HUTU CHAPTER 2

Advertisement

HUTU

CHAPTER 2


Kaman yadda Dad ya tsara komai haka abun ya kasance, yayiwa baba mai kano magana wanda yake kani a wurinshi sannan ya sanar da Mom inda itakuma ta sanar da KAUSAR. Murna wurin KAUSAR ba magana dan ji take kaman ta zuba ruwa a kasa tasha, tayi ta trying numbern HYDAR saboda ta mai albishir cewar ance ya turo wanda tasan se yafi kowa murna amma bai daga ba. Hankalinta ne ya fara tashi dan tasan bayakin daga wayarta koda kuwa sun samu sabani ne ze daga amma bazeyi magana ba, toh yanzu ba wani sabanin da suka samu kalau suke zaune amma be daga wayaba. Ajiye wayan tayi ta dauko laptop dinta tanaso ta karasa wani aiki da tafara tun a office amma ta gagara saboda tunanin HYDAR. +

KAUSAR


✴✴✴✴✴✴✴✴✴Iya galabaita ya galabaita dan bemasan inda kanshi yake ba, shiyasa ko ringing dinda wayanshi keyi beji ba bare ya dauka. “Zeena jeki taso yayanki hakanan yamma tayi”, fadar Ummi dake zaune da kayan fruits a gabanta, “toh Ummi” cewar Zeena tareda mikewa ta fice zuwa bangaren HYDAR, da sallama tashiga parlour amma taji shiru saboda haka ta karasa daki ta kwankwasa nan ma shiru se kawai ta bude kofan ta shiga abinta. “Ya HYDAR Ummi wai…..”, ai maganan makalewa yayi saboda ganinshi kwace yashe a kasa da tayi, hannunshi rike da mara bemasan inda kanshi yake ba.


Ai da sauri ta karasa gabanshi ta tsugunna tana ” Ya HYDAR!, Ya HYDAR!!” amma shiru da sauri ta tashi ta fita da gudu takalmin kafanta se kwaskwas yakeyi a kan tiles, ganin skirt dinta ze iya yarda ita kasa yasa ta tattareshi sama, da gudu ta shiga parlour tana haki Ummi ta kalleta hankali tashe tace “ke lfy?” “Ummi Ya HYDAR ne ba lfy, yi sauri kizo”, da fadan haka ta juya, ai Ummi ma mikewa tayi da sauri itama ta karasa dakin, tana ganinshi ta fara salati tace “babana lfynka kuwa, innalillahi me zan gani haka”, ta fada tana rikeshi ganin halinda yake ciki yasa tace ” ke dauki wayanshi ki kiramin khalil, daukan wayan tayi dan dama tasan sunanta yasa as password saboda haka ta rubuta Zeena wayan ya bude, miss calls din KAUSAR ta gani dayawa ta tsallake ta nemo numbern Khalil ta kirashi.
Ringing biyu ya dauka yana sallama, ba tareda ta amsa sallaman ba tace “Ya khalil kazo Ya HYDAR ba lfy, kayi sauri”, ta karashe da saka kuka, jin kukanta ba karamin tada mishi hankali yayi ba saboda haka ya kashe wayan ya dauki makullin motarshi da duk wani abu daze bukata ya fito. Cikin minti kalilan ya karaso gidan da sauri ya karasa ya taimakawa Ummi suka daroshi kan gado sannan ya mishi allura har biyu dan dama yasan matsalan HYDAR, su Ummi ne dai ke cikin duhu basu san komai ba. Ganin har bacci ya daukeshi yasa Ummi tace ” meke samunshi”, sosa keya yayi yace “ba komai ummi, dan zazzabin da baza’a rasa bane, kuma kisan be dade da dawowa daga Enugu ba, inaga canjin ruwa ne”, kai kawai ta kada badan ta yarda ba ta fice tareda cewa ” kafin ka wuce inason ganinka”.
Kallon Zeena yayi bayan ta fita yace “an daina kukan”, sunkuyar da kai tayi ya kuma cewa ” ya karatu, kin manta dani, bakya ma neman yayanki”, a shagwabe tace “toh ba kaine ka daina zuwa ba”, tsayawa yayi yana kallonta danshi a rayuwarshi Zeena na burgeshi, komai tayi yana mata kyau, inyace bayasonta yama Allah karya amma gani yake ya za’a ya tunkari yarinyar da aka haifa a gabansu da kalmar ‘so’ ai se ta raina shi. Kada kai yayi yace ” bari na leka Ummi, ki zauna nan ina zuwa”, da haka ta fita ita kuma ta koma gefen gadon ta zauna tana kallon yadda HYDAR ya rame lokaci daya. Yana fita wayan HYDAR ya sake daukan ruri Zeena ta dauka ganin KAUSAR ke kira yasata dagawa tareda cewa “hello Ya KAUSAR”, mamaki ne ya kama KAUSAR ganin Zeena ce ta amsa wayan amma ta share tace ” Zeena ykk, ina yayanki?”, “ina lfy amma Ya HYDAR ba lfy”, ai a zabure tace ” lfy meyasa meshi?”, “zazzabi ne, yana bacci ma yanzu”, cikin sanyin jiki tace ” inna ya tashi ki kirani”, “toh”, tace da ita sannan ta katse wayan.

Khalil ne zaune gaban Ummi data tsareshi da ido tana jira taji ya bata amsan tambayan da ta mishi, ganin yayi shiru ne yasata sake cewa ” kaifa nake sauraro, nace me yake samun babana, dan ma tabbata rashin lfynshi beda nasaba da zuwanshi Enugu”, sosa keya ya kamayi yana kame kame dan besan me zaice mata ba saboda ta harbo jirginsu tace “ranka ze baci in baka fadamin ba”, duk da Ummi batada fada amma yanayin da tayi magana yasan ranta ya baci saboda haka yace ” Ummi yanada bukatar aure ne, sha’awa ce tai mishi yawa, yanada bukatan mace a kusan dashi”, ajiyar zuciya ta sauke saboda tasan yanzu zata iya shawo kan matsalan, kallo Khalil tayi tace “tun yaushe ne yafara samun wannan matsalan?”, ” kusan shekara uku zuwa hudu kenan”, salati ta saki tace “shine baku fada a gida asan abinyi ba, nashiga uku ni Hafsatu yaran nan zasu kasheni tun lokaci na beyi ba”, dariya ta bashi amma ya gimtse ta kara kallonshi tace ” toh ya akayi bamu sani ba se yau?”, gyara zamanshi yayi yace “shine yace kar a fada muku saboda zaku iya cewa zaku mai aure kuma a lokacin yana tareda KAUSAR beson abinda ze rabasu saboda haka ya dau wa kanshi yawaita azumi da shan Lipton da maganin da namishi prescrib”, kallonshi takeyi da mamaki kafin tayi kwafa tace ” tashi kaje”, tashi yayi ya fita, yana zuwa compound ya furzar da iskan da besan yana rike da shi ba se yanzu.

HYDAR

8

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Wacece BINTOTO?

Shekara goma sha biyar da suka wuce.

