HUTU CHAPTER 1

Advertisement

HUTU

CHAPTER 1
ABUJA :- Wuse/ 1:30pm

Tangamemen gida ne, wanda kallo daya za’ayi a gane cewar gidan manyan mutane ne, masu hannu da shuni. Kwance take a kan tangamemen royal italiyan bed dinta tana bacci hankalinta kwance wanda kallo daya za’ayi mata a gane HUTU ya zauna a jikinta dan kuwa fatanta kadai ya isa ya nuna cewar ba ‘yar wahala bace. Wayanta kirar Samsung galaxy edge 8 ne dake ajiye kusa da ita ya fara ringing, firfigit ta tashi tareda daukan wayan saboda ta riga tasan me kiran dan ringing tone dinshi daban ne.

Cikin muryan ta me zaki da dadin sauraro tace “Amincin Allah ya tabbata a gareka ya nurul kalbina”, lumshe ido yayi ta dayan bangaren kafin yace ” Amin tareda naki gimbiyata, masoyiyata, sarauniyata kuma matata nan bada dadewa ba Insha Allah”. Ajiyar zuciya ta sauke tareda daukan pink Teddy bear dinta ta rungume tsam a jikinta kaman shi ta rungume sannan cikin kasallaliyar murya tace “Habibina nayi missing dinka sosai, yaushe zakazo na ganka?, naga kyakyawan fuskan ka da murmushin ka”. Kayataccen murmushin shi yayi yace ” guess what”, “kasan I’m not gud at guessing, so kafadamin kawai karka jamin rai kaji my husband to be”, ta fada a shagwabe kaman yana gabanta. Murmushi yayi jin tace mai ‘husband to be’ sannan yace “toh ki shirya yau zaki ganni dan yanzu muka sauka, ina ma mota bamu kai gida ba”.


Wani ihun dadi tayi tace ” da gaske sweety na kasan banason zolaya”, yace “ki saurareni nan da awa uku zaki ganni”, cike da jin dadi tace ” shikenan I believe u, me kakeso in shirya ma?”, “anything u wish, it will be my pleasure”, cike da murna da jin dadi tace ” ok, se kazo, bye, I luv u”, “I luv u more, take care of urself “, ” ok “, da haka suka kashe wayan tace ” ai banga ta kwanciya ba”. Tashi tayi ta yaye comforter dinda ta rufe jikinta dashi, se alokacin na karewa kayan da ke jikinta kallo, bum shot tasa amma da atampa aka dinka matashi tareda blue hoodie lose an rubuta always beautiful a gaban, wani takalmi ta zira kafanta ciki me gashi a saman pink color sannan ta dau teddy dinta da wayanta ta fita.

Dakin mahaifiyarta ta shiga bako sallama tace “Mom guess wat!”, mahaifiyarta dake zaune gaban dressing mirror tana bude drawers din da alama abu take nema ta juyo ranta a bace tace ” KAUSAR fitamun daga daki, duk sanda kika koyo sallama kin iya dawowa”, kallon Mom tayi tace “Mom wlh mantawa nayi banyi miki sallama ba”, ” ai se ki koma kiyi”, pouting lips dinta tayi tana bubbuga kafa a kasa alaman an takura mata sannan ta fita tayi sallama Mom ta amsa mata ta shigo taje ta tsaya gaban Mom tace “Mom zanyi bako yau”, kallonta Mom tayi tace ” HAYDAR yadawo ne?”, murmushi tayi dan jin sunanshi kawai wani irin nishadi yake sata wanda baze fadu ba tace “eh Mom, yanzu mukayi waya yacemin wai ya dawo anjima zezo”, Murmushi Mom tayi dan ko ba komai tasan ‘yarta tayi dace dan tasamu miji na nagari, na nunawa sa’a, kamilalle wanda yasan ya kamata, kallon KAUSAR dake faman murmushi tayi tace ” toh ai sekije ki shirya kar yazo yata jira, sannan kije ki fadawa Laure abunda kikeso ta girka kafin yazo”, amsawa tayi da “toh”, sannan ta fita daga dakin ta nufi hanyar kitchen, nan taga Laure na wanke wanke tace ” Laure zanyi bako nan da awa uku saboda haka inaso ki mishi fried coconut rice da coslow se pepper chicken”, Laure tace “toh KAUSAR zan gama kafin yazo Insha Allah”, ” toh ki daiyi sauri”, ta fita ta bar kitchen din ta koma dakinta dan tayi wanka.

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

ADAMAWA STATE :- Kauyen cakawa a karamar hukumar madagali ajihar adamawa/ 4:05pm

Gidan Malam Tanimu gidane dake kunshe da abubuwan al’ajabi wanda yasamo tushe daga wurin muguwar matarshi Zinaru, wacce batada tausayi kona miskala zarratin, indai akan ‘yar margayiya Shatu matar Malam Tanimu ta farko ce to koda zatayi tafiya tsirara se tayishi saboda tsabar kiyayya da takema baiwar Allah nan.

Ke BINTOTO ki shiga hankalinki dani, in baso kike in karairaya ki ba, in banda kin rainani in baki hamsin kisiyo min kayan miya shine zaki kwaso min wannan rubabbun kayan miyan kice na hamsin kenan dan kin raina uwarki wacce ke kwance cikin kabari dan kuwa bani kika raina ba”. BINTOTO dake durkushe gabanta tana sharar kwalla tace “Goggo wlh ban rage ko sisin ki ba, cewa sukayi ana tsadan kayan miya saboda lokacin rani ne”, cike da masifa Zinaru tace ” uwarki, uwarki nace dan gidanku ina ruwana da lokacin rani eh?, nace ina ruwana da lokacin rani?, toh inaso kafin na bude idona ki tashi ki dauki kayan miyan nan ki mayar dan bazan siya wannan a hamsin ba”. BINTOTO tanaji tana gani haka ta dau kayan miyan ta fita saboda gudun duka dan tasan ba karamin aikin Zinaru bane ta bubbugeta yanzu.

