ABBAS CHAPTER 22 THEND KARSHE

Advertisement

ABBAS

CHAPTER 22. THEND KARSHE

Ganin kamar zata 6ata mai lokaci ne sai yayi hanzarin wucewa da kansa ya za6o mata doguwar riga da hijab.

Da taimakon sa ta sanya kayan a jikin ta tare da rufawa kanta hijab ‘din still tana zubda hawaye suka fita zuwa clinic dake cikin barrack ‘din nasu.

Daya ke ma koda wani lokaci kaje suna aiki basa yankewa so ba tare da wata damuwa ba suka isa ga babban Doctor ‘din dake kan aiki a lokacin.

Abbas da kansa ya yiwa Doctor bayanin abinda ya kawo su Teemah kam sai hawaye take tana faman rarraba musu idanu daga gefe.

Wata nurse likitan ya ‘kira yayi mata bayanin abinda zatayi sannan ya ha’da su da Teemah suka je ta ‘dibi jinin ta sannan ta bata wani ‘dan k’aramin abu tasa ta yin fitsari a ciki.

Teemah kam duk da tana cikin wani yanayi na tsananin damuwa amma hakan bai hanata ta6e baki da ” mitar wai banda ‘kazanta to me ze sa ta haka, a hakan ne wai Yayah zai ce itama ta zama likita” sake kallon robar tayi tana sake jinjina rashin kunya da ‘kazanta irin ta likita.

Zuwa tayi ta mi’ka ma Nurse ‘din tana sake kallon ‘kwayar idanun ta amma sai taga bata wani nuna komai ba ta kar6a ta wuce laboratory da shi, bin bayan ta Teemah tayi da idanu har ta 6acewa ganin ta, ita kam wurin tap taje ta ringa dirzan hannun ta kamar zata sille shi sai da ta tabbatar ya wanku tas sannan ta bari ta koma office inda ta baro shi.

Zaune ta same shi shika’dai yana amsa waya ga dukkan alamu Doctor ‘din ma ya fita ne.
A hankali ta ‘karasa jikin sa ta zauna tayi luf, sai da ya kammala da wayar kafin ya tambaye ta har an gama ne kai ta ‘daga masa tare da fa’din ” Yayah wurin ma zafi yake min sosai”
Tayi maganar tare da nuna masa gurbin da aka ja jinin.
Hannu Abbas ya kai yana shafa mata a hankali yace ” Vry sorry…zai daina zafin ai kinji”
Cikin sakalci da marairaita ta d’age kanta sama tare da fa’din ” har da fitsarina fa ta kar6a Yayah”.
Abbas duban fuskar ta yayi sannan ya ce mata ” ba komai ai test za’a yi da shi”.
Sai ya kai hannu jikin ta ya ta6a yanayin zafin jikin sannan ya ‘kara da fa’din ” har yanzu cikin na miki motsin ne?”
Teemah sai tace ” Ah’ah…….ya daina amma Yayah ni tsoro nake ji”

Taran ta yayi da fa’din ” Nima inajin hakan Zahra.. but Doctor yace min ‘kila abin alkhairi ne zai same mu, amma bari dai mu jira ganin result ‘din ko sai muga ko menene?”

Teemah sai ta ‘daga kai alamar “to” tayi luf a jikin sa amma abin sai yana bata mamaki, kasa jurewa tayi sai ‘dago tare da sake fa’din ” Yayah dama akwai alkhairi a cuta ne?”
Abbas sai yayi murmushi sannana yace ” akwai mana Zahra komai ai da irin ‘kaddarar da yake zuwa dashi wani mai kyau wani kuwa akasin haka, inajin tamkar wani gagarumin farin ciki ne zai same ni, i feeel ths in my heart kuma ina fatan hakan ya kasance ki kwanatar da hankalin ki kinji ko insha Allahu ba abin damuwa bane”.

Story continues below


Mai da kanta tayi ta kwantar a jikin san sannan a hankali tace ” Allah yasa hakan ne to amma…. ni tsoro…nake ji Yayah bana son in…….”.
Sai tayi shiru.
Abbas ne ya ‘karasa mata maganar da fa’din ” bakya so ki rasa ni ko?”
Murmushi tayi ta 6oye kanta a ‘kirjinsa tare da tukuikuye hijab d’inta.

Shima Abbas murmushin yayi A saman la66an sa ya furta ” silly girl”. sannan ya kai hannun sa ya sau’ke shi a bayan ta a kunne ya ra’da mata ” babu abinda zai raba mu kinji, sai dai mutuwa insha Allahu”.

Shigowan likita ne yasa Teemah ta bar jikin sa ta zauna amma still kanta na jingine da gefen hannun sa tana wasa da hannayen ta, Doctor ha’kuri ya bawa Abbas na barin sa da yayi shi ka’dai inda Abbas yace dashi ba komai kar ya damu daganan suka ‘dan fara ta6a hira da Doctor ‘din sama-sama.


Sunyi jiran a ‘kalla 30mins kafin result ya fito, a hannun Doctor aka mi’ka result ‘din wanda hakan yasa Abbas zuba masa idanu danjin me ke faruwa, Doctor kuwa yana saka idanun sa kan result ‘din take sai fuskar sa ta fa’da’da da fara’a Abbas kam binsa da idanu kawai yake binsa wanda fara’ar data sau’ka kan fuskar tasa yasa Abbas ‘kaguwa yaji sakamakon dake ciki.

Tsaye likitan ya mi’ke tare da mi’kawa Abbas hannu, Abbas ma mi’kewan yayi sannan ya bashi hannun shima Doctor yana murmushi yace “Congratulations sir”
Abbas bu’de idanu yayi a kansa shima da alamar tambaya tare da fatan Allah ya tabbatar masa da zaton sa.
Juyawa yayi ya kallo Teemah da ke ta binsu da nata idanun ganin kalar game ‘din da suke yi akan result ‘din test ‘din da akayi mata.

Abinda dukkan su kunnuwan su ya jiyo musu shine “…….ur madam is pregnant….”
Daga bakin likitan.

Ba Abbas ba hatta Teemah sai da ta bu’de idanu a kansa tana sake kallon bakin sa daya furta hakan sannan ta dawo da kallon ta kan Abbas cike da mamaki, Abbas kam ido kawai ya waro a kansa da alamar wata tambayar Doctor sai ya lumshe idanu ya kuma bu’dewa alamar tabbatar masa da gaskiyar sa sannan ya ‘dago ‘dayan hannun sa ya mi’kawa Abbas papern result ‘din ya kar6a ya duba.
*Fateema Kabir* ya fara gani a sama daga shi sai
*Positive* idanun sa ya ‘kara sau’ka a kai bayan sunan ta dake saman.

Kan sa ya ‘daga ya kalli likitan yana murmushi duk da yanzu yagama tabbatar da hakan musamman daya tuno ‘dan ‘dagowa da cikin nata yai ga kuma motsin da ta ji wannan kadai ma ansawer ne amma duk da haka sai ya sake tambayar likitan cewa dagaske ne Fateemahn sa ne ‘dauke da ciki?
Tambayar bai yita dan neman amsa ba face tsaban farin cikin daya cika zuciyar sa.

Bai jira jin amsar likitan ba ya juya inda take ya ha’da da Teemahn da papern duk ya rungume su yana juyi da ita yake fa’din
” Zahra ta zaki haifi baby very soon, i’m going to be a father….” Teemah kam kukan farin ciki takeyi wai yau itace da ciki itama zata goyi babyn ta wanda za’a ‘kira da suna nata.

Abbas cigaba yayi da godewa mahalicci kawai a zuciyar sa da wannan babban kyauta da yayi masa, a fili kuwa banda mahaukatan kisses babu abinda yake aika mata.

Doctor kam tuni ya fice daga office ‘din ya basu wuri ganin yanda Abbas ya ‘dimauce da jin labarin.

A kunne ya ra’da mata ” u ar carrying my baby, my little angel, little me ….Zahra am about to become a father….”

Teemah kam kuka take yi da hawaye bata iya cewa komai ba kawai sai ta ‘kara rungume shi a jikin ta ganin har ya fita farin ciki da jin tana ‘dauke da ciki.

Abbas raba ta da jikin sa yayi ya cupping face ‘din ta da hannayen sa idanun sa cikin nata ya matso da kan sa dai-dai nata sannan yace ” Zahra zaki haifa mana baby ko? ashe motsin babyn mu kike ji a cikin ki….baby ne ke yi miki hello a cikin ki”
Teemah ma murmushi take yi hawaye na gangara mata.
Hijab ‘din ta Abbas ya fara ‘dagewa yana fa’din ” let me say hi to my little angel”.

Story continues below


Teemah da sauri tari’ke mai hannun sa tare da jijjiga masa kai tace ” plz Yayah ba anan ba”.

Abbas na jin haka yace ” to let’s go to our house “
yayi maganar tare da ri’ko hannun ta.
 Fita sukayi hannun ta ri’ke a cikin nashi yayin da result ‘din ke ri’ke a ‘dayan hannun ta.

A hanya suka ha’du da doctor sai ya tsaya inda yayiwa Abbas bayanin idan suna so suyi scanning cikin dan sanin sex ‘din baby zasu iya zuwa ranar monday, sannan akwai Anti-natal wanda ya kamata tafara zuwa in d next 3 days.

Godiya sosai Abbas ya yi masa tare da ‘daukan masa al’kawarin kyautar tukuici ta mussaman dan yanzu bai fito da komai ba, doctor kam cewa yayi bakomai ai aikin sa ne, daga nan suka rabu kowa da murmushi akan fuskar sa.

Kallo ‘daya zaka yi masa ka gane yanayin farin cikin da suke ciki, har ya  ‘dauki hanyar gida ya ma manta da cewar sunzo ne da mota Teemah ce ta tuna masa sannan suka koma wurin motar suka shiga yaja su zuwa gida. 

Suna shiga parlour Abbas ya janyo ta zuwa jikin sa ya cire hijab ‘din dake kanta tare da shafo cikin nata har zuwa ‘kasan marar ta yana sake jin tudun da cikin yayi.
   Gajiyan data ce masa tayi ne yasa yaja ta zuwa kan kujera mai zaman mutun biyu suka zauna sannan yaci gaba da shafa cikin a hankali ba tare da ya furta komai ba.
     Teemah kam murmushin jin da’di take yi tana tunanin wai yau itace da ciki itama zatayi babyn kanta. 

Abbas duk ya gama  susucewa a wurin yana ta shafa cikin nata ji yake wani zazzafan ‘kaunar abin da ke cikin nata na ratsa shi jijiya har 6argo da gangar jikin sa sai ya lumshe idanu kawai yayi shiru sai yanzu ne yake ganin wautar sa ji yake tamkar ya yi ta marin kansa na wautar da yayi, ace tsawon lokaci ya kasa gane cewa ajiyar sa na jikin ta, ya kasa gane gagarumar kyautar da Allah yayi masa ne ya canja ta ya kuma canza mata rayuwa gaba ‘daya, ya sanya ta zama chop-chop, sam tunanin sa bai bashi hakan ba da farko.
Duk kuwa da yasan cewa ba halin ta ba ne yawan cin abinci amma ya rasa mai yasa tunanin sa bai ta6a basa cewa zata ‘dau ciki a wannan ‘dan ‘kan’kanin lokacin ba da auren su, shi bai ta6a kawo hakan ba, bai ma ta6a saka hakan a cikin tunanin sa ba ya rasa mai dauke hankalin sa da har ya kasa gane cewa cikin sa ne ya hana ta ganin period ‘din ta ma gaba ‘daya duk da kuwa alamomi da suka bayyana kansu amma shi sam tunanin sa da hankalin sa sai ya karakata izuwa wani abu daban, har ya tsaya yana yi mata ihun tana damunsa da neman abin da tasan bazai samu ba, da yasan hakane da ko da wasa ba zai ta6a yi mata masifa ba akai, daya san hakane da ko a ina abin yake zai je ya nemo mata shi da kansa, ashe bai sani ba already Allah yayi masa kyauta gagaruma sanyin idaniya mai sanya farin ciki a zu’kata, haushin kansa ma yake ji yanzun musamman daya sake tuna janta da yayi har zuwa katsina inda tun acan ya kamata ya gano hakan amma ya kasa ganewa,
gaba ‘daya sai ya tattara laifin komai ya aza shi a kansa yanajin kansa tamkar wani mai laifi.

Kan fuskar ta ya dawo da hannun sa ‘daya yana shafa lallausan fuskar ta da hannun sa a hankali suna kallon juna, yayin da ya kamo hannun ta a ‘daya hannun sa in a slow but romantic voice yace ” ki yafe min kinji, kiyafe min duk abubuwan da nayi miki a baya, ban ta6a tunanin ciki bane ke saki wasu abubuwan, ban ta6a kawo cewar zaki iya ‘daukan ciki bane a wannan lokacin shiyasa ma hankalina sam bai ta6a zuwa wajen ba, Zahra inajin kamar nafi kowa laifi a duniya na yadda na kasa gane cewa Allah ya bani kyauta ta musamman 6oye a jikin ki, bansan mai zan fa’da ki gane ba amma plz ki yafe min kinji………”

Bakin sa Teemah ta rufe da nata bakin, abinda bata ta6a yi masa da kanta ba kenan iya zaman su da shi.
A hankali ta ringa kissing ‘din shi slowly Abbas kam mutuwar zaune yayi yama kasa mai da mata martani tsabar yanda ta tafi da imani da tunanin sa, tsawon mintina uku kafin ta saki bakin nasa ta koma kallon idanun shi lumshe ido tayi sannan ta jijjiga  masa kai.

Abbas rungume ta yayi sosai a jikin sa take kuma ya k’ara cire ta ya kama kafa’dun ta tare da matso da fuskar sa saitin nata hancin su na gugan na juna ya furta ” i luv u, i luv u Zahra with all my heart, i luv u my baby mama”

Story continues below


Itama a hankali ta furta ” i luv u more Yayah plz don’t ever leave me” 

Abbas jiyake tamkar ya ha’diye ta dan so, jiyake duk duniya tamkar yafi kowa sa’a da samun ta a rayuwar sa, duk da irin shirmen ta amma dai-dai da rana ‘daya bai ta6a jin son ta ya ragu masa ba ko kuma wani abu makamancin hakan, bai ta6a ‘kosawa ko dama sanin kasancewa da ita ba, yau gashi zata haifa masa baby, jiyake babu abinda ya kai masa hakan farin ciki.

Bai bata amsa ba sai kawai ya ha’de bakin su tare da kaiwa hannu ya bu’de zif ‘din doguwar rigar dake jikin ta ya sa6ule zuwa ‘kasa.

Sai da ya gama rikitata da mahaukatan kisses masu zafi sannan ya gangara har zuwa wuyan ta yana ‘ko’karin sau’kar da bakin sa zuwa ‘kirjin ta ta ‘dan saki kukan shagwa6a tare da furta ” Yayah plz…..”
“Shhiiiiii”
ya ce da ita tare da ‘daukan ta zuwa cikin bedroom.


*****
*Bayan kwana uku*
Abbas da kansa ya raka ta Anti-natal a clinic ‘din, inda anan ne aka gano cewa cikin nata har yakai tsawon wata hu’du da ‘yan kwanaki akai. 

Wannan labarin har sai da ya zame masa tamkar shine karo na farko daya ta6a jin labari mai kyau na farin ciki a rayuwar sa, musamman da ya fahimci cewa cikin ya samu ne tun a farkon satin auren su sosai hakan ya faranta ransa, lallai babu wanda ya kai mahalicci iya kyauta ta farin ciki, in bashi ba waye zai iya yi maka irin wannan kyautar ace tsawon lokaci yana tare da abin farin ciki amma bai sani ba, ina ma, ina ma, jiyake tamkar abin ya koma baya ko dan ya nuna mata kulawar da har sai taji kanta tamkar tafi kowacce mace a duniyan nan, kulan da sai taji cewa sosai tayi sa’an samun miji mai son ta da kaunar ta, ‘kaunar da shi kansa bai san da yaushe ya fara shi ba, tsintan kansa kawai yayi dumu-dumu cikin soyayyar ta tun ma kafin yasan miye so ‘din shikan sa balle ita da a lokacin banda shirme da tsokana babu abinda ta iya.
     Yanzu kam yasan cewa ‘kaunar su daga Allah ne, tunda gashi Allah da kansa ya adana masa ita duk kuwa da cewa ta auri wani miji amma sai ya killace masa komai nata ya kuma bashi ita a lokacin da baya zato batare da ya ‘daga hankalin sa ba, ‘karshe gashi yanzu ya azurta shi da samun kyautar d’a sukutum, ha’ki’ka Allah ne ka’dai abin bauta domin bashi da tamka koda wasa.

Abbas bai damu yaji sex ‘din babyn ba dan cewa yayi koma menene Allah ya bashi ya gode koma menene yana son abinshi, so ba shi da matsala da wannan Teemah ma bata ‘daga hankalin ta ba tabi ra’ayin sa har suka gama suka dawo gida wani lokaci ita kanta tana mamaki yanda yake yi ‘din tamkar wanda ya shekara ashirin da aure bai haihu ba,  irin yanda yake treating ‘din ta abin har yana ‘daure mata kai, yanzu ne ta gane ashe son babyn da take yi nata shirme akan nasa, kawai ya 6oye a zuciyar sa ne tsakanin sa da Allahn sa, idan ta bayyana nata kuma ko ta nuna soyayyar ta ga wasu ‘ya’yan sai yace da ita ta haifi nata mana sam a lokacin bata san cewa har da kansa yake wa baran babyn ba.

She is totally speechless lokacin da yazo ya sanar da ita cewa ya kar6i hutu har na tsawon 2wks kawai dan ya kula da ita da baby, sosai ta girmama wannan soyayyar dan acewar sa sai yayi har da wanda suka wuce shi a baya da be yi ba ba. 

Murmushi kawai tayi masa sannan ta ce “Yayah ai rayuwa baya koma wa baya abinda ya wuce ya riga ya wuce kuma ma ai a rashin sani ne yasa har ya wuce ‘din ba tare da mun lura ba so ba kawai sai mu godewa Allah ba daya bayyana mana a yanzu kuma muna cikin rayayyu duk kan mu” 

Abbas sai yace ” Na sani Zahra nasan hakan kuma nagode wa Allah ina kan yi kuma har kullum, amma idan ba ba’kin ciki zaki min dan kar na bawa family na kulawa ba plz leave me, i’m just trying naga na yi dukkan duties ‘din dake kaina” 

Murmushi tayi ka’dan tace “me yasa zanyi ba’kin ciki Yayah, kawai dai naga ne kamar hutun da ka kar6a ‘din bashi da wani amfani” 

“Ke kike ganin haka ai, amma ni na san akwai amfani sosai”
Yayi maganar yana cire rigar dake jikin sa.
Tasowa tayi ta fara taya shi rage rage kayan, sannan ta budi baki da niyyar sake yin magana ya tare ta da fa’din ” ya isa plz Zahra babu ruwan ki”
Sannan ya matsa daga gabanta ya ja gefe yaci gaba da rage kayan sa, tamkar wani ‘karamin yaro ya ‘kara sa da fa’din 
” ke dama ai ba’a yi miki gwanin ta”
‘Kasa-kasa yayi maganar amma da yake suna kusa da juna sai taji shi, sosai ya bata dariya amma sai ta gumtse ta dafe baki with smile on her face tace   ” Yayah ni d’in” 

Story continues below


‘Dan karamin tsaki yaja yace ” Zahra let me be plz, i’m here 4 my baby tunda ke bakya bu’katata baki son ki ringa gani na kusa da ke i know my little me want to, so leave me alone plz”
Yana gama maganar ya lumshe idanu.
Shiru Teemah tayi kawai tana kallon sa ganin kamar ya d’an d’au zafi kan maganar sai taji babu da’di har a ranta.

Ta kowa tayi a hankali zuwa inda yake ta kai Hannun ta cikin hannun rigar dake jikinsa da yake har yanzu yana kan 6alla bottles ne bai gama ba, a hankali ta tafara bin hannun a hankali tana masa tafiyar tsutsa tare da kwantar da kanta gefen kafad’ar sa sa tace “am really sorry Yayah i didn’t mean to…” 

Abbas kasa jure fushin yayi shima yakai hannun sa kan cikin ta ya shafo cikin yace 
” Little me ur Mummy is so sturbborn na kusan in zane ta a gidan nan” 

Sosai yanda yayin ya sata dariya domin idan ka ganshi zakayi zaton ko dagaske da mutun yake maganar, amma bata yi dariyar ba sai tayi murmushi kawai tace ” Yayah ai nace sorry ko? kuma in ka zane ni nima akan babyn zan rama”.
Itama tayi maganar cikin tsantsar shagwa6a, sai yanzun ya kalleta sai ta turo baki baki, he just knocked her head a hankali yana murmushi yace 
” silly mummy…kina ta6a min baby zaki biyani abuna right there” 

Murmushi tayi itama tare da sunkuyar da kanta ‘kasa.
Rigar ta Abbas ya fara ‘dagewa kawai ba tare da shima ya sake magana ba. 

Teemah bata hana shi ba har ya cire rigar duka ya saura mata sauran bra kawai, hannu Abbas ya kai ya shafo boobs ‘din ta dake cike fam cikin bra ‘din kamar zasu fashe.
Sai da ya kai hannu bayan ta kafin yace ” ki daina saka wannan abin plz ke bakya jin yana damunki ne?” 

Shiru tayi masa kawai ta lafe a jikinsa, sai ya 6alle bra ‘din daga bayan ta sannan ya dawo da hannun sa ta gaba da niyyan zarewa sai ta ri’ke mai hannun ” Zaki fara ko?”
Ya fa’da yana kallon cikin idanun ta sai ta ‘dana baki gaba ta fara k’if-‘kif da idanu. 

Share ta yayi kawai ya zame bra ‘din daga jikin ta sai ya tsaya kallon boobs ‘din nata sosai suke matu’kar tafiya da imanin sa. 

A hankali ya kai hannun sa ya shafo su take Teemah sai ta lumshe idanu jin yanda torches ‘din hannun nasa ya bata wani electric sparks har ‘kwa’kwalwan ta. 