Tafe yake zashi cikin garin Adamawa saboda ranar cin kasuwa ce, duk da daga kauyensu zuwa cikin gari da nisa a kafa amma wannan baya damun mutanen kauyen saboda sun riga sun saba. Mota ya hango da alama hatsari sukayi ya karasa wurin da sauri nan yaga mutane biyu cikin motan mace da namiji, namijin wanda ya kansance shike driving ya riga da ya rasu amma macen da alama da rai a jikinta saboda yayi haka yayi saurin bude kofan side dinta wanda da kyar ya budu sannan ya cirota ya goyata ya koma kauyensu da ita dan ya ceci ranta. Dayake ranan ya kama ranan kasuwa shiyasa ba mutane a garin bare a ganshi, shima dan ya makara ne da kuma yanada sa’an ganin hatsarin ne, da sauri ya shiga gida wanda yake cike, family house babba guda ya kama ihun “Inna! Inna!!” Da sauri ta leko tana cewa “Tanimu me kuma ya dawo da kai, sa’aninka duk sun tafi kasuwa?”, shiru tayi ganin ya goyo mutum kuma da alaman macece tace ” na shiga uku Tanimu me zan gani haka”, sauketa yayi kan tabarma yana haki yace “inna hatsari sukayi, dan uwanta ya mutu amma ita tanada rai, inna muyi wani abun kafin ta mutu”, a halin yanzu kishiyoyin inna duk fito gulma suna kuskus inna ta rafka salati idonta cike taf da hawaye gabanta na faduwa tace ” na shiga uku Tanimu ina kaga an taba irin wannan taimakon, yanzu idan ta karasa mutuwa a nan kuma muyi yaya da gawanta eh Tanimu? “, ta tambaya tana kallonshi”.
STORY CONTINUES BELOW

“Inna bazata mutu ba, muyi wani abu, nasan kinada zuciyar taimako”, shiru tayi na en wasu dakiku kafin tace ” shiga da ita ciki bari na kira Asabe me magani, da haka inna ta sabi mafayi ta fita tana tunanin rashin hankali irin na Tanimu koda yake dama ance ba’a raba Fulani da wawta. Ba dadewa sega inna da Asabe me maganin gargajiya, treatment ta mata yanda ya kamata da yake ba wani rauni taji sosai ba, se dogon suman da tayi wanda suna shaka mata wata ganye ta farfado tana maida numfashi sannan ta koma bacci, nan Asabe ta musu sallama ta wuce inna ta mata alheri. Zama inna tayi ta rafka tagumi tana kallon Tanimu daya kurawa baiwar Allahn dake kwance ido, kishiyoyinta ne su biyu suka shigo dan gulma sukace “ta farfado ko ta margaya ne”, suka fada suna dariya ita dai inna bata amsa musu ba, Tanimu kuma bemasan sunayi ba. Ganin ba wanda ya basu fuska yasa suka fita daya cikinsu tace ” yo da malam na raye ina ta isa ta shigo da waccen gida”, dayan tace “ai samun dama ne”, haka sukata gulma duk tanajinsu amma uffan batace ba.Seda ta kwashi kusan awa uku sannan ta tashi tana rike kanta, da sauri inna dake addu’a kan sallaya ta dawo kusa da ita tana mata sannu dan Tanimu bayanan ta aikeshi kasuwa yayo mata cefane. “Sannu baiwar Allah ya jikinki”, shiru tayi tana kallon Inna kafin daga bisani tace ” ina ne nan”, kallonta inna tayi tace “hatsari kukayi dana ya kawoki saboda yaga da sauran rai ajikinki, ya sanunki”, ” Aisha” ta bada amsa kai tsaye tanason tuno wani abu amma ta kasa, “bari kiyi wanka ki wanke baki sekici wani abu ko”, inna ta fada cikin sigar tambaya, kada mata kai kawai tayi inna taje ta hada mata ruwan wanka taje tayi tazo tayi sallah  inna ta bata abinci taci. Sanda Tanimu ya dawo yaji dadin ganin ta tashi nan sukasata gaba da tambaya saboda su samu su maidata wurin en uwanta amma ba amsa danta manta komai, daga sunanta se sunan garinsu kawai ta tuna wato Abuja. Sosai suka tausaya mata wanda wannan ne yayi sanadiyar zamanta a gidan dan basusan a wani waje take a cikin abujan ba.
Cikin kankanin lokaci shakuwa me tsanani ya shiga tsakaninta da Tanimu komai yasiyo Indo, in zeyi magana Indo, dan haka suke kiranta. Kishiyoyin mahaifiyarta kuwa kullum tsana da tsangwamarta suke amma sedai Allah yayi Aisha Indo mace ce  mai hakuri, tayi iya kokarinta wurin ganin ta tuna ko ita wacece amma abu ya faskara kaman baki  dole ta hakura ta zauna. Ana cikin haka shakuwan dake tsakanin Indo da Tanimu ya juye ya koma soyayya wanda yakaisu ga aure en uwanshi sunyi bakincin wannan aure saboda Indo macece kyakyawa son kowa kin wanda ya rasa. Bayan aure  da shekara biyu Indo ta haifo santaleliyar ‘yar ta me kama da ita, ba inda ta barota, idon,hancin, bakin komai na mahaifiyarta ne. Sosai Tanimu yayi murna ranan suna yarinya taci sunan mahaifiyar Tanimu wato FATIMATU BINTU ZAHRA, suna kiranta da BINTOTO.
A ranan suku suku KAUSAR ta wuni saboda ko kadan hankalinta ba a kwance yake ba jin ance masoyinta ba lfy. Lokaci zuwa lokaci take kira taji ko ya tashi amma Zeena tace be tashi ba. A haka ta hakura ta kwanta amma yadda taga rana haka taga dare. Da sassafe ta tashi ta wuce kitchen tace Laure ta hada mata breakfast zata fita dashi, daga nan kuma ta koma daki tayi wanka bata bata lokaci ba ta shirya cikin gown na atampha ta yafa veil ta fito ta shiga dakin Mom. Bacci ta sameta tanayi saboda haka ta juya dan bataso ta tasheta ta koma kitchen ta tarar Laure ta gama ta jera abincin a basket Laure ta kai mata mota, shiga tayi taja motanta to only God knows where.
+

HYDAR bashi ta tashi daga bacci se asuba saboda drip dinda Khalil yasa mishi har leda 4, koda ya tashi Khalil yagani kwance kusa dashi ya bacci, drip din hannunshi ya cizge ya tashi ya shiga bathroom ya sakarwa kanshi ruwa sannan yayi alwallah ya fito. Tashin Khalil yayi shima yayi alwallah sukayi sallah sannnan Khalil ya soma hada kayanshi ze wuce, “wai ina kake sauri zakane?”, HYDAR ya tambayi Khalil ganin saurin da yakeyi, ” inada patient dazan duba”, ya basa amsa batare da ya kalleshi ba, “amma ai yau weekend”, ya kara fada, Khalil cike da kusawa yace “ance maka doctors sunada hutu ne?”, kallonshi kawai HYDAR yayi be sake cewa komai harya  fice.
Seda ya leka Ummi ya gaisheta lokacin takwas harda minti goma tace “ina zaka da sassafe haka?, ka tsaya kayi breakfast mana”, girgiza kai yayi yace ” Ummi akwai patient dinda zan duba a hospital ne, bazan dade ba zan dawo “, ” toh shikenan, amma ka tabbata kasawa cikinka wani abu”, kada mata kai yayi yace “Ummi ki kula HYDAR, inaso ya samu issashen bacci sosai dan stress ya mishi waya kuma ya tara bacci, drip dinda na samai baze sakeshi yanzu ba, saboda haka zuwa anjima se sake komawa baccin, kar a dameshi”, kada kai tayi tace ” Insha Allah ze samu bacci”, da haka ya mata sallama ya fita.