Tafiya take tana sharar kwalla saboda tausayawa kanta da takeyi, duk wanda yazo wucewa seya kalleta ya kuma kallonta cike da tausayawa saboda a kauyen mutane dai dai ne basusan halin da BINTOTO ke ciki ba saboda duk sun san irin matar da BINTOTO ke zaune da ita amma ba halin taimaka mata saboda jaraban Zinaru danko Malam Tanimu da yake mahaifin BINTOTO ma bata barshi ba balle su en gari, tun suna taimakawa sukazo suka daina suka hakura dan Zinaru ba mutunci ne da ita ba.

Kallamu ne tafe yana en wake wakenshi zashi gida ya dawo daga gona ya hango BINTOTO wanda shi duk fadin kauyen babu wacce yakeso se BINTOTO duk da kuwa Zinaru ta gargadeshi akan ya rabu da ita amma ina, duk inda ya ganta seya mata magana kuma ya tunatar da ita irin son da yake mata. Karasawa wurinta yayi yace ” Fatimatu bintu Zahra, daga ina zuwa ina?”, shiru tayi tana wasa da gefen rigarta, ganin alamun tayi kuka yasa hankalinshi ya tashi yace “BINTOTO lfy kike kuka, me muguwar matar nan ta miki?”, cikin wani sabon kukan ta fara bashi lbrn abinda ya faru tace “Goggo ce tace in siyo mata kayan miya na hamsin, na siyo kuma shine wai in mayar wai bana hamsin na siyo ba wai yayi kadan, kuma ni wlh ban ragar mata ko sisin ta ba, shine wai ita bata yarda ba”.


Kallonta yayi cike da tausayawa yace ” karki damu ga dari nan, kije ki tsiya na hamsin ki kara mata ke kuma ki rike sauran hamsin din kinji, share hawayenki”, cike da murna ta karba ta fara zuba mishi godiya kaman yace mata ya biya mata hajji, murmushi yayi yace “ba komai BINTOTO, in ban miki ba wa zanyi wa, yi sauri kije kar taga kin dade ki kara wani laifin ta dakeki”, kallonshi tayi tace ” toh kallamu nagode”, tareda arcewa a dari bata damu waiko a gaban saurayi take ba, shiko dariya ma ta bashi ya girgiza kai tareda kallonta har ta kure mishi yace “BINTOTO kicigaba da hakuri insha Allah watarana da yardar Allah zan fitar dake daga wannan kangin wahalan da kike ciki bi izinillahi”, sannan ya juya yayi tafiyarshi cike da tunanin BINTOTO.

Wanka tayi ta wanke kai tasa towel ta tsane gashin kanta tareda goge jikinta sannan taja kujeran dressing mirror ta zauna, tayi drying gashin ta sannan ta shafa mai a jiki da gashi tayi combing gashin da se kyali yakeyi tayi pack dinshi, sannan ta tashi ta shiga closet dinta wanda yake damke da kayan sawa. Wani shadda maroon ta dauko wanda yasha aiki daga sama har kasa me bala’in kyau tasa ya riko dankwalinta a hannu ta fito ta koma kan dressing mirror ta zauna tafara makeup. Seda ta kwashi kusan awa daya tana makeup kaman wacce zata gasan kyau na duniya gabadaya sannan ta kashewa kanta dauri ta feshe jikinta da turaruka masu ni’imtaccen kamshi, ta kalli kanta a mirror ta sake kallo ta tabbatar komai zam zam sannan ta fito ta nufi kitchen dan ganin ko Laure ta gama abinda ta sata.

“Laure kin gama?”,” saura kadan KAUSAR na hada komai jira nake ta tsotse”,”Ok kinyi coslow da pepper chicken din?”,”eh nayi”, ta bata amsa cike da kaguwa saboda tambayan da take mata. Karasawa tayi ta bubbude coolers din da sliver tray din da akasa coslow din ta taga komai daidai sannan ta bude pot din taga ta kusa tsotsewa sannan ta rufe ta fita Laure tace “yarinya se shegen gata da lalata, komai bata iya ba a haka za’a aurar da ita”, duk maganan nan a zuciya tayi sannan taja tsaki a fili saboda takaici. Compound ta nufa ta kira Isa errand boy dinsu tace ” inaso ka dubamin garden ko a tsaftace yake”, “hajiya ai kullum a tsaftace yake ko yauma na share na gyara”, ya fada yana sunkuyar da kai, kaɗa kai tayi tace ” shikenan jeka”, sannan ta koma ciki tana zaman jiran isowar sanyin idaniyarta.

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

“Wai ina wannan algungumar yarinyar ta shigane? Daga taje ta maida kayan miya a kara mata shine taje ta saura”, Zinaru tayi kwafa tareda cewa “zakizo ki hadu dani, salon girkina yayi dare”, haka taci gaba da banbami tana masifa ita kadai cikin gida. Itakon BINTOTO tana can ta siya kayan miyan ta kuma siya alale da mai da yaji ta zauna wurin tanaci saboda tsananin yunwa dan tun daren jiya rabonta da abinci kuma tasan inhar Zinaru taga kudin da kallamu ya bata kwacewa zatayi shiyasa ta tsaya ta kashe abinta.

Loma kawai take sakawa baji ba gani saboda tsananin sauri, kwarewa tayi saboda yaji tanata tari wanda da kyar ya tsaya mata dan har idonta ya kawo ruwa tsabar azaba, tana gama cin abincin ta kora da ruwa ta mike ta kama hanyar gida tana addu’a Allah yasa kar Zinaru ta jibge ta.

