QANIN MIJI 6

Advertisement

QANIN MIJI🤵🏻
 6
 Da mugun qarfi ya rintse idanunsa yayin da zuciyarsa take luguden duka saboda tsabar shiga ruɗu da yayi, domin yadda wannan shaiɗaniyar ta shigo masa, ta sake rikirkita masa sauran nutsuwar da yake da itane

Bai kai ga samo nutsuwa da sassauci ba yaji ta a jikinsa, duk yadda zuciyarsa taqi abun da qyamatasa ya gagara control ɗin gangan jikinsa, saboda mahaukatan abubuwan da ta fara masa wanda suka saka shi rawar jiki, ba tare da ya iya tuna tsananin baqin duhun zina ba ya sallama wa Tina kansa suka shiga duniyar zina, a ransa yana raya cewa gwara ya sauke wa kansa nauyin da yake ji na yau kawai, daga nan sai ya ɗauki matakan kare kai daga sake afkawa mawuyacin hali irin na yau da ya tsinci kansa a ciki, sannan kuma ya raya cewa daga yau zai tuba ya daina kasancewar daman bai taɓa aikata zina ba sai a yau ɗin
Tina shaiɗaniyace kuma gogaggiyar ‘yar barikice, tana cikin qungiyar matan da suke da lasisin zina a qasarsu, qungiyarsu tayi qaurin suna cikin faɗin qasar, su zina ko kyauta suna iya yi da mutum ba sai ya biya ba, musamman idan suka ga mutum ya musu, toh fa duk yadda za su yi sai sun yi gurin samun damar  kwanciya da shi, ko kana qi dole sai sun san yadda suka yi suka rinjayeka ta qarfin tsiya da iya shege, a taqaice dai, qungiyar su tina qungiyace da ta shahara gurin fyaɗe wa mazaje😂🤭, Allah ya kiyaye matasan musulmi
Ba a nan qungiyar su tina ta tsaya ba, suna da kaifafan sunadaran da suke amfani da a jikinsu ta yadda zai yi wuya a kusancesu sau ɗaya ba a yi marmarin kumawa ba, saboda qarfin qwayoyin da sukesha, sun ɗau wannan matakinne tunda suka fahimci a karan kansu basu da wata cikakkiyar ni’imar da za ta iya ribace musu zuciyoyin mazaje kamar yadda suke buqata, toh ta hakane qungiyar ta yi qarfi domin kuwa karuwaine na manyan qasar, ba a isa a taɓasu cikin qasar ba, duk kuma wanda suke son gani cikin manya ba ɓata lokaci suke samun damar ganinshi, domin kowa rawar jiki yake akan qungiyar thousands butterflies, saboda yadda suka qware gurin iya sarrafa mazaje a shimfiɗarsu ta Allah tsine
Tunda fa’eez yake a rayuwarshi bai taɓa jin daɗin kwanciya da mace irin Tina ba, ba wai fareedah ba ta kai bane, fareedah mace ce iya mace a shimfiɗa kuma ta san me take yi, saidai bata ko kama qafar Tina ba a wannan fannin, duk da a zahiri fareedar ta fi Tina sahihiyar ni’ima ba ta coge ba wacce ake saya, amma fa’eez bai fahimci hakan ba saboda qarfin sinadarin da su Tina suke amfani da shi
Tina ta wahalar da shi matuqa kasancewar bai taɓa daɗewa da mace irin haka ba a shimfiɗa, duk haɗuwar fareedah baya bata lokacin da ya fi awa ɗaya, ita ma fareedar kunya irin ta ɗiya mace ɗiyar hausawa ta kan nuna masa awa ɗayan ma da qyar ta kaishi, dan haka ko da ita ba ta samu nutsuwar ba, ba ta nuna masa ganinta zai ga zaqewarta ko kuma da kunya tunda shi bai da dogon zango game da al’amarin mace
