hafeez ina jin tsoro”
“No, kar ki damu, ina tare da ke, akwai shirin da zan yi akan hakan, dan Allah kar ki bari hawayen nan su zubo”
Ai duk daɗin bakin da yake ta mata Fareedah ta qi kwantar da hankalinta, haka suka kusan kwana a zaune tana masa rigima, duk yadda ya so ya ɗauke mata hankali da wasannin da zai sa su gangara duniyar masha’arsu Fareedah ta qi yarda, duk nacinsa haka ya haqura, shi da ya samu tayi bacci daf asuba ma daɗi ya ji
**
Wani iskanci a gurin Faeez shi ne, tun kiran da hafeez ya ɗaga bai sake kiransu ba, ya maida hankalinsane gurin tunanin kewar Tina da zai yi, tsabar fushin Allah da ya gayyato har aka cire masa tunanin zinar haramunce ta hanyar ɗiga masa RAN a zuciyarsa, kwata kwata baya tunanin abinda yake aikatawa bai dace ba, shi hakan ma daɗinsa yake ji saboda an qawata masa hakan a cikin zuciyarsa
Wanka suke yi da Tina a swimming pool suna ta wasannin banzansu tamkar ba Hafeez ba, ya saje sak da turawa gurin sheɗana, toh idan ba haka ba, yaushe cikin tsakiyar guri zai zauna daga shi sai boxer kamar yana gidanshi ko ɗakinsa
Fitowa suka yi bakin gaɓar swimming pool ɗin Faeez daga shi sai boxer yayin da Tina ke sanye da pant da wata shegiyar bra da ni dai ban ga amfanin sanyata ba, zama yayi akan wata kujerar qarfe yayin da Tina ta zo ta ɗale masa cinya ta manna masa kiss tare da ɗan ciza lips ɗinsa cikin salon ‘yan bariki, wasshh yace sannan suka yi dariya a tare, ya fara mata cakulkul, zillo ta fara yi har ta sauka qasa ya bi ta ya kwanta a jikinta ya mata rumfa ya haɗa bakinsu ya fara kissing ɗinta kamar wani kare, ni ko nace jaki kawai, Allah ya shirya
Da yake ita ma ba baya ba dan haka nan ma sai da suka yi ta wasanninsu kamar yadda sauran turawan da suke bakin ruwan suke tayi da ‘yammatansu, wasu ma zina qiri qiri suke yi ko tunani babu balle kunya da kiyaye mutuntaka, ta gama dulmiyar da Faeez kawai, sai fatan Allah ya kyauta
“Tina ki bini qasata mana” cewar Faeez cikin harshen turanci bayan sun kammala dabbancinsu
“mene ne ba ka samu ba daga gareni a cikin watannin da muka yi da kai, wanda har sai na bika nigeria”?
“ji nake yi kamar jiya muka haɗu, ba zan iya rabuwa da ke ba, ko na tafi, nutsuwata da hankalina suna baya, pls ki bini mu cigaba da rayuwarmu a can, na miki alqawari zan zaunar da ke a gurin da zaki ji daɗin rayuwarki tamkar kina nan, ba za ki samu wata matsala ba”
Shiru tayi tana kallonsa, ta qi yin magana, cikin roqo da neman alfarma yace
“pls Tina, ki ce kin yarda”
Idanunta ta lumshe ta gyaɗa masa kai
Tsabar murna bai iya ba ta amsa ba sai ɗagata da yayi cak yayi cikin hotel ɗin da suka kama ɗaki
Cikin hauka da ɗabiun karnuka da ya saba da su yanzu suka lula duniyar zina da ita, ba tare da ya sanya komai na kariya ba, domin tun sau ɗaya a zinarsu ta biyu da yayi yunqurin sakawa Tina ta yaudareshi tace ba ta so tare da janye hankalinsa, shikenan ya daina sakawa, kuma bai taɓa tunanin hakan bai dace ba a ranshi, burinshi kawai ya ji daɗi ne kawai, domin a tunaninshi ba wani abu da zai iya biyo baya
**
Rana bata qarya..
Cikin shirin tafiya airport ɗauko Faeez suke, fuskar Hafeez a ɗaure kamar wanda aka masa mutuwa, duk ya bi ya tashi hankalinsa akan kishi, sai hararar Fareedar ma yake yi domin shi a ganinsa rawar jiki take yi mijinta zai dawo, ita kuwa sai lallaɓashi take yi dan ba ta so ya ɓallo musu wani liqin a gaban Faeez
