QANIN MIJI 4

Advertisement

 4
  
Ba ta samu bakin amsa masa ba, ita dai abinda ta tsaya akai shine kuka da shessheqa
Tsawon mintuna ya tsaya shiru yana kallonta yayin da kukan

yake tafasa masa heart, ba tare da ya tantance abinda ya dace yayi ba a wannan lokacin ya ja wata doguwar tsaki ya mai da idanunsa kan hafeez yace

“mu je dan Allah, bana son matsala wallahi, ban san waye zai iya fahimtata ba idan fareedah ba ta fahimceni ba”
Hafeez da yake tsaye qiqam kamar namijin soja, tsayuwarsu ya gyara ya ɗan kalli fareedah sannan ya dawo da kallonsa kan yayansa ya motsa bakinsa tare da yin gyaran murya kaɗan yace
“ni kuma a ganina yaya bai dace ku rabu a haka ba, kamata yayi ka lallaɓata, ka rarrasheta, four to five months abin….., is not easy fa, gaskiya da nine da ba haka zan yi ba, in ma na iya tafiyar kenan, pls yay……”
A harzuqe fa’eez yace
“rarrashi na nawa zan mata, ko kuma kawai dan ban da aikin yi sai in tsaya ina ta maimaita magana ɗaya?, ka kiyayeni fa, kai ka jira kayi auren mu ga irin tunaninka, shashanci kawai”
Murmushi mai kama da dariya yayi tare da zare glass ɗin idanunsa ya sanya idanunsa cikin na fa’eez yace cikin tsokana da wasa irin na tsakanin yaya da qani
“ai ni da ka barni na yi aure, da a gurina zaka koyi salo da iya zamantakewar rayuwar aure, ni fa ka ga mr boss ɗin nan, haka zan mai da mata wallahi, balle matar ma irin fareedah, ah… ina!, ai four legs as two,  ko za a ɗan gwadane yaya”?
Ya qarashe maganar da sake yin dariyar shaqiyanci
“um, da yake kai mahaukacine ba, an faɗa maka ko ina ake iya zuwa da mace, dallah ni kauce min a hanya in wuce, tunda kai ka iya rarrashi sai ka rarrasheta ai, kauce dallah, da ma hakurin ka bata da shegen surutun da ka tsaya yi min”
Ja da baya hafeez yayi yana dariyar halin yayan nasa, ganin ya zaburo kamar zai make shi
Har ya ɗaga labule zai fice sai kuma ya juyo kaɗan yace
“sai mun yi waya fareedah, sai na dawo, dan Allah ki daina kukan nan, na tafi”
Yana gama faɗin haka ya sa kai abinsa
Ita kuwa hamshaqiyar ta fa’eez tana ganin ficewarsa ta sake fashewa da wani kukan ta juya za ta koma cikin gidan, Allah ne kaɗai ya san damuwarta kan tafiyar mijin nata, ita kanta ba za ta iya misalta haukacewar da zuciyarta tayi kan tunanin rashin ganin kyakkyawar fuskar fa’eez ɗinta da murmushinsa ba har na tsawon watanni,
Ji tayi an riqo hanunta ba tare da tayi aune ba, hakan yasa tayi gaggawar juyowa  ta kalli wanda ya riqe mata hanun, kasancewar yanzu ta saba da yawan taɓa jikinta da yake yi ya sanya ba ta wani damu ba, sai ma cigaba da kukanta da tayi a gabansa danta san a irin wannan lokacin shi ne kaɗai mutumin da yake iya fuskantar matsalarta ya kuma rarrasheta da daɗaɗan kalamansa masu tafiyar mata da damuwa
Seconds biyar ya ɗauka yana bin fuskarta da kallo sannan ya fara magana cikin tausassar muryarsa wanda ya saba rarrashinta da ita