Ita kuwa Tina sheɗaniyar, daga wannan style sai wancan duk a dare ɗaya, kuma rura wuta irinta shaiɗan la’anatullahi alaihi sai ya mance ma da cewar yanzu fa zinace yake yi, ba halaliyarsa bace, haka yayi ta biye mata tare da nuna jin daɗinsa har zuwa lokacin da aka iso magaryar intaha, ta fahimci ta gajiyar da shi sosai sannan ta qyaleshi, nan kuwa suka saɓi barci suka runtuma suna rungume da juna, ba kyace fa’eez ɗin fareedah bane mai qin kula mace da ba ta muhimmanci, sai ga wannan kamar zai mayar da ita ciki
Hmmmm, wato matasa, qin jawuwa qin kamuwa, bahaushe yace tsalle ɗaya ake yi a faɗa a rijiya amma sai ayi dubu ba a kuɓuta ba, kada ka kuskura ka jefa rayuwarka cikin datti da gubar zina, ka sani ɗan uwa, zina masiface, zina bashi ce, malamai sukace ba kowane zai biya maka bashin zina ba sai ‘ya’yanka mata, yanzu tsakani da Allah mazaje kuna yi wa matanku adalci?, tsakani da Allah kuna yi wa ‘ya’yanku adalci, manzon Allah ne fa ya faɗi magana, kana ganin maganar ba za ta tabbata ba, manzon Allah s.a.w yace duk wanda yayi zina da matar wani sai anyi da tashi, duk wanda yayi zina da uwar wani sai anyi da tashi, duk wanda yayi zina da ‘yar wani sai anyi da tashi, duk wanda yayi zina da qanwar wani sai anyi zina da tashi, shi ka qaryata manzon Allahn ne?, me ka ɗauka zai sameka bayan ka ɓuya wa halittu ka yarda mahaliccinka ya ganka kana zina, wai ma wacce ribace cikin zina bayin Allah?, me zaki samu?, me zaka samu ga abokiyar zinarka wacce matarka ta aure ba ta da shi?, ashe ka gwammaci ka tozarta ‘ya’yanka mata ta hanyar ciyo musu bashin da zai taɓa mutuncinsu a duniya, qarshe ya gangarasu cikin fushin Allah da azabarsa a lahira?, mene ne ribarka bawan Allah, shin kana tunanin ranar da za a tona maka asiri a gaban waɗanda ka ɓuya daga garesu ka aikata laifin, ka manta akwai yauma tubulassara’ir, me ya aikeka ɗan uwa?, wallahi tallahi, billahi matuqar zaka riqe zina toh sai ta rabaka da mahaliccinka, domin ita zunubice da ba ayinta sai an cire wa mutum rigar imani, kai da zaka ga yadda kake a lokacin da kake zina toh da ba ta sake baka sha’awa ba, ka sani malamai sunce matuqar ka sanya kuɗi kayi zina da wata mace, toh kai wallahi kyauta za ayi da taka, ya zaka ji lokacin da aka ce maka ga ‘yarka can ba ma mazan ne suke bibiyanta ba, ita take bibiyarsu, ɗan uwa kar ka yarda da ganin hakan a rayuwarka, idan mace ɗaya ba ta maka ba akwai m asna, wasulasa, wa ruba’a, sam zina Allah ba a daina yace ba, kar ma a kusanceta yace, ita kanta kusantar zinar haramunce balle zinar da kanta,  ɗan uwa idan an maka wa’azi, kar ka ce ba yanzu zan tuba ba, kar ka ce na kusan tuba, domin ka sani wasu a kan gadon zinan suke mutuwa, me kake tunani zai sameka idan ka mutu a lokacin da aka zare maka imani?, ɗan uwa kar kayi, ɗan uwa kar ka cigaba da aikatawa, wallahi zina mummunan laifine, ko a wuta mazinata suna da baqin jini balle a duniya, ki duba zafin wuta da azabarta da aka faɗa amma dattin zina da yake fitowa daga farjin mazinata yafi ɗaga wa ‘yan wuta hankali akan zafin wutar, ɗan uwa aljanna kake so ko wuta?, kai a gaisheku matan mazinata, wallahi kuna da hakuri, Allah ya tsareku ya qara muku hakuri ya kuma kawo muku mafita amma kar ki garda ki biya bashin da ya ci ‘yar uwa, ki nemi tsarin Allah akan hakan, Allah ka shiryi matasa da dattawan musulmi, dan wani azzalumin tsoho da na gani da aids wai shima a neman mata ya samu ana ta gaisheshi, ya ban tausayi amma ban iya tsayawa a gurin ba, mu ji tsoron Allah ‘yan uwa😭
