MAIRO CHAPTER 1

Advertisement

MAIRO
CHAPTER 1AKWAI TYPING ERRORS AND OMISSIONS A CIKI SO DON’T MIND THE ERRORS JUST READ THE STORY

“Na rantse da Allah yau sai an biyani ni babu ruwana”
rik’e take da kunkuru tana marmaɗen ido da murguɗa baki jikinta sai rawa yake wai ita ga matsifaffeya.
yaron dake gabanta ya risina har k’asa yana bata hak’uri
“dan Allah Mairo ki yafe min wlh ba zan kara ba ni naga kinje wani gurin ne shiyasa na cika miki ban san ba kyaso ba”
sai a lokacin ta kalleshi cikin matsifa tace “saka nayi cewa nayi na cika min kai mai hegen salo yau ko saika busar dashi ko na maka hegen duka”

wata dattijuwa take wanki gefen kogin ta kalleta tace “ke Mairo wai miyasa baki jin magana ne yanzu miye laifin yaron nan dan ya cika miki tulu?”
harara ta watsa mata ta murguda mata baki “ke kuma tsohuwa ina ruwanki dake nake yi ne da zaki samun baki ko sashi nayi da zai cika min tulu wannan ai rainine”
“ke fa baki da kirki Mairo daga magan zaki wani taso min kamar wata warinki”
“mtsssss yau daman kin san ba warinki nake ba kika samin baki a magana dan neman tsokana”

daidai nan Almu ya iso da jakinsa da jalkunan ɗinba ruwa.
yana kallon Mairo yasan matsifa ce take ganin yadda take marmaɗen ido tana rawar jiki
murmushi kawai yayi ya gaida dattijuwar

“inna ina kwana?”

“lafiya kalau Almu an tashi lafiya?”

“Alhamdulillah inna”

kallon mairo yayi “ke lafiyarki kike wannan harare2?”

banza ta masa ta cigaba da karkada jiki.
inna ta taɓe baki

“ai haka take indai rashin kunya ne ta iya ga yar banzar matsifa”

juyowa mairo tayi kanta “wai ke ina ruwanki dani kinga ban hega saggarki ba ki fita tawa bana son shinshigi”

da marmaɗe2 ta ksrasa maganar tana murguda mata baki.
  mari Almu ya kai mata ya fizgota ya jefar 
“ke wai miyasa rashin kunya yayi miki yawa kamar inna zaki tsaya kina faɗawa irin wannan maganar sa’arki ce?”
wani ihu mairo ta saki ta shiga murk’ususu cikin kasa tana jan gashin kanta 
“wayyo na shiga uku ya kashe ni wayyo Allah ya kare ni wayyo gwaggo” 

tsoro Almu yaji ganin yadda take ihu duk’awa yayi ya rikota “tashi mu gani?”
wani mugun cizo ta kai masa a hannu saida ya saki kara ya saketa da sauri.
inna ta rike baki “oh ni hajjo wannan wace irin masifaffiyar yarinya ce haka?”
Almu dai shiru yayi yana murzar hannun dan ba karamin cizo tayi masa ba,
ya dade a haka kamin ya nufi kogin ya shiga cika jalkunansa.
       ihunta ta cigaba dayi tana murje2 daga Almu har inna babu wadda ya sake bi ta kanta.
Almu na daf da cika kayansa halilu ya iso gurin yana ganin mairo yayi saurin ta data “ke lafiya miya faru?”
langaɓe masa tayi ta cigaba da kukan
nan ya kalli inna da Almu ya shiga tambayar su ba’asi “wai miya sameta ne haka?”
inna tace “babu kawai rashin kunya tayi min Almu ya ɗan zungureta shikenan fa ta faɗi ta shiga koke2”
cikin kuka Mairo ta ɗago “wlh karya suke itace ta fasa kuka tace masa na zageta shi kuma ya ɗaga ni sama ya jefar na kare”
tana kaiwa nan ta saki wata kara kamar wadda aka sokawa wuka.
rik’e baki inna tayi jin irin karyar da Mairo ta zagga
Halilu ya kalli Almu “haba Almu ya zaka mata haka kamar wata warinka ko namiji”
Almu yayi murmushi “haba dai Halilu sai kace bakasan halin Mairo ba wlh karya take”
Halilu yace  “wai minene mafarin wannan masifa?
inna tace “ɗiban ruwa tazo fa saita eje tulun ta tafi yawonta shine haruna ya dauka ya cika mata shine data dawo tace sai ya biyata shine ya zubar da ruwan daya zuba kuma duk da haka tace wai saiya busar tulun yadda yake shine ya shiga bata hak’uri taki hak’ura wai ita saita dake sai natibmata magana shine fa ta shiga fada min magagganu har Almu saida tayi masa rashin kunyar”
Halilu yace “daman shine kawai take yiwa wannan kuka?”
“shine kawai babu wani abun da akayi mata”
cewar inna.
kai halilu ya kaɗa ya Nufi ecen dogon yaro ya k’allo ya juyo gurin mairo cikin zafin nama ya watsa mata ita,
mairo najin saukar bulala ta tashi da gudu ta nufi gida tana uhu. 

