QANIN MIJI 14

Advertisement

 Ina matuqar ba da hakuri wa masoyana masu bin littafin JININANE hakuri saboda tsaikon da aka samu gurin yin typing ɗin book ɗin duk da sun biya kuɗinsu, na san za ku ga na fi yin typing qanin miji, don Allah ina so su min afuwa ku

fahimceni, littafin qanin miji yana da matuqar muhimmancin da ya kamata in sake shi a daidai wannan lokacin ne saboda manya manyan dalilai, ku ban goyon baya mu isar da saqon, Alah ya tara mu cikin ladan, duk da shi ma jininane yana da nashi muhimmin saqon amma wannan ya fi ci ma mutane tuwo a qwarya, luv yu ma real fans, Allah ya muku albarka

14
Kallon Hafeez kawai ta tsaya yi, ta ma kasa ba shi amsa, shi ko cikin jin haushi yace
“shashasha yana magana ko”?
Yanzu kam dariya ya ba ta, rufe bakinta tayi tana ‘yar dariya yayin da shi kuma yake ta banka mata harara, sannan ya tashi zai bar gurin, da sauri ta riqo hanunsa ta miqe tsaye ta dakatar da shi ta fara magana cikin raɗa
“kai kaɗaine fa, tilo, kana ɓata ranka akan faeez abin da kai kanka ka sani, duk daɗewar nan da yayi a wata qasar, zai yi wuya yayi sati ɗaya a gidan nan bai sake wata tafiyar ba, toh ka ga muna tare ai, ni idan kace kar ya kusanceni ma shikenan an wuce gurin, kawai sai in fara neman takardar sakina daga gurinsa mu zo muyi auren mu”
Ajiyar zuciya ya sauke ya ɗanyi murmushi yace “dole sai an yi hakan swampy, ki je ki haɗa masa ruwan wankan”
Ba ta ce komai ba sai murmushi kawai da tayi masa, ta juya ta fara tafiya, shi ma ya juya ya fice zuwa ɗauko brief case”
Tunda ta shiga ɗakin yake wani yatsina fuska yana wani ɗaɗɗauke kai, ba ta kulashi ba ta cire hijab ɗin jikinta ta ajiye a kan resting chair tayi wucewarta toilet ɗinsa
Tana haɗa masa ruwan wankan ta fito, kamar za ta fice ba tare da ta masa magana ba, sai kuma ta fasa ta taka kusa da gadon da yake kwance idanunsa a lumshe ta ɗan bubbuga gefen filon da ya ɗora kansa a kai, ya buɗe idanu a hankali ya watsasu a kanta
Harara ta banka masa tana me haɗe fuska tace
“na haɗa maka ruwan wankan”
Murmushi yayi ya riqo hanunta ya janyota ta afko jikinsa, nan ta fara qoqarin qwace, dan ita har cikin ranta haushinsa take ji, ba wai saboda huɗubobin Hafeez ba kawai, yadda ya cutar da ita har ya kai ta ga kusantar qaninsane yake matuqar qona mata zuciya, ita yanzu ma da ta ganshi sai ta nemi son da take masa ta rasa
Mutsutsun ta gama har ta hakura dan ba riqon wasa ya mata ba, murmushi yayi yace
“sarkin rigima har kin gama?”
Ko alamar za ta yi magana ba ta yi ba, hakan yasa shi cigaba da cewa
“shi ne har da hararata ko?, dan kawai ban dawo da wuri ba, ban kuma ce ki je ba, shikenan kawai?, toh ai yanzu gashi na dawo, ki yi fatan zazzaɓin da yake damuna ya yi sauqi, ko zuwa jibi sai in baki abin da kike buqata, na san shi ne ko?, toh ai shikenan, an wuce gurin, yanzu dai kafin in fito coffe dan Allah”
Haushine ya taso mata ta taqarqare ta fisge jikinta, domin rainin hankalin yayi yawa, ta ma fara ganin abin a matsayin wulaqanci
Harara ta banka masa tare da jan tsaki ta juya ta fice abinta da ɗan banzan sauri, idanunsa ya waro cike da mamaki, a ranshi yana raya cewa lallai yanzu fareedah ta sauya, yau ita ce da masa tsaki?, gaskiyar magana tsakin nan ya taɓa masa zuciya, cikin qanqanin lokaci ranshi ya ɓaci, qwafa yayi ya tashi ya shige toilet ɗin
Kitchen ta shiga da nufin haɗa masa coffee, amma abin mamaki sai ta ga Hafeez a ciki yana haɗawa
Cikin farinciki ta rungumoshi ta baya tace “I love you mijin?”
Dawo da ita yayi ta kan qirjinsa ya rungumeta ta gefe yace “me too my swampy, komai zan iya dominki saboda bana so ki wahala, soyayyarki a cikin jinina take”