**
Duk yadda fareedah ta so ta samu relief akan sha’awarta ta kasa, sai ma qarin sha’awar da ta qara wa kanta, haka tayi ta juye juye ta lumshe lumshen idanu  har sheɗan ya so jefa mata wani abu cikin zuciyarta sai Allah ya taimaketa a wannan lokacin tayi istirja’i, da qyar bacci ya ɗauketa a wahalce, da safe da qyar ta tashi ta haɗa wa hafeez break fast saboda tafiya school, saidai duk yadda ya so janta da wasa yau ba ta da walwala, kallonta kawai yayi tayi har ya gama break sannan yayi murmushi yace
“matar zan wuce”?
Idanunta da suke lumshe ta watsasu a kansa ta buɗe baki da qyar tace “toh hafeeez, Allah ya ba da sa’a”
Ameen yace ya ɗora da cewa cikin tausasa murya tare da matsowa jikinta daf da ita kamar zai haɗa fuskarsu yace
“akwai baqon yanayi yau a tattare dake, bana sonshi domin na tsani damuwarki, ki je ki kwanta kiyi bacci, kar kiyi komai, idan na dawo zan mana ayyukan, ba zan daɗe ba amma zanyi kewarki matar” ya qarashe da murmushin da ya sanyata jin tsikar jikinta sun zuba, ba ta samu bakin amsawa ba sai lumshe idanu da tayi tana sauke numfashi a hankali
Hannunsa ya ɗora akan kafaɗarta yace
“matar ko in fasa school ɗin ne mu je asibiti, sai na ga kamar ba lafiya ko”?
Hannunsa ta janye daga kafaɗarta tace cikin juriya da qarfin hali
“No hafeez, baccine kawai bai isheni ba, yanzu zan je in rama, a dawo lafiya mijin, ina so ka cinye test ɗin nan duka” ta qarashe da ‘yar dariya
Yana murmushi yace “na miki alqawari kuwa, inshaa Allah, bye matar zan missing ɗinki”  yana gama faɗin hakan ya tashi yana mata murmushi kamar yadda ita ma take masa sannan ya juya ya tafi ta bi bayansa da kallo har sai da ta daina kallonsa,
ɗakinta ta wuce ta kwanta, maimakon ta yi abinda ya dace sai ta sake ɗaukar wayarta ta tafi wattpad duniyar novels ta fara bin wani ɗan banzan littafi na turanci wanda arnakun duniya suka rubutashi na batsa, wanda ake iskancin da gaske saboda ba addini, toh kema in kika yi koyi da su kin rushe addininki da mutuncinki da ta iyayenki,
Ba tayi nisa cikin novel ɗin ba muguwar sha’wa ta ninku mata fiye da farko, haka dan jaraba ta cigaba da karantawa har ta fitar da abinda kai tsaye ba za a kirashi releasing ba domin sauqi kaɗan ta samu amma tana nan tare da guguwar muguwar sha’awarta, amma ita a gurinta shaiɗan ya qawata mata abin dan haka ta ji yin hakan ya mata daɗi, ta ji kuma tana da ra’ayin cigaba da hakan
Hmmmmmm
***
Ba qaramar makara faeez yayi ba, dan haka yau ya rasa sallar jam’i da yake yinta kan lokaci a ɗakinsa, wannan ita ce illar zina, domin basa haɗuwa da sallah, wasu malam sunce matuqar ka ga kana yin zina kuma kana sallah, toh sallarce ba ka yinta daidai, domin ita Allah yace tana hanine ga aikata alfasha, Allah ya kyauta