“fareedah, ban san me yasa kika ɗauki kuka a matsayin magani ga kowacce matsalarki ba, na sha faɗa miki kuka bashi da muhimmancin da kika bashi, fareedah pls, kiyi hakuri, ina qara baki hakuri akan wanda yayana ya baki, ki daure, ki cije, nan da wata uku ne fa ko huɗu ko biyar?, za su zo kuma za su wuce, ke ina mai tabbatar miki ma, matuqar zai dinga tuna wannan kyakkyawar fuskarkin ba zai iya yin wata ukun ba balle huɗu ko biyar, musamman idan zai dinga tuno wannan kyakkyawan murmushin naki mai abubuwan mamaki, ga beauty point ga jerarrun fararen haqora, Allah ina mai tabbatar miki matuqar zai cika ukun ma to a daddafe ne, da ni ‘yasu da shiga uku ina faɗa miki” ya qarashe yana mai ɗan zare idanunsa irin na barkwancin nan tare da murmushi
Tsagaitawa tayi da kukan ta ɗan murmusa, hakan yasa shi ɗaura yatsarsa kan fuskarta yana share mata hawayen yana  faɗin “yawwa ko kefa, toh yanzu kin san abinda nake so da ke?, ki je ki cire wannan damuwar daga ranki ki kwanta kiyi baccinki, amma fa sai in kina son in dinga zama a gida ina tayaki hira, dan ni ba zan zauna ki isheni da kuka da kiran fa’eezu ba”
Ya qarashe da dariya, ita ma ɗan dariyar tayi ta ture hanunshi tare da masa hararan wasa ta juya ta fara tafiya cikin gidan abinta tana sauke ajiyar zuciya, ba laifi ta ɗan ji qarfin gwiwa kan lamarin tafiyar nurul-ma’eesh ɗin nata
Cikin tsokana hafeez ya ɗaga murya yace
“mai kukan tafiyar miji, sai ta yayah fa’eez mai daɗin girki”
Ba ta juyo ba sai dai ya juyo sautin dariyarta, hakan ya sanyashi mai da glass ɗinsa ya juya ya fice daga gidan yana murmushi mai sauti
**
Yana buɗe qofar motar faeez ya hau faɗa
“kun je kun tsaya shegen surutu ko?, ku da ba kwa gajiya da magana, kuma ba wai zan tafi ka ɗauka na barka sasakai bane, ko da wasa na samu labarin yawon banza ranka zai yi mummunan ɓaci, musamman yawon dare, balle ka je ka yaudaro ‘yar mutane, domin aure ba yanzu ba sai ka kammala wannan degree ɗin, lokacin ka haɗa degree biyu ka san meye duniya ka san ina za ka nufa, ba wai kayi aure cikin hayaniya ba, ko da wasa na ji labari zan sassaɓa maka, dan nima kafin alhaji ya min aure sai da na haɗa masters ma, kuma ban taɓa kula kowacce yarinya ba sai fareedah, dan haka kai ma hanyar da na bi ita za ka bi, kai kan ma na sauqaqa maka, tunda yanzu alhajin baya raye, ba sai ka kama aiki ba, kana kammalawa zan maka aure da wurwuri tunda na lura kai namamajone”
Sun fice daga gate ɗin gidan kenan faeez ya dire maganarsa, hafeez kuwa yace mai zai yi in ba dariya ba, dariya yayi sosai sannan yace
“toh boss, hafeez ya gode, Allah ya ja kwana, kai hafeez ka zama tamkar budurwa ‘yar shekara shashida, sai tsaronka ake yi, wayyo Allahna…”
Ya qarashe da yin magana wa kansa cikin marainiyar murya
Fa’eez da ke zaune a baya hannunsa ya kai ya ranqwasheshi, da sauri ya riqe gurin yace
“washhh…. yaya, am so sorry”
**
Zaune ƴyake a harabar hotel ɗin da yake a cikin babban birnin qasar da yaje domin shiga taron haɗaka na qara wa juna sani da yayi wanda idan har komai ya tafi yadda yake so, ɗaukakar companynsa za ta wuce na da sosai da sosai,
 shaqatawarsa  yake yi  abinsa cikin shigar baqaqen kayan sanyi da hularsu  kasancewar qasar qasace mai ɗan banzan sanyi mai ratsa jiki, yau satinsa biyu da zuwa qasar, tun satinsa ɗaya a qasar kewar fareedarsa ta fara kawo masa farmaki saboda  sababbin yanayin da ya shiga a zuwansa qasar
