QANIN MIJI 5

Advertisement

5
Da sauri ya zabura ya miqe tsaye har wayarsa tana faɗuwa a qasa tare da fisge jikinsa daga na baturiyar da ta rungumeshi

Yatsarsa ya nuna mata cikin fushi yace
“ke dabba mahaukaciya, idan kika sake kuskuren taɓa jikina sai na ɓaɓɓalaki ke da qasarku, duk tsiyar da za ayi a je ayi, ‘yan iska kawai karnuka”
Ya ma mance da ita wannan ɗin ba hausa take ji ba
Ita kuwa baturiyar da take tsaye cikin kayan da bai fi tsirara ba, da mamaki take kallonsa, domin ita na farko ba jin abinda yace tayi ba, na biyu kma ba tayi tsammanin haka daga gareshi ba, musamman yadda ta ganshi wayayye, saboda yanayin fuskarsa kawai ya nuna mata faɗa yake mata kan abinda ita ba ta ga laifinsa ba
Rashin hankali da fasali irin na matan turawa sai ta yi murmushi tace
“my name is Tina, and you”?
Ta qarashe da miqa masa hannu, mugun kallo ya mata sannan ya sunkuya ya ɗauki wayarsa ya fara tafiya zai bar gurin, da sauri ta yunqura ta riqo hannunsa tace
“pls can I help you”?
Cikin fushi ya juyo ya kwasheta da mari tare da faɗin
“is better for you to stay away from my life, don’t put your self in trouble with me, useless!!!”
Ya qarashe maganar da ihu tare da tofa mata yawu ya taka cikin sauri ya bar gurin
Gaskiyar magana a wannan rana Tina ta cutar da shi, saboda yadda ya ganta da surorinta sun mugun ɗaga masa hankali, saidai alhamdulillah tunda ya banki qwaya ya samu sauqi saidai ɗan feelings ɗin da ba za a rasa ba, hakan yasa shi kiran fareedarsa domin  ya kawar da wannan yanayin ta hanyar rage zafi amma aka yi rashin sa’a wayar fareedah switch off, haka yayi ta juye juye da tunane tunane har bacci ya kwasheshi
Ita kuwa fareedah a nigeria da saninta ta rufe wayarta domin kiranta da yake yi cikin dare yana mugun takurata, musamman yadda yake neman ya dinga ɗaga mata feelings ɗinta a matsayinta ta ɗiya mace, ita kuwa a ganin ba qira babu abinda zai ci gawayi, ni ko nace har ginkin matan kano😂🤭, afwa…
A tunaninta ba ita ta turashi ba balle ya zo ya dinga ɗaga mata hankali a banza da wofi ya hanata bacci mai daɗi
***
NIGERIA
A ɓangaren fareedah, tunda fa’eez ya bar qasar ta addabi kanta da tunaninsa da irin rayuwar da take ciki, saidai hakan bai ɗau lokaci ba hafeez ya janye mata hankali da wasannin da suka saba irin na qanin miji da matar yaya, kar ku manta fareedah yarinyace me addini amma shaiɗan yana son yin nasara a kanta saboda rashin kulawar miji, domin mu a muslunci wasan qanin miji haramunne, haramunne, haramunne, manzon Allah ya haramta har ma ya ɗora da cewa ai shi qanin miji mutuwane masu wasannin qanin miji idan kun shirya mutuwar toh kuyi tayi, Allah tura shegu biyu kabari, munkar da nakir suna nan, akwai calugude🤣😂, daman ance lahirar da gumi
Saboda ko da yaushe hafeez yana tare da ita yana bata labarurrukan ban dariya da nishaɗi tare da ɗebe kewa, tsabar jin daɗi ma game ya haɗa musu a gidan na tseren mota, idan ta kammala ayyukanta, shi kuma ya dawo daga school sai su cancaɗa kwalya su hau buga game ɗinsu, kasancewar an fi cinye fareedah yasa take dasa masa rigima tace yana mata wayo, shiko yayi ta tsokanarta da mata gwalo, hakan yake sawa ta ɗauki filolin kujeru ta fara jifansa yana kwashe mata da dariya, wani lokacin har remote take ɗauka ta wurga masa ya kauce, haka zasu yi tayi har magriba kafin su tashi su tafi sallah dan dukkansu babu mai wasa da sallah a cikinsu