Bakinsu ya ha’de ya bata lafiyayyan kiss tsawon mintina yana sake shafo ta, daga bakin ta ya sau’kar da kansa zuwa wuyan ta yana cigaba da kissing ‘din ko’ina ya ci karo da shi har zuwa wuyanta daga nan ya sau’kar da kansa a ‘kirjinta.
Ajiyan zuciya ta sau’ke tare da rintse idanun ta da k’arfi tana feeling yanda yake sucking boobs ‘din tan cikin gwanancewa.

Sosai ya tafiyar da ita a wannan lokacin har sai da ya tabbatar cewa ya cika rayuwa da zuciyar ta fam ta yanda babu wanda zai ‘kara samun space acikin zuciyar ta daga shi babu kowa a sannan ya bar ta batare da ya kusance ta ba amma, wanda shi kansa hakan da yayi ba ‘karamin samawa kansa sukuni yayi ba. 

  
Yanda Abbas yake yi mata a kwanakin abin har mamaki yake bata na yanda yake kula da ita da dukkan damuwar ta, har sai daya sanya wani sha’kuwa na fitan hankali ya shiga tsakanin su fiye da zaton mai karatu.

Teemah yanzu bata ko jin nauyin sa balle mitan zai ga jikin ta domin shine ke yi mata komai da kansa ciki kuwa har da wanka, shafa mai, drying na gashin ta da sauran su, wani lokaci kuma haka zata zauna susa hannayen su kan cikin suna jin motsin shi, wani sa’in ma ba motsin yake ba amma basa gajiya da shafa cikin koda wani lokaci wai suna jin lafiyar babyn.

Abbas idan yakai hannu yaji babyn na motsi rintse idanu kawai ya keyi ya ringa yiwa mahalicci tasbihi yana jin wani sabon connection tsakanin sa da cikin a koda yaushe.

Wai yau shine da baby wanda zai yi bearing sunan sa a ko ina. 

Sosai Abbas ke yin hidima da su cikin hutun daya kar6a ‘din Teemah kanta sai da ta jinjina masa ta kuma jinjinawa irin na shi salon, yanda yake son haihuwa ashe ma har ya fita son baby dan tasan duk wannan abin yanayi ne dan babyn sa ba wai dan ita ba.
    Girki ne dai ta’ki barin sa yanayi domin itama dagewa tayi tace bazai tayata wannan ba, amma a haka zasu shiga kitchen ‘din tare duk da ‘kin da ta keyi amma Abbas dole sai ya tayata wani abin kafin girkin ya kammala.

Story continues below


Ko yau ma hakane tare suka shiga kitchen sukayi tomato sauce da farin doya tace ita shi take so taci shine sukayi sai ya ha’da mata fruits salad suka kai dinning, da suka kammala komai suka zo wurin cin abincin kuwa sai da ya sha drama da ita daya ce shi zai yi feeding ‘din ta sai tace babu ruwan ta ita da kanta zataci, dan yanda take matu’kar sha’awan abincin bata jin in shi zai bata kamar zai gamshe ta, Abbas ma ‘kin yadda yayi yace shima bai yadda ba dole shi zai yi feeding ‘din su, Teemah sai tace ” Allah ni fah Yayah da kaina zanci”
Rage murya tayi ‘kasa-‘kasa tace ” abinda ma ba dan ni kake yin hakan ba ai na san da baby ne”
Sai ta kauda kanta gefe. 

Abbas kam dariya ma ta bashi ganin yanda ta ha’de ranta sai yayi murmushin gefen baki yace ” jealousy mummy…..ke dai kinji kunya, a duk fa’din duniya naki salon yasha bambam dana kowa “
Sai ya saki murmushi mai sauti sannan ya ce ” yau ga Mummy na kishi da unborn a gidan nan abin mamaki” 

Ganin ta juyar da kanta gefe ne yasa shi sake ‘debo abincin ya nufo ta dashi sai tayi saurin matsar da kanta baya.
“Allah idan kika haifa min baby as stubborn as u ko….hmm…zaki sha mamakin abinda zan miki…., bansan me yasa bakya ji ba sam, inajin sai na fara zane ki tukunna kafin ki daina”
  
Bata kula shi ba kawai sai ta sa hannu tafara cin abincin ta hankali tana satan kallon shi.
   Abbas kam baya yayi ya jinginu da jikin kujera yana kallon yanda take cin abincin a nutse. 

Sosai yarinyar ke bashi dariya bai san ranar da yarinta zata barta ba wani 6arin zuciyar sa ne yace masa ” may be idan ta haihu” Murmushi kawai yake saki a fili yana tunanin wai nan da 1yr shima gidan shi ya ‘karu ya zama mai familyn kansa.
A cikin ransa yace
“Hmm… i can’t wait to see that day, Allah ka nuna min wannan ranar ina cikin masu numfashi” 
     Sai ya lumshe idanu ya bu’de su tare da sau’kewa a kan ta suna ha’da ido da ita sai yace 
” Baby mama”!
Da sigar zolaya kuma cike da fara’a yayi maganar sai tayi saurin ‘dauke kanta batare da ta tanka sa ba.
A cikin ranta tace ” ni ba ruwanka da ni” 
Abbas ma be kulata ba kawai ya zuba mata idanu.
Teemah kamar da wasa tayi maganar kuma sai shai’dan ya ingiza mata maganar har a zuciyar ta yayi tasiri gani take wai dagaske dan babyn sa ne kawai yake kula da ita ba komai ba.

Tana gama cin abincin sai ta d’auki fruits salad ‘din ta mi’ke tsaye da nufin  barin wajen tana wani huhhura hanci,  sai yanzu Abbas ya fahimci fushin nata na gaske ne bana wasa ba.
Da sauri yabi bayan ta da idanu tsinkayan muryar shi tayi yana fa’din ”  stop there Zahra”
Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba sai ta kalli glass bowl na fruits salad ‘din dake hannun ta sannan ta maida idanun ta gaban ta kawai tayi shiru, tsawon mintina biyu tana a haka, bataji yasake magana ba, kamar yadda bai taso yazo inda take ba balle taji dalilin ‘kiran haka itama kuma bata waiga taje ta same shi ba, ganin kamar zai 6ata mata lokaci ne yasa ta ‘dan yi ‘ko’karin ‘daga ‘kafa da niyyar shigewa abinta sai taji yace ” one step nd i ll slap u”
Cak ta tsaya sannan ta juyo ta kalle shi jin yanda yayi maganar kamar da 6acin rai, sam bata ‘kaunar 6acin ransa ita balle har ta iya juran hukuncin sa, tun lokacin da yayi mata na farko bata fatab ganin ta sake 6ata ransa koka’dan. 

Da idanu yayi mata nuni da kujerar data tashin nufin sa ta dawo.
Teemah kam tuni har ta fara sau’ke hawaye haka ba dan taso ba ta dawo ta zauna tana mai share hawaye. 

Kanta a ‘kasa hawayen nata na ci gaba da sau’ka tana aikin sharewa Abbas kam ko ‘kala bece da ita ba kawai ya zuba mata idanu ya kasa tuno abin da ya sata fushin ma gaba ‘daya. 


Teemah kuwa jin be kulata ba ya sanya ta ‘daga kai ta kalleshi fuskarta cike da hawayen sai suka ha’da idanu take sai ta tashi da sauri ta dawo 6angaren daya ke ‘din ta rungume shi ta baya sannan ta saki kukan mai sauti.

Sosai ta bawa Abbas tausayi musamman yanda tayi abin tamkar ‘yar yarinya ‘karama wacce tayiwa mahaifiyar ta laifi.
Badan kuka takeyi ba da babu abinda zai hana shi yi mata dariya amma sai ya basar kawai ya yi ‘ko’karin dawo da ita ta gaban sa sai ta no’ke kanta a arms ‘din sa tana sake yin kukan. 

Story continues below


Lallashin ta yafara cikin hankali amma sai ta ‘ki daina kukan har se da ya daka mata tsawan “nace ya isa ko?”
    Kafin tayi shiru.
Bai sake magana ba sai da yaga ta nutsu tana sau’ke numfashi sannan ya ‘dago kanta yace ” me ya faru ne wai ?”
Cikin shagwa6a tace ” ba kai bane”
Abbas da mamaki yace ” Ni kuma Zahra yau kuma me nayi?” 

Sai ta tura baki tace ” ai baka so na kullum sai baby kake so”
“Shine kike kishi da babyn ?”
Shiru tayi kawai ta kalleshi cikin idanu sannan ta kawar da kanta.
  Abbas sai yaja kumatun ta da duka hannayen sa biyu sannan yace ” ‘yar ‘kauye da babyn naki kike kishi? Ke da zaki rin’ka goya babyn kullum kina bashi mama kina yi masa wanka miye abin kishi kuma?”
Wasa kawai takeyi da hannayen ta kanta na kallon ‘kasa.
  Sai yake fa’din “…owk..nagane…nima kina so idan lokacin yayi nayi kishin ko?” 

Sai ta jijjiga masa kanta alamar ah ah.
Yace ” zanyi mana, ai ni ya kamata ma nayi kishi dan baby zai kar6e min abuna dayawa dake wajen ki, kinga zai ‘dauke min hankalin ki ki nasan da ‘kyar ne ma idan baki daina kulawa dani ba, zaki iya daina tayani wanka, zai kar6e min abinda nafi so ma a jikinki kinga ai dole zanyi kishi” 

‘Daga kai tayi ta kalleshi da zararren ido alamar tambaya sai yayi mata nuni da boobs ‘din ta da idanun sa itama sai tabi wurin da kallo take sai ta gane mai yake nufi sai yaci gaba da fa’din ” abin tausayi zan zama may be ma ki daina bani abinci kin ga ai ni ya kamata nayi kishi ko? sai dai kinsan wani abu?”
Kai ta jijjiga masa sai yaci gaba da fa’din “amma kuma ni bazan yi kishin ba saboda nasan lokacin sa ne kuma zai wuce idan yayi wayo ma shikenan ni ‘din ne kuma za’a dawo ma wa domin ni ‘din special ne kuma na har abada……kamar yadda kike a cikin rayuwata, in banda shirmen ki ma a ina kika taba jin anso baby an ‘ki uwar da babyn ke jikin ta ke baki san albarkacin ki babyn yaci bane ma har nake kula dashi…….” 

Da irin wa’dan nan kalaman yayi ta lalla6a ta har ta ha’kura inda yace mata gobe zasu fita saloon. 

Kafin dare ta gama sakewa ta bar fushin gaba ‘daya Abbas kuwa koda suka je bacci sai da yayi ta faman tsokanan ta wai ” Jealousy Mummy  towards unborn”
Da ‘kyar ta samu ya bar ta tayi bacci har sai data zaune shi gaba ‘daya ta hau jikinsa ta ‘dane tare da ha’de bakin su kafin ta samu ya yi shiru a haka har bacci ya ‘dauke ta da hannnun ta kan dimples ‘dinsa, daga baya ne ya gyara mata kwanciyar ta.


*****
Washe gari ya kama ranar monday, Abbas da azumi ya tashi ranar dayake yana na nafila monday da thursday, 11:00am suka isa wajen saloon ‘din inda suka samu ma ba wasu mutane sosai, kitso yace ayi mata koma wani iri ne amma yace  banda ‘kari yace ayi mata haka da gashin ta kawai.

Teemah kam shiru kawai tashi amma tasan zata sha azaba domin rabon kanta da kitso tun kafin auren ta da Abbas tun da ta aure shi kuwa bata sake yin kitso ba har yau. 

Abbas a waje ya koma cikin mota yana jiran a gama mata su wuce. 

Minti sha biyar bai cika ba a wurin wata yarinya dake aiki a wurin madam ‘din tazo tayi ‘kiran sa.

Fita yayi da mamaki yabi bayan ta inda suka koma cikin shop ‘din, yana sa kai ciki sai kuwa  idanun sa ya sau’ka kan Teemah dake kuka da hawaye hannun ta ‘daya akan tana bin hannun mai kitson, tun fitar shi basuyi ko ‘daya ba tsagu kawai akayi Teemah ta tsaya rigima wanda hakan ne yasa madam ta aika a ‘kirashi. 

Cikin sassarfa ya ‘karaso gaban ta ya tsugunna ya ‘dan ha’de rai yace ” kuka kuma Zahra kitson da zafi ne?” 

Sai tayi saurin ‘dage kai wani sabon hawayen na sake sau’ko mata.
Da rawar murya tace ” Kace….mata ta dai….na yi min mai zafi…. to”.
” Naji shikenan to share hawayen ki wani iri kike so ayi miki?”
Ya tambaya yana share mata hawayen.
“Chukwun ibra zata yi min amma zafi yake min sosai ni bana so”. 

Da kansa ya sake za6a mata wani kitson kalba yace ayi mata shi ‘din ‘kila ba zaiyi mata zafi ba daga nan yafita ya bar su.

Sun kai 1hr suna kitson kafin suka kammala ta fito idon ta jajur da ‘dan kwalin ta a hannu ta fito veil ne kawai ta bari akan nata ko kunya bata ji tasha kukan kitso da girman ta.

Story continues below


Abbas ne ya koma ya biya balance sannan ya dawo cikin motan ya so suje yawo amma ganin ta kamar ba’a nitse ba yasa kawai ya maida ta gida.

Suna isa barrack gaban block ‘din su yayi parking Teemah fita tayi ta shige ciki da sauri. 

Abbas kuwa ganin Sam abokin sa ne yasa shi tsayuwa a wurin sa dan su gaisa. 

Tana shiga ciki ta zame veil ‘din tare da cire pencil skirt ‘din dake jikinta ya rage mata ‘dan guntun wandon skinny wanda yake iya gwiwa da rigar ‘dinkin 3quarter atamfar ta bari kawai ajikin ta.

Bedroom ta shige domin ajiye kayan sannan ta wuce wurin mirror ta na kallon kitson. 

Duk da bawani style mai kyau bane amma ita kanta tasan ta canja sosai goshin ta ya fito har iska takeji yana shigan ta. 

Tana tsaye gaban madubin tajiyo muryar sa yana ‘kiran ta sai ta fito a hankali tamkar bata son yin tafiyar ta nufo shi. 

“Zo inga kitson naki mana kuma”.
Yace da ita yana murmushi sosai ya shirya tsokanan ta a yau ‘din. 

Itama kamar ta sani sai ta shirya dakewa a zuciyar ta dan tasan sai yayi mata dariyar tayi kukan kitso. 

Kusa dashi tazo ta zauna tana wani shan kunu ita a dole zata tsare.

Abbas murmushi yayi yace ” kitson fa nace zan gani kika wani ci magani a can “
Matsowa tayi tare da ‘dora kanta akan cinyar sa ta kwanta sannan tace ” gashi nan ka gani”. 

Murmushi yayi ya shafo kitson yace “gaskiya matar nan ta taimakeki, jibi fah yanda kan naki yayi kyau shine ko kunya baki ji baby na kallon ki kika ringa rusa kukan kitso ko?” 

Baki ta tura gaba sannan tace ” ai wanan ‘din da zafi ne shiyasa”.
Hannun na kan nata yana ta shafa kitson yace
” Ke de kice baki so kawai amma miye abin kuka a kitso”. 

“Allah Yayah da zafi ne rabona da kitso fah tun kafin auren ka”.
Da mamaki ya tambayeta
“Aure na kika ce ? to ke kuma fa banda ke ko?
‘Kasa-‘kasa tace ” har da ni mana”
Abbas sai yace
” to tun kafin auren mu zakice not me alone…….kinje kina ta kukan fisabilillahi yanzu idan kika haifi baby girl kuma zakiyi mata kitson ko ?….ni kam idan kika dukar min baby akan kitso ni da kene a gidannan….ai na riga naga sirrin”

Shiru tayi masa itama tana tunani bata yi magana ba har bacci ya yi gaba da ita.

Da yamma ta shirya masa ‘kyataccen girki na gaban kwatance sosai kuwa yaji da’din hakan inda ya ringa saka mata albarka yanaci yana yaba mata.

Teemah bata tashi sanin tsananin son kitso da Abbas keyi ba sai da sukaje bacci yanda yarin ga yabon kitson yana shafo wa abin har mamaki yaso bata, dan tunda suke dashi bai ta6a nuna mata yana son kitso ba ko yanzun ma tasan ya kaita kitson ne dan yawan ‘kai’kayin da kan ke mata kuma wai dan kar tsefaffen gashin ya ringa damun ta.
Amma ba wai dan ra’ayin kansa ba.

Sosai take jinjina wa miskilancin sa a hakan ma ita bai fiya yi mata ba sosai yake sake mata fuska har take sanin wasu abubuwan sa, in kana son ganin asalin halin sa to ka tsince shi cikin uniform kaki a lokacin ne zaka tabbatar da ko shi waye amma banda cikin gidan sa.

Duk kuwa wannan abinda ke faruwa Abbas be sanar da kowa ba, ko su Ummah be iya ‘kira ya sanar dasu ba, ya dai sanar da Leesah inda tayi matu’kar farin ciki ta taya shi murna, Teemah kuwa wa  Maman Amal ka’dai ta sanar mawa. 

Tanas o ta bawa wani daga cikin dangin ta labarin abin farin cikin daya same ta amma ta kasa gaba ‘daya kunya ya ishe ta ganin shi da yake namiji ma bai fa’da ba sai ita toh ta ina ma zata fara.

Watarana da suna waya da Anty sai tayi tunanin sanar da ita don tasan yanzun Anty ta canza ba kamar da bane, bayan sun gama gaisuwa da ‘kyar Teemah ta harha’da kalaman tace 
“Anty ba…. da cikina na motsi ba sai mukaje wurin Doctor Yace mana…wai….wai….”
Sai ta kasa cigaba da maganar nauyin kalmar take ji.

Antyn ne ta ‘karasa mata da fa’din ” wai Fateemah na is about to become a mother ko?” 

Kunya taji sosai sai kawai ta kashe wayar tana murmushi jin Anty ta ‘dago ta da wuri.

Tun daga ranar kuwa Anty kullum sai ta ‘kirata taji lafiyar su ita da babyn, Anty ma ba ta sanar da kowa ba illah Abbah shima sosai yayi farin ciki zaton Anty duk sauran ma na da labari shiyasa tayi shiru kawai batayi maganar da su ba.

Hannah Teemah take so ta sanar mawa saboda itace ‘yar uwa kuma ‘kawar shawara da amana amma tsoron tsokanan Hannah take yi kuma tana jin kunya dan tasan Hannah zata iya sanar da Ummah, ita kuwa bata son hakan. 

Har watan ramadan yazo suka azumci watan a Ports ba suje Rivers ba, bayan sallah ne yaso suje gida amma sai ya fasa kawai suka yi zaman su, bai ma yiwa Teemah maganan ba dan yasan halin rigiman ta idan taji ‘kila tace masa dole sai sunje ‘din shi kuwa be so ta bar shi shi ka’dai anan.

A haka har zancen ya wuce bata da labari, suna waya da kowa da kowa ciki kuwa har da Mummy itan ce ma some time take tambayan ta wai babu wata matsala ko, ko kuma tace ya jikin ta, Teemah kam sai ta ce ” ni lafiya ta ‘kalau Mummy”
Murmushi kawai Mummyn keyi bata ‘kara wata magana.
Sai dai su canja hirar tasu.

Sosai Teemah tayi sa’a dan cikin ta ba mai yawan laulayi bane, amai ma ba kullum takeyi ba sai lokaci-lokaci, wani sa’in ma tana kaiwa sati guda ma batare da tayi aman ba, haka bata yawu sam-sam bata ma san mai ciki nada wannan problem ‘din ba, some times sai sunje wurin Anti-natal sannan take ganin wasu abubuwan agun mata masu cikin, bata komai sai dai tana yawan yin fitsari da kuma ciwon kai ka’dan-ka’dan. 

Kitso kuwa tunda ta fahimci yana birge Abbas sai take ‘ko’karin daurewa tana zuwa ayi mata duk bayan 2wks kuma ba laifi domin kwalliya tana biyan ku’din sabulu dan kuwa Abbas na ‘ko’karin yaba mata a fili kuma tana jin da’din hakan.

Wasa-wasa har cikin Teemah ya kai 6months su Hannah basu da labari, zuwa lokacin kuwa cikin ya fito 6ul abinsa inda kallo ‘daya zaka mata ka fahimci cewa ta shiga sahun masu ciki, sai ta ‘kara yin kyau abinta, hancin ta ne ka’dai ya ‘dan kara girma ka d’an a fuskarta baya ga haka babu komai sai ma wani fresh da tayi, kuma yanzu tarage yawan cin abinci ba kamar da ba yanzu tafi cin kayan itatuwa ne kawai.

Abbas ma bai fiya barin ta tana shan za’ki ba saboda an gaya masa cewa hakan nada illah musamman ga mai ciki irin ta. 

Koda ya koma office kuwa baya yin cikakken 1hr ba tare da ya ‘kira yaji lafiyar ta ba. 

Matan blocks ‘din su ma na nan-nan da ita musamman saboda karamcin Abbas a wurin su.
Bata aikin komai sai yi masa girki, duk kuwa da cewa tana son yi ‘din amma Abbas hana ta yin komai yake yi sai dai wani lokacin ta saci jiki tayi idan taga baya nan.
Amma da kansa yake yin komai a gidan. 

Matan block ‘din su ma da yake yawancin su manyan mata ne so sai suke tausayin ta da ganin ‘kan’kantar ta, su kansu duk ranar da sukayi katari da ita ta ‘dauki tsintsiya hana ta suke yi. 

Cikin ta na da wata bakwai sannan ta sanar da Hannah a chat dan sosai zuciyar ta ta kasa daure rashin sanar da Hannah labarin cikin, duk iya ‘ko’karin da ya kamata tayi amma ranta yakasa sakewa, inda suna cikin chat tace da ita ” Hajiya ki fara shirin raino fa dan Matar Yayah nada ciki har na tsawon wata bakwai” 

Hannah kam wasa ta ‘dauki abin dan haka sai itama tace ” wacce matar Yayahn kenan kike magana? Kinsan ai ni bansan ya ‘kara yin aure ba”. 