Na farko yanzu bai da yawan ayyukan da suke ɗauke masa hankali a kanta lokacin da yake tare da ita, duk ya handling ɗinsu wa maxwell da ja’afar abokinsa, suna tashi daga conference ɗin zai dawo hotel ɗinne ya zauna, sai ‘yan ayyukan da suke zuwar masa kan hanya ta cikin laptop ɗinsa, nan ma ba wasu masu jan lokaci bane, daga haka sai bacci sai sallah, wanka da cin abinci, daga nan kuma sai zaman harabar hotel ɗin da ɗan yawace yawacen zaga gari
Abin da yafi takurashi a qasar shine qarfin sanyin gurin da yake ɗago masa da sha’awarsa a kai akai, duk da qwayoyin da yake amfani da su, musamman idan ya zo bacci, da juye juye yake iya samun damar yin baccin, musamman idan ya ji muryar fareedarsa da take narka masa lakarsa kafin ya kwanta, haka zai yi ta narke mata a waya yana kunna mata wata wutar a can ita ma
Babban tashin hankalinsa farmakin da ya fara samu daga wata sheɗaniyar baturiya, domin tunda ta qyalla ido ta ganshi a hotel ɗin hankalinta ya tashi, ta ji duk duniya ba ta taɓa ganin namijin da take muradinsa matuqa kamar wannan ba, hakan ya sanyata tunkararsa tunda dai su ba su san wata aba wai kunya ba, saidai tun daga yadda ya amsa mata gaisuwar farko ta san wannan ba irin nasu bane, amma saboda baqar naci haka ta fara gabatar masa da kanta a matsayinta ta ‘yar iska, saidai tun bata qarasa ba ya korata ta bar gurin da wata mahaukaciyar tsawa da kallon da suka kusa sanyata fitsari a jikinta, shima ko minti ɗaya bai qara a gurin ba ya tashi ya shige ciki ya kulle ɗakinsa, dan ya san halin irinsu su bi namiji ba abin kunya bane a gurinsu
Toh tun daga nan bai sake ganin ta a hotel ɗin ba, saidai yana yawan ganin mata suna gilmawa cikin kayan da babu maraba da tsirara dan masifa, duk da sanyin qasar amma su ba sa ji, ko sabo da yanayinne oho
Hakan kuma na matuqar takurasa, saidai idan ya ga hankalinsa zai tashi sai ya koma cikin ɗakinsa yayi ta bincike a yanar gizo gizo da laptop ɗinsa, da haka yake qwatar kansa da mutuncinsa, sannan ya ɗora da tablet dan rage wa kansa zafi
Bai yi tsammani da zuwan mace ba saboda yayi nisa cikin rubuta saqon da yake yi wa maxwell a waya  kawai sai ji yayi an rungumeshi ta baya da waɗansu tausasan hannaye masu matuqar sheqi da laushi tare da saqalo kai ta gefen kunnansa aka raɗa masa “hi…..”!
Wani irin yarrrr ya ji a jikinsa
ISLAM IS MY IDENTITY

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

QANIN MIJI 1

Advertisement QANIN MIJI Daga alqalamin marubuciyar zamani✍🏼 MARYAM A.I GITAL @ Meerahgee pure moment of life writers👌🏻  SADAUKARWA GA…

QANIN MIJI 14

Advertisement  Ina matuqar ba da hakuri wa masoyana masu bin littafin JININANE hakuri saboda tsaikon da aka samu…

QANIN MIJI 9

Advertisement IYAYE KU JI TSORON ALLAH, ‘YA’YANKU SUN FARA KAWO MIN QARARKU, KUKAN HANASU AURE AKAN KARATUN GABA…

QANIN MIJI 12

Advertisement 12 Cikin zaro idanu tare da dafe qirji  Fareedah tace “what”? Shi ko gogan naku yalwataccen murmushi…