Kamar yadda Tina da Faeez suka kwana tsiyarsu, haka Hafeez da Fareedah suka kwana holewarsu, kasancewar cikin kwanakin zazzaɓinta ya tafi, babu kuma wani laulayi sai cin tsiya da ta buɗe babinsa, Hafeez kuwa murna yake yi da hakan dan har abu yake tanadar mata a kan bedside drawer idan ta farka cikin dare ta ci, yayin da shi ma zai tashi sai ya tabbatar babu abin da take buqata sannan su koma su kwanta
Hannayensa ta riqo tace “haba my love, dan Allah ka ɗauke wannan damuwar daga fuskarka, ka san ina sonka ko”?
Waro idanunsa yayi a kanta domin ba ta taɓa faɗa masa hakan ba
Murmushi ta masa ta kama hannunsa ta zaunar da shi ta ɗale jikinsa ta saqalo hannayenta a kafaɗarsa ta bashi kiss ta ɗago tana masa kallon love tace
“da gaske ina sonka Hafeez, kuma a shirye nake tsab da in rabu da Faeez in aureka, kaine irin  mijin da nake ta burin aura ba Faeez ba”
Farincikine ya lulluɓeshi, nan ya fara mata sambatun kalaman soyayya da qauna tare da fara mata wasanni, har ya manta da ɗauko Faeez, ita ma kuwa ta biye masa
Wayar Hafeez ce ta dakatar da su, ya ɗauko wayar yana tsaki ya picking ba tare da ya lura da mai kiran ba
Muryar maxwell ya ji, hakan ya sakashi ɗaure fuska kamar yana ganinsa yace “mene ne maxwell”?
Cikin ladabi yace “Oga yace in faɗa maka, ya kira nambarka ya qi tafiya, wai bai biyo jirgin ba, sai gobe”
“ok” yace tare da katse wayar ya ja doguwar tsaki ya ajiye wayar ya juyo ya cigaba da abin da yake yi yana cewa “shashashan ba zai dawo ba sai gobe” ba ta amsa ba dan ta san da wa yake yi, ga shi wasanninsu yayi nisa ba ta son su katseshi, dan tana matuqar nishaɗantuwa da wasannin, ita koda yaushe suka shiga duniyar nan da Hafeez ba ta so a daina, ta rasa me yake faruwa da ita, musamman a kwanakin nan
Ni ko na ce bashin da mijinki ya ci, kike biya abinki😂
*
A ɓangaren Faeez, ya daɗe da shigowa qasar tare da Tinarsa, hotel kawai yayi wucewarsa da ita ya kama mata ɗaki mai tsadar gaske tare da niyyar gyara mata ɗaya cikin gidajensa ya mayar da ita can dan su fi jin daɗin holewarsu, ko tunanin mutuwa Faeez baya yi, ya gama hallakar da kanshi saboda son zuciya
*
Suna zaune a dining suna cin abinci suka jiyo horn ɗin mota tare da qarar shigowarta cikin gidan, Fareedah da take zaune jikin Hafeez yana ba ta abinci a baki ce ta fara magana
“Hafeez kamar qarar shigowar mota”?
“eh nima haka na ji, tashi ki je ki saka hijab dan ban san ko waye bane, kar ya kalle min ke a haka” ya qarashe da kashe mata idanu, ita ma idanun ta kashe masa ta tashi daga jikinsa ta haura ɗakinta yayin da Hafeez ya bi bayanta da kallo
Hijab ɗin ta sako ta fito, tana tako matakalar da za ta sauqo da ita gurin dinning ɗin sallamar Faeez ta doki kunnuwansu, duk tsanar Faeez da Hafeez yake ji, da rashin tsoronsa cikin zuciyarsa sai da gabansa ya faɗi, balle Fareedah uwar tsoro, a toh marar gaskiyane ko a ruwa sai yayi gumi
A dabarbarce suka amsa sallamar suna bin fuskarsa da take haɗe da kallo, dan tun a hanya ya shirya shi ma makircin da zai wa Fareedah, gudun kar ta buqaceshi a yau ɗin, dan ya matuqar gajiya a gurin Tina, ba ya ma da wata buqatar mace a yanzu, dan haka ma ya sayo magunguna da yawa a wani chemis wanda zai mata qarya da su