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Zaune take tana chatting a wayarta wayar ta soma ringing, murmushi tayi ta dau wayan tareda karawa a kunne tace ” hello habibina”,”na’am gimbiyata”, ya amsa mata cikin sanyin murya, “awa ukun ka har yanzu beyi ba? Ko so kake kwalliyata ta kode ne?”, dariya yayi saboda yanda tayi maganan a shagwabe yace ” ai gani yanzun nan zan shigo gidanku”,”da gask……”, ai kuwa bata gama magana ba ta hango motarshi na shigo ta cctv din gidan, nan take ta kashe wayan ta haura sama da dan saurinta taje ta tsaya gaban mirror tana duba kanta. Seda tayi en gyare gyare ta kara wanka da turare sannan ta dauko wani munafikin mayafi wanda shida babu duk daya ta rayata a kafada ta nufi dakin Mom, shiga dakin tayi da sallama tace “Mom yazo”,” toh ai sekije karki barshi zaune “, da murnarta ta fita ta nufi compound nan ta ganshi zaune cikin mota yaci black jeans da red shirt me design din checkers na company din Gucci, hannunshi nannade ta agogon Rolex baki, kanshi yasha gyara se sheki yakeyi.

Seda ta lumshe ido sannan ta bude saboda shaukin ganin sanyin idaniyarta, hannu tasa ta kwankwasa mishi glass din motar ya dago kai ya kalleta suka sakema juna murmushi a tare sannan ya bude kofar motar ya fito ya kulle ya nufeta tareda cewa “gimbiyata na siya wannan kwaliyan”, murmushi tayi tace ” a nawa?”,”a nawa za’a siyarmun?”, ya tambaya yana murmushi “uhhmm”, tace tana daga kai alaman tunani kafin tace ” 1mila”, yayi er guntun dariya yace “an siya sarauniya”. Haka sukaci gaba da hiransu cike da barkwanci da nuna kewan juna da sukayi har suka karasa parlourn baki ta nuna mishi wuri ya zauna sannan tace ya bata minti biyar tana zuwa.

Fita tayi ta nufi kitchen ta dauko duka abinda ta bari aka dafa mishi daya bayan daya tana kawowa tana ajiyewa harta gama, bayan ta ajiye plate dinda ke hannunta ta dago taga ita yake kallo ko kiftawa babu, murmushi tayi ta tashi ta karasa gabanshi ta hura mai iskan bakinta a ido ya lumshe idonshi masu kamada na mai jin bacci sannan ya bude ya kalleta yace ” princess kina kasheni da wannan salon naki”, murmushi tayi tace “bismillah food is ready, nasan bakaci abincin Ummi ba”, ” inafa zanci nata na bar ma gimbiya”, dan duk a tunaninshi ita ta dafa, share zancenshi tayi tace “toh zo kaci ka koshi sannan ka bani lbrn garin Enugu garin iyamurai”, dariya yayi yace ” ai nan zan kai ki musha honeymoon “, tace ” a’a rabani da garin iyamurai bazan iya ba nikam”. Ya mike yana dariya ya zauna kasa gaban abincin itama ta zauna tayi serving dinshi sannan tasa mishi spoon ta ajiye gabanshi. Dago kanda zatayi taga idanuwanshi kur a kanta, murmushi tayi tace “habibina baka gajiya da kallona?”,” taya za’ayi in gaji da kallon sanyin idaniyata?”, ya tambaye ta still idonshi a kanta, ta lumshe ido sannan ta bude tace “bismillah kar abincinka yayi sanyi”, daukan spoon yayi ya kai bakinshi yace ” hum, amma na dade banci abinci mai dadi irin wannan ba”,shiru tayi tana kallonshi dantasan santi yakeyi shikuwa gaskiya ya fada dan a watannin nan daurewa kawai yakeyi amma ina yaga abincin kwarai a garin iyamurai.

Seda yayi three spoon sannan ya dago ya kalleta yace “zoki zauna nan”, ya nuna kusa dashi, bata musa ba taja jiki ta zauna gefenshi ya debo abinci ya kai bakinta ba musu ta karba ya mata murmushi tareda lakace mata hanci, haka sukaci gaba da cin abincin batare da waninsu yace kala ba saboda tasan rules dinshi ne baya magana in yanacin abinci, suna gamawa ta tattare wurin ta kai kitchen ta dawo ta zauna kusa dashi kan three seater sukaci gaba da hiransu.

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Jiki na bari, gabanta na faduwa, hankalita a tashe tayi sallama ta shiga gida, ba tareda ta amsa sallaman ta ba tace ” sanda zuwa gantalalliya, dayake kinci kafan kare shine daga kiji a kara miki kayan miya shikenan an sallameki koh?”, murya na rawa tace “Goggo akwai layi a wurin ne shiyasa”, “layin uwarki da ubanki, kinje kina gantali shine zakizo kicemin akwai layi, bari dai banda lokacin ki yanzu, maza gyara mun kayan miyan nan ki jajjage minshi, kuma minti biyar na baki, in kin cika ‘yar halak ki kara minti daya akai”, seda ta kai mata rankwashi sannan ta dauki buta ta shiga kewaye. Cikin sauri da zafin nama BINTOTO ta dauki kayan miyan ta fara gyarawa kuma gashi kayan miyan da yawa, tazo kan albasa zafinshi ya dinga shiga mata ido ta tsaya tana murza idonta, batasan Zinaru ta fito tana tsaye a bayan ta ba.

Dundu ta kai mata a baya tareda cewa “minti biyar din kenan harna gama abinda zanyi na fito, kina nan tsaye kina wani murza ido sekace ba mace ba, eh?, bari na fito daga daki kina nan zaki gane kuranki”. Duk da idonta sun cika da kwalla amma haka ta daure taci gaba da jajjagen ta, tana gamawa ta shiga dan kitchen dinsu ta fara kokarin hura wuta amma ta duba sama da kasa ta rasa makamashi, dole ta fita waje dan nemo abinda zata hura wutan dashi. Tana dawowa ta shiga da sauri amma me?, se ganin Zinaru tayi tsaye rikeda kwankwaso da hannun hagu hannun damanta kuma rike da dogon itacen dalbejiya wanda tasamo shi saboda dukan BINTOTO.