Duk jikinsa a mace yake dan haka koda ya farka motsi kawai yayi amma ya kasa ture Tina daga jikinsa, ita ce ta ji motsinsa ta buɗe idanunta ta kalleshi, idanu kawai ya qura mata ba tare da yayi magana ba, murmushi ta masa tace cikin harshen turanci
“kana buqatar taimakone”?
Kai ya gyaɗa mata ya buɗe baki a hankali yace
“ina son yin wanka”
Bakin da yayi maganar ta sumbata tare da masa murmushi ta sauka a haka tsinanniyar ta shige toilet ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi daidai yadda ta tsara ta fito ta yaye masa lulluɓin jikinsa ta kamo hanunsa zuwa toilet ɗin, da kanta ta masa wanka ta mammatsa masa jiki saboda fahimtar da tayi bashi da qarfi, kafin ta gama masa wanka cikin hikimominsu na butterflies faeez ya nemi gajiyarsa da mutuwar jikinsa sun sakeshi, tsabar yaudara irin na Tina sai da ta so ta rinjayeshi a toilet ɗin, da qyar ya yaqi zuciyarshi yace ta bashi minti biyu, da qyar ta fice ta barshi ya yi wankan tsarki cikin gaggawa ya fito ɗaure da towel, yayi saurin sanya jallabiya tare da dakatar da Tina ganin tana shirin raɓarsa, ya fara gudanar da sallah misalin qarfe takwas da rabi na safe, a gaggauce yayi adduoi ya tashi saboda ya makara da halartar conference hall ɗin
Cikin gaggawa Tina ta shiryashi tunda ta fahimci sauri yake yi, shiko ya wani sake mata jiki tamkar wanda aka canza wa qwaqwalwa, sai ma kallonta yake yi shaiɗan na raya masa wasu abubuwa game da ita dan har yanzu ba kaya a jikin Tina
Yoh toh ta zo da su ne?😔
Da zai fita kuwa cikin karuwanci da barikanci ta maqalqalesa ta bashi kisses sannan ta ce “I love you, you are the best among the men”
Cikin jin daɗi da qawatawar shaiɗan ya manneta a jikinsa yace “ki zauna da ni, kar ki fita daga nan, ki bari in dawo, duk abinda kike so za a kawo miki, pls”
Murmushi jakar ta masa ta sake haɗa bakinsu sannan ta janye hannayenta na rataye a kafaɗunsa tace
“kana sona?, ban ji matsayina a darenka ba”
Abin tsoro abin mamaki sai ga faeez yayi murmushi ya sumbaceta yace “baki da misali, kin fi qarfin furuci, darena dake rayayyene a cikin sauran dararena”
Murmushi tayi tace “then say…, you love me”
Ba msu ya raɗa mata hakan a kunne sannan yayi saurin kama hanya tare da janyeta yana waving mata hannu, ita kuwa ta hura masa kiss
Toh mata, da haka ake qwace muku mazaje, ke kin zauna, kune na bara kune na bana, kwanciyar aure ɗaya kika iya, bance kiyi koyi da turawa ba domin su sun zaɓi jin daɗin duniyane ko da zasu cutu amma ki canza, ki nemo waɗanda babu cutarwa a cikinsu, amma ke tun irin kwanciyar iyaye da kakanni ba canji toh a gurin mazajen yanzu da kwai matsala, ki shiga hankalinki
ISLAM IS MY IDENTITY

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

QANIN MIJI 14

Advertisement  Ina matuqar ba da hakuri wa masoyana masu bin littafin JININANE hakuri saboda tsaikon da aka samu…

QANIN MIJI 12

Advertisement 12 Cikin zaro idanu tare da dafe qirji  Fareedah tace “what”? Shi ko gogan naku yalwataccen murmushi…