KAUSAR bata tsaya ko ina se a unguwar su HYDAR wato Asokoro, seda tazo layin sannan ta fara tunani taya zata shiga gidan surukanninta, tace me ya kawota, duba Hydar kikazo yi wani abu ya fada mata, nisa da gidan tayi parking ta kasa karasa tana nan zaune cikin mota tana tuanin yadda zatayi motar Khalil ya fito daga gidan, da sauri ta fito ta karasa shima yayi parking ya fito yana murmushi yace “Amaryar mu kece da sassafe haka”, kunya taji dan kuwa tasan tayi sammako dawaya, dagowa tayi tace ” ina kwana Khalil”, “lfy lau, nasan HYDAR kikazo dubawa kina kunyar shiga koh?”, kai ta kada kanta kasa yace ” muje in miki jagora”, nokewa tayi wurin tace “kana ganin ba matsala”, ” babu kedai muje”, motanta ta koma ta dauko basket din abincin Khalil ya karba hannunta suka karasa cikin gidan gabanta na dukan uku uku.
Part din Ummi ya fara kaita dukda ba yau bane farkon shiganta gidan ba amma kullum tazo shiga se gabanta ya fadi, da sallama suka shiga parlourn Ummi tace “kayi mantuwa ne?”, ” a’a Ummi bakuwa kukayi”, tasowa tayi daga wurin dinning tace “bakuwa daga ina”, KAUSAR ta shigo kanta kasa ta duka har kasa tace ” ina kwana Ummi”, Ummi a ranta tace “hmmm wannan sammako lfy daiko?”, amma a fili cewa ” a’a KAUSAR ya kike, ya gida, ya mamanki, tashi daga kasa”, duk ta fada lokaci daya, murmushi KAUSAR tayi tace “duk lfy lau, dama Zeena ce tacemin HYDAR ba lfy, shine nazo dubashi”, ” ai kuwa kin kyauta, Khalil kaita ta gaida HYDAR din”, tashi tayi tabi bayan Khalil tana tafiya kaman tsuntsun da ruwa ya mai duka.

Da sallama suka shiga dakin HYDAR da waya a hannunshi da alama kira yake sonyi, dagowa yayi yana kallon Khalil kafin ya maida dubanshi zuwa KAUSAR dake shigowa yanzu, da sauri ya tashi fuskan dauke da murmushi yazo gabanta kaman wanda ze rungumeta se kuma tsaya yana kallon Khalil dake kallon ikon Allah, ajiye basket din hannunshi yayi ya juya yafita, HYDAR yajata ta zauna kan coach dinda ke dakin yace, “ke naketa kira baki daga ba, ashe kina hanya”, se a lokacin ta tuna ymta bar wayanta a mota, murmushi tayi tace ” wayan na mota, ya jikin, hw are u feeling nw?”, kallonta yayi cike da so da kauna yace “I’m feeling much better after seeing u”, murmushi tayi tace “I’m glad, ga abinci nakawo ma”, ” ya akayi kikasan banda lfy?”, ya tambaya ba tareda ya kalli inda take nuna masa ba, “na kira phone dina Zeena ta dauka take fadamin”, girgiza kai yayi a haka tayi feeding dinshi har ya gamaci sannan yace mata ” ya magananmu princess, ke naketa sauraro?”, murmushi tayi tace “jiya na kira inma albashir amma unfortunately bakada lfy”, kallonta yayi yanason tabbatar da wani game da ita kafin yace ” ance na turo?”, kai ta kada mai nan ya tsaya yana kallonta chan dai yace “wai da gaske kike”, ” kasan bazan maka wasa da wannan maganan ba”, tsalle ne kawai beyi ba dan murna shima kuma saboda KAUSAR na wurin ne, kallonshi tayi tace “bari ma tafi kar Ummi taga na dade”, be hanata ba ya fito ya rakata tawa Ummi sallama sannan ya rakata har bakin mota sukayi sallama yace ” insha Allah gobe gobe za’a kawo kudinki dinta  gobe Sunday”, itada murmushi kawai tayi ganin yadda yake zumudi ta daga mishi hannu sannan taja mota shikuma ya koma gida saboda yayiwa Ummi albishir.

STORY CONTINUES BELOW

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


Bayan haihuwan BINTOTO komai ya tsayawa Malam Tanimu cak kaman baki, asara ba irin wanda beyi ba, gona ya kone, kayan da yasa a store din gonan ma ya kone, a takaice dawowa yayi beda komai, gabadaya dawowa yayi to square zero starting from the root once again amma it’s not easy, wannan hali daya fada yasa hankalinshi ya tashi, duk inda yaje neman rance saboda ya fara business baya samu, abu yaci tura, nan en uwanshi sukama BINTOTO lakabi da mai ‘kashin tsiya’, basa kiranta da sunanta se da mai kashin tsiya, a haka Malam Tanimu yake gwagwarmaya yau akwai gobe babu har da taimakon matarsa Indo komai yake zuwa masa da sauki saboda tana tausasa masa zuciya ya yawar fahimtar dashi cewar kaddara ne Allah ya dora mai, kuma kaddara tana kan kowa jarrabawa ce Allah keyiwa dan Adam saboda yaga irin hakurinshi da yadda da kadaran da yayi.

Ana cikin haka BINTOTO ta girma shekaranta tara a duniya amma inka ganta bazaka yarda ba saboda karamin jiki wanda rashin samun abincin kirki ne ya janyo mata, a wannan shekarar ne wata date kowa na bacci gari yayi shiru gidan iyayen Malam Tanimu ya kama da wuta wanda har yau ba’asan me ya janyo gobarar ba, mahaifiyarshi da kishiyoyinta, yaran kishiyoyinta da duk wani mahaluki dake cikin gidan seda ya bakwanci lahira mutum da dabba dan babu abinda aka tsira dashi se fili dake shafe saboda komai ya kone dan mutanen kauyen basusan anyi gobara ba seda asuba an fito za’aje massalaci, kukan kam Malam Tanimu yayishi dan yanzu beda kowa dagashi se matarshi da ‘er shi wacce kallo daya zaka mata kasan lfy be isheta ba.
Bayan sadakan arba’in Malam Tanimu yaje wurin mai gari akan yanaso ya siyar da gidan iyayenshi in yaso yayi wani abu da kudin, mai gari da kanshi ya siya gidan da ya riga ya koma fili, anan ne fa Malam Tanimu ya dawo kan kafafunshi murna shi da iyalanshi ba magana. Bayan shekara daya a afkuwan wannan lamari kwatsam Malam Tanimu ya tsiro da maganan aure saboda yanason yara dayawa amma da alama In do bame haihuwa bace, nan Indo ta bashi goyon baya dari bisa dari dukda kasan ranta tana kishin mijinta, ana haka watarana ya fito zashi gona Allah ya hadashi da Zinaru wacce ta fito daga neighboring village dinda ke kusa dasu zuwa wurin wata kawarta, dayake indan Allah ya tsara bawa rayuwa ba mahalukin da ya isa ya canzashi sannan da bawa na ganin gaibu da Malam Tanimu beyi gigin shiga rayuwar Zinaru da maganan aure ba, amma sedai Allah ma daukaki ya riga ya tsara komai saboda haka yana mata maganan bukatarshi ta karbeshi hannun bibbiyu.

