QANIN MIJI 2

Advertisement

 2
Yanzu ma bayansa suka bi da kallo sannan suka juyo suka haɗa idanu, kowa da irin kallo da yake yi wa ɗan uwansa, cike da damuwa fareedah ta sunkuyar da kanta qasa yayin da hafeez ya matso kusa da ita cikin muryar rarrashi da tausasa lafazi yace

“kullum irin wannan damuwar takan bayyana akan fuskarki, in tambayeki, idan tana maganin wani abu, ya kamata a sake ganin wata damuwar a fuskarki”?
Idanunta ta watsa masa ba tare da tace komai ba, hakan bai hana shi fahimtar amsarta ta cikin idanunta ba, murmushi ya mata ya lumshe idanunsa ya buɗe yace
“then smile”
Ba ta iya riqe kanta ba, dole ta murmusa kaɗan, dan hafeez yana da muhimmanci a gurinta, duk da ta daɗe tana yakiceshi daga jikinta saboda qyamatar wasu abubuwan da yake mata amma yanzu ya fara yin galaba a kanta domin mafi yawancin farincikinta da walwalarta daga hafeez ne
Duk da dai murmushin mai kama da yaqene amma ya ji daɗin ganinshi kan fuskarta, saɓanin damuwar da ta shiga da farko
“sai mun dawo matar, ki shirya mana haɗaɗɗiyar supper, dan ni dai bayan hajiyarmu duk duniya babu matar da ta kai ki iya abinci”
Sai da ta ɗan dara cikin muryar dariyar tace
“um um dai hafeez, bana son ganin ido”
Yana qoqarin ficewa ya ɗan juyo yana dariya yace
“Allah kuwa matar, shiyasa nake sonki sosai, ba ke ba kishiya, i realy love you, ki ji daɗin rayuwarki kawai kiyi yadda kike so”
Bai saurari amsarta ba ya fice da gudu-gudu sauri-sauri
Dam dam fareedah ta ji zuciyarta ta mata lugude, sai da ta nemi guri ta zauna kan ɗaya cikin kujerun falon saboda yadda maganar ta shigeta, kalmar i realy love you ta fi komai dukan zuciyarta
Wannan kalmar ba a bakin hafeez ya kamata ta ji shi ba, a bakin mijinta ya dace ta ji, amma idan ba mantuwa ba, ko a first night ɗinta ba ta ji wannan kalmar ba balle a sauran zamansu na tsawo shekaru   uku da watanni, rabonta da wannan kalmar tun a filin nema, wato dandalin soyayya, nan kam ta ji su har ba iyaka, amma tunda ta shigo gidan, ba za ta iya tuna rana ɗaya da ta ji wannan kalmar daga bakin fa’eez ba, ko ita ta faɗa masa hakan ma sai ya ga dama yake nuna jindaɗinsa ko yayi murmushi kawai, ranar da ‘yan rahar suke kusa kuma ya ja hancinta, shikenan an gama, babu wani abu da yake biyo bayan nan,
Tun tana ɗaukar lamarin wasa wasa, kamar za ta iya canzashi, sai gashi sun kwashi shekaru ba canji, ita kuma ta kasa sabawa da hakan sam sam, dan ba haka ta tsara ba ko a cikin mafarkanta, rayuwar soyayya ta so shimfiɗawa filla fillah
Hawayene suka fara gangaro mata a fuskarta suna bin haɓarta, daga qarshe ma dai ta fashe da kuka ta tashi ta bar falon ta haura ɗakinta
Ta daɗe tana kuka ta ji wayarta da take kan side na gado tana neman agaji, tsayar da kukan tayi ta je toilet ta wanke fuskarta ta fito daidai da shigowar wani kiran, hafeez ta gani, hakan yasa  ba ɓata lokaci ta clearing throat ɗinta ta picking call ɗin
Dawo da sallamar da ta masa yayi cikin raha yace
“ina kuma kika shiga matar”?
Qirqirar walwala tayi cikin muryarta tace
“ka ganni nan wai baccine yaso ɗaukana”
“kash amma ban ji daɗin katse miki barcin da nayi ba matar, ki gafarceni”
Ya qarashe cikin marairaice murya   
Qyalqyalewa tayi da dariya tace “ni daɗi ma naji da ka tasheni, aiki zan yi yanzu”
Daga muryarshi ta gane ya ɗaure fuska sannan yace “ba kin qi mai aiki ba, sai kiyi ta tiqar aikinki ke kaɗai ai”
Dariya tayi cikin sigar lallashi tace
“sorry mijin, tun a gida ina da qyanqyamin girkin mai aiki, ni ko wanke wanke aka yi mana sai na sake wanke waɗanda nake amfani da su”
“ok, toh ki bi a hankali dai, kar ki dinga gajiyar da kanki”
“na gode hafeez”
Shiru suka yi sannan ya ɗora da faɗin
“kiranki nayi in faɗa miki na kai miki mijinki office lafiya, yanzu haka ya shiga meeting da ma’aikatansa”
Murmushi tayi tace “ka kyauta”
“toh sai mun dawo ko?”
“Alah ya tsare ku dawo lafiya”
“ameen matar”
Ajiye wayoyin suka yi, sannan fareedah ta wuce kitchen bayan ta kalli agogo, a ranta tana raya cewa dole ta sake wa fa’eez ɗinta abinci duk da bai ko kalli wanda ta shirya masa ba, toh yaushe ma ya zauna?