Dam taji gabanta ya fadi dan kuwa tasan yau bame kwatanta hannun wannan muguwar matar se Allah, jiki na bari ta karasa ciki tana cewa ” Goggo makamashi naje nemowa”, cike da masifa ta fara harzuko mata tana cewa “makamashin gidanku, tin dazu kinata batamin lokaci salon girkina yayi dare, zo nan dan uwarki”, ta fada tana kokarin kamo BINTOTO wacce ta falla da gudu suka fara zagaye gidan Zinaru na binta har ta cimmata ta fara tsula mata bulalan hannunta, BINTOTO se hakuri take bayarwa amma ko a jikinta baji ba gani haka taci gaba da dukanta kaman Allah ne ya aikota, tana me cigaba da balbalin bala’in se cewa take ” shegiya ‘yar mayya jikan mayu,ki bari inna nakada miki na jaki seki shide ki sheka barza’u ‘yar banza”, haka taci gaba har seda taga ta galabaitar da ita sannan ta kyale ta tare da cewa “zaki tashi kiyi abinda na saki ko sena kara miki?”, duk da taji jiki a hannun Zinaru amma gudun kar akara mata wani dukan yasa ta tashi da kyar ta shiga kitchen ta soma kiciniyar hura wuta.

Wani dadi yaji kaman ya goyata dan tun ba yau ba yake mata maganan turo magabatanshi tana dagashi da sunan se ta kamalla degree dinta. Cike da jin dadi yace ” da gaske sarauniyar mata?”, tace “da gaske nake”, rasa inda ze sata yayi saboda murna se sa mata albarka yakeyi tana amsawa da ameen tana mishi dariya ganin yanda ya rasa nutsuwarshi, mikewa yayi yace ” kinga bari naje gida nayi sharing wannan gud news din da ummina, duk yadda kukayi da Mom ki kirani”, “ba matsala ka gaishe min da Ummin mu”, ta fada tana mikewa itama, yayi murmushi yace ” zataji”.
Har gaban mota ta rakashi tana daga mishi hannu kaman bazasu rabu ba, seda taga fitanshi daga gidan sannan ta koma cikin gida cike da murna tana ihun “Mom! Mom!! Mom!!!”, mom dake zaune parlour tana kallon lies of the heart a zee world tace ” lfy irin wannan kira haka?”, zama tayi kaman zata shige jikin Mom tace “Mom HAYDAR yace ze turo”, mom ta saki salati tace ” na shiga uku yaran zamani, shine dan rashin kunya zakizo kina nuna min jin dadinki a fili”, rufe fuska tayi da mayafin ta wai ita kunya mom tace “ai shikenan zan sanar da mahaifinku in munyi waya tinda kin gaji da zama dani, in yaso ko wurin baba mai kano ne se suji suyi magana tinda baban naki baya gari”, mikewa tayi tace ” yauwa mom yace na gaida ke”, “bazan amsa tinda be shigo ya gaisheni”, ita dai murmushi tayi ta mike ta haura sama zuwa dakinta cike da murnar HAYDAR ya kusa zama nata halak malak.


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


Ta samu ta hura wutan ta daura tukunyar tuwo dan tasan ita dince zata tuka ba wani ba, garin masara taje ta debo tazo ta tuka tuwon yayi laushi yayi sumul sannan ta kada kuka, seda akayi isha Malam Tanimu ya shigo gida Zinaru ta aika mishi da abincinshi sannan ta gargadi BINTOTO cewar in ya tambayeta taci abinci tace ” eh”, haka kuwa akayi koda ya tambaya ce mishi tayi tace alhalin ko miya batakai baki ba bare azo ga maganan tuwon. Seda Zinaru taci ta rage duk ta jagwalgwal abincin sannan ta tura mata wanda be wuci loma uku ba, haka taci ta side kwano taje ta ajiye wurin wanke wanke ta dauraye hannunta ta shiga tawa mahaifinta seda safe ta fito tawa Zinaru dake kwance tsakar gida daga ita sai daurin kirji seda safe sannan ta dauko tabarmarta ta fito soro dan ana take kwana (kuji wani rashin imani, ita ta kwana a daki me dumi ta bar yarinya a soro ga sanyi ga sauro fisabillahi hakkin wannan marainiyar kadai ya isheta shiga wuta amma tsabar son duniya an mata cewar za’a mutu, wlh muyi hattara mata! muyi hattara a daina musgunawa yaranda ba namu ba saboda muna ganin bamu muka haifesu ba, da na kowa ne kuma kiwonsu Allah ya bamu, gobe kiyama Allah ze tambaye mu yadda muka kiwata masa amanan da ya bamu, Allah yasa mu dace).