Ba’a dau lokaci ba akayi aurensu dayake ba budurwa bace bazawara ce, aurenta hudu, Malam Tanimu ne na biyar, tinda Zinaru ta shigo gidanan kwanciyar hankali ya kauracewa gidan, kullum cikin kullawa Indo makirci takeyi wanda saboda shige shigen da takeyi gidan malamai yasa Malam baya ganin bakin ta se farinta inda Indo kuma kullum itace mai laifi dukda ba haka bane. Duniya tayiwa Indo da BINTOTO kunci da zafi, basu da madafa se ubangijinsu, kullum se Indo ta kai kukanta wurin Allah, sannan duk dare kafin sun kwanta seta ma BINTOTO nashi kamar haka “BINTOTO ke mace ce, nasan bazaki gane abinda nake kokarin fada miki yanzu ba amma nan gaba zaki gane, inaso ki kare mutuncin ki, ki kare mana mutunci, duk namijin da ba muharramin ka ya bataki karki yarda, ki mishi ihu harse an kawo miki dauki saboda da zaran ya tabaki zakiyi ciki ki haihu, kizo kina tafiya ana nunaki ana cewa ga mai cikin shege chan, saboda haka ki kiyaye kinji, Allah ya miki albarka”, kullum nashihanta kenan itadai BINTOTO sedai tace ” toh”, amma badan tana gane abinda ummanta keson fada mata ba.

Kwance tashi asarar mai rai, Malam Tanimu gabadaya ya canzawa Indo da BINTOTO, kullum cikin masifa take shida beson magana, Zinaru tana juyashi son ranta, se abinda tace yake faruwa a gidan, Indo da BINTOTO sun zama kaman bayi dan aiki gidan kaf su sukeyinshi, ana haka ciwon zuciya ya kaman Indo na lokaci daya saboda bakin ciki da takaici, wayan barin dumuwanta a zuciya yasa ciwon zuciya ya mata mugun kamo wanda bata ganin zata iya tashi. Cikin dare se tari takeyi jini na biyowa sunan BINTOTO take kira har ta tashi daga bacci ta karasa kusa da Ummanta tace “Umma gani, lfy”, ” BINTOTO kiramin abbanki da goggonki dan Allah”, da sauri taje ta kirasu sedai seda suka bata lokaci sannan sukazo, a bakin kofa suka tsaya suna jin abinda take fadawa ‘erta.
“BINTOTO inaso ki rike abinda nake fada miki kullum, ki rike mutuncinki, badan yawan bin maza, ko hali kika shiga a duniyar nan ban yarda ki bada budurcinki, duk randa kika budewa wanda ba muharraminki ba kafa yayi abinda yakeso dake ban yafe miki ba”, da sauri BINTOTO ta dago fuskarta sharkaf da hawaye tace ” Umma wlh bazan yi, na miki alkawari”, dukda batasan me Ummanta ke fada mata ba amma kalmar ‘ban yafe miki ba’ ya daki zuciyarta sosai. Kallon Zinaru Indo tayi tayi murmushin karfin hali tace “ga ‘yata amana zan baki, kika cuceta Allah ze saka mata”, daga haka bata sake cewa komai ba ta juya ta kalli Malam Tanimu da jikinshi ya gama sanyi tace ” nayi bakin ciki zan tafi ba tareda ka samu damar neman yafeya daga wurina ba, amma dukda haka na yafe maka duniya da lahira sedai nima inaso ka yafemin, kuma inaso ka duba BINTOTO da kyau tinda ita kadai Allah ya baka”, zuwa yanzu BINTOTO kuka take sosai Malam Tanimu ma na hawaye banda Zinaru da fuskarta take nan wasai. A gabansu tayi Kalmar shahada tace ga garinmu, kuka kam BINTOTO da Malam Tanimu sunyi shi har ya kular da Zinaru, bayan mutuwanta da kwana biyu Zinaru tayi fice da shigenta akan Malam Tanimu wanda malamin nata ya nuna mata cewar duk randa Malam Tanimu ya fara dawowa hankalinshi kashinta ya bushe dan kuwa se asirinta ya tonu na cewar ita ta bari akawa Indo asirin da yasa mata ciwon zuciya na dare daya har yayi sanadiyar mutuwarta. Da wannan ta dawo gida taci gaba da cin karenta ba babbaka tana musgunawa BINTOTO wacce lfy be gama isarta ba dan mutane mamakin yayin jikinta sukeyi. Wannan dalili ne yasa randa Zinaru taga Malam Tanimu ya tsayawa BINTOTO ta gane cewar ya fara dawowa hankalinshi kuma muddin batayi wani abunba asirinta ze tuno, saboda haka ta wuce gidan Malaminta inda ya shaida mata cewar sedai su kashe Malam Tanimu kawai saboda asirinta ya rufu dan bayan wannan basuda wata hanya wanda wannan ne yayi sanadiyar cikawar Malam Tanimu sedai muce Allah ya jikanshi.
Kaman yadda HYDAR ya fada haka kuwa akayi, ya fadawa Ummi inda tafadawa Abbanshi shikuma ya fadawa kawu da wani abokinshi a ranan sunday sukaje Kano inda baba mai kano ya musu tarba mai kyau cike da karramawa, bayan sun tautauna baba mai kano ya yanke musu sadaki dubu dari nan take suka bayar tareda sa rana wata daya. Sanda lbr ya kai kunnensu ba karamin dadi sukaji anan Mom ta bari aka kawo mata mai gyaran amarya daga mai guduri, yayyanta duk sukace ana saura sati zasubar koma me sukeyi suzo.1

Yau ya kasance Wednesday kuma yau suke sa ran daddy ze dawo saboda haka Mom tinda ta tashi yau batayi baccin safe ba, tsaye tayi tana ba masu aikinta command, goge chan, share chan, dora wannan, haka taita kai kawo inda KAUSAR ke dakinta kwance da laptop a gabanta tana duba wasu interior designs, wayanta ne yayi ringing ta duba taga secretary dinta ce saboda haka ta dauka, “God mrnn Ma”, ” Mrnn Aliya, hw ar u”, “I fyn ma”, ” gud tell me wats popping “, ” Ma it’s almost to 11 now and u ar yet to come, kuma yau zamu hadu da sabon client dinnan”, ai da sauri ta mike dan ita tama manta, batace  komai ba ta kashe wayan ta fada bathroom.
Fitowa tayi jikinta sanye da brown kimono me ratsin black, half cover shoe da bag ma black se white veil, sosai tayi kyau kaman ba ita ba. Fitowa tayi taga abinda Mom dinta keyi tin daga sama tace “Mom wannan aiki aise ki gaji”, ta fada tana saukowa, kallonta Mom tayi tayi murmushi tace ” ya na iya, yau Dad dinku ze dawo”, kada kai kawai tayi kafin tace “ni zan wuce, akwai wani client danakeson gani yau, amma bazan dade ba”, “se kin dawo Allah ya bada sa’a”, cewar Mom a yayinda take taba center table taji koda dust. Seda tasa shades dinta sannan ta shiga mota taja in high speed kowani mutum yazo wucewa ya gan yadda takejan motan se yayi magana, haka masu motan suma se sunyi magana amma ita batamasan sunayi ba, gudu kawai takeyi saboda tayi latti.
Parking tayi ta fito tinda daga waje secretary dinta tace mata ya dade da zuwa yana ciki, kada kai tayi ta shiga office dinta kai tsaye mutumin ya jiyo yana binta da kallo harta zauna tace ” sannu”, se a lokacin ya kau da idanunshi yace “yauwa, amma baki iya sallama bane”, wani kallon ta mishi kafin tayi murmushin gefen baki tace ” nida office dina kuma senayi sallama”, “kwarai kuwa, yanada kyau ko ina zaki shiga kiyi sallama sabo…..”, ganin he’s trying to lecture her ta katseshi da cewa ” back to business pls”, shiru yayi chan kuma ya girgiza kai yace “kaman yadda kikasani sunana Auwal Muhammad, mahaifina ya bani position din CEO na company dinshi amma danaje naga office dina se naga be min ba, it doesn’t suite my taste, bayi kyaun da za’ace na CEO bane saboda haka na zo wurinki danki canza min tsarin office din”, kada kai tayi kafin tace ” ok na fahimta, amma de zaka canza kayan cikin office dinne ko yaya”, “yes change everything entirely”, ya fada yana kafeta da ido.