Story continues below


***   ***   *** 

da ihu ta isa gida tana murxa gurin da Halilu ya buga mata bulalar.
da sauri gwaggo ta tare ta “lafiya Mairo miya sameki?”
rumgumeta tayi “wayyo gwaggo zasu kasheni gwaggo basa sona sun min taro suna ta duka na”
gwaggo ta dagota “su waye Mairo faɗa min uban wa ya taba ki cikin garin nan?”
cikin kuka ta shiga yima gwaggo k’arya data saba “tsohuwar gidansu hajara ce tace wa Almu wai na zageta shine shi kuma ya daga ni sama ya jefar gwaggo ya k’arya ni na bani mutuwa zanyi”
da sauri gwaggo ta zaunar da ita ta shiga duba ta tana matsifa “wannan wace irin k ‘etace haka wlh duk suka karyaki sai munyi shari’ah dasu mugayen mutane azzalumai”
gwaggo na taɓa mata k’afa ta saki wani mahaukacin ihu “wayyo na shiga uku gwaggo nan gurin Halilu ya buga min ecce”
gwaggo tayo waje da ido “ecce kuma yaushe mi kika masa?”
“ban masa komai ba daga zuwansa suka fada masa k’arya shine ya dauko k’aton ecce ya buga min gwaggo basu sona na shiga uku”
tashi gwaggo tayi ta shiga ɗaki ta ɗauko mayafinta ta nufi kofa. 

   
        ”’
NOTE”’
*_Assalamu Alaikum ina bawa fans ɗina hak’uri bisa ga rashin ganin cigaban novel ɗina mai suna LAMARIN DUNIYA na k’are novel ɗin gaba ɗaya kamin na fara posting sai phone ɗina ya samu matsala kuma wadda nayi publishing a blog ɗina blog ɗin ya samu matsa. ta dalilin matsalar da phone ɗina ya samu amman ana kan gyara blog ɗin da zarar an kare zanyi muku C & P Insha Allah ko kuma na baku blog address ku karanta bayan haka dan Allah ina rokon duk mai novels ɗina ko wane iri ya turo min ta wannan number_* 

*_taku har kullum Khadeeja Candy_* 

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:37 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*2* 