Tinda asuba ta tashi tayi wanke wanke, tayi shara ta debo ruwa ta cika randunan gidan sannan ta shiga wanka. Wani kaya ta dauko kayan kan igiya tasa ta wanke wanda ta cire ta shanya ta zauna tana jiran fitowar Zinaru. Bayan Zinaru ta fito ba maganan sallah bare salati ta talga koko da ruwan da BINTOTO da daura sannan ta fito ta aika ta siyo mata kosai ta zauna gabanta taci tasha batare da taba baiwar Allahn nan ba.
Tsugunne take a gaban Zinaru a yayinda Zinaru ke kirga kuka, kubewa da daddawan da take kulla mata tana kai mata talla, seda ta gama sannan ta dago tace “gashinan na dari biyu da saba’in ne, biyar inta bata ki bata dan kuwa kika dawo gidanan kudina basu cika ba kinsan sauran, tashi ki wuce”, cikin sanyin jiki take kokarin mikewa amma taji saukan rankwashi a kanta ” baza kiyi abu da jiki ba,kin tsaya kina abu kaman wacce batada jini a jiki”, kallon Goggon tayi sannan ta dauki tray din ta daura akai tace “Goggo sena dawo”, ” saura kije ki saura”, Goggo ta fada tana hararta cike da tsana, fita tayi ta dinga shiga gida gida tana “ga kubewa, ga kuka, ga daddawa”, duk gidan da za’a siya se a kirata in baza’a siyaba kuma se a cemata ” Allah ya bada sa’a”.Kafin rana ta fito har ta siyar da duka, cike da murna ta dinga sauri ganin tallanta yayi saurin karewa,tasan yau zataci abincin safe da wuri, shiga gida tayi da sallamanta Zinaru dake tsakar gida tana bakace shinkafar hausa tace “har kinyi me?”, ” Goggo na siyar, duk sun kare, ga cinikin ki nan”, ta fada tana mika mata kudin, karba tayi ta kirga taga sunkai cif cif ta soke kudinta a gefen zani sannan tace “tashi ga gujiya chan kan wuta ya dawu, tsiyaye ruwan ki juye kan paranti”. Tashi tayi tayi abunda aka sata sannan ta dawo tace ” Goggo na gama”, Goggo da ko kallon inda take batayi ba tace “dauka ki tafi dashi talla, na dari uku na dafa saboda haka inason ribar dari biyu ya hau kai, dari biyar kenan zaki kawo min”, cikin sanyin murya tace ” Goggo bansan yadda zan dinga auna gujiyar ba”, wani wulakantaccen kallo Goggo ta watsa mata sannan tace “dan uwarki yau zaki koya”, sunkuyar da kai tayi dan tanajin zafin zagin mahaifiyarta da Goggo keyi, cike da tsoro da fargaba tace ” Goggo yunwa nakeji”, hararanta Goggo tayi cike da masifa tace “banga daman bada abinci yanzu ba, tashi ki wuce”, ba musu ta tashi jiki a sanyaye.
Malam Tanimu dake daki duk yana jinsu ya fito yace ” yanzu Zinaru saboda Allah ace karfe goma ta gota amma yarinyar nan bata karya ba, kuma a haka kikeso taje miki talla, haba mana wani irin rashin imani ne wannan?”, wani kallon kai asuwa ta mishi sannan ta juya wurin BINTOTO tace “ke tashi ki wuce kafin na bude idona”, Malam Tanimu yace ” ba inda zata, ke ajiye tallan nan ki shiga kicin ki dau abincin ki”, wani tashi Zinaru tayi kaman wacce aka tsikarawa allura tace “wlh malam ka kiyayeni, ka fita daga idona in rufe, naga nan ka mika min yarinyar nan kace ka bani halak malak, toh yanzu ina labatar da ita yadda ya dace kana hanawa”, girgiza kai yayi yace ” amma kinji kunya wlh, wannan wace irin ladabtarwa ce ace tun safe baki ba yarinya abinci ba?, har goma ta gota, ke kinci kinyi nak ita kin barta da yunwa kuma kin turata talla” cike da masifa da kumfan baki tace “eh din naki na bada abincin kuma talla setajeshi”, daukan parantin tayi ta daurawa BINTOTO ta kama hannunta tajata ta kaita waje tace ” wuce dan uwarki, kuma wlh kika kawomin kasa da dari biyar kinsan sauran”, sannan ta koma cikin gida tace “kai kuma zanyi maganinka”, tana magana kaman da dan cikinta take magana, daki ta shiga ta dauko mayafinta ta fita ba tare da ta tambayi izini ba, shi kuwa girgiza kai yayi yana takaicin halinta, tafiya take tana sumbatu tana cewa ” a’a ina nagata zama?, malam na nema ya botsare min ai wlh wurin bokana zanje yamin maganinshi”. Duk wannan daga muryan da takeyi makota na jinta, kuwa na fadan albarkacin bakinsa ana Allah wadar da hali irin nata.

Banda murmushi ba abinda yakeyi cikin mota, ya kure wakan praize show me love, gidan mahaifiyarshi dake Asokoro ya nufa tareda danna horn wani soja yazo ya bude mishi yana daga mishi hannu amma abin mamaki shine yana zuwa kofan gidan ya gimtse murmushin da yakeyi ya hade rai dan ko kallon inda sojojin da suke sara mishi beyi ba. Parking yayi a parking lot sannan ya fito ya wurga wa daya daga cikin sojojin key tareda cewa “wash it now!”, sannan ya nufi hanyar da ze sadashi da main house din. Door bell ya danna sannan ya tsaya tareda sa hannuwanshi cikin aljihun wandon shi yana jira abude mishi kofa, wata yarinyar ce wacce kwata kwata baza wuce sha bakwai ba kyakyawa da ita sannan daka ganta kan ganshi saboda kaman da sukeyi, bude kofan tayi tareda danewa jikinshi tace ” Ya HYDAR I miss u, dazu na dawo daga school Ummi tace ka dawo amma ka fita”, dariya yayi kaman bashi bane ya hade rai a gaban sojojin nan ba yace “lil sis zaki karyani, bakisan kin girma ba yanzu, nan da lokaci kankani zan miki aure”, ai kuwa ta sakeshi tareda haurawa sama a guje tana dariya dama kuma abinda yakeso kenan dan dama da biyu ya fada haka saboda bataso ana mata maganan aure shikuma yanaso ya gana da Ummi dan in be mata haka ba bataza kyale shi ba.
Shima din saman ya haura ya nufi right wing din wurin dan nan dakin mahaifanshi yake, a nutse yayi sallama aka bashi izinin shigowa daga ciki, ya shiga tareda zama kasa kan carpet a yayinda mahaifiyarshi ma ke zaune kasa ta kishingida da tintin tana latsa waya, dagowa tayi bayan ya zauna ta mishi laulausan murmushi tace ” har an dawo daga wurin sirikar tawa”, sosa keya yayi yace “na dawo Ummi”, kallon shi tayi tace ” ina jinka dan da ganinka da magana bakinka”, murmushi yayi saboda mahaifiyarshi akwai saurin dagoshi yace “dama nawa KAUSAR maganan zan tura kuma tace ba matsala zatawa Mom dinta magana dan Dad dinta baya gari, shiyasa inaso ki fadawa su Abba saboda a fadawa su kawu su zauna cikin shiri dan ko wani lokaci za’a iya cewa su fito”, hamdala tayi tareda da daga hannu sama tana godiyewa Allah dan dama batada burin da ya wuce taga ta aurar da HYDAR saboda ya fara girma dan shekara talatin da hudu ba wasa bane.
Kallonshi tayi tace ” shikenan zan sanar da Abbanku, kaima seka fara shiri dan zan fadawa Abbanku in an tashi sa rana kar asa dayawa”, daga kai kawai yayi yana murmushi tace “ko ban tambaya nasan sirikata ta cika ma ciki”, dariya yayi yace ” wlh kuwa Ummi kaman tasan da yunwa naje”, “ai tasani dinne tinda gudun abincina kake”, murmushi yayi yace ” toh Ummi ya na iya?, bari na leka Khalil na dawo”, tabe baki tayi tace “kai da Khalil din ma bansan wa yafi wani ba, gwara ma kai ka dauko hanyar da ze sadaka da gidan aure shikuwa ba’a ma san ina yasa gaba ba”, dariya yayi yace ” yace shi yarinya yakeso teenager “, girgiza kai kawai tayi dan shida abokinshi halinsu se su, sallama ya mata ya fita, seda ya leka dakin Zeena yaga tana kallo a laptop dinta sannan ya fita ya bar gidan.