Laptop dinta ta janyo ta kunna sannan ta shiga wani folder inda pictures ne na office kala kala sannan ta fara nunamai saboda ya zaba wanda yakeso amma banda kallonta ba abinda yakeyi, murmushi tayi tace ” u can stop starring now”, ta fada ba tareda kalleshi ba, “and why?”, ya tambaya”, sosai ya kullar da ita saboda haka kai tsaye tace ” saboda matar aure ce”, wani wawan dariya ya kece dashi yace “kin ban dariya, kece zakiyi aure amma duniya basu sani ba, ai ke u ar nt living a private life saboda babanki senator ne, so kome kikeyi media na sane dake, in takaice miki lbr sunanki KAUSAR ABUBAKAR ALIYU JAN WUYA, shekararki ashirin da biyu a duniya, kinada sauriya mai sunanshi HYDAR ALI MAHMOUD MAI TURARE, aurenku nan da wata daya, fiancée dinki soldier ne ko nayi karya”, shiru tayi kafin daga bisani tace ” duk a ina kasan wannan?”, murmushi yayi yace “a media off course, ai ku ‘ya’yan manyan nan komai kukeyi se an rubuta, da ace en paparazzi zasu daman rubuta lokacin da kuke fitsari a rana da sun rubuta, ni ina kallonki badan kimin ba sedan kawai ina mamakin yadda Allah ke lamarishi da bayinshi”, shiru tayi bata tankashi taji yace ” na zaba wannan”, yana nuna mata wani photo”, wani album ta dauko ta bude wani page ya ajiye gabanshi, design din sak ya gani a kasa kuma ansa price, murmushi yayi da yaga 5mila a zuciyarshi yace “so cheap”, amma a fili kuwa yacewa yayi ” kai amma yayi tsada, karfina be kai nan ba”, wani murmushin gefen baki tayi tace “koh?”, yace ” kwarai”, tace “toh ka zabi daidai kai, ko kuma ka hakura da wanda mahaifinka ya baka”, da sauri yace ” a’a wannan nakeso, zan tura miki 2.5mila kafin ki gama na samu balance din”, shiru tayi tana karantar shi kafin daga baya tace “naji, amma banson disappointment, sedai decoration ze dau lokacin, let’s say a week or so”, ” ba damuwa ni dai fatana aiki yayi kyau, na miki alkawarin in aiki yayi kyau zan baki mamaki”, kada mishi kai kawai tayi ya tashi ya fita ta bishi da kallo a zuciyarta tace “not bad”.2

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


HYDAR ne zaune a office dinshi aiki ya taru ya mishi yawa se neman wani file yakeyi amma be gani, fitowa yayi ya kama tafiya cikin zafin nama kowa ya ganshi seya tsara mishi amma shi batasu yake ba, wani daki ya shiga inda files na ajiye bila addadin ya kalli daya daga cikin sojojin da ke wurin yace ” inaso ku dubomin file din wannan complaint dinnan na bomb dinda ya tashi a maidugiri last Friday”, gabadayansu shiru sukayi suna zaro mishi ido ya daka musu tsawa yace “where is the damn file”, cikin rawar baki daya daga cikinsu yace ” sir file din na hannun colonel Idris”, wani iska ya furzar daga bakinshi wanda besan lokacin da ya furzar dashi ba, yasa hannunshi cikin suman kanshi yana ya mutsawa saboda yasan shikenan yanzu zasu rufe case din bayan ga bayin Allah chan suna mutuwa wannan wata irin kasa ce ya tambayi kanshi, dagowa yayi ya kallesu yace “be ready to take off ur uniforma if I didn’t get the f*cking file back. Daga haka ya fita be zame ko ina ba se office din Colonel.

Colonel na ganin shi ya cire medicated glass dinda ke idonshi yace ” our incorruptible general HYDAR”, ya fada yana wani shu’umin murmushi “ya akayi karaso mana”, ya kuma cewa yana kallon HYDAR dake wuci kaman wani mayuwancin zaki, idon nan nashi yayi ja ran soja ya baci, karasawa yayi ya tsarawa colonel sannan ya kara da cewa ” sir nazo karban file din da aka kawo petition daga Maiduguri akan bomb dinda ya tashi ran Friday”, shiru colonel yayi kaman me tunani sannan yace “sorry but a can’t remember having dat file with me, bakai aka mikawa case din ba”, cike da takaici yace ” yes ni aka mikawa amma presently file din na hannunka, I need to check out some strategy kafin na hada kan soldiers dina mutafi dan I can’t risk their lives saboda haka I want it back” wani bazawarin dariya colonel yayi yace “well as u can see file baya hannuna, kuma kasan u have only 24hours to take off”, wani iskan ya sake furzarwa ba tareda yace komai ba ya fita.
✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


Yau kwana uku kenan da rasuwan Malam Tanimu, BINTOTO ta rame ta kara kanjamewa saboda wahala, dan yanzu abinda takeyi yafi nada. Kaman kullum yauma tsugunne take gaban Zinaru dakecin abinci tace ” dan Allah Goggo ki taimakamin kar yunwa ta kasheni, yau kwana biyu kenan ba abinda ya shiga bakina banda ruwa”, ta fada tana hawaye maganan ma da kyar takeyi, wani wawan kallo Zinaru ta bita dashi tace “da ubanki ya mutu meya bari banda tsiya, kinga abincin nan da nakeci kwalelenki dan kuwa bada kudin ubanki na dafashi ba, shegiya mayya”, wasu sabbabin hawayen ne suka zubawa BINTOTO ta tashi ta koma gefe ta hada kai da gwiwa tana tunanin makomar rayuwarta. Zinaru da gangan taje ajiye kwanon shinkafar da taci wurin wanke wanke bayan ta rage kadan sannan ta wanke hannunta ta shiga daki ta tsaya ta wurin window tana jira taga me BINTOTO zatayi.