Qanqameshi tayi sosai a jikinta ita ma tana qara jin sonshi na huda mata zuciya
“washh my swampy, kar ki tsokanoni, bar ni haka” yace yana mai dakatar da ita daga wasannin da ta fara masa
Siriruwar dariya tayi ta sake shi ta bar jikinsa tana masa kallon love, hancinta ya ja yace
“ai kin ma tsokanoni, sai na rage zafi” bai jira amsarta ba ya janyota jikinsa ya fara sumbatarta, ni ko nace ikon Allah, abu kamar maita
sosai yayi abin da ya so sannan ya sake ta yana kallon cikin idanunta ya ce “shimfiɗata za ta yi kewarki yau, ba  zan iya bacci ba”
Lumshe idanu kawai tayi ta kwanta a jikinsa, dan ita kanta ta san za ta yi kewar Hafeez, duk da Faeez zai kusanceta amma ta san ba zai nishaɗantar da ita tamkar Hafeez ɗinta ba
A hankali ya janyeta daga jikunsa ya juye coffee ɗin a wani cup da yake ajiye a gefe ɗauke da wata qwaya, cikin qanqanin lokaci qwayar ta narke ya ɗauko cup ɗin ya miqa mata yana cewa “pls my Reedah, kar ku ba wa babyna wahala, kin ji”
“wannan alqawarinane, ka kwantar da hankalinka”
“ok, je ki, zan yi kewarki”
Lips ɗinsa ta sumbata tayi saurin ficewa dan har ta ga qwalla sun taru masa a cikin idanu
Ko da ta koma ɗakin Faeez ta samu ya fito daga wanka yana goge jikinsa, yana ganinta ya haɗe fuska, ita ma fuskar ta haɗe ta je ta ajiye cup ɗin akan bedside drawer ta juya za ta fita, ya ɗaga murya cikin ɓacin rai yace “keh”!!
Juyowa tayi cikin haɗe fuska, yayin da shi ma ya fara takawa zuwa inda take
Sai da ya je daf da ita ya janye towel ɗin da ya ɗaura a jikinsa ya sanya hannu ya fisgota jikinsa cikin huci da zuga irinta sheɗan yace “ni kika yi wa tsaki, toh wlh sai na yi maganinki, ba dai na san abinda kike buqata ba?, toh nan da sati biyu ma ba za ki sameshi ba, ai jiki dai nawane ko, kuma qwalelenki, idan kin isa marar kunya ki kamani da qarfi ki kwanta da ni dole, gani a gabanki, wlh sai kin zo kin ban hakuri akan gwiwowinki, idan kin qi kuma, ke ce a wahale, shashasha”!!!
Maimakon ya ga ɓacin rai a tare da ita ko fushi, sai ma dariya da ta dinga tuntsire masa da shi, sai da ta yi mai isarta sannan ta tsagaita ta masa kallon banza ta ce
 “toh malam me jiki, idan ma mafarki kake yi toh ka farka, wannan ba Fareedar da ka sani da ba ce, da kai da jikin naka bana buqatarsu har abada, maganar in zo in durqusa a gabanka kuma, hmmmm, tsakanin ni da kai, zan ga mai durqusawa a gaban wani, nice dream malam Faeez” ta qarashe da kashe masa ido ɗaya ta juya ta fita tana dariya
Sandarewa yayi a gurin cike da tsananin mamaki, lallai lamarin fareedah ya girmama, da qyar ya ja qafarsa daga gurin ya je yayi zaman ‘yan bori a kan gado, ya daɗe kafin ya tashi ya shirya cikin kayan bacci yayin da Tina ta faɗo masa a rai, bai san lokacin da murmushi ya kubce masa ba, a hankali ya furta my darling
Hhh ko ba darling ba?, za ka ci babanka
Tas ya shanye coffee ya ajiye cup ɗin ya kwanta abinshi tare da kiran nambar Tina da ya haɗa mata duk a yau ɗin,  layukansa cikin na nigeria ya bata ɗaya kafin ya haɗa mata wani layin
Sun yi nisa cikin hirar batsarsu ta waya ya fara jin wani azababben yanayi, tun yana ɗaukan abun wasa har dai ya ji ya kai maqurar qarshe, duk yadda Tina tayi ta masa sheɗana a waya ya kasa samun nutsuwa, sai ma sake rura wutar sha’awarsa ake yi, ba shiri ya katse wayarsu da Tina, dan ya ɗauka maganganun da suka yine ya yi tasiri a jikinsa haka, saidai fa duk yadda ya so lamarin ya sauqaqa masa abu ya ci tura, ba shiri ya fice zuwa ɗakin Fareedah a gigice yana ji kamar yayi kuka, dole ko da rigima da bala’i ya durqusa ya roqi fareedah ta bashi kulawa, idan ba haka ba, bai san halin da zai shiga ba, dan  ji yake yi kamar zai mutu