Teemah bata ba ta amsa ba sai kawai ta ‘kirata video call tana murmushi ta nuna mata cikin. 

Hannah mamaki, murna da farin ciki gaba ‘daya sai suka hanata magana ta bu’de baki kawai tana kallon ta. Teemah ma kallon t take yi sai dai ita murmushi ne akan fuskar ta mai sanyi. 

Hannah nuna ta tayi tace wai dagaske ciki ne a jikin ki?” 

Teemah cikin ta k’ara nuna mata tace ” ga zahiri kuwa kina gani Hajiya” 

Hannah ihun murna ta sanya tare da tashi ta nufi wurin Ummah tana ‘kwala mata ‘kira. 

Da sauri Teemah ta yanke ‘kiran tare da kashe wayar ma gaba ‘daya tana dariya. 

Taso ta ‘kyale Hannah kawai sai dai taga suprise ‘din baby kamar yanda take ganin take-taken Yayah, amma sai ta kasa jurewa saboda sam bata ga dacewan ace har tana da cikin daya kai ciki amma Hannah bata da labari ba. 

B’angaren Hannah kuwa tana isa wurin Ummah ta dago wayar tana fa’din ” Ummah kalla kiga abin mamaki, Fateemah na da babban ciki tace min har ya kai 7months…..”
Gani tayi Teemah bata kan layi sai ta sake gwadawa amma baya tafiya, ta kira voice call shima akace mata switch up. 

Ummah kuwa gaba ‘daya hankalin ta ta tattara ta mayar kan Hannah jin ta kusan samun jika, ganin Hannah na jan tsaki ne yasa ta tambayar ta ” meya faru?”
Sai Hannah tace ” Wallahi Ummah kinga tayi disconnecting call ‘din kuma na ‘kira baya tafiya”
Ranta duk a jagule tayi maganar ga dukkan alamu bataji da’din hakan ba.
Ummah cewa tayi ” amma kin tabbatar cewa cikin na ajikin ta?”
Sai tace ” Allah dagaske ciki ne Ummah ai ta nuna min kuma tace har 7month……” 

Story continues below


Taranta Ummah tayi da fa’din shikenan naji ‘kira min mijin nata, tunda isheshshe ne shi wato har yayi wayon 6oye min abu irin wannan ko?
‘Kira min shi da sauri zai zo yasame ni ne” 

Hannah ba tayi magana ba sai ta hau ‘kiran nashi wayar amma cikin rashin sa’a sai na shin ma bai tafi ba.
‘Dago wa tayita kalli Ummahn sannan tace ” ba fa na samun sa Ummah shima ‘din” 

“K’yale shi zuwa anjima may be za’a same shi” 

Hannah kam kasa hak’ura tayi ta ringa gwadawa nashi da na Teemah amma gaba d’aya ya ‘ki shiga, abin ya ‘kona ran Hannah sosai jitake tamkar tayi tsuntsuwa ta taho Ports a lokacin kawai dan taga Teemah. 

Teemah kuwa bata sani ba ashe da gangan Abbas ya’ki sanar mawa Ummah gudun kar ta uzzura masa akan ya maida ita gida dan yasan Ummah najin wannan labarin ba barin sa zata yi ya runtsa cikin kwanciyar hankali ba.

Shikuwa yanzun sam baya so yaga yayi nisa da iyalin sa ba ma ya ‘kaunar abinda zai kawo rabuwar koda kuwa menene shi.

Sosai yake so ya cika rayuwar ta da zallan ‘kauna da soyayya.
Hatta hakkin sa da ke kanta daya zama dole ma daina kar6a yayi dan gani yake tamkar abin zai yi mata yawa ne, musamman ma da yake ya san kansa yanda yake galabaitar da ita a duk lokacin daya kusanceta shiyasa ma ya sau’ke mata wannan nauyin, sosai yayi ‘ko’kari wajen ganin ya danne nashi bu’katan, in dai ba ita ta nema ba da kansa kam baya ta6a kusantar ta kuma itama Teemah yanzu da sau’ki ba sosai abin ke motsa mata ba sai tayi sati biyu zuwa uku ma bataji wani abu ya dame ta ba game da hakan, itama kuma bata sanyawa ranta damuwa ba musammn data ga cewa shima baya ra’ayin hakan sai itama take ‘ko’karin binsa akan yadda yake so ‘din duk da bai fito fili ya gaya mata dalilin daya sashi yin hakan ba amma tasan dai ba zai ta6a yin abu dan ya cutar da ita ba.

Har kusan 2hrs Hannah bata gaji da ‘kiran layin sa ba dan yanda ta ‘kagu ta tabbatar da labarin, ga Ummah ma da nata masifan a gefe, da ‘kyar suka same shi a nashi wayan har sai data sau’ke ajiyan zuciya data ji ya shiga, da murnar ta ta mi’kawa Ummah wayan tare da fa’din “yesss ya shiga Ummah”. 

Ummah kar6a tayi da sauri ta sada wayar da kunnan ta da fatan Allah yasa abinda taji daga bakin Hannah ya kasance gaskiya ne. 

Abbas na office yaga ‘kiran Hannah, bai san dalili ba amma haka kawai sai yaji zuciyar sa ta tsinke bawai dan basa waya ko bata ‘kiran sa ba ah’ah, dan ko jiya ma sun gaisa da ita a waya amma haka kawai yau ‘din ya tsinci kansa da fa’duwan gaba ganin ‘kiran ta. 

‘Dauka yayi sannan ya kai kunnan sa, ba halin sa bane fara yin magana idan zaiyi waya matu’kar bada iyayen sa bane amma yau ‘din sai yaji bakin sa ya furta sallama. 

Muryar Ummah yaji ta amsa sallamar tare da fa’din ” Muhammad kaji kunya kai kam” 

Kai Abbas ya sosa duk da bai san laifin sa wurin Ummahn ba da har ta fa’di hakan amma sai yaji shi wani iri sai yace.
” Afuwan Ummah, barka da war haka” Ummah bata bi ta kan gaisuwar tasa ba sai cewa tayi
“Ina ‘yata take?”
Amsa ya bata da fa’din
” tana gida Ummah ni na fita aiki ne”.
Ummah sake cewa tayi
“Ina fatan dai lafiya take?”
Sai yace “Ehh Ummah lafiyar ta ‘kalau”
” to masha Allah, yaushe zaka dawo min da ita gida dan gaskiya banaso ta haihu cikin inyamuran nan?”

Cike da mamaki ya zaro idanu tare fa’din ” haihuwa kuma Ummah? waye ya sanar da ke ciki gare ta?” 

D’an 6ata rai Ummah tayi tace da shi ” Ni bana son shashanci Abbas tambayar ka nayi answer me kawai”. 

Abbas sai ya lumshe idanu tare da shafo kansa sannan yace ” Ummah ki bari watan haihuwar yayi mana sai in kawo ta…”.
Tun ma kafin ya idasa rufe bakin sa Ummah ta tareshi da fa’din ” ban amince sam kama canza shawara” 

Shiru yayi yana jin wani iri a zuciyar sa tare sa tunanin yadda zai 6ullo mata, Ummah kam ganin yayi shirun ne yasa ta fa’din ” ni dai ina jira nan da 2weeks in ga ‘yata a gefe na, in ba haka ba kuwa zaka sha mamaki na Muhammad, domin da kaina zanzo har Rivers ‘din in ‘dauko ta”.
Ummah na gama fa’din haka ta yanke wayar ba tare da ta jira jin na bakin sa ba, dan ma abin ya ha’du mata da farin cikin jin labarin cikin shiyasa ma masifar batayi tsayi ba.
Abbas kam da kallo ya bi wayar tare da mamakin inda Ummah tajiyo wannan labarin, yasan in ba Teemah ba babu wanda zai sanar da ita tunda kam shi babu wanda ya fa’din mawa. 

Story continues below


Lokacin daya koma gida sai ya tarar da ita har tayi masa abinci mai ‘dan sau’ki, tuwon semo tayi da miyar egussi, sosai yake ya bawa ‘ko’karin ta ta wannan fannin, domin shi ka’dai yasan yanda yake ji a duk lokacin daya tarar ta tanadar masa abinci koda kuwa wani iri ne sosai yake appreciating, dan ya fahimci bata wasa da abincin sa musamman data san cewa ba ya cin komai a waje so bata ta6a barin sa ya nemi abinci ya rasa ba, ko da kuwa mai sau’ki tana matu’kar ‘ko’karin yi masa kuma yana yabawa da hakan. 

Haka idan ya dawo a kullum tana ‘ko’karin ganin ta tayashi rage kayan jikin sa, a yana hana ta ma amma dole kullum bata barin sa, hatta wanka da wasu abubuwan idan ya kama duk tana taya shi, shima kuma ba laifi lokaci-lokaci ya kan yi mata massaging ‘kafafuwan ta dan wani sa’in yana ‘dan yin kumburi ka’dan. 

Sai da ya kammala da cin abincin kafin ya dube ta yace da ita ” Ummah ta ‘kirani”.
Teemah na jin haka sai ta zaro idanu waje tana kallansa, take sai ya gane rashin gaskiyar ta sai kuma tace ” me tace maka kuma?” 

Shiru yayi shima ya zuba mata idanu.
Duk da bawai yau ne karo na farko da Ummah ke ‘kiran sa ba, kusan kullum sai sunyi waya da Ummah hatta ita Fateemah ma suna waya dukkan su da ita amma yanzun kallo ‘daya zakayi mata ka fahimci ta shiga wani yanayi da jin ‘kiran Ummah. 
Maimakon ya bata amsar tambayar ta ah ah sai yace da ita 
” mara kunya….ai na lura tunda kika samu cikin nan kika zama mara kunya kuma shine har da sanar da Ummah cewa kinyi ciki ko?” 

Kai ta kawar gefe tace ” Ni fa bance mata ina da ciki ba”.
Sai yace ” To a ina ta samu labari?”
Shiru tayi masa tana ‘kara ha’de goshin ta.
Sai shine yaci gaba da fa’din
” Ni dai let me tell u…idan kika kuskura kika haifamin baby mara kunya ko kuma mara son makaranta ni da kene”.
Hawaye ta fara tare da mi’kewa ta shige cikin bedroom taje ta zauna dirshan a ‘kasan tiles tana zubda hawaye, ji take ranta babu da’di a duk lokacin da Yayah ya ambaci makaranta ko kuma yayi mata gugar zana da hakan, ta so ta yi ‘din kamar yanda ya bu’kata amma sam takasa shigar da shi cikin ranta domin koka’dan babu niyyan a zuciyar ta, shiyasa ma ta ha’kura, amma a kullun addu’ah takeyi Allah ubangiji ya cire masa abin a ransa shima ko zata huta da mitar sa akan hakan. 

Abbas ma tashi yayi biyo bayan ta a ‘dakin yazo ya zauna daga gaban ta ya fuskance ta, bai bi ta kan kukan nata ba illah tambaya da ya jefa mata inda ya sake fa’din ” waye ya sanar da Ummah cewa da ciki a jikinki ai nasan kece kika fa’din mata”.
Ya ‘karasa maganar tare da ‘dage gira ‘daya sama. 

Teemah kam da muryar kuka tace dashi ” Ni dai bani bace sai ko in Hannah”.
Sai yace ” ita Hannah a ina taji labarin ?”
Teemah shiru tayi kawai tayi ‘kasa da kanta wani hawayen na gangarowa, sai shine yaci gaba da fa’din ” ai kema kin san tsakanin Hannah da Ummah dole ne idan taji sai ta gaya mata, gashi yanzu tace wai dole sai dai in maida ki Abuja wai bata son ki haihu a nan” 

Yanayin da ya ‘karasa maganar ma kanaji kasan ransa baya son tafiyar koka’dan, amma sai tayi ‘ko’kari wajen ganin ta ri’ke kukan da take yi tace dashi ” duk ‘daya ne ai Yayah da can da nan ‘din ba wata matsala”. 

Muryar sa da sanyi yace ” kenan kema kinfi son can ‘din ko?”
Itama a hankali tace ” ah’ah fa Yayah ba haka bane….”.
Sai ya tare ta da fadin ” …….haka ne mana, kin fi son ki tafi ki barni ko tausayina bakiji ko?, yanzu fa idan ba kyanan komai ma ni zan rin’ka yi hatta abinci ma babu wanda zai na dafamin……”. 

Bai ma ‘karasa maganar ba ta sanya kuka inda cikin kukan tace ” Yayah to ya zanyi ni kam, Allah inajin tausayin ka amma ai kaga Ummah ce da kanta ta nemi hakan ba yadda zamu yi ne shiyasa”. 

Hannun ta ya kamo cikin nasa hannun yana murza ‘yan yatsun ta cikin natsuwa yace ” kawai kice mata ke ba yanzu zaki koma ba in taji daga bakin ki i’m sure zata ha’kura”. 

Kai Teemah ta jijjiga masa tare da fa’din ” Allah ni kam bazan iya ba Yayah, Ummah ce fa”. 

Shiru yayi yana kallon ta ko da wasa bai son abin da zai raba su, sam baya son tayi nesa da shi amma kwatsam rana tsaka Ummah ke ‘ko’karin shiga tsakanin su, bai san yadda zai yi ba amma gaskiya yana jin tamkar hakkinsa za’a shiga akana hakan, gashi ma tun kafin ranar tazo ya fara shiga wani hali na damuwa. 

Story continues below


Janyo ta yayi jikin sa ya share mata hawayen tare da rungumar ta a jikinsa sannan yace ” kukan fa na menene haka Zahra?, ba kince ba kya son barina ba?”.
Da kai ta bashi amsa akamar “ehh” sai yaci gaba da fa’din ” Kar ki damu kinji, ni duk abinda kike so shi zan miki, so ki kwantar da hankalin ki bana son kukan nan, ko kina son baby yayi miki dariya yace Momcyn shi cry-cry ce?” 

Kai ta jijjiga tana murmushi sai yace ” to oyah wipe all da tears ur husby ll always be by ur side ok…”
Da haka ya rarrashe ta har tayi shiru maganar ta wuce batare da sun tsayar da magana ‘daya ba.

*****
*Bayan sati ‘daya*
Zaune yake akan dadduma yana karatun al’qur’ani mai girma cikin sautin sa mai dad’i inda yake karanto suratul Anbiya’i.
Abbas kenan da hakan ya riga ya zama jinin jikinsa a duk bayan kowacce sallar asubah ya kan zauna yayi karatun sa cikin natsuwa in da watarana suke yi da Fateema wataran kuwa shikad’ai yake abin sa musamman ma yanzu da baccin asubah ke yawan damun ta sanadin cikin. 

Wajaje 5:30am ne na safe, yayin da Teemah ta tashi ta shiga bathroom dan watso ruwa a jikin ta, domin wani yanayi da take jin kanta tunanin ta ko ruwan sanyin zai ‘dan sanyaya mata, da ‘dan ‘karamin towel ‘dinta ta fito ‘daure a jikin ta bayan ta watso ruwan ta fito, a hankali take tafiya, da ‘dan madaidaicin cikin ta a gaba ya ‘dan ‘dago daga cikin towel ‘din, sai hips ‘din ta da ya ‘dan ‘kara bu’duwa shima da mazaunan ta ta yadda bata isa tayi tafiya ba sai sun motsa. 

Duk kuwa da ta watsa ruwan amma koka’dan bata nasaran jin wani sauyi tattare da ita ba na daga cikin yanayin ta data keji sai ma abinda ya k’aru, ta rasa mai yasa hakan yanzun bata sani ba ko dan shi baya neman ta ne yake sata itan oho. 

Zuwa tayi ta zauna a gaban mirror tayi shiru tana kallon sa ta cikin madubin. 

Abbas dake faman karatun sa tamkar ance ya ‘dago sai kuwa suka ha’da idanu ta cikin mirror ‘din, Teemah sai ta lumshe ido ta yi ‘kasa da kanta a hankali. 

Abbas kam tuni ya fahimci yanayin da take ciki da suka ha’de idanu, don tuni ya gama karantar ta zuwa yanzun ba sai ta bu’di baki ta sanar da shi yanayin da take ciki ba da kansa ma yake fahimta. 

Takaita karatun yayi tare da rufe Qur’anin ya dawo inda take ya tsugunna daga gabanta tare da kamo hannun ta ya ri’ke cikin nashi yana wasa da shi. 

Da idanu tabi hannun nasu sannan ta ‘dago da kanta ta kalli fuskar shi. 

” Akwai matsala ne?”.
Ya tambayeta idanun su cikin na juna.
Sai tayi saurin kawar da nata idanun tare da jijjiga mai kai alamar “ah ah” nufin ta ta 6oye masa damuwar da take ciki. 

Abbas kam murmushi yayi mata tare da maida hannun sa kan cikin ta ya dora sannan yace ” Baby na na son gaidani fa naga yana ta waving min hands”. 

Yanzun kam itama murmushin tayi jin shirgin ‘karyan daya shirga wa abinda ke cikin cikin ta da be san mecece rayuwa ba balle ya nemi mahaifin sa. 

Abbas kam cikin towel ‘din ya maida hannun sa wanda har sai da ya sata lumshe idanu dan yanda taji wani irin abu ya ziyar ce ta sakamakon hannun sa da taji kan cikin nata.
A hankali ya ringa shafa cikin yayin da Teemah ma tabi kan hannun san da nata hannun suka cigaba da shafa cikin tare suna zuba murmushi, shi kam har ‘kasan marar ta yayi da hannun sa a hankali yana mai cigaba da shafawa yana fa’din ” Baby na Boss ne da alama tun da har yana yana da wayon son gaidani da sassafen nan”
Teenah kam zuwa yanzun shiru tayi tana jin yadda yakeyi matan tasan ba wai dan baby bane kawai.
Da haka a hankali ya dawo da hannun sa saman ‘kirjin ta sai ma ya janye towel ‘din tare da ha’de musu baki, sosai ya warware mata jiki da salon sa kafin ya d’auke ta zuwa kan bed. 

Abbas sai daya tabbatar ta gama satisfying sannan ya raba jikin sa da nata ya ‘kyale ta dan be damu da kansa ba a yanzun, domin yasan ada ba ‘karamin ‘ko’kari tayi ba wajen ‘daukan nashi bu’katun duk kuwa da cewa ‘karama ce amma bata ta6a nuna gajiyawa da bu’katar sa ba, dan haka shima yanzun a cewar sa turn ‘din sa ne dole zai ‘daga mata ‘kafa ba zai takurata ba har zuwa lokacin da zata sau’ke nauyin dake jikin ta. 

Story continues below


Kwance yake a gefenta yana ‘ko’karin dai-dai ta nutsuwar sa wanda da ‘kyar yake samun hakan domin matu’kar ya kusance ta hankalin sa sosai yake tashi, Teemah kanta tasan hakan har ma ta ta6a yi masa magana sai yayi mata musu ita kuwa ta san ba gaskiya yake fa’da mata ba dan ko be fa’da ba tasan me yake ciki, shiyasa ma cikin kwana kinnan take danne damuwar ta in dai ba abin yafi ‘karfin ta bane sam bata bayyana wa cuz bata ga anfanin ya biya mata nata bu’katun shi kuma ya hana kansa ba, bacin ita ba wani ciwo ko wani abu take ji ba da zai hana shi sakewa da ita, amma ta rasa ta yanda za’a yi ya fahimce ta. 

Ko yanzun ma tana iya feeling yanda gurbin zuciyar sa ke beating so fast, daya ke kwance take bisa ‘kirjin sa sai take jin tausayin sa sosai yake kama ta. 

Sai da ya dai-dai ta kansa ne kafin ya sau’kar da idanun sa kan fuskar ta ya kalle ta.
Muryar shi kawai ta jiyo yana fa’din ” idan kin tafi Abuja kika barni zaki iya jure rashi na?”. 

Hannun ta na yawo akan fuskar sa dana faman shafa fuskar tashi zuwa gurbin dimple ‘dinsa, jin yayai maganar ne yasa ta saukar da hannun ta daga kan fuskar tasa ta dawo dashi k’irjin sa sannan a hankali tamkar bata son yin maganan ta bashi amsa da fa’din ” kai ma ai ka juri rashi na Yayah duk da ma ina tare da kai, balle ni ai kaga dole zan iya jurewa tunda na ‘dan lokaci ne”.
Ta karasa maganar hannun ta na yawo akan ‘kirjin sa. 

Zai sake magana yin magana sai Teemah ta jijjiga masa kai, shirun yayi kamar yanda ta bu’kata yana kallon kitson dake kanta. 

Bazata kawai yaji ta sau’ke hannun ta ajikin sa wanda yasa shi sau’ke ajiyan zuciya ba tare da ya shirya ba.

Sosai Teemah tayi ‘ko’kari wajen ganin ta faranta masa tare da rage masa abinda yake ji ‘din batare da jin kunya ko ‘kyan’kyamin sa ba, dan tasan ko da ta bashi dama da jikin ta bayi zaiyi ba, ada kullun inzai kusanceta sai yayi kusan salo a ‘kalla kala uku da ita, koda tagaji kuwa sai yayi son ranshi sannan ya barta, sa6anin yanzu da kullun ‘daya kawai ya keyi kuma duk tasan saboda condition ‘din ta ne yasa.
Shima Abbas yau ‘din ba ‘karamin mamaki ta bashi ba, sosai ta birgeshi ta sanya masa nisha’di a zuciyar sa.
Bai ta6a zaton zata iya yi masa irin hakan ba domin bata ta6a ko kwatanta yi mai ba sai yau da tayi surprising ‘dinsa, wani gurbi na musamman ta samu ke6antacce a zuciyar sa wanda yake jin babu mai iya ratsa wajen illah ita ka’dai, sosai yaji da’din yanda ta tafiyan tar da shi da bu’katun sa a wannan lokacin. 

Albarka kawai ya rin’ka sanya mata da har sai da ta rufe mai baki da nata kafin yayi shiru.

Haka rayuwar su taci gaba da tafiya kowa na ‘ko’karin ganin ya farantawa ‘dan uwansa da duk wani abinda zai iya na kyautatawa, zaman su gwanin sha’awa inda suke shimfi’da zallar salon so da ‘kauna tare da mutuntaka a tsakanin su. 