Ai kuwa tana shiga BINTOTO ta tashi ta karasa gaban kwanon taga shinkafa da be wuce loma daya ba amma haka ta dauka ta cinye sannan ta shide kwanon tana hawaye dan kaman ma kara mata yunwa abincin yayi, tana kokarin mikewa Zinaru ta fito da bulalanta a hannu tace ” ke ‘yar matsiyata zonan, a kanki na ajiye abincin dazaki dauka kici wato kema kin koyi halin sata ko?”, BINTOTO data gama tsurewa ba abinda takeyi banda girgiza kai hawaye na ambaliya a fuskarta ta hade hannunta wuri daya alaman roko tayi hakuri amma Zinaru ko kallon BINTOTO dake tsaye kaman zata fadi batayi ba. Taku daya tayi da karasa gaban BINTOTO ta tsula mata bulala wanda yasata dauke numfashi na wucin gadi saboda azaba, seda Zinaru ta kara mata sannan ta dawo daidai ta tsala ihu tana neman hanyar gudu amma ina ba dama, zagaye suka kamayi makota nata jimamin halin da BINTOTO ke ciki amma ba damar zuwa cetonta, BINTOTO tin tana ihu har tayi shiru tana shesheka kafin ta zube kasa warwas kaman wacce ba rai a jikinta, riganta duk ta yage saboda bulala, jikinta yayi jina jina. Wurgar da bulalan Zinaru tayi tace “shegiya ance miki zan kula dake ne? abinda ba dagin iya bare na uba, kodan ina gidan ubanki kike gani kaman zan ciyar dake?, banza mayya kawai, shegiya me kamada aljanai, Allah yasa ki sheka barza’u in huta da jarabarki”, da haka ta shiga daki abinta ta kwanta ko minti biyar ba’ayi ba bacci ya dauketa se munshari takeyi kaman wata giwa ta bar baiwar Allah a waje kwance rai a hannun Allah ga duhun dare, ga sauro ga sanyi (oh Allah).
Isowan Daddy kenan daga Cairo,  KAUSAR da kanta taje daukoshi duk da akwai drivers dinshi da masu tsaronshi, tana hangoshi ta karasa wurinshi da gudu ai tun kan kai ya ware mata hannu yana jira tilon ‘yarshi mace ta fada. Fadawa jikinshi tayi tace “I miss a lot Daddy”, ” I miss u more my princess, ya naga kaman kin kara kyau, meye sirrin fadamin”, yayi maganan cikin sigar zolaya, murmushi tayi tasaka hannunta cikin nashi tace “bakomai dad”, da haka suka fito harabar airport din inda suna fitowa flash din camera ne ya fara musu sallama en paparazzi sai daukan hoto akeyi dama sunsan se anyi haka, da kyar ya kusa kai tareda taimakon securities dinshi suka samu suka shiga mota bodyguards dinshi suka mara musu baya, ai kan sukai gida pictures dinsu ya gama yawo, Senate President Jan wuya is back from his trip to Cairo. Suna zuwa gida Mom taje ta rungume mijinta harda exchanging peck a gaban KAUSAR, ita dai murmushi tayi tana imaging ita da HYDAR dinta a wannan yanayin.

+

A ranan cikin farin ciki en gidan suka wuni kowa kaga fuskanshi kasan yana cikin farin ciki, da yamma HYDAR yazo yayiwa Dad ya hanya sosai suka gaisa har yake cewa zuwa gobe ba mamaki su hadu da Mahaifinshi a house of assembly, bayan ya fito ya dauki waya ya kira KAUSAR yace ” Hello gimbiya”, murmushi tayi tace “ni ina fushi dakai, yau tinda se yanzu ka kirani, kuma inna kira baka daukan wayan ba”, murmushi yayi me sauti har ta jishi sannan yace ” yi hakuri swthrt wlh yau kaina ne yayi zafi, amma yanzu haka ma ina cikin gidanku ki dan leko”, ya fada a hankali, murmushi tayi tace “gani zuwa”, wani gown ne a jikinta me spaghetti hands bata damu da tasa hijab ba ta dauko hula me turban tasa ta fita.

Tin daga nisa ya hango ta, take ranshi ya sosu yaji wani kishinta ya tashi ganin ga guards nan ta ko ina se kaikawo sukeyi cikin gidan ita kuma ta fito ba lillibe hannunta da shape nata gabadaya a waje, isakan da ta hura mishi ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya fada, ” welcome one and only”, be amsa gaisuwan da takemishi ba yace “bakida hijab ne zaki fito haka?”, kallon jikinta tayi tace ” me kayana yayi da har zansa hijab”, dan Allah harga Allah bataga aibu a abinda tasaba, “ke bakida duk suran jikinki a waje ba?”, murmushi tayi tace ” forget dan Allah, cikin gida fa nake, kar na sha iska?”, rai bace yace “don’t ask me silly question, ke har wani iska kikeso banda wanda kikesha kullum, ai bance karkisa rigan ba amma in zakisa kisa a cikin gida ba a compound inda kartin maza zasu kalleki ba”, kallon shi takeyi tana karantar yanayinshi sarai tasan ranshi ya baci amma ita ko a gida ba’a tukura mata, tasa bum shots ma ta fito ba’ace komai ba se yanzu datasa gown wanda har jankasa yakeyi. Sauke idonta tayi daga kallonshi tace ” ba’a takuramin a kan abinda nake ra’ayin sawa ko a gida, kuma kaima kasan da haka, saboda  haka plss ka daina maganan nan kar rayuka su baci yanzu, kazo ne dan mu gaisa ba dan mu samu sabani ba”, wani kululun bakin ciki ne ya turnukeshi ya kalleta yace “fine do wat u feel like doing tinda ba’a isa a fada miki kiji ba, ke gaki ‘yar hutu” yana fadan haka ya wuce inda motanshi yake ya shiga ya kama gabanshi ranshi bace, ita kuwa ko a jikinta dan tasan HYDAR baya fushi me tsayi da ita saboda haka ta kada kafadunta ta shige gida.


Wai shin wacece wannan KAUSAR din da har  take ikirarin ba’a takura mata akan abinda tayi niyya and waye HYDAR.


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴ 

BINTOTO tayi kusan awa daya wurin kafin Allah ya saukar da ruwan sama wanda seda ruwan ya mata duka sosai sannan ta farfado da kyar ta iya mikewa ta shiga inda ruwa baze tabata ba ta rakube tana kuka ciki, ta rasa ina zatasa kanta taji dadi, “wajen wa zataje neman taimako, waye ze dauketa daga wannan kangin wahalan datake ciki?”, ta tambayi kanta amma sedai ba amsa, ” ina ma Umma da Abba basu mutu ba, ina ma banzo duniya ba, ina ma Abba be aure Goggo ba, ina ma Inna na raye, ina ma mala’ikan mutuwa zezomin yanzu”, ina ma, ina ma, haka ta dinga magana da kanta ita kadai cikin ranta, a nan wurin baccin wahala ya dauke ta amma da asuba ta tashi saboda yadda sanyin safiyan ya addabeta, tashi tayi ta mike da kyar ta fita daga gidan dan yau ko sallah ma batajin zata iya yi, tafiya takeyi tana hada hanya gari yayi shiru dan asuba ne ba’ama fara fitowan zuwa masallaci ba, gidan malam Mamman ta nufa abokin Malam Tanimu wanda gida uku ne tsakaninsu, kofan ta fara bugawa amma ba karfi jikinta bare aji bugun kofan da takeyi, gajiya tayi ta zube wurin tana maida numfashi. Ba’a wani dadeba Malam Mamman da babban danshi wanda yazo hutu dan karatu yakeyi a birni suka fito zasu masallaci suka tarar da BINTOTO a wurin, da sauri Malam Mamman ya tsugunna yace “wannan kaman BINTOTO”, ” Abba ka santa ne”, saurayin ya tambaya yana kallonshi Abbanshi dake kokarin daga BINTOTO daga kasa, “nasanta Umar ‘er gidan marigayi ce”, Umar dinne ya taimaka mishi suka shiga da ita ciki, ya kira matanshi yace ” Ku dubata bari muyi sallah mu dawo”, da “toh”, suka bishi su kuma suka tsaya suna kallon BINTOTO.1