Kamar ba Hafeez ɗin Fareedah ba, wanda idan ya dawo za ta je da gudu ta rungumeshi, yau kam duk da tana tsorace sai ta ɗaure fuska ita ma, ta qarasa gurin dining ɗin ta ja kujera ta zauna tayi banza da shi
Hafeez ne ya kalli fuskokinsu duka yayi murmushi ya kalli Faeez da ya ja kujera kusa da Fareedah ya zauna yace
“amma ka shammacemu ya Faeez, kai da ka rage mana murna ka ce sai gobe”
Yamutsa Fuska yayi sannan ya murmusa yana kallon Fareedah yace “na so in baku mamakine kawai, amma yadda kboy ya ɗaga min hankali a waya dolena in dawo ai, ko shi yasa mutumiyarka yin fushi haka”?
Yaqe Hafeez yayi ya ce “ba ita kaɗai ba, nima a cike nake da kai yah Faeez”
Fara ɓalle botir ɗin jikin coat ɗin da yake jikinsa yayi yana kallon Fareedah yace
“toh ai sai a min uziri ko madam, kar ku haifoni, yanzu haka wallahi da zazzaɓi na sauko qasar, ga gajiya da bacci da suke jikina, mu je ki haɗa min ruwan wanka in watsa in sha magani in ɗan kwanta ko zasu sake ni, wallahi duk jikina ciwo yake min, wasshh” ya qarashe da rintse idanu, haɗa idanu Fareeda da Hafeez suka yi suka taɓe baki
Da sauri ya buɗe idanun ya miqe riqe da coat ɗin yace “ina jiranki, kai kuma Hafeez je ka shigo min da briefcase ɗina” babu wanda ya amsa masa, har ya fara tafiya ya juyo yace “amma fa ban ga alamar kun yi kewata ba, na ga kowanne qara girma yayi da haske, ko da yake ita wancan na san me ya kawo hakan”
Cikin alamun rashin gaskiya suka kalleshi cikin yanayi na tambaya, murmushi yayi kaɗan yace “eh, na sani mana, tun shigowata fa take ɗura abinci, ba ji ba gani”
Allah ne ya kare, tsakin da Hafeez ya ja ta qi fitowa, yana kallon fuskar Fareedah yace “lafiyace ta kawo haka, da kuma kwanciyar hankali”
Cigaba yayi da tafiya yana cewa “shiyasa ai nace ba ku yi kewata ba”
Yana shigewa ɗakinsa Hafeez ya ja wata shegiyar tsaki yace “banza, ko uwar me yake mana idan yana nan da za mu yi kewarsa oho, ko garin yaya ma ya miki kallon qurillah haka oho, wallahi ni dai kar ki sake da shi sosai, kina haɗa masa ruwan wankan ki fito daga toilet ɗin, kar ki yarda kuyi tare, ko plan ɗinmu ma cikin baqin duhu zaku gudanar, wallahi ban yarda ba, dan ni ba sakaraine irinshi ba, ina kishin abinda nake so, nan ma ki bashi  minti goma zuwa shabiyar, duk qarqari kar ya wuce ishirin, kuma dole ya kusanceki a yau, ba zazzaɓi ba ko mutuwa zai yi, na ji daɗin hakan ma da zata kasance a halin bashi da lafiya, zan baki abu ki sanya masa cikin jarababbiyar coffee ɗinsa, dole sai ya kusanceki a yau ɗin” qarfin hali irin na Hafeez har idanunsa sun rine saboda kishi
ISLAM IS MY IDENTITY

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

QANIN MIJI 8

Advertisement _Jinjinar ban girma ga gaba ɗaya writers ɗin pure moment of life, da writers ɗin  fasaha, ku…

QANIN MIJI 12

Advertisement 12 Cikin zaro idanu tare da dafe qirji  Fareedah tace “what”? Shi ko gogan naku yalwataccen murmushi…

QANIN MIJI 1

Advertisement QANIN MIJI Daga alqalamin marubuciyar zamani✍🏼 MARYAM A.I GITAL @ Meerahgee pure moment of life writers👌🏻  SADAUKARWA GA…

QANIN MIJI 7

Advertisement kafin in fara dolene in tsaya kuma mata ‘yan uwana in faɗa muku gaskiya, wallahi mata mu…