Har watan ramadan yazo ya wuce Teemah bata koma Abuja ba, duk kuwa da cewa kusan kullun Ummah bata gajiya da yi masa tuni akan dawowar tata amma ya kasa kaita sai dai kullun ya ringa bata tabbacin insha Allahu suna hanya. 

Da haka yayi ta jan Ummah har cikin Teemah ya kai 8months da kwanaki kusan ashirin, wanda a lokacin ne Ummah ta nuna masa 6acin ranta sosai barin ma da Hannah ke ‘kara zuga ta a gefe dan itama sosai ta matsu taga Teemah a kusa da ita tana mamaki ita kam wai Teemah ne da ciki abin na bata dariya sosai. 

B’acin ran Ummahn ne yasa shi fara tunanin kawai gara ya maida ta Abujan, ita kanta Teemah ma ta kan yawaita yi masa magana akan tafiyar amma sai yayi kamar be ji taba, da farko idan tayi maganar yana bata amsa da fa’din ” zaki je ai amma sai na shirya tukunna”
ko kuma yace ” Ina sane da batun karki damu”
amma daga baya ma sai ya zamana ko ‘kala baya furta mata, ya daina tankata indai akan maganar ne, hatta Anty Leesah na yawan tambayar sa wai ” yaushe zata dawo gida? ko can ports ‘din zasu je sunan ?” sai dai yace mata ” ah ah ” kawai a takaice, dayake yanzu Leesah ma ta zama ‘yar gida tun lokacin da suka fahimci cewa ita ‘din sister ‘din Bilal ce shikenan sai zumuncin su ya ‘kara ‘karfi, ko da akayi tambayar auren Hannah kuwa sai ya zamana date ‘din auren su rana ‘daya a kasa sanya Leesah da Hannah duk a watan December. 

Story continues below


Itama Teemah da ta gaji da maganar sai ta kyale shi ganin cewa kullum abu ‘daya suke ta maimaitawa. 

Sai yanzun ne yafara yi musu shirye-shiryen tafiya ganin ya gama tunzira ran Ummah, cikin kwana biyu kuwa har sun gama komai inda a kwana na biyar da yin wayar Ummahn suka dira garin Abuja babban birnin tarayyar Nigeria. 

Sau’kan su keda wuya kuwa Ummah ta ringa sau’ke masa buhun masifa da ‘kyar ya samu tayi shiru, dayake dama fa’dan ba wai na zafi bane kawai na haushin rik’e Teemah da yayi ne acan da kuma wasa da hankalin ta da yayi tayi a banza. 

Hannah kuwa abin nema ya samu ganin ga ta ga Teemah ga kuma tu’ke’ken cikin ta a gaba. 

sai da ta gama dariya son ranta da kwatan ta irin tafiyar Teemah sannan tafara gwad’ata wai wlh cikin kyau ya ‘kara yi mata tayi fresh skin ‘din ta ya ‘kara yellow da shai’ki, tace ” sai dai kinyi bombom gaskiya da boobs sosai, har da kama baki tace “kai wannan babyn akwai wayo wallahi yana son Dad ‘dinsa ya shana”
ta ‘karashe da dariya. 

Teemah kam bata damu ba sai ce mata tayi ” soon kema ai kina hanya zan rama ne Hannah” 

Hannah tace ” Allah kuwa ba batun wasa anan, inaga ma shiyasa Yayah ya kasa dawo dake gida tuntuni ‘din irin wannan kaya haka?, kai tubar kallah!” 

Murmushi Teemah tayi tace ” Hannah ke kam bazaki ta6a canza wa ba, inajin sai ranar da Bilal ya koya miki hankali tukun”
Hannah Tace
” kamar yanda Yayah ya koyar dake ba, ai naga kin wani nutsu ne duk kin canza ko dai kawai dan ana shirin zama uwa ne?”.
Teemah sai tace
“Bansani ba Hannah kijira naki idan yazo kawai sai ki bani labari” 

Dariya Hannah tayi tace ” ai nawa daban ne da naki kema kin sani…., yauwa ni ya batun birgiman ki? Allah yasa de kin daina dan in ba haka ba yanzu kam sai dai ki koma ‘dakin Yayah kiyi ta bajewar ki ke ka’dai da wannan ‘katon cikin” 

Teemah cewa tayi
“Zamu gani ai Hannah sai ki kore ni” 

Murmushi kawai Hannah tayi ta tashi ta fita jin Ummah na ‘kwalla ‘kiran ta. 

Washe gari Leesah tazo ta yi musu barka da zuwa, su Hannah sai sunkuyar da kai take yi ita a dole kunya, sai a bayan tafiyar Leesah ne sai Teemah tayi ta tsokanar ta wai mai kunyar iskanci bayan tana ganin yanda take satan kallon ta idan ta juya kai. 

Hannah tana dariya tace ” ai dan tana ‘dan kama da Bilal ne shiyasa” 

Teemah ma dariya tayi tana nuno ta tace ” mara kunyar yarinya kawai, wato dan tana kama da Bilal ne shiyasa kike satan kallon ta”. 

Hannah murmushi tayi mai sauti tace ” bazaki gane bane matar nan, Allah ina tsananin son Bilal fiye da yanda Yayah ke son ki “. 

Ta k’arashe da zolaya.
Teemah kuwa take ta tare ta da fa’din ” kar ma ki fara yaudaran kanki da wannan ‘karyan, an gaya miki soyayyan Yayahn irin naku ne?” 

Hannah ‘kin yin magana tayi sandiyyan ganin Abbas tsaye a bakin ‘kofa sai kawai ta fara ‘kif-‘kif da idanuwa Teemah bata san me ake ciki ba ita kam har sai da ta gama fa’din me zata fa’da ta mi’ke sannan ta ci karo da shi a tsaye. 

Hannah tasowa tayi ta nufi ‘kofar fita daf da shi sai tace ” Ina yini Yayah?” 

Da ” lafiya” kawai ya amsa ta kamar yadda ya saba. 

Teemah da idanu ta bi bayan Hannah har ta bar ‘dakin sannan ne ta dawo da kallon kan Abbas, sanye yake da dogon wandon jeans da armless shirt, sosai kayi suka amshi jikin sa. 

A hankali ya tako zuwa inda take ya zo ya tsaya a kanta batare da yayi magana ba. 

Teemah ‘daga kai tayi ta kalle shi suna ha’da idanu sai yayi sama da girar shi tan ‘ko’karin sau’kar da idanun ta sai ya sa hannun ‘daya ya ‘dago ta tsaye ran’kwafowa yayi ya rungume ta baya hannun sa ya kai kan cikin ta yayin da kansa ke a wuyan ta saitin kunnan ta a hankali ya furta ” na ji ana gulma ta!, laifin me na aikata kuma?” 

Story continues below


“Ba komai”
Ta ce da shi itama cikin sanyin murya. 

Kiss ya sau’ke mata a kunnan tare da fa’din ” ban yarda ba “
Sai tace
“Da gaske Yayah ba komai……”
Maganar tata yankewa yayi sanadiyyan cizon dataji ya sake mata a kunnan sai ta ‘karasa da fa’din 
” awshh……Yayah ka cinye min kunne na”. 

Murmushi yayi yace ” da zafi ne?” 

Kai ta ‘daga masa masa tana shafa kunnan tamkar zata yi hawaye.
Sai yace ” tell your sister that dafin son Yayah ya zarce na kowa, bai ma da makamanci kinji?” 

Shiru tayi masa kawai tana jin yadda yake ‘ko’karin kai hannun sa har zuwa ‘kasan ta. 

Ri’ke mai hannun tayi tayi kalar tausayi tare da ro’kon sa akan ” please yayi ha’kuri” 

“Dalili?”
Ya ce da ita. 

Sai tace ” Ayyah Yayah gidan Ummah ne fah kuma kaga Hannah na iya shigowa ako wani lokaci” 

Shima ‘din ya san abinda ta fa’dan gaskiya amma duk da haka sai ya’ki sakin ta har sai da ya gama kashe mata jikin kafin nan ya bar ‘dakin, Allah ma ya taimake ta har ta gama kintsa kanta Hannah bata dawo ba. 

Satin Abbas ‘daya a Abuja sannan ya koma Rivers, ranar daya koma kuwa a ranar Teemah ta bar ‘dakin sa ta koma na Hannah bisa umarnin Ummah. 

Sosai Teemah ke jin kewar sa musamman lokacin da tazo bacci, dan ta saba bacci ajikin sa yanzun kuwa sai take jin ta wani iri, in bama maganar da Hannah tayi mata akan birgima ba ai ita tuni ta mance da cewar tana yi, dan kullun yanda ta kwanta ajikin sa a hakan take tashi bata ganin ta canza wuri saboda baya raba jikinsa da nata har gari ya waye, so ta ina zata samu damar yin birgima a hakan, yau da gobe kuwa yasa har ta saba da bacci a nutsen especially ma idan tana jikinsa dan ko fa’da sukayi da shi kuwa wannan yanayin baccin nasu baya ta6a canzawa ko ta’ki ma dole sai ta ha’kura saboda ba barin ta zai yi ba. 

Aranar da ‘kyar bacci ya ‘dauke ta da tunanin sa a ranta har kuwa cikin mafarki sai da ta ganshi. 

Washe gari da suka tashi Hannah da yake bakin ta baya shiru sai tace ” gaskiya Yayah ya iya displine kin koyi bacci mai kyau, da ai har ina fargaban ki danne ni da wannan ‘katon cikin naki”.
Teemah cewa tayi ” ke de kika sani Aku uwar magana, ina nan in da raina watarana sai na rama insha Allahu”. 

Hannah murmushi kawai tayi bata yi magana ba tana tuno cewa wai itama watan watarana sai gata ga ciki. ” hmm” kawai ta furta a fili with smile on her face. 

Zaman Abuja yayi wa Teemah da’di, dan sosai Ummah ke bata kulawa tare da bata wasu addu’o’i tana karantawa kullum, bata da damuwar komai yanzu face tunanin mijin ta da kuma fatan Allah ya sau’ke ta lafiya. 

Shima Abbas ‘din suna waya akai-akai dashi dan a’kalla suna waya a rana kusan sau biyar in dai yana da lokaci baya gajiya da ‘kiran ta. 

Tun lokacin da watan haihuwar ta ya kama sai ya kasa jin kwanciyar hankali, kullum baya bacci mai kyau da dare haka zai ‘dau lokaci yana yin sallah yana ro’ka mata ubangiji sau’kin na’kuda, haka ma Mummy ba’a bar ta a baya ba tana iya ‘ko’karin ta. 

Da yamma kullum sai sun fita cikin compound ‘din gidan ita da Hannah su ‘dan zaga tana warware ga6o6in ta, ko ina kuwa zata da ruwan ta a hannu take tafiya, dan yawan shan ruwane da ita akai-akai yanzun. 

According to her EDD an ce haihuwar ta zai kama ne zuwa kwanaki takwas masu zuwa ko kuma ‘kasa da haka, sannan kuma zai iya haura hakan it’s depends basu da tabbaci, kuma duk ba matsala bane. 

Dalilin haka ne yasa yanzun Ummah sam bata nutsuwa kullum hankalin ta na kan Teemah, hatta baccin dare ma bata yin shi gaba ‘daya, ta ringa zarya kenan a ‘dakin su, haka ta hana Hannah ma dogon bacci duk wai dan kar wani abin ya taso kuma basu sani ba.

Story continues below


*****
Ranar wata lahadi ne wanda ya kasance kwana na biyar cikin kwanakin da aka gindaya mata, kenan idan aka bi lissafin da aka tana da sauran kwanaki har uku kafin cikin EDD ‘din ta, shiyasa ma bata damu ba koda taji marar ta na ‘dan haura mata da ciwo ka’dan-ka’dan, zaton ta ko zai daina kamar yanda ya saba yi mata dan haka sai bata sanar da Hannah halin da take ciki ba ganin tana baccin ta, shiyasa ma ko motsin kirki ta ‘kiyi dan kar ta ta she ta. 

Zirga-zirgan zuwa bathroom ta fara dan yawan fitsarin dake matsata, in ta je ‘din kuwa ba wani abin kirki take yi ba sai dai ta dawo tana cije baki tana tafiya da ‘kyar kuma a hankali saboda azaba. 

Gajiya tayi da yawon zuwa bayin ga ciwon marar nata na k’ara tsanani kawai sai ta sanya kuka a hankali ta dur’kushe daga bakin gado dai-dai farkawan Hannah ha’de da turo ‘kofan Ummah a lokaci guda. 

Da hanzari suka yo kanta Ummah kam sai ta daka wa Hannah tsawan rashin hankalin datayi inji Ummah da yake ta mata warning akan kar ta yadda ta ringa yin dogon bacci saboda irin hakan. 

Take sai Hannah taja gefe tana rarraba idanu tayi kicin-kicin da fuska. 

Ciwon Teemah kam kamar jira yake yi yaga idanuwa sai kawai ya tashi gadan-gadan, Hannah ma kuka ta sanya ganin halin da y’ar uwar ta ke ciki kafin kace kwabo har hawaye ya wanke mata fuska gaba ‘daya. 

Ummah fita tayi da sauri taje ta d’auko wayar ta da mayafin ta bata dawo ‘dakin ba sai da ta fita waje ta yiwa driver magana, Allah ma cikin ikon sa yasa yau ‘din agidan su drivern ya kwana saboda daren da yayi bai koma gida da wuri ba shiyasa kawai ya kwana be tafi ba. 

Hannah kam sai aikin sannu take ta yiwa Fateemahn gwanin ban tausayi idan ka gansu. 

Ummah na dawowa sai ta umarci Hannah data ta ‘daukowa Teemah mayafi su wuce asibiti. 

Gefe da gefe suka kama Teemah a hankali har suka fice waje wurin mota inda suna shiga driver yaja suka fice daga gidan. 

Yayin da Fateemah ke jin ranta kamar zai bar jikinta dan azaba, ha’ki’ka haihuwa ko ka’dan ko yake bashi da sau’ki, babu kuwa wanda zai gane hakan har sai abin ya same shi. 

Tun da suka je asbiti ake abu ‘daya tun ‘karfe uku na’kuda yasa ta a gaba da azaba sai ya tashi sai kuma ya kwanta har tazo tayi bacci ma kusan na mintina arba’in sannan ta farka da wani matsanancin ciwon, gaba ‘daya Teemah ta fice a hayyacin ta ta gama saduda da rayuwar ta ya ‘kare dan bata ta6a zaton akwai irin wannan ciwon a duniya ba, duk jarabar ta da son yara sai da taji bata ‘kaunar haihuwa muddin ranta, fa’di take yi kawai ” ku cire min wannan cikin wallahi banaso, ku raba ni dashi dan Allah mutuwa zanyi……waiyo kuyafe min dan Allah…..Yayah na waiyo zan mutu…”
Tun tana kukan da hawaye har tazo hawayen ya daina fita mata ta koma salati, duk wanda yazo mata yi take yi ko da bata kai ‘karshe ba sai ta kamo wani, abin dariya abin kuma tausayi. 

Hannah kam kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita haka takeji, a ranta take tunanin ashe haka haihuwa take sosai ta tsorata da haihuwa ita kam, lalle uwate abin girmamawa ne dole kabisu, tausayin Teemah gaba ‘daya ya cika mata ‘kirjin ta har ji take da zata iya data rage mata ciwon. 

Ummah bata sanar da kowa halin da ake ciki ba hatta Abbas kansa, cuz gaba ‘daya hankalin ta na kan Teemah ne yanzun ganin yanda take shan wahala gaba ‘daya ta karya mata zuciya ganin na’kudan yayi tsayi. 

Dai-dai an fara ‘kiran sallahn shiga masallacin Asubah abu yataso mata gadan-gadan, bayan ta take jin tamkar zai 6alle biyu, Allah kuwa cikin ikon sa mintina biyu basu cika ba sai ga kukan jariri domin da kukan sa ya taho kamar an doke shi. 

Yana fita daga jikin ta kuwa Teemah ta fara sau’ke ajiyan zuciya a hankali take furta “Alhamdulillah” har bacci ya ‘dauke ta. 

Sai hamdala kawai su Ummah keyi yayin da Hannah ke farin ciki da guntun hawayen ta a idanu.

Story continues below


Abbas na alwala yaji tsinkewar zuciya da bai san dalili ba, dan haka sai ya ringa maimaita _innalillahi wa inna ilaihi raji’un_ har ya kammala alwalar tasa har kuwa ya idar da sallar bai ji zuciyar sa tayi dai-dai ba, kuma ya rasa dalilin da ya kawo hakan, Qur’ani ya ‘dauka kawai ya yi ta karantawa har gari yayi haske. 

Baby lafiyar sa ‘kalau, Teemah ce dai ta ‘dan samu matsala sai da aka mata aiki amma ba sosai ba ‘dan ka’danne daga nan aka yi discharging nasu. 

Ummah bata ‘kira shi ba sai ‘karfe 8:00am bayan har sun koma gida ta gama gyaran mai jego da baby inda aka shirya shi cikin kayan sa sky blue sun fito ras abinsu sannan Ummah ta ‘kirashi da duk wa’dan da suka dace ta sanar mawa. 

Abbas ne ‘karshe da Ummah ta ‘kira, shi kam godiya kawai ya ringa sake wa mahalicci yana tasbihi musamman dayaji cewa lafiyar su ‘kalau ita da babyn har ma sun koma gida ai farin cikin sa da’duwa yayi akan nada. 

B’angaren Teemah kuwa zama tayi gefen yaron ta tana kallon shi tana sau’ke murmushi, wai yau gata ga babyn ta wanda ita ta haifa da kanta, baiwar Allah kenan yawa ne da ita yakan kuma baka ta inda baka zato ko kuma akasin haka, sosai ta ringa gode Allah a zuciyar ta, bazata iya misalta yanayin farin cikin data ke ciki ba a wannan lokacin. 

Babyn ta tsurawa idanu tana so ta gano kamar sa amma takasa, sam bazata iya iya ce ga kamar yaron ba ayanzu domin kuwa ita bagane kamar jinjiri takeyi ba, shiyasa dole ta ha’kura ta barshi, yatsun ‘kafar shi ka’dai ta iya gane kamar su irin ta Abbas ne sak sai dai hasken sa da kamar kam takasa ganewa. 

Baby baccin sa yake yi cikin kwamciyar hankali, tunda akayi masa wanka yake bacci, itan ma garin kallon shi har bacci ya ‘dauke ta a gaban sa, ba ita ta tashi ba sai da azahar. 

Hannah ce ke gaya mata wai ai Yayah ya yi ta ‘kira abata wayar tana bacci kuma Ummah ta hana a tashe ta. 

Shiru kawai tayi dan wani azaban zafi da take ji tun daga ‘kasan ta har zuwa cinyoyin ta. 

Da ‘kyar ta daure ta tashi ta zauna tana cije baki, koda zata tashi tsaye kuwa zafin datajin har sai daya sata sau’kar da hawaye. 

Matar da ta gani zaune a gefe ne tana bawa jinjirin zam-zam tace da ita ” yi a hankali Fateemah, sai kin daure kinji” 

Wa Hannah matar ta mi’ka yaron sannan da kanta ta tashi taje ta ha’da mata ruwa mai ‘dumi a bathtub tace idan ta shiga zauna aciki. 

Kafin ta mi’ke sai ga Ummah ma ta shigo, tana ganin ta zaune kuwa sai ta washe baki tare da yi mata sannu, Teemah ta amsa sannan ta tashi a hankali kamar mai koyon tafiya ta wuce bayin. 

Da hawaye ta samu da ‘kyar da azaba ta iya yin fitsari, da farko ma tsoron shiga ruwan tayi amma sai ta daure musamnan data tuna first night ‘din ta irin yadda ruwan zafin ya taimake ta shiyasa yanzun ma ta daure ta shiga.
Sai data yi brush kafin ta fito daga bayin tana ‘danjin da’din gabo6in ta ba kamar lokacin data 
tashi a baccin ba. 

Tana fitowa kuwa aka gabatar mata da abinci, inda ta ‘dan tatta6a ka’dan ta bari domin ba da’din bakin ta takeji ba yunwar ma bata ji tun safe da Ummah ta bata wani ha’d’den tea mai kauri tasha har yanzu bata ji yunwa ba, sai ‘kirjin ta dake ‘dan yi mata zogi saboda cikar da sukayi. 

Matar ne tace ko zata bashi yasha da yake tun safe daga zam-zam babu abinda ke cikin sa, take Teemah sai ta jijjiga kai alamar “ah ah” matar ma bata matsa mata ba cuz tayi zaton ko zuwa an jima zata bashi. 

Kamar wasa kuwa har yamma Teemah bata bawa baby mama yasha ba wai tana tsoro yana mata zafi. 

Ummah bata so ta matsa mata itama dan haka kawai sai ta bar ta, amma abin na damun ta azuci. 

Da yamman aka sake yiwa baby wanka yana ta faman kaiwan hannun sa baki yana ‘ko’karin tsotsa, tausayin shi sosai yake kama Ummah amma bata san yanda zata yi da Teemah ba sam, ko da aka gama shirya shi sai aka bashi ruwa yasha, yana sha kuwa tale sai ya koma bacci abin sa. 

Story continues below


Itama Teemah wankan ta sake yi bisa jagorancin wata dattijuwar mata tayi shirin ta cikin riga da zani na atampa tayi simple ‘dauri ba na ‘daga hankali ba daya ke ma ba wani da’di sosai take ji ba shiyasa powder kawai ta murza a idanun ta tare da sanya kwalli, sai uban turaruka data ringa fesawa ajikin ta kamar baza su ‘kare ba. 

Fita sukayi dukkan su suka bar Hannah da Teemah a ‘dakin yayin da ta sa Babyn agaba ta zuba uban tagumi, so da tausayin sa na ratsa ta, sai ta kamo hannun sa ta ri’ke cikin nata tare da kwantar da kanta agafen sa tana kallon fuskar sa, ita kanta tausayin sa take ji sosai amma tana tsoron sa mishi maman abakin shi dan yanda take jin yake yi mata zogi, koda za’a wanke ma da yamman nan har kuka tayi saboda zafi da zogi gashi sai ‘kara cika yake yi base k’aramin takura ta yake yi ba. 