Abin haushi da takaici, duk lokacin da hafeez zai ga fareedah da kwalya sai ya yaba mata ya koɗata tamkar shine mijinta, hakan kuma yana mata matuqar daɗi a ranta tare da qara wa zuciyarta shaquwa da hafeez, har tana Allah Allah tayi kwalya ya zo ya gani ya koɗata ya kambamata
***
Yau ba school a gurin hafeez, dan haka tun safe babu inda yaje yana gida, daman ko da school ɗin ma yanzu yana dawowa baya qara fita da mota, sallace kawai take fitar da shi masallacin unguwarsu
Tun da suka yi break ɗin safe suka haɗa game sai yi suke yi cikin raha da barkwanci, gashi suna zaune gab da gab kan two seater, duk wanda ya buge wani zai yi ihun murna, tamkar dai wasu mahaukata, yayin da ɗayan zai yi harara, daga qarshe dai hafeez ya buɗe wuta ya dinga doke fareedah, ganin yana ta cinyeta sai kawai ta jefar da abin yin game ɗin ta tashi ta fara tafiya tana bubbuga qafa irin na rigima ta juyo cikin muryar kuka da shagwaɓa tace
“ba za ayi game ɗin ba, na qi ɗin, sai wayo kake min…😢
Dariya ya qyalqyale mata da shi yana mata gwalo da faɗin “woooh loozer”
Dawowa tayi da nufin jifansa da filo shi kuwa ya tashi suka zuba a guje sai zagaye falon suke yi ta kasa riskarshi yayin da yake ta qyaqyale mata da dariya
Haushine ya kamata ta zabura za ta kai masa duka ya kauce ita kuma ta tafi zata faɗi saboda taka remote ɗin da tayi wanda ta jefa masa ya kauce, ta tafi suuu zata kai qasa hafeez kuma cikin zafin nama ya tareta yayin da shima kuma qafarsa ta bugu da jikin kujera ta harɗar da shi saboda saurin da yayi gurin tarota, dan haka tana faɗawa qirjinsa suka zube dukkansu a qasa😳
Tsabar tsorata da fareedah tayi na mummunar faɗuwar da za ta yi a qasa yasa tana jin jikin hafeez a nata jikin ta qanqameshi qam cikin tsoro tare da rufe idanu
Shi ko hafeez jin tattausan jikin fareedah a jikinsa ya sa dukkan netwrk ɗinsa ɗaukewa tare da tsinkewar laka da jijiyoyin jikinsa
Shine kwance a qasa yayin da ita kuma take kansa qanqame da shi, duk buguwar da hafeez yayi wannan qanqamar ta fareedah ta hana shi jin zafin, ko motsawa ma bai yi ba, dan numfashinsa ya kusa ɗaukewa
Fareedah kuwa tsoron na sake ta ta dawo cikin hayyacinta, hakan ya sanya ta sauri sakin hafeez tare da zabura ta bar jikinsa, cikin jin kunya
Hafeez kuwa idanunsa ma a rufe suke ko motsi ba yayi, cikin tsoro fareedah ta bubbuga kafaɗarsa tana cewa “hafeez, hafeez!”
Idanunsa da suka yi jajir ya buɗe a kanta yana binta da kallo, ita kuwa ganin idanunsa haka ta ɗauka zafin faɗuwarne, dan haka cikin tausayawa tace
“sannu hafeez, kayi hakuri dan Allah, ban san haka zata faru ba”
Shi dai bai ce komai ba, sai ma binta da kallo da yake yi, hakan yasa ta shiga tashin hankali ta miqa masa hannunta tace
“pls hafeez kayi magana, kama hannuna ka tashi”
Sai a lokacin yayi murmushi ya miqe ya zauna gurin yana mata wani irin kallo yace “kalleta dallah, ke yanzu in na ce zan kamaki in tashi ba saidai mu sake zubewa ba, wasshh amma gaskiya na bugu”
Ya qarasa maganar da dafe bayansa, dariya ta yi tace
“kai hafeez, kaman ba namiji ba, dubi idanunka yadda suka yi ja”
Hararanta yayi yace “eh dole ki min dariya, da yake ba yayana bane ya faɗi ko?, da yanzu kin rikice mana a gida da ihu”
Dariya ta sake yi tace “toh ai shi wannan mijine, kai kuwa qaton….”
Ba ta qarasa ba ta rufe baki, wani irin kallo ya mata yana murmushi yace “qaton banza ko”?
Girarta ɗaya ta ɗaga masa cikin tsokana tace “yesss…”
Murmushi yayi yace “toh shikenan qaton banza ya gode”
“yi hakuri kaide wasa nake maka mijin” tace tana murmushi