Koda suka dawo daga masallaci har matanshi sun mata wanka sun sa mata rigan karamar ‘ersu wacce a kalla BINTOTO zata iya bata shekara uku amma kayanta ne daidai BINTOTO, zama Malam Mamman yayi yace ” taci abinci”, daya daga cikin matan tace “Malam taya zataci abincin a wannan halin, batamasan inda kanta yake ba”, Malam Mamman maida kallonshi yayi kan BINTOTO yaga yadda idonta ke kafewa yake budewa ya girgiza kai yace ” tabbas lokaci yayi daya kamata a takawa Zinaru birki, bazeyu mu zuba ido tana muzgunawa marainiyar Allah ba, kalleta fa sekace kasheta zatayi”, dayar matan dake tsaye tun dazu tace “Malam danake mata wanka jikinta duk shatin bulala”, girgiza kai yayi yace dole naje wurin maigari yau, kai kuma Umar ga dubu biyar nan, in gari yadada wayewa kai da mahaifiyarta ku kaita asibitin cikin gari a duba lfynta, in kudin be kaiba kubari na sani”, shima da ” toh”, yabi mahaifinshi yanawa BINTOTO kallon tausayi, tashi Malam Mamman yayi be zame ko inaba se gidan maigari yace ace yanason magana dashi.
Gari na wayewa Umar ya goya BINTOTO tareda mahaifiyarshi, kishiyarta ma ta rakasu inda zasu samu mota se jimamin abinda ya faru sukeyi, seda ta tabbata motansu ya tashi sannan ta koma gida dan ta kula da yaran. Sun samu sunje asibitin inda da kyar suka samu ganin likita saboda asibitin gwamnati ne, sosai ya dubata tareda mata end gwaje gwaje kafin ya shaida musu cewar yunwa yasa ulcer ya kamata sannan kuma ita din bamai issashiyar lfy bace dan kuwa sickler ce”, sosai hankalin Umar ya tashi danshi yasan me ake nufi da sickler kuma a iya saninshi basu cika yin rayuwa mai tsayi ba, rayuwarsu raggage ne, da kyar suke tsallake stage din da insun kai za’a iya samun hope (falling under dis category sucks😥).
Doctor ne ya kwantar musu da hankali tareda musu alkawarin zata samu sauki indai zasu dinga kula da ita sosai sannan ya rubuta musu magunguna ya kuma bata gado yasa mata drip, a takaice dai seda Umar ya cika kudi dan kudin da Malam ya basu bekai suba,  sanda yama mahaifiyarshi bayani har hawaye tayi saboda tausayin BINTOTO.
WACECE KAUSAR

Alhaji Abubakar da ne ga Alhaji Aliyu wanda ya kasance attajirin mai kudi wanda yayi fice ta fannin gidan mai da kayan masarufi, Abubukar ya kasance shi kadaine da a wurin iyayenshi saboda haka mahaifinshi da mahaifiyarshi wato Hajiya Kubura suka dau son duniya suka dora mai, besan wahalan nema ba sedai a samo a bashi har Allah ya dau ran tsohonshi wato Alhaji Aliyu, sanda Alhaji Aliyu ya rasu sosai suka shiga ibtila’i sakamakon danne musu kudi da baki tayi da sunan Alhaji Aliyu yaci bashin kusan sama da naira miliyan hamsin wanda ba haka bane, abokin aikinshi ne yaci bashin kudin da sunanshi. A wannan lokacin ne Alhaji Abubukar ya fara neman na kanshi tun yana siyan kayan masarufi yana siyarwa saboda hatta company dinsu yana hannun banki, cikin ikon Allah business dinda ya fara ya soma bunkasa cikin lokacin kankani ya fara samu har yana zuwa banki biyansu kadan kadan duk da yasan se an dau shekaru kafin ya samu ya gama biyansu.


Ana cikin haka ya hadu da Halima (Mom) a wani tafiya da yayi zuwa Mali da yake ita er Mali ce, anan suka kulla soyayya har Allah ya daurashi bisa kan iyayenta suka yarda suka bashi aurenta tareda mishi gargadin basaso nan gaba suga kalar wahala tattare da ‘yar su dan bata saba dashi ba, haka ya yarda ya samu wa’anda suka tsaya mishi a familyn shi akayi abinda za’ayi aka bashi matarshi. Bayan ya dawo suna zaman lfy da matar shi da Hajiya a gidan mahaifinshi kwatsam sega lawyers da en banki sunzo nemanshi, sosai ya tsorota dan a zatonshi wani abun ne ya sake faruwa se daga baya ya gane cewar ashe sun gano cewar ba Alhaji Aliyu ne yaci bashin ba abokinshi ne saboda lawyer din Alhaji Aliyu be zauna ba seda ya binciko komai. Sunyi murna sosai a lokacin saboda yanda komai da suke tunanin sun rasa ya dawo musu lokaci daya.


A kwana a tashi asarar mai rai bayan wata shida da aure Halima ta samu ciki inda cikin ikon Allah ta santalo danta kyakyawa namiji suka sa mishi Aliyu sunan margiyayi, bayan shekara uku kuma suka sake samun wani dan suka mishi Ahmad, bayan Ahmad basu sake haihuwa ba seda sukayi shekara takwas sannan Allah ya basu KAUSAR wacce daga ita basu sake haihuwa ba. Alhaji Abubukar bayason yaranshi suyi irin rayuwar da yayi na rashin sannan zafin kudi saboda haka ya tsaya tsayin daka na ganin sunyi karatu mai zurfi sun samu aiki a inda Aliyu ya zama pilot yanada mata Raheena da ‘yarsu daya Ibtihal, itama matarshi zaman hutu takeyi a gidan ta kaman yadda yaga mahaifiyarshi bata aikin baki balle fari shima be takurawa matarshi ba, Ahmad kuma he’s the manager of his father’s company wanda suke dealing da kayan abinci wato HABU & SONS FOOD LMTD inda mahaifinsu ya bar mishi kujeran shikuma ya koma siyasa.

KAUSAR tin tana yarinyarta takeda son karatu ganin yayyenta ma ba banza ba wurin zuwa school, sunfi bawa boko himma akan arabi danma Hajiya na tsawata musu wani lokacin, wani mummunar akida mahaifinsu ya cusa musu na son boko da rayuwar hutu, in yana gida ko spoon baki isa kice yaranshi su tashi su dauko ba, koda yaushe suna zaune komai sedai a musu daga uwar har yaran sedai in Hajiya ce zata tsawata musu. KAUSAR banda karatunta ba abinda tasa gaba, a aikin gida kuwa hatta wanke wanke bata iyashi ba wannan itace rayuwar da iyayenta suka daurata akai.Sanda KAUSAR ke 200level a school tana karantar business admin ta hadu da HYDAR a wani zuwa da yayi school din. A ranan wata litinin Khalil ya tasa HYDAR gaba akan lallai lallai seya rakashi Nile university ze kai sako, haka ya shirya suka tafi zasu shiga school din wata mota tazo tasha gabansu tareda badesu da kura har suka isa wurin parking tare Khalil ya fita yana masifa shidai HYDAR yana zaune cikin mota har ta fito daga nata motar ta tsaya tanajin me Khalil ke cewa ba tare da ta tanka ba har ya gama banbaminshi HYDAR na mota yana kallonsu. Seda Khalil ya wuce sannan HYDAR ya fito sanye yake da jeans trouser da vest na sojoji yace “baiwar Allah kiyi hakuri in abokina ya bata miki amma sedai kema bakida gaskiya dan yanzu da kin bigemu kinga da kin ja mana asara”, shiru tayi tana kallon kwayar idonshi tareda mamakin yadda akayi lokaci daya ya shiga ranta, murmushi tayi bayan ta kare mishi kallo tace ” ba komai, next time zan kiyaye amma kuma fa sorry to say kafi wannan masifaffan abokin naka hankali”, dariya HYDAR yayi yace “yajiki ba ruwana”, itama dariya tayi tareda mishi sallama zata wuce yace “toh ai bansan sunan me wannan kyakyawan fuskan ba, saboda nan gaba koda an hadu”, murmushi tayi lokaci daya taji ya kwanta mata saboda yadda yake da nutsuwa maganan shi ma a hankali kaman bayason yi, seda ta matsa kusa dashi sannan tace ” I’m KAUSAR by name and you?”, yace “HYDAR” ta kada kai tace “it’s nice meeting you”, shafa sajenshi yayi yace ” me too, in bazaki damu ba zanso ki bani numbernki”, ita ba gwanar bada number bace amma yau dai taga wanda ba zata iya hanashi numberta ba saboda haka ta mika hannu ya mika mata waya tasa mishi number sannan sukayi sallama.
STORY CONTINUES BELOW