Cikin kayan barcin da ba su fi tsirara da komai ba Fareedah ta kwanta saboda ta san plan ɗin su, suna hira da Hafeez ɗinta a waya ta ji shigowarsa tare da buɗe qofar a gigice, kashe wayar tayi gaba ɗaya ta haɗe fuska tana masa kallon banza
Da sauri ya je jikin gadon ya durqusa akan gwiwowinsa cikin rawar murya yake magana
“Fareedah dan Allah ki yi hakuri ki taimakeni, gani bisa gwiwowina, ina roqonki da ki yi hakuri da maganganun da na faɗa miki, sharri shaiɗan ne, ba zan sake ba Fareedah, dan Allah”
Sake haɗe fuska tayi tace “na yi hakuri, je ka, ai sati biyun basu yi ba balle su wuce”
Kasa magana yayi saboda mawuyacin halin da ya shiga, har hawaye sun fara bin kumatunsa, tashi yayi kawai daga durqushen ya haura gadon tamkar mayunwacin zaki, ita kuwa Fareedah dama plan ɗinsune dan haka ta biye masa suka lula
Saidai dukkansu sun fahimci baqon al’amura ga junansu mabanbanta, abubuwan da Faeez yayi ta mata su a yau ɗin baqine a gurinta da ba ta sanshi da su ba, shi ma kuma hakan take a gurinsa, abubuwan da ta dinga masa bai sansu ba a gurinta, hakan kuma ya taimaka gurin daɗewarsu a tare, saidai abinka da marasa gaskiya, dukkansu sai zargin juna suke yi, musamman Fareedah da kunnenta ya so ya ji kamar ya kirata da wani suna na daban
Dan haka suna dawowa hankalinsu suka kafe juna da idanu cikin alamar tambaya
“wace ce Tina”? Cewar Fareedah
Waro idanu Faeez yayi cikin rashin gaskiya yace “wace ce kuma me wannan sunan”?
Ajiyar zuciya ta sauke tace “ok, sai na ji kamar ka faɗi hakan”
 Ajiyar zuciyar shima yayi ya janyota jikinsa yace “kunnenkine kawai”
Ba ta yi magana ba ya ɗora da cewa “amma yau kamar ba Fareedar Faeez ba” duk da ta ji faɗuwar gaba sai da ta dake tace
“ni kaina gani nake kamar ba Faeez ɗin Fareedah ba”
Dammm ya ji qirjinsa ya buga, cikin in ina yace “kai wallahi bacci nake ji, zan wuce ɗakina, mu kwana lafiya” yana gama faɗin hakan ya bar jikinta ya sauko daga gadon ya sanya rigar baccinsa ya fara tafiya ba tare da ya yadda sun haɗa idanu ba har ya fice daga ɗakin
Bayansa ta bi da kallo tana ɗora alamar zargi a kansa, ji tayi ba ta yarda da shi ba, ni ko nace toh ke kin yarda da kanki fareedah?, hhhhh
Toh fa, cakwakiyar aure, Hafeez saidai hakuri fa, dan yau unborn ɗinka ya ci qaniyarsa, Allah sarki duniya, ku ji matasa masu zina, cikin.mutanen da Allah zai inuwantar da su a qarqashin inuwar al’arshi akwai matashin da mace mai kyau da nasaba ta bashi kanta ya qi yace yana tsoron Allah, toh ku mazinata masu bin boobs da hips kuna ina kenan?, wallahi zaku sani,idan baka shiga wannan inuwar ba za ka ci ubanka a lahira, yanzu dai shi hafeez da faeez ma, sun rushe wannan damar wa kansu, toh yaya kenan?, ku kenan bin matan masu kuɗi da kyawawa kuna zina da su, wani a fbook yace “duk wani wanda yake zuwa gurin budurwa dan ya lalatata Allah ya talautar da shi” abun kunya, wlh har da masu tsine masa, toh kuma Allah ya tsine muku, ko kuma ku shiryu
ISLAM IS MY IDENTITY

Leave your vote

-2 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

QANIN MIJI 8

Advertisement _Jinjinar ban girma ga gaba ɗaya writers ɗin pure moment of life, da writers ɗin  fasaha, ku…

QANIN MIJI 7

Advertisement kafin in fara dolene in tsaya kuma mata ‘yan uwana in faɗa muku gaskiya, wallahi mata mu…

QANIN MIJI 9

Advertisement IYAYE KU JI TSORON ALLAH, ‘YA’YANKU SUN FARA KAWO MIN QARARKU, KUKAN HANASU AURE AKAN KARATUN GABA…