Lumshe idanu yayi ya buɗe yace “ya wuce matar, amma fa yau ya kamata mu ɗan zaga gari ko, wallahi ni dai zaman gidan nan ya isheni, haka kawai an min kulle kamar wata mace, an hana ‘yammata ganin babban yaro mai qtr million, mu ɗan fita ko shan ice cream ne matar”
“lallai fa babban yaro, amma dai duk tsiyar mutum bai kai mijina haɗuwa ba balle a min iyayi”
Harararta yayi yace “toh kin ji na sako mijinki ko neman magana, ki faɗa masa kawai da yamma mu je mu kashe qwarqwatar idanu”
Miqewa tayi tana tafiya tace “wai dai na tuna makane, ka daina mantawa akwai kyawawa a gabanka, zan mishi magana, sai mu fita 4:00, nima na gaji da zaman gidan wallahi”
Bai amsa ba sai bin bayanta da yayi da kallo har ya daina kallonta sannan ya tashi yayi ɗakinsa
***
Cikin shiga ta alfarma fareedah ta fito ta sha kwalya iya kwalya domin ta ɓata lokaci gurin yinta, sai wani dal dal dal take yi tana wani wal wal wal
Qaran takalmantane ya janyo hankalin hafeez da yake zaune yake duba saqonninsa na istagram
“wow……..”
Hafeez yace tare da miqewa tsaye yana mata kallon up and down, ita kuwa sai murmushi take yi domin ta san yba mata zai yi
“matar ke kin ganki kuwa, ke kin san wutar da kika bayar kuwa?, kai matar da ana kallon hurul’een a duniya sai ince ke jinsinsu ce, mashaa Allah, gaskiya na sara miki, ke sarauniyar matace, daga kin fito kike daqushe haskensu, kai ki gode wa ubangijin da ya qeroki cikin gwanayen iya kwalya da tsara ado”
Cikin farinciki da jin daɗi fareedah tace “kana koɗani da yawa mijin, na gode, mu je ko”
ɓata fuskarsa yayi yace “kin gode kawai zaki ce min, kullum ni sai na yaba miki ke kuma ko sau ɗaya”
Cikin muryar lallashi tace “tuba nake nawan, ai bama haka da kai, wallahi kayi kyau, kuma daman kai kyakkyawane, ga iya gayu tamkar jinin sarauta”
Ai ko ya ji daɗin yabawar, murmushi yayi tare da godiya sannan suka fice tamkar miji da mata
*
Sai da suka je gidan su fareedah suka ɗauki kboy sannan suka wuce, yawo sosai suka yi tare da saye sayen banza da wofi suka yi ta zuba hotuna abinsu sannan suka mayar da kboy gida tare da tsarabobinsa sannan suka dawo gidansu cikin nishaɗi da walwala, domin dukkansu babu wanda bai ji daɗin fitan ba saboda wasannin da sukayi da yadda suka yi ta hotuna a gurare daban daban, hoto ɗaya kawai suka tura wa faeez shine wanda fareedah da kboy suke kan lilo suna dariya, hafeez kuma na ta lilasu
Suna shiga cikin gidan kowa yayi ɓangarensa da sauri, saboda yau sun yi missing sallar magrib cikin jam’i
*
Ko da faeez ya ga hoton dariya suka bashi, duk da sun masa kyau, sai da ya kira kowannensu a waya yace musu lallai baku da aikin yi, wasa dai wasa dai, sana’ar kenan, toh Allah kyauta muku, kamar sun haɗa baki kuwa, kowanne dariya ya masa suka manna masa, ni ko nace yo toh me za su ce😂
**
Yau watan faeez ɗaya a can da kwana biyar, zuwa yanzu baya samun daman wuni a hotel ɗin saboda taron nasu ya fara ɗaukan zafi, sai dare yake dawowa ko daf magriba, amma fa har yanzu wannan yanayin yana tare da shi na saurin motsawar sha’awa saboda yanayin sanyi da kuma yawan kallon tsaraicin mata a ko da yaushe, ya shiga damuwa sosai, da har ya so ya faɗa wa fareedah ta biyoshi sai kuma shaiɗan ya hanashi da wasiyoyinshi na banza, kullum yana nuna masa bai dace ya kawo fareedah wannan qazantacciyar qasar ba, saboda zinace zinacen kan hanya da yake gani, sannan kuma ya kan tuna masa ga tablet yayi ta sha kawai, amma fa bai tuna masa yin azumi ba dan mugunta