Yayi baccin a’kalla mintina kusan hamsin kafin ya farka, sai kuma ya tashi da kuka, wanda ya rikita Teemah ta rasa ma ko ta yanda zata ‘dauke shi dan haka kawai itama sai ta sanya kukan. 

Hannah ce dake bayi tayi saurin fitowa ta ‘dauke shi ta fara jijjiga shi amma kamar ziga shi take ‘kara yi kukan nasa sai ‘kara ‘karfi yake yi ga dukkan alamu an ‘kure ha’kurin sa ne. 

Hannah tayi-tayi da ita ta bashi yasha amma ta’ki sai kuka kawai takeyi. 

A haka Ummah ta shigo ta same su, sai tace 
” wai ya akayi ne? Ya tashi ko?” 

Hannah ce dake hautsine ta bata amsa da fa’din 
” ehh ya tashi Ummah”. 

Kar6an sa Ummah tayi itama ta ‘dan jijjiga shi da kukan ya ‘dan ragu sai ta kifa shi akan ‘kafafun ta tace da Teemah 
” Yunwa fah yaron nan yake ji kar ashi ga hakkin sa dayawa ki daure ki bashi yasha kinji”. 

Kai Teemah ta ‘daga wa Ummah kamar da gaske.
Ummah sai ta ‘dago shi ai kuwa kamar yana jira sai ya saki wani sabon kukan kuma, mi’kawa Teemah shi tayi tace 
” yauwa Fateemah maza bashi ‘kilan zai yi shiru”
Ummah da kanta ta dai-dai ta mata zaman yaron a cinyar ta sannan ta koma gefe. 

Teemah kam a hakan ta rungume shi tana bin bakin sa da kallo yanda yake kukan hawayen ta na cigaba da sau’ka. 

Ganin hakan ne yasa Ummah ta fice tunanin ta wai ko kunyar ta ne yasa Teemahn ta’ki bashi a lokacin dan haka sai ta fita ta bar su da Hannah a ‘dakin. 

Hannah kam gaba ‘daya taji zuciyar ta ya karye da kukan yaron ita kanta ji take tamkar ta taya shi kukan amma sai ta daure batayi ba. 

Zama tayi agefen Teemah ta ringa bata baki akan ta taimaka ta daure ta bashi kar kukan yayi masa yawa daga zuwan shi duniya ya yi sabo da kuka. 

Rashin kautawar ta tagani ga tausayin yaron ta daya cika ta dan haka sai ta daure ta ciro maman a hankali kamar tana tsoron ta6awa dan yanda yake yi mata zafi, wanda hakan shine babban dalilin daya sanya tun ‘dazun take tsoron bashi.
Da dabara ta gwada saita masa a baki wanda har ya kama sai kuma tayi saurin cirewa ta maida abinta ta rufe, take wani sabon hawayen ya sau’ko mata sai ta kalli Hannah tace
” Allah Hannah da zafi bazan iya ba” 

‘Bata rai Hannah tayi tace ” Haba-haba ke kuwa, ki daure ki bashi dan Allah, ke baki ganin irin kukan daya ke yi ne?
Tun fa a safe baki bashi yasha ba, kina ganin kyauta kenan?
Ko irin tausayin shin nan bakijji ne ke?” 

Teemah kam sai cewa tayi ” d’auke shi Hannah please ki bashi ko zam-zan ‘din ma yasha may be zai yi shiru”
Ta fa’da cikin hawaye. 

Tsaki Hannah ta ja tare da sa hannu ta ‘dauke shi a zuciye tayi waje da shi.
Gani take yi kamar rashin imani Teemahn ya zarce misali ne da har bata iya tausayin ‘dan jinjirin dako kwanaki bai ma fara irgawa ba a duniya. 

Da idanu Teemah ta bisu har suka fice, inda suna fita ta kifa jikin ta a kan gadon tana kuka da hawaye, ita da kanta haushin kanta takeji akan abinda tayi. 

B’angaren Hannah kuwa koda ta fita da babyn jijjiga shi taci gaba dayi tana tafiya, sai sukayi kici6us da shi a corridor, shogowar kenan yajiyo kukan baby ya cika ko’ina agidan hakan yasa ya ‘karaso nan ‘din da gaggawa. 

Da ‘dan hanzarin sa ya iso kusa da Hannah.
Hannah ja tayi ta tsaya sai ya sa hannu ya kar6i babyn tare da fa’din ” me ya same shi ne haka yake ta faman kuka?” 

Amsa Hannah ta bashi da fa’din ” tun safe bai sha komai ba sai zam-zam da ruwa inajin yunwa ce ke damun sa” 

Yana jijjiga babyn yace mata 
” ina Fateemahn kuma take me yasa ta barshi haka?” 

Hannah sai tace 
” tsoro takeji wai maman na mata zafi”. 

“Where is she now?”
ya tambaye ta sai ta bashi amsa da fa’din ” tana dak’i na” 

Tafiya ya fara yi da Babyn a hannun sa ba tare da ya sake fa’din komai ba ya nufi hanyar ‘dakin Hannah ‘din. 

Hannah ma ‘karasawa tayi ‘bangaren Ummah ta dubo ta jin bata fito ba duk wannan uban ihun sai ta tarar ma ashe sallah take yi shiyasa. 

Tambayar ta Ummah tayi wai ” tabashi ne?”
Sai Hannah tace ” ina kuwa ta bashi, har fa ta ciro kamar zata bashin kuma sai tace wai zafi yake yi mata”
Ummah cewa tayi
” To ai da kin taho min da shi nan d’in….” 

Taranta Hannah tayi da fa’din ” Yayah ne ya kar6e shi ai, yanzun nan inajin isowar shi ma” 

” ai kuwa ba mamaki dan ko ni ma bansan da zuwan nashi ba”.
Ummah tayi maganar tana mai cire hijab ‘din data yi sallah dashi a kanta. 

Teemah kam kasa zama tayi a ‘dakin dan yanda take iya jiyo tashin kukan babyn gaba ‘daya ya kara’de gidan nasu, ga shi maghrib tayi sam hankalin ta sai ya kasa kwanciya, dan haka sai ta yun’kura ta taso da niyyar bin bayan Hannah, tana ‘ko’karin bu’de ‘kofa sai kuma taji kukan babyn na sake tunkaro ‘kofan daga waje. 

Kafin ma ta bu’de sai ya riga ta bu’de wa sai suka tsaya kallon kallo. 

Ita kallon mamakin ganin sa takeyi musamman da ta gansa rungume da Babyn, yayin da shi kuma yake yi mata kallon ” kin kyauta ai”
Amma fuskar sa wasai babu wani alamun 6acin rai akai sai ma wani 6oyayyen sihirtacce kuma ‘kayataccen murmushi.
CAPTAIN ABBAS – P93 – Page 7

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD* 

Luv story😍

*Wattpad @* 
*Serlmerh-md* 


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER’S ASS* 
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all…..
*DA BAZARMU* *MUKE TUN’KAHO*

_Dedicated_ 
my family😍

~*2nd 2d LAST PAGE*~

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

  _Wishes are always granted but you just have to wait for the perfect time._

🅿 *93*

Da sassarfa ta k’arasa inda yake tsayen ta rungume shi daga ‘daya gefen sa ta saki wani kuka. 

Shiru Abbas yayi kawai duk da kukan da take yi ‘din amma bai bi takai ba sai ya dawo da idanun sa kan fuskar Babyn yana kallo tsawon da’ki’ku fuskarsa ba yabo ba fallasa sannan ya ‘dan juyo da kansa 6angaren da take a kunne ya ra’da mata ” what’s wrong kuma?, why ar u crying ko kina taya yaron ki kukan ne?”
Teemah ‘dagowa tayi ta jijjiga mai kai, sai ya ‘dage gira ‘daya yana kallon ta yace ” to shi’din kuma kukan me yake yi? Me yasa me shi?” 

Kwa6a baki tayi tace ” Wai fa yunwa yake ji…ni..ni kuma..maman tun ‘dazu zafi yake min tsoro nake ji”.
Abbas cewa yayi ” Haba! haba!!, tsoro kuma kike ji?, kika iya haifan shima balle wannan, come on zo muje ki gwada bashi in gani yanzu”
Yayi maganar tare da ‘karasawa cikin ‘dakin, itama Teemah a hankali ta biyo bayan sa tana fa’din ” Allah Yayah da zafi fah, ni gaskiya bazan iya ba”. 

Sai yace ” ka’dan zaki bashi ba da yawa ba kinji?” 

Da haka ya ‘karasa bakin gado ya tsaya yana jiran isowar ta, daya ke a ‘darare take bin bayan san so sai bata ‘karaso da wuri ba. 

Tana isowa sai yayi mata nuni da bakin gadon, Teemah kam a tsorace ta zauna tana matse ‘kwalla.
Shi da kansa yasa mata yaron a cinyar ta tare da dai-dai ta mata shi inda yanayi yake fa’din ” ke ko tausayin sa bakiji ne?, kuma ma idan ke da kika haife sa baki bashi ba to waye zai bashi? in kuma kin daina son shi ne sai ki gaya min inje in kyautar shi wa wata wacce zata kula dashi da kyau,  hakan yafi ko? 

Ya ‘karashe yana kallon cikin idanun ta dake cike taf da ‘kwalla.
Wani hawayen ne ya sake gangaro mata jin abinda ya fa’da sai ta share da ‘dayan hannun ta tana sake rungumar yaron zuwa ‘kirjin ta. 

Abbas hannun sa ya kai bayan ta yana bu’de mata Zif yace ” Ni ina can kin barni da tunanin zaki iya haihuwa ko kuma akasin haka, ban sani ba ashe ke kam kina nan kina ta yiwa Baby na rowa ko?”
Sai yanzun ta bu’di baki cikin shagwa6a tace
” Ni fa ba rowa nayi masa ba”
Abbas jinjina kai yayi yace ” to naji bashi in gani in dagaske ne…kin gama ai har ya gaji da kukan ya ha’kura dan haushi”. 

Kallon sa tayi itama fuskar sa har ta dawo ja saboda rikicin kukan da yayi yanzun, a hankali ta ‘daga rigar ta sama Abbas ya taya ta ri’kewa sai ta ciro maman dake saitin babyn, ya cika sosai ita kanta tana jin nauyin sa har tsoron ta6awa take yi ma. 

Juyowa tayi ta kalli Abbas tare da marairaice fuska zatayi magana ya tare ta da fa’din ” Zahra please…….”
Tace ” ni fa Allah zafi yake min” 

Abbas shima sai yace ” ai zafin sai janye miki in ba haka ba fashewa zaiyi kin fi son haka ko?” 

Jijjiga kai tayi sai yasake fa’din “…..ka’dan zaki bashi to kinji y’an matan Yayah?” 

Sai ta ‘daga kai sama a hankali.
Sai da ta sake ‘dago babyn tare da ran’kwafawa saboda  saman da maman nata yayi, da taimakon sa ta samu ta sanyawa babyn a baki, yana kamawa kuwa sai ta cije baki ta jinginu da jikin Abbas dake ta gefenta, ‘ko’karin cirewa ta farayi dan zafin sosai yake ratsa ta har kan ta, Abbas na ganin haka sai yayi saurin zira hannun sa yana shafa mata saman a hankali yana jero mata “sorry sorry.. sorry babe, so sorry momma….” 

Story continues below


Da haka ya yaudare ta har babyn ya ‘koshi yayi bacci abinsa, sannan ta cire maman har da zufa tayi.

Kar6an sa Abbas yayi tare da fa’din ” Thank u”
Yana murmushi yace ” koke fah?
Murmushin ‘karfin hali tayi itama, ita kanta da ta bashi yasha ‘din sai ta ‘dan ji ta dai-dai sa6anin ‘dazu da bata bashin ba kuma hankalinta bai kwanta da hakan ba gashi kuma ciwon bai ragu ba, yanzun kuwa hatta cikan ma sai ya ‘dan ragu da zafin. 

Hu’duba Abbas yayi masa a duka kunnuwan sa biyu bayan ya gama sai ya rungume ‘dan sa a jikin sa yana jin sau’kan numfashin sa yayin da ya zuba mata idanu yana murmushi ba tare ya furta komai ba. 

Teemah ma murmushin tayi ta sunkuyar da kanta tana wasa da ‘yan ya tsunta. 

Dai-dai nan Ummah ta shigo, bayan ta kuma Hannah ce.
Ummah na shigowa bayan ya amsa mata sallamar ta sai ta tambaye shi cewa ” ta bashi yasha ne?” 

Da ” ehh Ummah yasha” Abbas ya amsa mata tare da gaida ta, kar6an yaron Ummah tayi a hannun sa bayan ta amsa gaisuwar tana gyara masa kayan dake jikin sa tace ” Maman ka matsoraciya ce sosai gaskiya”
Tana murmushi ta ‘dago ta kalli Abbas tace ” da ba ka zo ba da bansan yanda zanyi da ita ba yau ‘din nan”
Ta ‘karashe maganar tare da ‘dan sakin dariya.
Abbas sai yayi murmushin shima yace ” Ummah ai ke kika ‘kyale ta da zane ta kika yi tun farko da baza ma akai wannan matakin ba”
Murmushi sukayi dukkan su har Teemah da jin abinda ya fa’da ‘din wai Ummah ta zane ta. 

Daga lokacin kuwa bata sake jin fargaban bashi ba duk da zafin bai daina ba amma da sau’ki yana ‘dan raguwa mata musamman idan ya sha. 

Washe gari Anty ta iso, ba’ki dayawa daga 6angaren Ummah ma sunzo, kama daga kan  ‘kawayen ta da matan abokan Daddy har ma dana Abbas da wasu ‘kawayen Hannah  duk sun sukayi ta sam barka wa yaron, duk dacTeemah bata san kowa agarin ba in ya wuci Maman Nasreen amma duk da haka gidan baya ta6a rabo da jama’ah kullum,  Mummy ce dai sai ana jibi suna kafin ta iso. 

Jinjirin ma sai tayi sa’a bai fiya yin kuka ba sai dai idan yaji yunwa sannan shiyasa baya ma wuni a tare da ita.
Sau tari dan shayar dashi kawai ake kawo shi wurin ta inda tana gama bashi kuwa za’a kuma tafiya dashi.
Wani sa’in har ji take yi tamkar ta ri’ke abinta ta rungume shi a ‘kirjin ta amma kunyar jama’ah yasa take basarwa, bata ma hakan aka ba kuma saboda tasan na’dan lokaci ne watarana ma su ka’dan su zasu yini batare da kowa ba.

Abbas kansa idan ya zauna yasa su a gaba banda godewa Allah babu abinda yakeyi musamman idan ya gansu wai ace iyalan sa ne su ‘din familyn sa ne na kansa abin na matu’kar ratsa shi kalar yanayin farin cikin dayake tsintan kanshi aciki kuwa abin ba’a cewa komai. 

Matan abokansa duk sunzo da mazajen su suka gaida Teemah wasun su tasan su yayin da wasun kuwa bata ta6a ganin su ba sanadin haihuwar ne ha’duwar su.

Maman Amal ma ta zo tun daga Lagos inda Teemah tayi matu’kar farin ciki, musamman da taga yanda baby Amal ‘dinta ta ‘kara girma tayi wayo tana gudun ta ko’ina. 

Leesah ma babu ranar da gari zai waye bata zo gidan ba, wani zobe na gold ta siyo ta sawa yaron a hannu mai kyau da tsada itama kullum son Babyn na ‘kara ratsa ta barin ma da taga ya na kama da baban sa ai shikenan idan tazo kuwa bata barin kowa ya ri’ke shi sai ita ka’dai.
Tun kafin ayi suna 
ma Leesah tafara ‘kiran sa da Annoor ta kuma ce sunan da za’a ‘kirashi dashi kenan kenan. 

Hannah kam bataso hakan ba dan ita da niyyar ta a k’irashi Irfan sai kuma Haleesah ta riga ta sanya masa suna dole badan taso ba ta ha’kura da nata sunan tana jin badan wani abu ba da Leesah bata isa ce zata saka wa jinjirin suna ba amma sai Hannah tayi mata kara ta bari saboda darajar abu ‘daya. 

Ranar suna yaro yaci sunan *Mahmud*,  babu wanda bai mamakin sunan da Abbas ya sanyawa jinjirin ba, inda jama’ah da dama suka yaba masa tare da yaba irin karamcin daya yi, especially wa’danda suka ji abin a sama cewa kawai sunan marigayi mijin matar sa na baya ne, sai suke ganin kamar shi ‘din halin sa daban ne dan bakowa zai iya irin hakan ba. 

Story continues below


Wa’dan da kuwa suka san asalin zumuncin dake tsakani sai sam barka kawai suke yi, wannan dalilin kuwa ba ‘karamin farin jini ya jawo wa  babyn ba. 

Anty kuwa har kuka tayi dan farin ciki take ta ‘kira Abbah tayi masa albishir cewa an yiwa marigayi takwara,  ta ‘kira mahaifin ta ma ta gaya masa tana hawaye, shima Alhaji Muhammad albarka ya ta sanyawa Babyn masu yawa tare da yiwa mahaifin little Mahmud ‘din fatan alkhairi mai d’orewa. 

Irin 6arnar ku’din da Abbas yayi a wannan ranar abin ba’a cewa komai, dan wurin event ‘din da akayi sunan idan kagani zaka saci ko wani ‘kayataccen biki za’ayi a wurin, jakunkuna aka rin’ka rabawa mai ‘dauke da turmin atampa mai kyan gaske, sannan ga wani jakan kuma shima mai photon baby shima ciki kayan ciye-ciye ne fal duk akayi ta rabawa mutane.
Duk wanda ya halacci taron sunan da farin ciki akan fuskarsa ya tafi domin kuwa ko ka’dan ba’a yi wani abu da zai sosa ran wani ko wata ba a wurin har taro ya watse. 

Kyaututtuka kuwa da Teemah ta samu suma ba’a magana, cikin masu bada kyautar kuwa hadda Anty inda ta yiwa Baby da maman sa kaya masu yawan gaske kowa da nashi akwatin, Daddy ma ya aiko nashi kyautan da yake bai samu yazo ganin baby ba. 

Ana kammala suna Abbas ya koma Rivers, haka ma su maman Amal da wasu mutanen na nesa duk kowa ya kama gaban sa suna masu farin cikin samun ‘karuwar da Abbas ‘din ya samu, inda aka bar Ummah da Anty har ma da Mummy suka cigaba da kulawa da mai jego har tsawon sati biyu sannan Anty ta koma Lagos da yake itama a halin yanzun abokiyar zaman ta nada tsohon ciki ne haihuwa yau ko gobe. 

Mummy kam sai da ta kai 1month cif kafin ta koma Dubai, bayan tafiyar ta ne kuma Abbas yazo ya duba iyalan sa inda ya same su cikin ‘koshin lafiya da kwanciyar hankali baby yayi 6ul-6ul a binshi, dan ma kullum sai sun tura masa photon shi a duk wankan da aka mishi su Hannah sai sunyi masa photo sun turawa Abbas wataran dukkan su sukeyi wataran kuwa Baby da mamar sa wataran kuma shi ka’dai.
Haka ma yana yawan ‘kiran su video call a haska mishi babyn wataran ya ganshi yana bacci, wataran kuwa zai ganshi idanun sa biyu yana wasa da hannun sa abaki.
Abbas idan yaga hakan kuwa sai yace mata wato har yanzu tana masa rowan ko?” 

Teemah sai tace ” ah ah”
“Toh meyasa yake kai hannu baki?”
Ha’de goshi takeyi tace ” Wasan shi fah kawai yake yi Yayah, kai dan baka ga yanda yake tsotseni bane shiyasa ai zaka ce wani ina masa rowa” 

Sai cewa yayi ” rama min yake yi ai kema kin tsotseni”
Teemah da sauri tace
” wallahi ba wani nan, to in dai haka ne ma bazan ‘kara nuna maka shi ba” 

Abbas ha’kuri ya bata yana dariya  yace ” to shikenan ya wuce, ni wasa nake miki maman Baby”

Lokacin da Abbas yazo ya gansu ba ‘karamin farin ciki yayi ba har ji yake duk fa’din duniyan nan babu abinda ya kai masa farin ciki sama da su.
Wani kyau yaga Teemahn tayi masa da yake already Anty ta aiko an fara yi mata gyara ga haske datayi kamar ba mai jego ba, ko irin ‘karnin nan da wasu masu jegon keyi sam bai ji a wurin ta ba illah ‘kamshi daga ita har lil Mahmud ‘din, da yake ma dama Teemah gwanar son ‘kamshi ce kuma Anty tasa an kawo mata wasu ha’din su humra da sauran su masu bala’in ‘kamshi shiyasa bata wasa da amfani dasu,
dayake kuwa bata wasa da kayan ‘kamshi ciki da waje tana ‘ko’karin kulawa sosai.

Aranar da yazo ‘din kuwa Teemah da kayar ta sha, duk da tana yi masa tuni da cewa gidan Ummah ne ya bari fah kar tazo amma Abbas bai saurare ta ba yaci gaba da abinda yakeyi har sai daya gama rikita mata lissafi da salon wasannin sa cuz he really missed her a lot ji yake kamar ba zai sake iya ‘daukan lokaci ba tare da ita ba, Teemah kuwa duk da ranta ba’a sake ba amma yanda yake sarrafatan yasa har ta fara ‘daukan layi itama. 

Kukan da Annur ya saka lokaci guda ne ya ceceta domin kuwa da sauri ta ‘kwaci jikin ta tafi ta ‘dauki ‘danta ta rungume tana jijjiga shi. 

Abbas kam tana barin jikin sa yayi baya ya kwanta tare da lumshe idanu a fili ya furta ” Uwa! Uwa kenan!”
Wannan shine step na farko dake raba soyayyar mace ga mijinta domin matu’kar ta samu Baby to dole ne soyayyan babyn sai ya rinjayi na kowa ciki kuwa har da mijinta duk da dai baza’a ta bar son shi ta komawa danta ba amma na ‘dan sai yayi rinjaye fiye da komai. 