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


Tana shiga daki ta rage kayan jikinta sannan ta zauna kan gado daga ita se bra da leggings dinta, wayanta ta dauko ta kunna data sannan ta shiga wani grp an rubuta FOREVER FRIENDS❤ sallama ta musu ai kuwa kaman jira sukeyi duk suka fito su hudu kadai ne a grp din, fada musu tayi an kusa kawo kudin aurenta ai kuwa suka fara murna kowa na fadan albarkacin bakinshi kafin daga baya suka fara tsara yadda zasu gudanar da bikinsu saboda harkar manya za’ayi ba kanakan harka ba, itadai jinsu kawai takeyi na dariya tayi dariya har aka kira magrib sannan suka sauka, wani abin mamakin sauran contacts dinta da suka mata message batabi ta kansu ba, iya grp din kawai ta tsaya tana gama abinda zatayi kuma ta sauka.

Kaman yadda Mom ta mata alkawari da sukayi waya da Daddy ta fadamishi yace mata zema su Baba mai kano magana sai asan yadda za’ayi, sanda Mom ta fada mata murna a wurinta ba magana, da dare sukayi waya da HYDAR ta fada mishi yadda sukayi ai kuwa shima yayi murna sosai. “Swthrt bakisan yadda naji yanzu ba da kikace magana zakai kunnen Dad dinki”, murmushi tayi tace ” a duniya banda buri daya wuce in zama matar general HYDAR ALI MAHMOUD MAI TURARE”, dariya yayi yace “ai ki kwantar da hankalinki dan kin riga kin zama mayar HYDAR ALI”, da haka sukaci gaba da hiransu soyayya kala kala suke nunawa junansu kaman ba dazun suka rabu ba.✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

BINTOTO tafiya kawai takeyi ba tare da tasan a ina zata siyar da gujiyar nan ba, daga karshe data gaji wuri ta samu a gaban gidan mai gari ta ajiye gujiyar ta zauna karkashin bishiya tana dauka tana barewa tanaci hankalinta kwance, tana zaune aka soma zuwa makarantar cikin gidan mai gari nan yaran makaranta suka soma siyan na biyar na goma amma inta sa musu a leda se taga kaman yayi kadan seta kara harse ta kusa ledan sannan zata basu, yara kuwa ganin arhanshi yasa sukata siya harya kare, tanajin dadi ya kare amma tana kirga kudin ta ko dari biyu be kaiba ai nan da nan hankalinta ya tashi ta rasa yadda zatayi.Kuka ta zauna tanayi har Kallamu ya fito daga gida dan dama dan gidane mai gari ke rikonshi, nan ya ganta ta tambaya da sauri ya karasa wurin ya tsugunna yace ” BINTOTO, lfy kika zauna nan kike kuka, meya faru?”, wani kukan ta sake sawa cikin shessheka tace “Goggo ta bani gujiya in siyar mata, ni kuma bansan yadda zan auna ba, yanzu ya kare amma ko rabin kudin ta be kai ba, wayyo Allah na na shiga uku”, cike da tausaya yake kallon ta kafin ya nisa yace “nawa ne kudin ta?”, ” dari biyar”, jinjina kai yayi kafin yace “nawa ne a hannunki?”, ” dari da arba’in da biyar”, wani iska ya furzar dan kuwa ba isasshen kudi a hannunshi dan yanzu nema ze fita kasuwa, kallonta yayi yace “jirani ina zuwa”, shiga gida yayi ba dadewa se gashi ya fito da dari biyu a hannunshi yace ” ungu wannan ki hada dana hannunki ki kai mata, nasan zata dakeki saboda kudin be kai ba amma ki hakuri na dan lokaci, wuya baya kisa wata rana se lbr”, karba tayi tana mishi godiya kafin ta mike ta kama hanyar gida tana kuka dan tasan duka yau dole ta shashi.
A gaban gidan ta tsaya da kyar ta iya karasawa ciki da sallama amma taji shiru alaman ba kowa dan kuwa Zinaru bata dawo ba, Malam Tanimu kuwa ya tafi gona, ajiye tray din hannunta tayi ta karasa kicin ragowan tuwon jiya ta dauka taci duk yayi sanyi ya daskare amma a haka ta dinga turawa, tana gamawa yayi wanke wanke ta gama ta zauna zaman jiran dawowan Zinaru tareda da sakamakon rashin cikar kudin gujiya. Tayi nisa da bacci a nan tsakar gida Zinaru ta shigo da murmushi kwance a fuskarta, ganin BINTOTO tayi kwance a kasa tayi makirin murmushi tace “yarinya yanzu zaki tabbata marainiya” (niko nace me take nufi), maimakon ta tashe se zuwa tayi gaban randa ta debo ruwa tazo ta watsa mata a fuska ai da sauri ta mike tsaye tana kakkarwa saboda sanyi, Zinaru bata damuba tace “bani kudina”, jikinta na rawa tasa hannu a bakin zani ta dauko dari uku da arba’in da biyar ta mikawa Zinaru, Zinaru ta kirga taga basu cika tace ” ina sauran”, cikin sheshekar kuka tace “wlh abinda aka samu kenan daga cinikin”, Zinaru hankalinta kwance tace ” ina sauran gujiyar”, dan a tunaninta bai kare bane se taji tace “ai ya kare”, zaro ido Zinaru tayi ta kalli kudin hannunta tayi kukan kura se kan BINTOTO, dukan ta dakeyi kaman Allah ne ya aikota itakuwa baiwar Allah se ihu takeyi tana neman taimako, ana cikin haka aka shigo da Malam Tanimu.
Washegari tunda da safe HYDAR ya shirya cikin uniform dinsu na sojoji ya wuce barrack dinsu ba tareda yawa kowa sallama a gidan ba dan yasan basu tashi ba, yana zuwa direct office dinshi ya wuce duk wasu masu gaishe shi da sara mishi basu isheshi kallo ba, yana zama ko minti biyu ba’ayi ba aka aiko mishi da cewar colonel Idris na nemanshi, dan tsaki yaja saboda bayason takura sannan ya mike ya wuce office din Colonel din. Magidancin mutum ne zaune fuskarshi ba yabo ba fallasa HYDAR ya sara mishi sannan suka gaisa kafin yace “kaikuma HYDAR haka akeyi ne, mun turaku Enugu mission akan robbers dinda suka addabesu amma kai kaje kana bin diddigin en kunar bakin wake, kayi son ranka, yanzu da gawan ka aka kawo mana fa? wai yaushe zaka daina take doka ne?”, shiru HYDAR yayi kanshi na kasa, a zuciyarshi kuwa Allah kadai yasan irin curses dinda yake janyo wa mutumin dan ya tsaneshi, ” da kai fa nake magana”, Colonel yayi magana yana kallon HYDAR daya kame wuri daya, kanshi a kasa yace “Sir, naga en kunar bakin waken sunfi robbers din addabansu, and a matsayi na soja sanda nake swearing in seda nace I will protect my country and it’s citizen no matter wat, to ni banga laifi ba dan na taimakesu, saboda a kallum kashesu akeyi, kum……”, ” Shut up u bloody fool”, Colonel a fada a tsawace dan dama shi irin corrupt soldiers dinnan ne kuma da politicians yake aiki. Shiru HYDAR yayi kaman ruwa ya cinyeshi kafin kuma daga baya yace “I’m sorry sir, something like that will never happen again”, ” better make sure it doesn’t, now leave”, seda ya sake sara mishi sannan ya fita, yana fita yaja wani dogon tsaki (nikuwa nace gaba da gaba gabanta).