Yau ya dawo hotel ɗinne cikin muguwar sha’awar da bai taɓa jin irinta ba, sai kuma aka yi sa’a a yau ɗin harabar hotel ɗin cike yake da tantirai ana ta tantiranci, abubuwan babu kyan gani, da qyar ya kawo kansa ɗaki saboda jiri da yake ta ɗebansa, burinsa kawai ya je ɗaki ya sha tablet ɗinsa ko zai ji relief, saidai neman duniyan nan yayi wa tablet ɗin ya rasa, sai daga baya ya tuna da cewa sun qare, ragwaf ya kwanta a gado tare da riqe kai, yana son fita ya je ya sayo tablet ɗin amma baya buqatar sake ɗora idanunsa a kan baɗalar da ake yi a wajen, don haka yayi lamo a kan gadon, ya ɗau lokaci a haka kafin ya tashi a daddafe ya je yayi wanka ya sanya kayan barci ya zo ya sake kwanciya ruf da ciki
A hankali ya sanya hannunsa ya ɗauko wayarsa ya fara dialing number fareedah, cikin sa’a kuwa wayar ta shiga, hakan yasa shi juyowa yayi rigingine yana kallon seiling, fareedah da ba ta daɗe da kwanciya ba dan yau basu yi game ba saboda hafeez yana da test mai zafi a school, wayarta ta janyo ta kara a kunnenta ba tare da ta duba mai kiran ba
Abin da ta ji ya fara faɗa kawai shine “fareedah wallahi nayi begen wannan daren ace muna tare, gaskiya neman halak da wuya, ina cikin wani hali”
Muryar da yayi amfani da ita sai da ta ɗaga mata kaf tsikar jikinta, sosai ta rintse idanunta, duk da haka sai da tayi magana cikin kasalalliyar muryarta da ta gama narkewa tace “haramun ɗin ma ba baya bane fa’eezzz….”
Sake burkitashi muryar fareedah tayi, cikin mawuyacin hali da kasalalliyar murya yace “fareedah pls, kiyi duk abinda ya dace ki samar min da nutsuwa plss, fareedah…….”
Qofar ɗakinsa ya ji an turo, bai san lokacin da wayar hanunsa ta zame daga hanun nasa ba, saboda teena da ta shigo ɗakin cikin tsaraici, daga ita sai wani ɗan jan qyalle daga iya qirjinta zuwa kan cinyarta, ko pant da bra babu, sheɗaniyar tana gani ya zuba mata idanu sai kawai ta janye qyallen, ta fara takowa gurinsa, subhanallah
*
A nigeria kuwa, yadda faeez ya burkita fareedah da muryarshi kuma ta ji yayi shiru alamar yana sauraronta, sai hakan ya ba ta haushi ta datse kiran tare da jefar da wayar gefe, ji take kamar ta ja masa Allah ya isa, haka tayi ta jan tsaki tana juyi a kan gado ita kaɗai, maimakon ta fara ambaton Allah ko ta tashi ta fara nafila, sai ta  qanqame kanta a kan gado tana jin wata muguwar sha’awa tana taso mata tana bibiyar duk wata magudanar jininta, can wata dabara ta faɗo mata, a kasalance ta tashi, shi ko oga shaiɗan la’anatullahi yana ta zugata, tunawa tayi da wani littafi da ta ji ana labarinsa a wtsp groups da take, saboda abubuwan da ta ji ake labari na book ɗin ta san in ta karanta ita ma za ta samu sassauci kan yanayin da faeez ya jefata, ta gane hakan ne daga comments ɗin da ake yi a kan book ɗin, hmmmm
Anya kuwa tusa za ta hura wuta readers?
ISLAM IS MY IDENTITY

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

QANIN MIJI 8

Advertisement _Jinjinar ban girma ga gaba ɗaya writers ɗin pure moment of life, da writers ɗin  fasaha, ku…

QANIN MIJI 6

Advertisement QANIN MIJI🤵🏻  6  Da mugun qarfi ya rintse idanunsa yayin da zuciyarsa take luguden duka saboda tsabar…

QANIN MIJI 1

Advertisement QANIN MIJI Daga alqalamin marubuciyar zamani✍🏼 MARYAM A.I GITAL @ Meerahgee pure moment of life writers👌🏻  SADAUKARWA GA…

QANIN MIJI 9

Advertisement IYAYE KU JI TSORON ALLAH, ‘YA’YANKU SUN FARA KAWO MIN QARARKU, KUKAN HANASU AURE AKAN KARATUN GABA…

QANIN MIJI 7

Advertisement kafin in fara dolene in tsaya kuma mata ‘yan uwana in faɗa muku gaskiya, wallahi mata mu…