Story continues below


Abbas tashi yayi ya zauna yana kallon yanda take faman jijjiga shi da dukkan kulawa sai yaui mirmushi a hankali yace da ita ” ki kaishi wurin Ummah mana please sai ki dawo ” 

Sai cewa tayi ” ah ah Yayah barshi kawai ai zai yi shiru, Ummah ta gaji dayawa yau ‘din duk a wurin ta ya wuni tun da rana” 

“Hmm” kawai yace tare da ‘ko’karin sau’kowa daga gadon, sai daya sau’ko da ‘kafar sa ‘kasa sannan yace ” wato dai kince Annur ya fini ko?” 

Da sauri ta furta ” ah ah fa Yayah ai kaga d’azun kuka yake yi ne shiyasa” 

Tana maganar tana tahowa inda yake ta zauna daga gefen sa tare da raba Annur ‘din daga kafa’dar ta sai ta ri’ke shi a cinyar ta, Abbas ne ya ‘dauke sa ya ‘dagashi sama yana jijjiga shi yana murmushi, yaron ma kallon fuskarsa yake yi kamar an ce masa mahaifin sa ne. 

Abbas yana murmushi yace ” Ai dama na gaya miki, idan kin haihu nasan guduna zakiyi ki tattare duk ki komawa ‘dan ki, kika ‘ki yadda, ni kuwa nasan hakan dama sai ya faru gashi tun ba’aje ko’ina ba zance na ya tabbata gaskiya”

Murmushi tayi ta koma daga bayan sa ta rungume shi tare da fa’din ” afuwan Yayah ba haka bane fa, banaso yayi kuka sosai ne har Ummah taji kuma tazo kaga da kunya sosai hakan ai”
Yana kallon babyn yace ” to ni sai yaushe kenan za’a kulani… kin san fa gobe zan koma akwai aiki a gaba na, ko zamu je can ‘daki na mu kwana?” 

Kanta ta kawo gefen fuskar shi tace ” da sauran lokaci fa Yayah,kuma ma ni gaskiya ina jin kunya ace daga zuwan ka har na bika ‘dakin ka?” 

‘Dan b’ata rai Abbas yayi yace ” bana son fi’ili ni, yau kika fara kwana acan ‘din ne ko kuma yau ne kawai kunyar tazo miki?, ke ‘din nan naga alama kin gama gaji dani ko? shikenan  bakomai i know what to do kar ki damu”
Ya ‘karashe maganar cikin basarwa kamar wani da gaske. 

Ita kuwa jin yanayin da yayi maganar ne yasa ta sanyaya murya dan sai taji ba da’di cikin sanyin jiki tace ” me zakayi Yayah?”
A tsare yace ” amarya zanyi wacce bazata gaji dani ba” 

Cike da firgici ta saki wuyan sa tare da juyawa ta koma ta jingina bayan ta da nashi tana kuka tace ” an gaya maka ni ‘din gajiya nayi da kai ne?”

Sai yace “ah to nima na sani ne? In kina son in yarda baki gaji dani ba then tashi mu tafi ” 

Kuka ta sanya mishi tana hahharba ‘kafa tace ” Ni dai kagaya min in kaine ka gaji dani…ai ni ban fa’da ba. 

“Ban yi tunani akan hakan ba tukunna”
Ya fa’da cikin halin ko in kula. 

Shiru tayi mata yi magana ba, sai ta cigaba da kukan ta, shi kam tashi yayi ya nufi ‘kofa da babyn a hannun sa ba tare da ya sake kallon inda take ba. 

Bai damu ba yasan ko badan bayn bama dole zata biyo shin idan ya tafi ko dan rigimar ta ma dan haka hankalinsa kwance ya fice a ‘dakin. 

Dan haushi ma ita yana fita sai ta ta shi kamar an tsikare ta ta shige bayi, bata san me ya kawo ta bayin ba dan haka sai ta watsa ruwa kawai ta fito, tana fitowa sai suka ci karo da Hannah da shigowan ta ‘dakin kenan itama. 

Kau da kai Teemah tayi tamkar Hannah ce tayi mata laifin sai ta nufi gaban mirror tana goge jikinta dake ji’ke da ruwa. 

Hannah ta6e baki ganin bata ko kula ta ba itama bata damu ba dan tasan bazai wuci fushin Yayah bane take yi da har itama ta samu rabon ta. 

Duba gadon Annur tayi bata ganshi ba haka ma nasu gadon ma baya kai wannan dalilin ne yasa ta juya ta kalli Teemah tace da ita ” ina yaro na yake in mai gudnyt rabo na da shi tun da maghrib gashi bacci nake ji yanzun” 

Teemah bata juyo ba ta bata amsa da fa’din ” ki je ki kar6o shi a wurin Yayah”
Hannah sai cewa tayi
“Ta6’di ke de shirya ki kar6o shi ina jiranki kun fi kusa ai”. 

Story continues below


Shiru Teemah tayi ta cigaba da goge jikinta, bata shafa mai ba sai kawai ta ‘dauki turaren humrar ta tabi jikinta da shi sannan ta nemi kayan bacci riga da dogon wando ta sanya dan ita tafi son irin su dama. 

Tana gama shirin ta ‘dauki hijab ‘din ta babba ta sanya da silifas ta bar ‘dakin ba tare da ko kallon inda Hannah take ta sake yi ba. 

Zuwa lokacin kuwa tuni hankalin Hannah ya riga ya ‘dauku ga wayar data keyi bama tasan lokacin da Teemah ta bar ‘dakin ba. 

A hankali ta tura ‘kofar tare da yin sallama ‘kasa-‘kasa sai amsa mata shima ba tare da ya ‘dago ya kalle ta ba fuskar sa na kan ta Annur yana yi mai wasa. 

Shigowa tayi tare da tura ‘kofan sai ta ja ta tsaya ta na kallon su, ita haushin ta ‘daya warning ‘din da Anty tayi mata akan sa, sam bata son ya wargaza mata gyaran da aka soma yi mata tun ba aje ko’ina ba dan ko itama tana so ta tsumu ba yanzu ta so ha’duwar su ba, amma ga dukkan alamu ba fahimtar ta zaiyi ba har da cewa wani amarya zaiyi.
Tsaki taja a ranta ta dan ta tsani wannan kalmar sam.. 

A hankali ta ‘karasa inda yake ta tsaye nesa ka’dan dashi sannan tace ” Yayah kawo shi mu tafi kaga dare na ‘kara yi kuma Hannah ma na so ta ganshi “
Sai yace
“Ni kuma so nake mu kwana da shi ya za’ayi?” 

Shiru tayi ta tura baki gaba tare da ‘kura masa idanu, bata san yaushe Yayah ya koyi irin hakan ba bata san me ya canza shi ba dan Yayan ta data sani ada ha’kurarre ne akan komai, kallon kallo suka tsaya yi kiwa abinda ke ransa daban, shikam ransa fes babu komai illah so da ‘kaunar ta bayaga haka babu komai, shine ya yanke shirun nasu da fa’din ” Zo ki zauna ki bashi abincin sa naga yana shan yatsu” 

Zaman tayi kamar yanda ya fa’da ‘din ta mi’ka masa hannu akan ya bata babyn sai bai bata ba sai yayi mata nuni da hijab ‘din dake kanta. 

Ja tayi ta cire shi ta ajiye a gefe.
Abbas sai ya mi’ka mata Annur ‘din  sannan ya taya ta 6alla botiran saman rigar guda uku yace to ta bashi. 

Shi kam zuba musu ido yayi yana kallon yanda babyn ke sha cikin nutsuwa, babban abinda yafi tafiya da imanin sa ajikin ta bai wuce boobs ‘din ta ba, yanzun kuwa ganin yanda suka sake cika suka tsaya sai yake jinsa cikin wani yanayi, dan basuyi komai ba illah da ‘da cika da sukayi sosai yake kewar su yake kuma jin son sarrafa su. 

Har Annur yayi bacci Abbas na gefe yana kallon su, Teemah sai ta cire shi tana rufe bottles ‘din ta Abbas ya ‘dauke babyn cak ya kwantar da shi sannan ya rungumo ta ta baya tare da ri’ke hannun ta a hankali yace ” saura ni ko”. 

Shiru tayi sai ya juyo da ita ta fuskance shi ya sake fa’din ” aji dani nima” 

Tana ‘ko’karin yin magana ya ‘dora yatsan shi saman la66an ta alamun tayi shiru dan yasan bai wuci complain zata yi ba, matso da fuskar sa yayi kusa da nata ya ha’de musu hanci suna jin ‘dumin numfashin juna tare da sau’ke hannun san dake saman bakin nata ya jone bakin nasu wuri guda ya fara shan harshen ta, tsawon da’ki’ku kuma sai ya tsaya tamkar ya manta me yakeyi yayi jim, Teemah kuwa da ta ga haka sai ta cigaba da kissing ‘din nashi kamar dama can ita ta fara.
Ita kanta tasan tayi kewar shi kawai dai bata son ta watsar da maganar Anty ne shiyasa take ‘dan denying ‘dinsa, kuma gashi tana jin nauyin Ummah bazata iya sakewa da shi a gidan ba.
Tana cikin tunanin sai taji hannun sa a cikin rigar ta yana mata tafiyar tsutsa har zuwa saman ‘kirjin ta. Ajiyan zuciya kawai ta sau’ke duk dama bai fito fili ba amma yanda yaga yake samun response ‘din ta ma sai bai yi tunanin kusantar ta ba ya tsaya a iya romance ne kawai ba komai da ya mata.
Inda ya ‘dau tsawon lokaci yana juya ta son ran shi haka kuma itama dan sai da ta tabbatar tayi easing abinda ke damun sa kafin sukayi bacci manne da juna tuni ta manta da fushin amarya.

Hannah kam har ta gama waya tayi zaman jiran Teemah amma shiru har kusan 11pm kawai sai itama ta kwanta tayi baccin ta ganin basu da niyyan dawowa. 

Story continues below


Da asussuba Teemah ko ta gudo daga ‘dakin sa wai dan kar Ummah tazo ta ga basa nan.
Sallah ta samu Hannah nayi dan haka sai ta kwantar da Annur ta tafi bayi itama sai da tayi wanka kafin ta ‘dauro alwala ta fito. 

Da ta idar da sallar ne Hannah ta jefa mata tambayar
” Yayah ne ya ri’ke ku ko” 

Da’din tambayar Teemah taji dama bata so Hannah taga kamar itace ta ‘ki dawowa dan haka da wuri ta bata amsa da fa’din ” ai wallahi kamar kinsani…Yayah cewa yayi wai shi sai da ‘dan sa zai kwana, ni kuma wallahi kunyan Ummah nake ji kar ta gane a wurin sa muka kwana shiayasa ma kika ganni sassafen nan”
Hannah kuwa sai tace
” Hmm, kin makara ai Ummah da dare tazo duba Annur wai ko yau ma ya’ki yin bacci irin na jiya? sai nace mata ai kun tafi wurin Yayah” 

Zaro idanu Teemah tayi tace ” dan Allah Hannah dagaske?, na shiga uku ni kam yanzu ya zanyi duk fa laifin Yayah ne Allah” 

Hannah murmushi tayi tace ” Firgici haka sai kace dagaske bayan kinje kin ‘din kuma miye abin damuwa?”
Teemah sai tace
“Ba zaki gane bane Hannah ke kam, ai da kunya irin wannan abin, ni dan Allah ki gaya min ya zanyi?” 

Murmushi Hannah tayi yanzun ganin yanda duk Teemah tabi ta rikice sai tace da ita
“Wasa ni nake miki dan Allah ki nutsu, bata zo ba kuma yanzu kam ai bazata sani ba tunda kun dawo,  amma shine kuma kuka barni na raba dare ina zaman jiran ku bayan kin san bazaku dawo ba…Allah naji haushi?”
Ajiyan zuciya Teemah ta sau’ke tare da fa’din 
“Very sorry lil sis baza’a sake ba”
Ai ma baki san wani abu ba? Yaron nan in gaya miki yau ko damuna baiyi ba yayi ta baccin sa….”
Hannah sai tace
“Ah to yaga innar sa taje neman lada ba dole ya risina ba”
Fa’din Hannah tana murmushi. 

Teemah sai tayi murmushi kawai batare da tayi magana ba.

Aranar kuwa Abbas ya koma kamar yanda ya fa’da mata, ita kam da fatan alkhairi ta bisa dan bazata iya ce ga takamamman yanayin data ke ji game da shi ba, fama take da zuciyar ta tana ta ‘ko’karin ‘karya ta kewar shin data ke ji ‘karfi da yaji ta sanyawa ranta ‘karfin hali da nuna halin ko in kula game da tafiyar sa tasa.

Teemah tun bayan sati da haihuwar ta tafara yin sallah, gyaran da ake yi matan kuwa ba ‘karamin fitar da ita yayi ba, idan ka ganta tashin farko bazaka ta6a cewa itace ta haifi Annur ba, dan yanda tayi ‘das abinta abin ba’a cewa komai. 

Kullum matar take zuwa daga 10:00am zuwa 12:00pm tayi mata duk abinda zata yi ta tafi so gyaran bai wani takura ta ko shiga lokutan wasu al’amuran ta ba. 

Shi da Abbas a nufin sa wai suna gama 40days ‘din nasu zasu koma amma Ummah ta tayi babakere tace sam bata ji zancen ta haka ba sai sun ‘kara hutawa. 

Abbas har ransa ya ‘dan 6aci da hakan amma sai ya 6oye bai nunawa Ummah ba, sai dai Teemah da suka ke6e da ita ya bayyana mata halin daya ke ciki inda ta matu’kar tausaya masa tana jin ba dan Ummah mahaifiya ba ce da babu abinda zai hana ta bin mijinta, domin ita kanta tasan yayi ha’kuri sosai sai dai bazata iya ja da batun Ummah ba dan haka kawai sai tai ta bashi baki har ya ha’kura ya koma Ports. 

Wasa-wasa har sai da suka haura 2months da ‘yan kwanaki kafin Ummah ta bashi matar sa, hakan ma sai data ga ya shiga wani yanayi kafin nan ta sallame su domin a wani zuwa da yayi ya ri’kewa Teemah wuta Annur nata faman ihu amma bai ko kula da hakan ba, Teemah ce ma hankalin ta ya kasu biyu amma shikam yayi nisa cikin son kasancewa da ita, k’aran bugun ‘kofa ne yasa shi ‘kyaleta ba wai dan yaso ba yayi saurin kintsawa tare da zuwa ya bu’de ‘kofan, ganin Ummah yasa shi jin kunya take yayi ‘kasa da kansa yabi ta gefen ta ya fice daga ‘dakin batare da ya ha’da ido da ita ba, Ummah kam da kallo ta bishi cikin ranta tace ” kaji kunya ai fitinanne kawai”. 

Duban ta ta mayar kan Teemah dake faman jijjiga Annur tana sussunne kai itama Ummah sai tace ” ki bashi ko ruwa ma yasha zaiyi shiru”
Da kai Teemah ta amsa mata batare da ta ‘dago kai ta kalli Ummahn ba. R

“Hmm”
Kawai Ummah tace a zuciyar ta kana tayi waje da tunanin yanda Fateemahn zata iya kulawa da iyalan ta Annur dacwannan fitinannen ita ka’dai, ita Ummah tausayin tane yasa ta kasa barin ta koma masa har yanzu, dan gani take Teemahn bazata iya kulawa da babyn ita ka’dai ba, a hakan ma cikin kwanakin nan tana barin ta tana yiwa Babyn abubuwa da kanta wai dan ta koya ta saba kama daga kan wanka, shirya shi, goyo rarrashin sa idan yana kuka harma da canza masa pampers duk ita ke yi da kanta, Alhamdulillah kuwa ba laifi tana ‘ko’kari sosai dan haka washe gari Ummah ta sallame su suka koma gidan su, da yake ma already ya kammala ginin sa dan haka babu 6ata lokaci suka dira a can. 

Sosai tsarin gidan ya bambanta da gidansu na farko dan wannan mansion ne guda ga kyau ga girma, kallo ‘daya zaka yi masa ka tabbatar yaci ku’di na gaban kwatance. 

Sosai gidan ya birge Teemah, ga ‘dakuna wadatattu wanda mutane kusan goma ko ma sama da haka zasu iya rayuwa aciki batare da wani ya takura ‘dan uwan sa ba. 

A ranar kuwa Teemah har sai data gane ashe dama shayi da zallar ruwa ake yinsa, sosai ta daku a wurin sa ta sha uwar wuya dan kac-kaca yayi mata, ‘dinkin da akayi mata ne ha’de da gyaran da tasha sai ya suka ha’du suka matse ta. 

Shi kam Abbas baya jin gari sai yi yake yana ‘karawa har da bashin sa na baya sai da yayi, shikan sa yayi mamakin yanayin daya same ta domin bai yi zaton haka ba duba da haihuwa da tayi amma sai ya same ta ba yanda ya zata ba hakan ne kuwa ya kusan zautar dashi. 

Sai da komai ya lafa bayan har sunyi wanka ma sun koma sun kwanta dayake abin na ransa sai bai yi ‘kauron baki ba hannun sa cikin gashin ta a hankali yace da ita ” ban fa gane ba wai dama haka ake sake canzawa idan an haihu, gaskiya in dai haka ne next year ma zaki ‘kara haifa min little princess ‘di ta, kinji yanda kika koma kuwa har nayi zaton ma ai ko da amarya ta nake tare fa?”
Ya ‘karashe maganar da murmushin tsokana. 

Teemah kam bata ‘dago ba sai hannu da ta kai ta kamo kunnan sa taja da ‘karfi  sai ya ce ” awshhh zaki ciremin kunnn fa?”
‘Dan sassautawa tayi tare da fa’din “can’t u see yanda ka ci zalina ko ?”
Abbas sai yace
” Sorry babe ba laifina bane ai duk laifin kine da kika rikitani…ban ma gaji ba fa na barki ne ki ‘dan huta kawai kafin nan”. 

Cikin shagwa6a tace ” ni dai ba ruwana ai baka jin tausayina shine har kake cewa next year in sake haihuwa kama san wahalar dana sha  kuwa kafin na haifi Annur?” 

Yace ” ina tausayin ki mana kinfi son sai na fa’da da baki ne?”
Sai tace ” ai cewa kayi wai in ‘kara haifan baby” 

“Ehh mana zaki haifa min Doctor mana daga ita shikenan sauran kuma ganin damar kine?”
Teemah kam kafa’da ta no’ke tace
” Ni dai ah ah baga Annur nan ba?”
Abbas amsa ya bata da fa’din
” shi ai zai gaje ni ne, burina uku ne kacal a duniya a yanzu nasamu biyu, kinga na farko na sameki wannan ya wuce, sauran kuma shine inga na samu yara na sun kuma cika min burina na zama doctor da kuma airforce ko bana raye ki cika min wannan Burin kinji…..insha Allahu Annur ‘dina Major Mahmud Muhammad Al-hassan ne kinga insha Allahu in da raina Burina na biyu zai cika da yardar Allah is just d matter of time, kinga saura na ukun sai ki sake haifamin wata babyn wanda ko su biyu ka’dai Allah ya bani bazan yi takaici ba zan gode masa dan sune cikar BURINAH, idan ma suka fi hakan duk ina so bazan ‘kiba sai dai fatan Allah ya bamu masu albarka” 

Teemah a ranta ta amsa da Ameen a zahiri kuwa kawai sai tayi shiru.

Yace ” kinyi shiru baki ce komai ba me yafaru?” 

A hankali tace ” ba komai” 

Murmushi yayi tare da fa’din ” matsoraciya an gaya miki ana surrender ne addu’ah akeyi sai kiga Allah ya kawo da sau’ki ko har kin daina son yaran ?” 

Teemah cewa tayi
“Ah ah baga Annur ba ai shima ya isa ” 

Sai yace
” ni bai ishe ni ba to”
  

“Allah ya kawo masu albarka to”
ta fa’da da ‘kosawa. 

Abbas kuwa cikin farin ciki ya ce ” yauwa uyan mata na abinda ya kamata ki fa’da tun ‘dazu kenan ai” 

Da haka bacci ya ‘dauke su kantacakan hannun sa tayi pillow dashi. 

***** 
*Wai ina labarin Munnira ne?* 
Munnira na can yanzu rayuwa tai mata ba da’di domin bata samun ku’di kamar baya, hatta kasuwancin da mahaifiyar ta ke yi ma sai da ya ja baya saboda ‘karancin ku’di, ita kam Munnira hakan bai wani dame ta sosai ba, babban abinda ya dame ta a yanzun shine neman gafarar mahalicci bisa ga abubuwan data aikata a baya, tun daga yawace-yawacen bin maza, zuwa wurin boka rashin cika ibadar ta ga kuma hakkin bayin Allahn data ‘dauka wanda duk da da kunnan taji Mahmud yace ya yafe ta amma sai ta kasa sakin ranta gani take yi kamar alhakin bazai ta6a barin ta ba. 

Bata da abin yi a yanzun daya wuci ibada da istighfari tare da ro’kon ubangiji neman samun kyakkyawar ‘karshe, bata damu da komai na duniya ba a yanzun, tuntuni ma ta yanke cewar zata koma sokkoto gidan kakannin ta gaba ‘daya da zama ko dan ta samu islamiya mai kyau ma ta shiga ta nemi ilimi. 

Allah cikin ikon sa kuma kafin tafiyar sai Allah ya ha’da ta da wani bahaushen ba kano, babban mutun ne domin matan sa har gudacbiyu da yara kusan bakwai, kasuwanci ya kawo shi garin ikko da nufin ubangiji kuma sai ya ha’da su inda ba’a wani ‘dau lokaci ba aka saka ranar auren su wanda akayi kafin bikin su Hannah aka kaita kano cikin matan sa, da da’di ba da’di haka dai rayuwar tayi ta gungurawa.