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Karfe goma KAUSAR ta tashi daga bacci, seda ta shiga tayi wanka shirya cikin wani lace dikin riga da skirt . Saukowa tayi kasa wurin dinning ta nufa taci breakfast hankalinta kwance se dannan waya takeyi har ta gama sannan ta kuma sama, dakin Mom ta shiga da sallama, Mom na kwance tana baccin safe ta dukunkune cikin bargo, murmushi tayi kafin ta karasa a hankali dan motsi kadan ze iya tashinta, zama tayi kan bedside drawer ta duka daidai cheeks din Mom ta bata peck, bude ido Mom tayi KAUSAR tayi saurin cewa “sorry na tashe ki”, murmushi tayi tace “har kingama ne”, agogon hannunta ta kalla tace ” eh na gama office zan wuce “, ” Allah ya taimaka ya bada sa’a”, Mom tace sannan KAUSAR ta mike tana amsawa da ameen tawa Mom sallama ta fita.

Seda ta koma dakinta ta dauko handbag, phone, car key da veil dinta sannan ta fito”. Karo sukaci da Laure duk da matan zata girmewa KAUSAR amma ita ta duka tana gaisar da KAUSAR, sama sama ta amsa ta sannan ta fita, wurin wani black Audi ta nufa motan da kudinta ta siyeshi ba iyayenta ba, wanda Dad dinta ya siya mata ma bata cika hawanshi ba. Gate aka wangale mata ita kuma ta fita tana tukinta a hankali harta kai wani dan karamin building inda nan company dinta yake, ita take managing dinshi, infact nata nema, a sama an rubuta KAUSAR FASHION & DECOR shiga tayi fuskanta a sake tanata amsa gaisuwa har secretary dinta ta karaso suka gaisa sannan ta shiga office dinta, company din ba wani babba na azo a gani bane amma kuma ya tsaru iya tsaruwa sannan ma’aikatan basu dayawa kuma a haka tayi fice a cikin garin Abuja duk wani aure idan za’ayi ita ake kira taje tawa dakin amarya jera yadda kowa ya shiga seyace “wow”, ammafa sedai aikinta se mai naira a hannu dan ana kashe kudi.Tana zama secretary dinta ta shigo da wani file a hannu tazo ta zauna itama kaman ba secretary ba tace ” wannan file contract dinda mukayi da Alhaji lawal ne, yau da safe naga alert a account din company ya biya 750k, na kirashi na tambayeshi me yasa be biya complete ba yace wai siyaga irin kayan da akasawa er shi da quality dinsu sannan ze biya sauran”, dagowa tayi rai a bace tace “mayar mishi da kudinshi, mun fasa, inaga a gabanshi yarinyarshi ya zaba irin bed da kujerun da takesu hardasu dinning, akan ya biya 2mila tinda 1bedroom ne yaki yace sedai 1.5 shine zezo ya raina mana hankali, ki kirashi kice yaje wani wurin amma bani KAUSAR decor ba”, shiru secretary din tayi sannan daga baya ta tashi ta fita.

Story continues below


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


Zinaru salati ta kamayi ganin yadda aka shigo da Malam Tanimu, “meya faru dashi haka?”, ta fara tambaya, wani tsoho ne ya bata amsa da cewar ” muna noma daga sama mukaga ta fara aman jini, shine muka dawo dashi gida”, salati ta dinga jerowa har suka shinfideshi anan tsakar gidan kan tabarma suka fita sun mishi addu’an Allah ya kara lfy. Suna fita Zinaru ta sheke da dariya yayinda BINTOTO tayi kan mahaifinta tana kuka, kallon Zinaru dake dariya tayi Zinaru ta ware mata idanu kafin tace “daina kallona, mahaifinki zaman duniya ya riga ya gamashi danni duk wanda yace ze dinga shiga sabgata idan ina muzguna miki se naga bayanshi, kaman yadda naga na mahaifinki”, BINTOTO duk da batada wani yawo sosai amma tabas ta gane me Zinaru ke fada, wato ita ta mayar da mahaifinta haka, shikuwa Malam Tanimu yana jinta amma ba bakin magana.