***
 Zaune suke su ukun suna taking supper ɗinsu, sai qarar spoons kawai yake tashi, ba magana, yayin da fa’eez yake haɗa cin abincin da danne danne a waya kamar wani admin😁, hhh gaskiya matan admins kuna da hakuri, admin mai zuga kenan amma na……😍, gaskiya kana shan 143 admin, Allah ya sawwaqa dai😂😂😂, dan Allah mata aji mana plss
Hafeez kuwa sai kallon fareedah yake yi yana mata murmushi, yayin da ita kuma hankalinta ke kan nurulhayat ɗinta, gaskiyar magana fareedah tana qaunar fa’eez qarshe, kullum zuciyarta ruruwa take da wutar qaunarsa, ta rasa wacce irin kamo mijin nata ya mata haka, kuma fa fa’eez ɗin ya kai a soshi, dan ubangijinsa ya qerashi maqurar qira, kamar jinin annabi yusuf dan haɗuwa da zallar madarar kyau, muninsa kawai halayensa
Gyaran murya hafeez yayi ya calling attention ɗinsu kansa sannan ya kalli fareedah ya mai da kallonsa kan yayan nasa yace
“kai gaskiya mu kam mun yi sa’a”
Da kallon tambaya duka suka bishi yayin da yayi murmushi yace
“anya yaya kana ganin bayan girkin aljanna ba sai wannan ba kuwa a daɗi”?
Kallon juna fa’eez da fareedah suka yi sannan faeez ɗin ya kalli hafeez da ‘yar harara a fuskarsa  ya ɗauke kai ya cigaba da cin abincinsa
 Murmushi hafeez yayi ya sake cewa
“mu dai muna godiya wa Allah, yayanmu ya iya zaɓe, gangariya, kai abincinma sun kai ayi hotonsu, bari in ɗauka”
Buga cokalin hanunsa yayi akan plate ɗin abincin yace
“kai…. Hafeez, wallahi ka cika surutu, ku qarata ni sai da safe, zaka hanani aiki, idan kana da buqatar wani abu ka tambayi fareedah dan za ka iya wucewa school ban fito ba”
“goognyt yaya, bana da buqatar komai”
Ko amsawa bai yi ba ya wuce samansa abinsa bayan ya ɗauki laptop ɗinsa da yake kan kujera kusa da inda suka ci abincin
Harara fareedah ta banka wa hafeez tace  “ka ga ka kora min miji, haba!!!” tana gama faɗin haka ta tashi ta bi bayan fa’eez tana    cigaba da surutu wa hafeez
“ni dai ban kora miki miji ba malama” cewar hafeez cikin dariyar tsokana, ko kulashi ba ta yi ba ta haura ɗakin mijinta
Ta sameshi har ya cigaba da aikin da yake yi ta waya, zama tayi kusa da shi ta kwanto a jikinsa ta marairaice murya kamar za ta yi kuka tace “my  man kamar kayi fushi”?
Kallonta yayi ya ɗan murmusa kaɗan da gefen bakinsa, in ba ita da ta san halinshi ba ma babu wanda zai ɗauka murmushi yayi sannan yace
“wa ya faɗi hakan”?
“toh ba gashi ka taso ka bar mana gurin ba”
Janyeta yayi daga jikinsa yana cewa “je ki kuyi hiranku dan Allah ki barni in yi aikina, bana son hayaniya”
Marairaicewa tayi     tace “nice hayaniyar”?
Yana janyo laptop ɗinsa yace   “idan haka kika ɗauka ba”
 Wani baqincikine ya tokareta, sai ga hawaye ɗaya na korar ɗaya
Galala ya tsaya yana kallonta sannan cikin muryar mamaki yace “me aka yi”?
Maimakon amsa sai ta fashe da kuka ta kife a gurin tana rerawa abinta
“ok….., na fahimceki, kina da buqatar mijinki ko”?
Ba ta yi magana ba sai ma cigaba da tayi da kukanta
Agogo ya kalla sannan ya taɓe baki yace
“ban da abin fareedah kwata kwata kwana nawane ba a haɗu ba, na ga ba a wuce two weeks to three ba, kina son wahalar da kanki, ina so ki sani, nima fa ba wai buqatarce bani da ita ba, kawai na cire wa rainane saboda bani da lokaci, ayyuka sun min yawa, kema da kin cire wa ranki zai fi miki, mtss bari in gani ko zan iya  baki 30m, je ki shirya ki zo, ban minti biyar” ya qarashe yana mai duba agogo again
Readers in kece me zaki ce?, yi maganar kamar kece fareedah
More comments, in ba comments daman ayyukan suna da yawa, na tsani tanx
ISLAM IS MY IDENTITY

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

QANIN MIJI 12

Advertisement 12 Cikin zaro idanu tare da dafe qirji  Fareedah tace “what”? Shi ko gogan naku yalwataccen murmushi…

QANIN MIJI 1

Advertisement QANIN MIJI Daga alqalamin marubuciyar zamani✍🏼 MARYAM A.I GITAL @ Meerahgee pure moment of life writers👌🏻  SADAUKARWA GA…

QANIN MIJI 14

Advertisement  Ina matuqar ba da hakuri wa masoyana masu bin littafin JININANE hakuri saboda tsaikon da aka samu…