Kishiyar Anty ma ta haihu inda Allah ya nufi Abbah da samun kyautar ‘yan biyu mace da namiji tsaban murna Abbah har sai da yayi hawaye haka duk wanda yaji ma farin ciki sosai yake tayashi.
Ranar suna yara suka ci sunan Mahmud da Khadija (takwaran Mummy.
inda Abbah ya hana acanza wa namijin suna yace a ‘kirashi da Mahmud ‘dinsa macen ce dai ne ake ‘kiran ta da Nanah.

Sati ‘daya da komawar su suka nufi Dubai inda suka yiwa Mummy diran mikiya, bazata kawai ta gansu da mamaki dan batayi zaton haka ba. 

Yanayin yanda ta saki baki da ganin sun yasa suka kwashe da dariya Teemah har da ri’ke ciki taje ta rungume ta gudu tana fa’din ” mu ‘din ne de Mummy ba mafarki kike yi ba”. 

Murmushi Mummy tayi tace ” kun shammace ni ne ai shiyasa” 

Daddy kam daya gansu kar6an lil Mahmud yayi a hannun Mummy yana fa’din
” Masha Allah yaro har yayi wayo yace da Mummy ta bashi abokinsa su gaisa yasan cewa yana da babban aboki.
Kusa da Abbas yaje ya zauna da babyn a hannun sa ya kamo kunnan Abbas yana ja tare da fa’din wai dan yayi familyn kansa shine ya manta da shi ko a wayar ma bai fiya ‘kiran sa ba sai sa’in da yaga dama…..” 
yana yin yanda Abbas ke neman agajine ya saka Teemah murmushi Daddy kuwa ya’ki sakin shi sai ji sukayi yace 
” Daddy Annur fa na kallo kuma zai min dariya”.
Sakin kunnan nashi Daddy yayi suka ‘dan dara gaba ‘daya, sai Daddy ya ‘daga Annur sama yana ‘dan jujjuya shi yana murmushi, shima Annur  idanun sa na kan Daddyn kamar wanda yana gane kamar sa ne, Daddy albarka ya ta sanyawa yaron tare da yiwa mai sunan sa addu’ah kana yace daga yau ya samu aboki tunda Abbas ya ‘kisa. 

Su Teemah kam na ganin Mummy ai sai shagwa6a ta dawo sabuwa fil, kacokam ‘dawainiyar Annur ta tattara ta barwa Mummy, ita kam sai dai zuwa yawo da Abbas suje can suje nan har mantawa take yi da tana da yaro ma a gida, kwanaki ka’dan ne kawai suka fita dashi da yake ma bashi da rigima sosai indai a ‘koshe yake baya kuka shiyasa ma take barin sa hankalin ta a kwance. 

Satin su biyu a Dubai sai suka dawo inda suka sau’ka a Lagos gidan Anty ya barsu shi kam ya tafi hotel, duk da Abbah ya nuna rashin jin da’din sa akan hakan amma Abbas bai ce da shi komai ba dan shi haka kawai yake jin nauyin Abbah fiye da yanda yake jin na Daddy ma, har gani yake tamkar Abbah shine Father in-law ‘din nasa ma, Anty ce de har yanzun ya kasa sabawa da ita da ma halayyar ta, kallon ta yake yi a komai yana ganin tamkar gaskiyar ta ka’dan ce a kullum. 

Sun ziyarci gidan Umar ma inda iyalan sa suka yi matu’kar farin ciki da hakan tarba mai kyau suka samu daga wurin Maman Amal inda suka rin’ka yabon kyan Baby Annur da yaran ta, har ji suke tamkar Fateemahn kar ta tafi. 

Abakin Anty suke jin labarin irin muguwar cutar infection ‘din da ya ci ‘karfin Anty chiddy ya ri’ke harda ‘kafafun ta hatta tafiya ma bata iyawa a yanzun, mijin ta ma wai ya koreta daga gidan sa saboda asirin da ta tayi masa duk sun samu matsala hankalin sa ya dawo jikin sa kamar kowa, basu ma san inda take ba a halin yanzun. 

Teemah kam yanzu ko sunan matar ma bata ‘kaunar tunawa gode wa Allah kawai take yi da bai bawa Anty Chiddy nasara akan ta ba ta cimma burin ta, tasan ba dan ikon Allah ba da yanzu itama ta zama wani abu daban ” Alhamdulillah”  kawai take ta nanatawa tare da tuno rayuwar ta na baya, sai hawaye ya gangaro mata, fakan idanun su Anty tayi ta goge shi Abbas ne ka’dai ya lura da ita amma bai hana ta ba kawai ya ‘kura mata idanu.(Allah ubangiji kayi katanga da sharrin shai’dan kasa mufi ‘karfin zu’katan mu AMEEEN). 

Story continues below


Har gidan amaryar Abbah suka je inda taga ‘yan biyun Abbah gwanin sha’awa sosai suka birgeta, ga Nanah name sake d’in Mummyn ta itama kyakkyawa da ita.
Photo ta ringa ‘daukan su a wayar ta gwanin birgewa, sosai twins ‘din suka shiga ranta sai taji tana sin su amma da ta tuna wahalar da ake sha kafin a haihu sai kawai ta basar ji take badan haka ba da babu abinda zai hana ta ta ringa ro’kon ubangiji ya bata itama.
Amma wahalar da ta sha kafin ta haifi Annur yasa take jin shika’dai ma ya isheta rayuwa. 

Kwanan su uku a Lagos suka koma gida bayan Abbah yayi musu kyauta ta musamman wanda da ‘kyar Teemah ta kar6a da yake ku’dine cash ya bata sai taji nauyin kar6a har sai da Anty ta sa baki kafin ta kar6a, suna isa gida kuwa ta ha’da Abbas da su. 

Bayan komawar su ne Teemah ta bawa Hannah labarin abinda ya sami Anty chiddy, Hannah ita kam ” Allah shi ‘kara” tace cuz ta tsani matar dama sosai tun asali. 

Daga baya sai suka hau hirar Dubai inda Hannah ke jin haushin rashin zuwan da bata yi ba da yake tun bayan bikin Teemah da Mummy zata koma Hannah ta so binta amma makaranta ya hana ta amma still burin hakan na nan acikin ranta.
Hannah bata koma ba sai da yamma bayan sun gama hirar ta su kafin Hannah ta koma gida cike da tsarabobi. 

A kullum Teemah nazarin kalar rayuwar yanzu take yi musamman lokacin da sukayi waya da Anty ta sanar da ita cewa ashe Anty Chiddy Momcyn ta ma koran ta tayi saboda dama tana kawo ku’di ne shiyasa ta ke jan ta ajiki yanzu kuwa da baubu ku’din sai cuta sai taga cewa ai tatsanta kawai zatayi daga cikin ‘dan abinda take dashi tunda ita yanzun bata da wani amfani, dan haka sai ta korata ta’ki zama da ita, koda tabar gidan kuwa cikin rashin sa’a da wani dare ‘yan iskan gari suka zo ‘dan inda suke fakewa da wasu ‘kawayen ta da basu guje ta ba anan suka yi raping ‘din su inda suka yi musu kaca-kaca sa’annan suka cire mata mama duka biyu da ranta da komai azaban hakan ne ya kashe ta inda aka tshinci gawansu su biyu a wula’kance.
(Rayuwar dama kenan, shuka alkhairi ne ka girbi khairi sa6anin haka kuwa kaima kasan makomarka, dama duk wani mutun a duniya sarai yasan abinda yake aikata wa, wallahi kowa yasani inma sharri kake yi kasani haka ma khairi, sai dai idan shai’dan yayi galaba akan kane shine sai kaga ka kasa fuskantar gaskiyan balle har ka bita).
ALLAH UBANGIJI KA SHIRYAR DAMU BISA HANYA MADAIDAICIYA KASA ‘KARSHEN MU YAYI KYAU AMEEEN.
Labarin mutuwar Anty Chiddy sosai ya ta6a zuciyar Teemah sai yanzun take jin tausayinta amma kuma hakan baida amfani saboda a kurarren lokaci ne, kuma gashi bata kasance cikin musulunci ba balle tayi al’kawarin tunawa da ita cikin addu’ar ta.
Abbas kam data sanar dashi shiru yayi ba furta komai akai ba sai ma ya fara ‘ko’karin mantar da ita damuwar data ke ciki da salon sa. 

Teemah na kula da Annur ‘din ta kamar yadda kowacce uwa kake yi dan a kullum ta kalle ahi jin kanta takeyi tamkar wata babba ga wani son Annur ‘din dake ratsa ta kullum ta dube ahi, har bata so taji muryar shi yana kuka, idan ka ga yanda take lalla6a abinta har zakayi mamakin ta, har ayanUn ta kuwa idan Annur ya rikice da kuka ta kasa rarrashin sa itama kukan take sanyawa cuz idan yafar irin kukan baya sauraren komai ko me zata bashi ba shiru yake yi ba. 

Akwai ranar da Abbas ya same ta a irin halin sosai sai ta bashi dariya amma bai kulata ba sai ya ‘dauki Annur daga cinyar ta yayi ya lalla6ashi har ya tsagaita kukan, kafin ya dawo da kallon sa gareta a lokacin Annur na kwance akan ruwan cikin sa yana sau’ke numfashin kukan da yayi.
Suna ha’da idanu sa ita sai ya saki murmushi yace ” wai dama haka kuke yini kuka idan bana nan?” 

Share hawayen tayi da hannun tana ‘kif’kif da idanu tace
” Shine ai baya jin magana kullun sai ya ringa kuka”
ta fa’da cikin shagwa6a66iyar muryar ta, abin sosai ya bawa Abbas dariya sai yace da ita ” har kin daina son shi dan yana kuka ko?” 

Da sauri ta jijjiga kanta alamar ah ah, sai ta ‘kara da fa’din ” ai idan yayi shiru shikenan”
Murmushi yayi mata kawai ya ya kai hannun sa bayan ta sai ta taho itama ta kwantar da kanta a jikin sa Abbas sai ya cusa hannun sa cikin gashin kanta.
A hankali yace da ita ” idan kina kuka haka ai shima bazai daina ba, ko kina son ya raina ki yace kema kina kuka irin nashi?” 

Story continues below


Jijjiga kai taui sai yace ” toh kar kina yi masa kuka idan yana shi sai ki rarra she shi kawai har yayai shiru kinji?” 

Yayah ai shi’din ne ba yaji idan ya fara kuka”
Sai ya tareta da fa’din
“…karki damu zane shi zanyi ai ince ya daina yiwa ‘yan matana kuka”
Murmushi yai kawai dan ta fahimci da gangan kawai yake yi mata in ba haka ba miye abin duka ajikin Annur. 

Kwanaki sun ‘dan ja har lokacin bikin su Hannah yayi inda ranar wata juma’ah aka ‘daura auren Hannah da Bilal bayan sallar juma’ah haka ma Leesah wacce aka kaita gidan mijin ta dake Kaduna. 

Hannah kama tana nan cikin gari aka bar ta a wuse 2 dan Bilal bada ita zai tafi ba saboda makarantar ta sai aka barta a Abuja kafin ta kammala gaba ‘daya. 

Ana kammala bikin su Hannah Abbas ya tattara iyalan sa suka koma Rivers, dayake dama hutun kwanaki ya kar6a kuma ya koma shi ka’dai ya bar su su ‘dan kwana biyu ma ya’ki amincewa.
Hatta Ummah tasa baki amma ya’ki yadda Ummah kam sai cewa tayi ” fitinanne kawai ni dai Allah yasa kar yaron nan ya biyo wannan halin naka da ba’a gane kanka sam”. 

Duk kissa da marairaita tayi dan ya barta amma ya’ki dole badan taso ba ta tattar suka koma a taren. 

Zuwa yanzun Annur yayi wayo sosai har yana gane mamar sa dan watan sa shida da haihuwa yayi 6ul-6ul abinsa, yayin da yana girma kamar sa da Abbas na sake bayyana ajikinsa da fuskar sa ma gaba d’aya. 

Watarana da dare lokacin tana yi masa shirin bacci diaper take sanya masa yana ta irin surutan su na yaran nan da hannunsa abaki, Abbas ma na gaban mirror fitowan sa kenan daga bathroom yana tsane jikinsa da towel a hannun sa Teemah sai tace ” nifa Yayah bangane wannan abin ba, yaron nan na lura ko kalar farce na bai ‘dauko ba kawai ya biyo ka gaba ‘daya dube shi dan Allah da wani idanu ko ina zai kaisu oho”
Abbas na jin abinda ta fa’da ‘din sai ya taho a hankali zuwa inda suke ‘din yana murmushi yace ” kina ba’kin ciki ne dan yaro na ya biyoni? so yake ya gaji babansa shiyasa amma ai wannan ‘kananun surutun da yake yi  kam ba nawa bane sai de in ke kike koya masa irin nakin nan…, ni kuwa bana son ya ‘dauko irin surutun kin da ‘kin makaranta kinnan….. in kika kuskura kika koya masa kuwa nida kene” 

Teemah murmushi tayi kanta na ‘kasa tana cigaba da shirya Annur tace ” ai ba haramun bane dan nace bazan yi makaranta ba” 

Juyawa yayi yana komawa gaban mirron yace
” ke de fa’di gaskiya ‘yan mata”
Itama sai tace
” gaskiyar kenan ai”
Murmushi yayi mai sauti bayan ya isa gaban madubin yace ” kinsan me yasa ya yi kama da ni?” 

Waigowa tayi tace “ah ah ” tare da juya kanta ta kalle shi.
Cigaba yayi da fa’din saboda jarumtar da na nuna ne gurin ‘daukan cikin sa kema in kina son mai kama da ke sai kiyi ‘ko’kari ki nuna taki kalar jarumtar” 

Bata ma san lokacin da ta banka masa harara ba tana murmushi. 

Sai yace ” ni kike yiwa haka ko, zaki ha’du dani ne yarinya zaki gane da waye kika yi”
Ya ‘karashe maganar yana ‘dan dariya.

*****
*Bayan shekara ‘daya*
Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa  har da haihuwar Anty Leesah inda ta haifi baby girl ‘din ta mai suna Aisha amma suna ‘kiran ta da Nihal, Hannah kuwa yanzu ne ma take da cikin da bai fi 2-3month ba ga uban wahalar laulayi da take sha duk ta fita hayyacin ta gaba d’aya, har mamaki takeyi irin cikin Teemah yanda har cikin ya zama mutun ajikin ta ba tare da sun san da shi ba, ita kuwa tun baa je ko’ina ba ma ya bayyan kansa, cuz tun yana 1month ya fara wujijjiga ta da su amai ga za6an abinci kamar masifa, Teemah kanta tausayin ta takeji yanzun.
Domin taso rana tsokanan ta amma yanda yanayin Hannah ake sai ta ma manta da waccen batun tausayin ta duk ya cika ta. 

Munnira kuwa babu labarin ciki agareta dan ta ziyarci asibitoci kusan uku ma amma duk ce mata suke yi mahaifarta ta riga ta lalace ikon Allah ne ka’dai zai sa ta haihu ko da gaba ne. 

Story continues below


Munnira tayi kuka sosai da jin sakamakon ta amma daga ‘karshe sai ta ha’kura ta fawwalawa Allah komai dan tasan shine ka’dai mai bayarwa da hanawa in da rabon ta samu ko min daran da’de wa wataran zata haihu. 

Anty ma kullum mutuwar Mahmud sabo yake dawo mata musamman idan taga yanda Abbah ke nan-nan da twins ‘din sa gashi kullum cikin farin ciki zaka ganshi saboda bashi da damuwar komai, koda kuwa ranar da yake gidan ta ne Abbah dole sai yayi waya da yaransa duk da dama ba maganar suka iya sosai ba amma a hakan wai shi muryar yaran sa yake son yaji, cikin dokar kwanan su ma sai da ya ro’ki Anty akan ta yi ha’kuri koda lokutan girkin tane yana so yana zuwa  dubo yaran sa dan bazai iya har kwana biyu kuma suna gari ‘daya amma bai gansu ba tare da ‘daukan mata al’kawarin babu cin amanar ta koka’dan da zaiyi bayaga ganin gudan jininsa. 

Dolen Anty ta amince batare da ta nuna masa damuwar komai ba a fili, duk da bata ba’kin ciki da yaran nasa amma ita ka’dai ta san yanda take ji idan taga Abbah na zumu’di akan ‘yan biyun yaran sosai ta ke ‘kara neman gafarar mahalicci akan banzatar da rayuwar nata ‘dan da tayi sanadin haka ma yasa kullum sai Mahmud ya samu kyakkyawar addu’ah daga wurin ta bata ta6a shagala da hakan ba.
Gashi itama Allah sai ya jarabce ta da masifar son twins ‘din, ji take kamar ta ‘kwato su a wurin ta, amma babu dama lura da hakan da Anty Sadiya tayi yasa ta yanke aranta cewa idan ta yaye su zata bata little Mahmud kyauta ya zama ‘dan gidan ta in yaso ita sai ta ri’ke Nanah in Allah yasake bata wani kuma sai ta hada ta ri’ke su, kuma tana da ya’kinin Abbah ma bazai ‘ki amincewa ba, inyaso sai suyi yarjejeniya koda a rubuce ne akan bazata ta6a goran ta mata ko kuma kar6an sa ko da kuwa menene zai faru yariga ya zama ‘dan ta, ta dan itama Anty Sadiyan tausayin Anty take ji sosai. 

Tana yaye su kuwa ta sanar da Abbah ku’durin ta sai dai Abbah ya so ya nuna ‘kin amincewar sa sai da ta ta fahimtar dashi kafin nan ya yarda, amma ba wai har ransa ba dan shi yaso yaransa su taso a tare kamar yanda aka haife su kuma a hannun mahaifiyar su saboda ya yaba da hankali tarbiya da nutsuwar ta k’warai da gaske shiyasa bashi da haufi akan tarbiyar da zata bawa yaransa. 

Da Anty ta sami labarin hakan kuwa har sai da tayi kuka dan farin ciki, tun da aka yaye su aka kawo mata shi sai ta sa aka nemo mata mai kula dashi tun daga kano tazo tana tayata rainon sa da kukawa dashi Anty kam sosai taji da’din wannan karamcin kawai sai take ta godewa mahalicci bisa ga chance ‘din daya sake bata akaro ba biyu matsayin mahaifiya wannan karon kam tana jin rayuwar ‘danta zai kasance ne kishiyar rayuwar da ta bawa Marigayi bazata sake yin haukan da tayi a wancan lokacin ba zata ja ‘dan ta ajiki ta bashi tarbiyar data dace ta kuma cika rayuwar sa da farin ciki har sai yaji cewa yafi kowa sa’an mahaifiya. 

Wannan abin da amaryar Abbah tayi ba ‘karamin daraja ya ‘kara mata a idanun Anty ba, sai take jinta tamkar ‘yar uwarta ta jini domin tayi abinda ba kowa ne zai iya ba a wannan zamanin da kishi ya zame wa mata tamkar ibada a zu’katan su.

*****
Teemah ma tuni ta yaye Annur ‘din ta tun yana da 15months da haihuwa ganin yanda yake girma, tsayi da wayo duk lokaci guda, yana da 7 month yafara takawa, da kansa ma sai bai damu da yasha maman ba, dan wataran a yini bai fi sau biyu yake sha ba kuma ko bata bashi ba baya rikici, ganin hakan yasa Abbas yace da ita kawai ta daina bashi ma gaba ‘daya ita kama ai dama gaba ta kaita dama bata son ta jima da shi abakin mama har ranta take jin tsoron kar su lalace ganin cewa Abbas nan yafi so a ilahirin jikinta shiyasa take nan nan da shi itama. 

Ginin makarantar ta da Abbas yace za’a yi mata ma an kammala shi tuntuni amma a Abuja aka yi, wanda makarntar ta tsaru iya tsaruwa, sosai Abbas ya kashe maku’dan ku’da’de dan ganin makarantar ta ginu bisa tsari da daraja  har an luncher shi, inda ake bayar da karatu arabi da boko daga 8am to 5pm ha’de da babban masallaci aciki 6angaren mata da maza, inda suke ajiye fannin boko ‘karfe ‘daya bayan sun yi sallah sun ‘dan huta kuma  2:30 sai su siha fannin islamiya sosai ake horara da yara kan dukkan 6angarorin biyu.
Abbas ne ya sanyawa makarantar suna A-Z international School, kuma ba laifi makarantar ta samu kar6uwa sosai musamman da yake suna da fannoni da dama tun daga 6angaren Nursery, primary har secondary duk aciki. 

Story continues below


Haka kuma Abbas bai manta da su Innah ba, bai sake komawa ba kam amma a duk ‘karshen wata yake transfer ‘din ku’di wa Rabi’u wanda yasan zai ishe su hidimar makaranta da kuma gida, kuma Rabi’u na ‘ko’karin ‘kiran sa akai-akai yana ha’da su da Innah ma su gaisa da ita.
Yanayin yanda yake jin ta ka’dai ma ya ishe sa sanin cewa Rabi’u bai ci amanar su ba daga abinda yake tura masa.

*****
Wata ranar Alhamis da ‘karfe biyu na rana 2:09pm,
Abbas ne ya shigo gidan jikin sa uniform kaki ne da hular sa da wayar sa duk ri’ke a hannu. 

A gajiye yake gaba ‘daya dan haka sai ya zube a parlour kan kujera yana ‘kwala ‘kiran sunan ta. 

Teemah iska ta hura a bakin ta ta furzar da jin muryar tashi bata so ta amsa da ‘karfi har baccin da Annur ya fara yanzun ya yanke gashi daga jin tashin muryar Abbas ‘din har ya bu’de idanu dayake baccin ya ‘dan fara cin idanunsa sai take ya kuma mai da wa ya rufe su tasan badan baccin ba da ko ita bata isa ta riga shi isa wurin Abbas ‘din ba, dan wata muguwar sha’kuwa ce a tsakanin su, itan ma shiru tayi bata amsa ba dan kar ta tashe sa tun safe be yi bacci ba sai rigimar tsiya yau ‘din yake ji dashi, hatta bathroom bai barta ta shiga ba sai da ya bita sukayi wankan tare, inda da dabara ta samu da tayi masa nasa sai ta ha’da shi da abin wasa cikin bathtub daya ‘dauki hankalin sa sannan ta samu ta faki idanun sa tayi wankan ‘kar’kashin shower tana yi ma tana kallon sa dan kar ya lura da ita bata wanke fuska ba ma sai bayan ta d’aura towel jikin ta sannan ta wanke fuskar tata daga nan sai ta ‘dauko shi suka fito. 