Tin daga wannan lokacin shakuwa me karfi ya shiga tsakanin KAUSAR da HYDAR har suka fara soyyaya a gidansu ba wanda besan HYDAR ba shima a nashi bangaren haka, in tana gida ko cikin kawayenta batada magana sena HYDAR, yaso ya turo magabatanshi amma ta tsayar dashi saboda karatunta haka ya hakura harta gama, a lokacin da ta gama yaso turowa amma ta dakatar saboda tanaso ta shiga decoration school. Haka yanaji yana gani ya kara mata lokaci a daidai wannan lokacin ne aka turashi Enugu mission ita kuma taje Lagos ta shiga MAVEN SCHOOL OF INTERIOR DECORATION & DESIGN dake cikin Ikeja, wata shida tayi ta gama abinda zatayi ta dawo Abuja inda ta bude nata office din kuma cikin kankanin lokaci tayi fice tayi suna. Wannan shine takaitattacen tarihin KAUSAR.


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


Suna nan zaune a hospital har aka gama sa mata ruwa leda uku sannan aka basu sallama saboda suncewa doctor ba cikin gari suke ba daga kauye suke, napep suka samu ya kaisu har cikin kauyen kofar gidan Mallam Mamman sannan suka biyashi ya wuce. Dakin mahaifiyar Umar suka kwantar da ita dan har lokacin bacci takeyi, alluran basu saketa ba. Koda mallam mamman ya dawo sosai ya tausayawa BINTOTO jin sickler ce dukda seda Umar ya mishi bayani sannan ya gane. Zaune suke gabadayansu sunacin tuwon dare banda BINTOTO dake daki idonta biyu amma duk jikinta yayi weak saboda haka ta saura kwance. Sungama cin abinci suka wanke hannu sannan suka dawo suka zazzauna kishiyar mahaifiyar Umar tace “Malam ya kukayi da mai gari akan zancen yarinyar nan?”, gyara zama yayi sannan yace ” dukda tayi kankanta amma aurar da ita zamuyi, hakan ne kawai hanyar da zamu kubitar  da ita daga kuncin da take ciki”.

Kada kai matan sukayi sannan sukace “Allah yasa hakan shi yafi alkahiri”, duk suka amsa da ” Ameen”, kafin Umar yace “Amma Abba matar babanta fa?”, mallam mamman yayi murmushin takaici yace ” hauka tazo ta mana a gaban mai gari”, nan ya fara basu lbrn abinda ya faru a gidan mai gari.

FLASHBACK

Sanda Zinaru ta tashi daga bacci ta fito taga BINTOTO batayi aikin gidan ko daya ba ranta baci yayi, cike da masifa da bala’i ta fara neman BINTOTO amma bata cikin gidan saboda haka ta sabi mayafi ta fara shiga makota tana cewa a fito mata da ‘yarta, duk inda ta shiga sedai suce “ai batazo ba yarinyar da bata shiga makota”, haka ta dinga bi daga karshe ta yanke hukuncin zuwa gidan Malam Mamman amma sedai tana shakkarshi, bataso suna hada hanya amma yanzu ya zama mata dole taje gidanshi dan tasan a nan ne kawai zataga BINTOTO, tafiya kadan ya kawota gidan dan dama ba nisa tayi sallama kamar mutuniyar arziki aka amsa mata daga ciki sannan ta shiga, kishiyar mahaifiyar Umar ta gani tana damawa yara koko tace ” ina kwana”, “lfy lau”, ta amsa ta a takaice Zinaru tace ” dan Allah BINTOTO bata shigo nan ba”, wani takaici ne ya tokare ta amma saboda bazata iya da masifan Zinaru ba tace “bata shigo ba”, da haka taja bakinta tayi shiru, Zinaru ganin ba alaman BINTOTO yasa ta ficewa ta koma gida tana tunanin in BINTOTO zata shiga.
Bata kai ga zama ba aka maka sallama da sauri ta leka dan a tunaninta anga BINTOTO ne amma sega dan aiken mai gari, ko gaisuwan arziki basuyi ba yace ” ana bukatar ki a gidan mai gari nan da minti goma”, yana fada ya juya yayi wucewarsa. A tunaninta BINTOTO na gidan mai gari saboda haka tayi zamanta har seda ta bata lokaci ita da aka bawa minti goma sannan ta fita, a gidan mai gari ta yada zango daga mai gari har manyan mutanen kauyen duk suna gaban gidan ta karasa ta zauna kan tabarma ba gaisuwa tace “wai ance inzo, inajin dai lfy koh”, shiru mai gari yayi yana kallon yanayin ta da rashin nutsuwar dake tattare da ita sannan daya daga cikinsu wani yace ” ba lfy ba, mun samu lbrn kina muzgunawa ‘yar gidan marigayi Tanimu saboda haka muka yanke hukuncin karbanta daga hannunki, zata dawo gidan mai gari da zama har lokacin da muka yanke mata na aurenta”, da sauri ta dago tace “aure kuma”, yace ” tabbas aure fa, aure zamu mata da dan gidan mai gari Kallamu dan mun samu lbrn yana sonta, kinga ita ta huta kema kin huta duk kowa ma ya huta”.

Wani irin zabura tayi ta mike tsaye tace “ai wlh baku isa ba, ni da yarinyata amma ace kune zaku yanke hukuncin aurenta, inaa baku isa ba, mahaifin BINTOTO mika min ita yayi hannu da hannu yace ya barmin halak malak saboda haka bakuda yancin yanke mata hukunci, sannan kai kuma…..”, ta juya wurin Malam Mamman tace ” nasan kai zakawo wannan gulma da tsegumin, sannan nasan BINTOTO na gidanka saboda haka awa ashirin da hudu na baka ka dawo min da ita in ba haka ba kuwa komai ya same kai da iyalinka kai kaso”, da haka ta juya se kuma ta dawo tace “maganan aure babu shi, dan wlh tlh blh lazi duk wanda ya tsayawa BINTOTO aka daura mata aure seya gwammace mutuwarshi da rayuwar shi”, yana fadan haka ta wuce gida fuuuuuu sukuma duk anma rasa mai bakin magana se daga baya mai gari yace ” barazana takeyi karku dau maganarta da muhimmanci, kai Malam Mamman da an dawo da ita daga asibiti ka kawota gidana sannan daurin aure juma’a mai zuwa ana kofan gida dan aure kam ba fashi”, da haka aka watse kowa na jimamin abinda ya faru.

END OF FLASHBACK

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like