Ke BINTOTO tashi ki daura ruwan da za’a mishi wanka dashi, bari naje na siyo likkafani”, da sauri BINTOTO ta dago gabanta na wani mugun faduwa tace ” Goggo ai ba mutuwa yayi ba, kalleshi fa da ranshi, dan Allah bari mukaishi asibitin wajen gari”, wani harara ta maka mata kafin tace “ki tabbata kin daura kafin na dawo”, da haka ta fita tana dariyan makirci (oh Allah), BINTOTO hannu ta daura a kai tana rusa kuka tana ihun azo a taimake ta amma bameji saboda siririn muryanta, ji tayi kaman an kirata ta juya taga Malam Tanimu na cewa ” FATIMA”, bata taba jin ya kira ainihin sunanta ba se yau, saboda sunan mahaifiyarshi ce, da sauri ta karasa kusa dashi ta rike hannunshi tace “baba gani”, kara matse hannunta yayi cikin nashi harseda yayi kara sannan yace ” FATIMATU BINTU ZAHRA, yarinya me babban suna”, cikin karfin hali yake magana yana murmushi, itama murmushin tayi tana hawaye yace “FATIMA nasan kwana na ya kare, ki yafe min saboda ban sauke hakkin da Allah ya daura min a kanki ba, na zalince ki na zalince mahaifiyarki, dalilina mahaifiyar ki ta kamu da ciwon zuciya amma bata tankamin ba, duk wulakacin da nake mata nida Zinaru, Indo ta kasance mai hakuri da juriya, kema inaso ki kasance mai hakuri da juriya a duk halin da zaki tsinci kanki, ki rike wasiyan Mahifiyarki na karshe, karki yarda ki bada budurcinki, ki rike mutuncin ki, ki rike Allah ki rike Annabi insha Allah bazaki taba tabewa ba a duniya ba”, tari ya farayi wanda jini kadai ke fitowa ita kuwa kuka takeyi dukda maganganunshi ba wani ganewa takeyi ba dan she’s 13 amma tsabar karamin jiki in aka ganta kaman ‘yar 10yrs, ganin tarin bame tsayawa bane yasa ta riko kanshi ta daura kan cinyarta tana mishi sannu.
” Fatima nasan bakisan en uwan mahaifiyarki ba se nawa, Fatima en uwan mahaifiyarki suna cikin birnin garin Abuja”, shiru yayi saboda tarin da yaci karfinshi kafin ya soma kalmar shahada ” La….. il….aha illa…..laha muha…ammad…..rasul”, be samu ya karasa ba harshenshi ya karye bakinshi yayi gefe idonshi a lumshe, fuskanshi yayi haske, jikinshi yayi sanyi. Murya can kasa BINTOTO tace “baba bacci kayi”, jin shiru yasa ta sake maimaita abinda ta fada nanma shiru, murmushi tayi ta goge fuskanta tace ” yi bacci baba, bazan dameka ba”, da haka tayi shiru tana kallon fuskanshi da taga ya mata wani extra ordinary haske. Malam Mamman abokin Malam Tanimu na ya shigo gidan da sallama saboda yaji lbrn Malam Tanimu ba lfy, BINTOTO da sauri tasa hannunta a baki tace “shhhhh”, sannan a hankali tace ” yayi bacci karka tasheshi”, girgiza kai Malam Mamman yayi saboda kallo daya yama Malam Tanimu yasan rai yayi halinsa, hawaye ne suka ciko mai a ido yayi sauri ya share kafin ya fita daga gidan ya samu yaro ya aika yace “jake sanar wa mai gari Malam Tanimu ya rasu a sanarwa jama’a”, yaron jikinshi a sanyaye ya tafi saboda yasan Malam Tanimu beda wani matsala ga bashi da magana.
Zinaru ce ta dawo daga idan ta tafi sannan tayi sauri ta shiga daki batama bi takan su BINTOTO ba dan ita tasan ya riga ya rasu, seda ta ajiye likkafanin sannan ta fito ta daura hannu aka ta kwala ihu tana ” na shigu na lalace Malam ya tafi ya barmu, Malam ya mutu, Malam ya rigamu gidan gaskiya, wayyo Allah na, katanganmu ya fadi, wayyoooo na shiga uku”, kaman wata jahila haka ta dinga ihu wanda yaja hankalin makota ai kan kace me an fara shigo mata ana kallon Malam Tanimu ana mata sannu, Malam Mamman ne ya shigo da wasu maza yace matan su basu wuri a masa wanka a shirya shi dan gidan beda wani girma shiyasa dole a tsakar gidan zasu mai wanka. Haka aka dinga fita Zinaru kuwa daki ta shiga ta dauko leda ta mikawa Malam Mamman tace “ga wannan”, karba yayi ya duba yaga likkafani ne se ya sake kallonta da sauri tace ” shi ya siya yace duk randa ya koma ga mahallicinshi a samai”, girgiza kai kawai yayi ta koma ciki ta zauna gidan aka watse ya saura daga su Malam Mamman se BINTOTO da tunda Zinaru ta fara kukan karya tayi mutuwan zaune ga Malam Tanimu a jikinta, Malam Mamman ne ya dagata daga wurin ya turata daki duk batasan yanayi ba dan hankalinta ya tafi wani wurin, kiran Zinaru yayi ta leko yace “zo kiwa mijinki wankan karshe”, kuka tasa tana ” wlh bazan iya Malam Mamman ku mai bazan iya ba”, juyawa kawai Malam Mamman yayi dan gabadaya be yarda da ita ba, gashi sanda ya shigo dazu bata nan.Ina familyn Malam Tanimu, sannan kuma wacece BINTOTO?.
Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like