Tsawon mintina biyar tana lalla6a shi tare da mai wasa cikin kunnan sa da hannun ta sannan ta samu baccin ya ‘danyi nauyi, sai ta sau’ko daga gadon a hankali ta baro mishi ‘dakun bayan ta daidaita masa ‘karfin fan yanda iskan baze yi masa yawa ba….jikinta bomshot ne na blue jeans da wata ‘yar 6ingilar riga mai bu’da’d’den gaba sky blue sosai tayi kyau cikin kayan kamar ‘yar turawa. 

A parlour ta hango shi zaune idanunsa a lumshe ya kishingi’da ga dukkan alamu agajiye ya dawo domin yanayin sa ne ya fallasa asirin zuciyar sa, ‘kafafunsa kawai ya iya sa6ewa daga cikin boot ‘din dake ‘kafar sa baya ga haka babu abinda ya sauya daga yanayin shigar sa. 

Isa tayi ta zauna daga gefen sa taja hancin sa a hankali tana murmushi, shima ‘din murmushin yayi batare da ya bu’de idanu ba.
Sai da ta zauna da kyau kafin tace ” Saura ‘kiris ka hana min yaro na bacci da wannan ihun naka fa, da bai yi ba kuwa yau ‘din zaka koyi goyo babu ruwana” 

Bu’de idanun yayi ya sau’ke su a kan fuskar ta a hankali ya kuma sau’kar da idanun yabi jikinta yana murmushi yace ” really?” 

Itama murmushin tayi tare da jinjina mai kai sannan ta mi’ke ta ‘dauko mai ruwa mai sanyi da cup dayake tasan halinsa matu’kar ya dawo gidan ruwa yake fara nema kafin sauran hidimomin su biyo baya. 

Shi kam a fakaice yabita da idanu har taje ta dawo in baka sani ba zakaui zaton ko idanun a rufe suke saboda yanda ya ‘kan’kansu. 

Da isowanta sai ta cika mai glass cup ‘din da ruwan ta mi’ka mai sai yasa hannu ya kar6a. 

Ganin ya riga ya cire takalman dake ‘kafan sa ne yasa sai ta zauna daga gefen sa tare da ‘dago hannun ta tana shirin 6alla mai bottles ‘din gabar rigar sai ya cire cup ‘din daga bakin sa ya kalle ta suna ha’da idanu sai tace ” a kara ne?” bai yi magana ba kawai ya dire cup ‘dib tare da janyo hannun nata ta fa’do jikin sa, baki ta tura gaba tana ‘ko’karin tashi daga jikin nasa sai ya ‘daga kanta ya sau’ke mata kiss a samna lips din ta kad’an yana raba bakin su sai idanunsu ya sar’ke cikin na juna tuni ma har gannunta ya keawaya bayan wuyan sa, ganin hakn kuwa yasa shi mi’kewa tsaye da ita ya nufi bedroom ‘din su yana fa’din 
” wariyar da ake min ya isa haka nima yau dole ki kar6i ajiyar princess ‘dita na san ita ba zata na ware ni ba” 

Bai dire ta ko’ina ba sai a tsakiyar gado sai ya kuma sau’ke wani kisa ‘din gefen wuyan ta sannan ya ‘dago ya kalle ta bai yi magana ba illah gira ‘daya da ya ‘dage mata yana murmushi, Teemah ma sai ta maida masa martani tare da fa’din ” nifa ban ware ka ba Allah Yayah, ai kasan duk yanda zan so Annur ba zai ta6a kamo ‘kafar Yayah na ba cuz shine farin cikina kuma haske na “
Tayi maganar ne a hankali cikin sanyi da shagwa6an ta kamar yanda ta saba yi masa a kullum. 

Story continues below


Fuskar sa ya kawo kusa da nata hancin  su na gugan na juna, idanun su ma sar’ke da na juna sannan shima a hankali yace da ita ” ban yadda ba ni, sai kin nuna min zahiri na gani”
Yayi maganar yanda ita ka’dai ce za taji tare da kai hannun sa zuwa marar ta yana shafowa a hankali still idanun su sar’ke da juna. 

Itama hannayen ta kai ta dafa kafa’dun sa da shi batare da tayi magana a zahiri ba illah murmushi a cikin ranta take aytana irin yanda take jin son shi a zuciyar ta wanda yariga yayiwa dukkan ga6o6inta dabaibaiyi ta maimaita kalmar ” i love cikin ranta har sau biyu na ukun ne bata san cewa har ya fito fili ba tsaban yanda shau’ki yake ‘diban ta. 

Shi kam yana jin abinda ta furta ‘din sai ya lumshe idanu domin har tsakar kansa yaji sau’kan kalmar. 

Bai amsa ba sai da ya sau’ke bakinsa kan nata ya ya sumbaci lips ‘dinta daya furta maganan kafin yace ” Love u more habibty”
Hakan da ya fa’da ne yasa ta fahimci cewa maganar tata ta fito fili domin amsa shi’din ya bata. 

Yana fa’din hakan sai ya bar jikin ta ya koma gefen ta ya kwanta duk idanun su na kallon saman ceiling, hannun ta dake gefen sa ya kamo ya sau’ke shi saman ‘kirjin sa saitin zuciyar sa sai ya lumshe idanu yace ” bansan asalin lokacin dana fara son ki ba i just found my heart cike da ‘kaunar ki, sometimes har mamakin kaina nake yi cuz bana iya controlling feelings ‘dina akan ki matu’kar zuciya ta ta bu’kaci ganin ki ban iya jurewa har sai na gankin sannan nake nutsuwa, tun ada na tsani inga kin fifita wani akaina duk da kuwa nasan rashin sha’kuwa ta dake ne zai sa hakan amma duk da haka ban tantance meke damuna ba a lokacin nayi ta dulmiya cikin ‘kunci da takaici, ban tabbatar da girman son da nake miki ba sai lokacin da Mahmud yazo min da labarin auren ku, a lokacin jinayi tamkar ‘karshen farin cikina kenan a duniya, ji nayi tamkar nayi hauka… idan na tuna za’a yi auren ki, wallahi Zahra a lokacin tafiya kawai nake yi amma komai idan inayi sai inji tamkar bani bane har sai dana ‘kwammaci mutuwa ta fiye da rayuwa duk da kuwa nasan hakan zunubi ne but i cant help it, saboda irin suyar da zuciyata keyi min a duk lokacin da na tuna kin zama mallakin wani ba ni ba sanadin haka na tafi Borno duk da nasan suna shan fama da ‘yan ta’adda saboda ina ganin shine hanya mafi sau’ki da zan iya rabuwa da soyayyarki idan na daina numfashi, ban ta6a zama na fa’dawa wani damuwa ta ba balle na samu shawara saboda ban saba hakan ba, sa’a ‘daya nayi kawai saboda wani 6angare daga zuciya ta na bani shawara akan na sanya dangana cikin al’amurana, wannan shawarar nabi na mida damuwa ta wurin ubangijina sai dai ban ta6a accepting d fact that wai kin bar ni kenan har abada ba, shiyasa salon addu’ah ta bata canza ba akanki amma ban ta6a tunanin mutuwa ce zata dawo da ke hannu na ba hakan bai ma shigo cikin tunani ba sam kuma ban fatan Allah ya rabaki da mijinki ba, ni dai fatana a kullum shine Allah ya bani Zahra musamman da nake da yak’inin cewa u too had feelings d same as i had 4u is just that babu wanda ya bayyana shi ga ‘dan uwansa shine ka’dai damuwa ta da kaina na fahimci son da kike min tun kafin auren ki da marigayi. 
  Sai gashi a lokacin da dangana ya fara zama a raina, na sanyawa raina cewa ‘kaddarata kenan, shine soyayyar da babu ranar cikar ta sai kuma Allah ya nuna ikon sa akan hakan ya dawo min dake hannuna….
Zahra our love is like an eternal flame that no one can touch or break it, it can’t be blown out, it carries many colors, until the end of time….our love is like d wind….i can’t see it, but i can feel it all over me….idan nace miki zan misalta miki girman farin cikin dana tsinci kaina a ciki lokacin da akayi min albishir ‘din auren ki bazaki ta6a fahimta ba…all i knew ws u ar my woman, my life, my everything….may be 2 d whole world u may be only one, but to me u ar my world, my happiness my weakness also d strong part of me…..banajin akwai kalaman da zan iya furtawa Zahra to tell u all d love i have 4u within my heart….i wan’t u to always remember that i do love u, i’m with u, still with u, nd always be with u 4ever…. ko yau Allah ya ‘dauki raina nasan na cika BURINAH a kanki tunda na mallake kuma muka so juna wannan ka’dai ma ya isheni alfahari”. 

Juyo da kansa yayi ya kalle ta tare da bu’de idanu ya sau’ke shi a kan fuskar ta da suka ji’ku da ruwan hawaye bakin ta sai rawa yake yi kamar tana so furta wani abu amma takasa still kuma hannun ta kan ‘kirjin sa da ji’ka’k’un idanun ta sanya ‘kwayar idanun ta cikin nashi tana jin wani sonshi mai ha’de tarin kwarjinin ‘kaunarsa na ratsa dukkan gangan jiki da zuciyar ta hawayen tane kawai suke ‘kara ‘karfin speed suna sake sau’kowa batare da ta janye daga kallon nasa ba.
Idanun su sar’ke da juna yace ” I so much luv u ‘yan matan Yayah, ke na fara so a rayuwata kuma insha Allahu dake zan ru’fe murfin zuciya ta,  ha’ki’ka ke ta dabance a rayuwa ta gaba ‘daya……”

Story continues below


Rintse ido tayi da ‘karfi tana jin yanda zuciyar sa ke bugawa da sauri, ko haka ya bar ta ko da bai furta komai ba ita kanta tasan Yayah na matu’kar ‘kaunar ta ko daga bugun da zuciyar sa ke yi bazata ‘karyata kalaman sa ba. 

She is totally speechless, bata san mai zata ce da shi ba da har zata iya kamo kwatankwacin irin son da shi yake yi mata ba, tana jin nata son ba komai bane compare to nashi duk kuwa da cewa tana jine a yanzun tamkar idan babu shi rayuwar ta bashi da da anfani, tana jin bazata iya rayuwa batare da shi ba bama ta fatan wani abu da zai zo ya shiga tsakanin su koda kuwa menene shi, hatta mutuwa in so samu ne zata fison ya ‘dauke ta kafin shi. 

Bata bu’de idanun ba taji shi a saman ta yana faman shinshinan wuyan ta tare da share mata hawayen dake   fuskart kamar ba shine ya gama zayyano mata kalaman ‘kauna cikin sanyin hali da nutsuwa ba, dai-dai kunnan ta taji ya ra’da mata ” kin shirya kar6an ajiyan belove baby nurse ‘din nawa?” 

Shiru tayi bata yi magana ba shima bai damu ba kawai yaci gaba da abinda ya keyi inda kamar wani ba’a son ran shi ba yake shafo ta  very slow but so romantic tare da ‘ko’karin kaiwan hannun sa can ‘kasan marar ta, ita kanta yanda yake yi ‘din yafara ‘daukan hankalin sa har ta fara tunanin irin abin birgewan dazata yi masa a yau ‘din in return to his tadaddun love words ‘din da taji daga bakin sa yanzun, wanda ta tabbatar zai faranta ransa shima. 

Shikam har ya fara ‘daukan layi inda ya gama bu’de gaban rigar dake jikin ta yana yamutsa ta yayin da hannun sa ‘daya ke kan mararta ‘ko’karin 6alle hook ‘din bomshort ‘din dake jikinta yakeyi caraf kunnuwan su suka jiyo muryar Annur yana fa’din
” Daddy! 

“Subhanallah”!! yace acikin zuciyar sa tare da barin abinda yake yi cikin sauri, amma bai juya ya kalli Annur ‘din ba sai ya tsaya kallon cikin idanunta kawai a hautsine. 

Itama Teemah sai yanzun ta bu’de idanun ta da jin muryar Annur ‘din tafara ‘ko’karin jan rigar ta rufe jikin ta da kyau, suna ha’da idanu a hankali sai  yace “shine dagangan kika ‘ki rufe ‘kofan ko?” 

Tasan ba laifin ta bane cuz shine ya kawo ta ‘dakin kuma shima ‘din tasan yasan hakan kawai dai rasa abin fa’da yayi ko kuma ya mance a yanayin da suka shigo shiyasa, dan haka sai ta saki murmushin mugun ta da guntun hawayen ta tayi masa fari da ido tare da fa’din ” Ai kaine ka bar ‘kofan bani ba kuma kaga Annur ma yace ka ‘kyaleni baya so shima” 

Lakatan hancin ta yayi da hannun sa yace ” zan kamaki ai” sannan ya bar jikin ta ya sau’ka daga gadon ya nufi wajen Annur dake ‘ko’karin tahowa inda suke, Abbas  ‘daga shi yayi sama yace ” Oyoyo my boy na dawo bangan ka ba”
Dariya Annur yayi masa yana jan hancin sa duk da kuwa bai warware daga baccin daya tashi ba amma yanda yake son Abbas ‘din ya sanya shi ‘dan warwarewa dan sosai Abbas ke yi masa wasa idan yana gida shiyasa suka sha’ku hatta Teemah ‘yar kallo take zama idan Abbas na gida wa’kan da yake yi masa ma yanzu har Annur ‘din ya iyata dan sama zai idaga shi yana dariya yana cewa ” wah…wah…waladin…Muhammad Nury waladin…., yaron Daddy waladin, yaron Mummy waladin,  mai sunan Daddy waladin”
Annur ya rin’ka dariya kenan idan yaji wataran kuwa hannayen sa yake kamawa kamar sa’ani suyi ta wa’kar su a tare.
Haka hatta wanka shike yi masa idan yana gida ya kuma bashi abinci sannan ya kaishi ‘dakin dayake kwana yayi masa addu’ah yana lalla6asa har sai yayi bacci.
Sau tari Teemah sai dai ta ta binsu da idanu ko kuma tana rakashi musamman idan zai kaishi bacci sai ta bisu abaya ita kanta tana jinjina wannan sha’kuwar cuz idan kaga Annur ya manne mata to Abbas baya gida ne in kuwa yana nan kallo ma bata ishesa ba.
      Sha’kuwa ce mai mugun ‘karfi a tsakanin su hatta yawo wataran fita suke yi su biyu su barta agida wani sa’in ne idan zasu fita Annur sai ya je ya janyo mayafin da duk yagani a fili ya kawo mata yace ” mummy let’s go”
Abbas idan ranar baiyi niyyan fita da ita ba sai yace “ah ah banda mummy, ita ta ta zauna a gida zamu kawo mata abin da’di”.
Cuz wataran office suke zuwa wataran kuma yawo kawai zai kaishi, wani gyaran kai da Abbas ya kaishi akayi masa wai wanda yagani, Annur yaro ne amma ba laifi yana da suman kai sosai, hakan yasa Abbas yake kulawa da kan nasa kamar wani babba yasa akai masa low cut aka gyara gashin kamar ba ‘dan hausawa ba, kafin Abbas ya zama ma aikacin soja ba irin gyaran kan da baya yi, amma tunda ya shiga aikin sai ya zamana gashin ma ba bari yake ba shikuwa yana da masifar son tara gashi shiyasa ma daga ya ‘dan ‘dauki hutu zaka ga har ya tara suma ya kuma gyara shi gwanin birgewa kafin cikar hutun Teemah kanta yana bata sha’awah da zarar hutunsa ya ‘kare kuma shikenan zai je ya cire su, wannan dalilin ne yasa yake yiwa Annur dan shi bai da damar yin hakan, shi mutun ne mai son cika BURIKAN SA, sai dai baya binsu a gaggauce cikin natsuwa take binsu shiyasa idan bai samu daman yin abu ba sai ya ‘dorawa wani nashi burin, kamar yanzun burinsa na son Teemah ta zama doctor wanda ta’ki bai yi fushi ba sai ya ‘dauke burin daga kanta abin na nan a cikin ransa amma sai ya bari akan ‘yarsa idan har Allah ya bashi….ita zata cika masa wannan burin. 

Story continues below


Yanzun kuwa da  Annur yake ri’ke a hannunsa sai yake ta faman jan hancin Abbas yana dariya,  Abbas kuma yana kaucewa tare da mai wasa acikin sa da bakin sa da yake jikinsa babu riga illah pant ne kawai so idan ya hura cikin sai yayi ‘kara wanda yake matu’kar sa ka Annur dariya idan yayi masa hakan. 

Gurin da Teemah take ya koma da shi yana fa’din ” Annur baya son zama da kaya agida da alama halin ki yayo” 
Teemah kam murmushi mai sauti kawai tayi batare da ta tanka masa ba sosai take jin da’din yanda Abbas yake kulawa da Annur duk kuwa da abubuwan dake gaban sa amma sam bai sa sun rinjayi tattalin iyalinsa ba, sosai yake ‘ko’kari akan hakan har tausayi yake bawa Teemah wani lokacin idan taga Annur na ma’kal’kale masa, ita kanta tana so suna ‘dan barinsa yana samun natsuwa, sau tari sai dai in tana son ya barshi sai ta yi masa wayo tace “bamboo Annur, come on zo in goya ka kayiwa Daddy dariya” Annur idan yaji goyon ne kafin yake zuwa ya bar Abbas ‘din, wataran ma har datse ‘kofa take yi da key dan ya samu yayi bacci, tun Annur bai gano ba har ya gane so idan baiga Daddyn nasa ba kuma yaga ‘kofa arufe sai yaje yayi ta bugawa yana ‘kananun kuka tare da ‘kiran “Daddy”! 

A gefenta Abbas ya zauna inda ya maida idanunsa kan fuskar Annur batare da ya kalle ta ba ya fara yiwa Annur wa’kansa ta waladin ” wah…wah…waladin….
Annur kam sai dariya yake yi Teemah kuwa binsu take da kallon ‘kauna tana murmushi, tasan idan kowa irin Abbas ne to da babu macen da zatayi ‘korafi akan raino amma ina tasan bakowa ke sa’an samun hakan ba dan hgaka sai ta furta ” Alhamdulillah” da dacen samun miji nagari da tayi mai son ta mai kula da dukkan al’amuranta, mai baiwa bu’katun muhimmanci uwa uba kulawa da ahalin gidan sa. 

Sai da ya gama wa’kar tasa kafin yace da Annur ” Yaron Daddy… you need a baby sis to play with right?” 

Annur sai ya ‘dage kai sama tare da fa’din ” yes Daddy just like Anty Ummah’s baby” yana washe fafaren ‘kananun ha’koran sa waje.
(Anty Ummah wata mata ce a block ‘dinsu data haihu sati biyu yanzu da suka je da Teemah ta ‘dauki babyn  shine ya ‘kare mata kallo harda wasa da ‘kafafuwan ta ). 

Abbas kam kamar Annur ya ziga shi sai ya ya sake fa’din ” Oyah tell ur mum that u want ur baby sis from her like Anty Ummah’s baby..” 

Annur kallon ya dawo da shi kan Teemah data zuba musu idanu tana murmushi cikin maganar sa da bata gama mi’kewa ba yace 
” yesh Mummy …i wan my lil prinshesh right away” 

Teemah zaro idanu tayi tace ” see u, right away ‘din ‘kaniyar ka a ina zan samo maka yanzun?” 

Abbas kam murmushi yayi  ya bashi hannu tare da kama chicks ‘din sa yace ” That’s my boy, we need our princess right now ko ?” 

Kai Annur ya ‘daga masa yana washe baki, Abbas kam yana murmushi yayi pecking ‘dinsa a goshi. 

Teemah kuwa tashi tayi da sauri ta fita taje ‘dayan ‘dakin ta ‘dauko teddy bear ‘din sa da yake wasa dashi ta kawo masa tace ” ga lil princess ‘din taka….bana son damuwa ni”
Tana maganar tana cusawa a tsakanin sa da Abbas. 

Annur yana ansa sai yayi jifa dashi gefe tare da fa’din 
” Not ths mummy i want d yeal one” 

Dariya dukkan su suka sanya ilah Annur, Teemah kam harda zama Abbas yana cikin dariyar yace 
” yaro na na son d real princess ba fake ba sai ki shirya kar6an lil sis ‘din Prince ‘dina an jima ” 

Kafa’da ta no’ke tace ” ni dai ah ah…Allah Yayah duk kai kake koyawa yaron nan iyayi…..har da wani now sai kace an gaya masa haihuwan sau’ki ne dashi, nawa ma yake shi’din 19months ne fa yake har yanzu dan Allah, ni dai gaskiya ba yanzu ba….kuma ya dameni da zancen babyn nan zane shi zan fara ni kam” 

Abbas sai yace
” Kina ta6a min yaro to kuwa sai kin haifi triplet ba ruwana ” 

Sai tayi saurin no’ke kafa’da kamar ‘yar yarinya ‘karama tana tunzura baki gaba. 

Abbas ma sai yace ” do ur worst ‘yan mata zaki kuwa sha mamaki…yaron da nake planning kai shi school kwanan-nan ‘din ne zaki ce min bai kai ya samu sister ba?
Kin ma yaudari kanki yarinya is better ki fara shiri ma cuz next year like ths insha Allhu i’m with my 2 kids”. 

Jikin sa ta fa’da tana kukan shagwa6a tare da kaimar bugu a ‘kirjin sa shikam dariya ma ta bashi da shegen tsoron nata Annur ma ganin yana dariyar shima sai ya bu’de bakin sa da ‘kananun ha’koran sa guda 12 yana taya Abbas ‘din dariya.
_They live happily ever._ 

*ALHAMDULILLAH WASSALATU WASSALAMU ALA NABIYUL KAREEM*. 

Anan na kawo ‘karshen littafin

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like