gwaggo na k’ok’arin fita halilu na k’ok’arin  shigowa sukaci karo nan taci kwalarsa ta k’asara shigowa dashi tana masifa “ashe baka da hankali halilu dan kana magu zaka sa ecce ka bugawa Mairo bancin bugun da Almu yayi mata wai mi ta tare maka ne?”
kai ya girgiza “haba gwaggo wai miyasa duk tazo tayi miki k’arya saiki yarda ya za’aiyi na buga mata ecce fisabilillahi?”
“ai halinka na sani ba sonta kake ba zaka iya mata komai”
kallon mairo yayi da tayi shiru tana kallonsu kamar wata munafuka yace “ke dukanki nayi?”
kai ta daga ta turo baki tana matsar kwallah.
“eh gurin da Almu ya karyani ka buga min ecce”
gwaggo ta kara ciyo kwalarsa “mugu yanzu abunda kake ya kamata kenan a gaban idonka ka bari Almu yayi mata wannan illar wai miyasa baka son yarinyar nan ne halilu?”
“ohhh gwaggo haba haba wane irin illa Almu zaiyi mata rashin kunya fa tayiwa tsohuwar mutane shine ya dan zingureta fa”
gwaggo tace “tho ina ruwansa ya zingureta haihuwarta yayi kuma karya kake karyata yayi”
“haba gwaggo yarinyar da aka karya zata iya kawo kanta gida har ta iya faɗa miki an karya ta ai saidai a kawo miki ita”
saki kwalarsa gwaggo tayi ta nufi Mairo ta shiga duba k’afar.
aiko nan mairo ta k’ara marairaicewa tana “wayyoh k’afata” gwaggo ta duba bata ga alamun kariya a k’afarta ba ko alamun jimuwa babu barre karaya ta data gwaggo tayi tsaye “tashi kiyi tafiya na gani”
nan ta lak’e kafar “wayyo bazan iya takata ba gwaggo ta riga ta karye”
cikin dabara halilu ya cire takalminsa ya jefa mata iya karfinsa aiko da gudu ta faɗa ɗaki tana ihu.
matsowa yayi kusa da gwaggo ya ɗauki takamin yana faɗin “yanzu wadda aka karya zata iya wannan gudun?” 

shiru gwaggo tayi halilu yace “gwaggo wata rana saita saki kunya matukar duk abunda tazo ta faɗa miki kina yarda dashi tho ko zaki ɓata da kowa”
tsaki gwaggo taja “mtsss tho sai mi dan na ɓata da kowa akanta so kake na zuba ido ina kallon ana cin amanarta? ko kai ka taɓa ta saina taɓa ka bare wani can”
halilu bai kara cewa komai ba banda kan da ya girgiza ya fice ya barta tana masifarta.
saida Mairo taji fitarsa sannan ta fito tana kukan munafurci.
nan gwaggo tayi cikinta ta masifa “Allah mairo in kina zuwa kina min karya saina ɓata miki rai kuma na ɓata dake na fita harkarki”
    kwantowa tayi jikinta tana kukan shgwaɓa “tho ai ba karya nake ba Almu ya dakeni kuma Halilu ya zaggamin bulala”
tureta gwaggo tayi “amman ai cemin kikayi shiya buga miki ecce Almu kuma ya karyaki”
turo baki tayi 
“eh karya nake amman dai sun dakeni dukansu” 
“tho miyasa kika min karya kuma halilu yace ai tsohuwa kikayiwa rashin kunya”
“tho gwaggo ai itace ta samin baki a magana kuma tace min masifaffiya”
“amman ai kinsan na hanaki rashin kunya da karya ko ni daga yau babu ruwana dake”
kuka ta shiga rerawa “na daina gwaggo dan Allah kar kiyi fushi dani ba zan kara ba”
gwaggo bata so kuka mairo ko kaɗan janyota tayi jikinta “shi kenan bazanyi fushi dake ba amman ki daina kinji ba kyau kuma bana so”
“na daina daga yau ni ko kallon mutane bazan sakeyi ba”
gwaggo tayi dariya tace “rufe da ido zaki rika yawo kenan?”
“eh bazan sake kallon mutane ba bare suce nayi musu rashin kunya”
gwaggo ta shafa kanta “a’a kawai ki rika jin magana kibar rashin kunya yayi basai kim rufe idoba”
dariya mairo tayi “ai wasa nake miki gwaggo ya za’ayi na rufe ido kina son na fada rijiyane ko rame?”
dundu gwaggo ta kaimata a baya tana dariya “oh baki daina karyar ba kenan ko?”
“na daina Allah yanzu ko zanyi kaɗan zanyi”
gwaggo ta girgiza kai “a,a ki daina gaba ɗaya dai wai ina kika baro min tulu?”
“yana can kogi ni gaskiya gwaggo daga yau bazan kara zuwa ɗiban ruwa ba kullum ni nake zuwa kuma yar k’ank’anuwa dani shi halilu da yake k’ato bazai jeba sai ni shiyasa suke dukana sunga ni banida girma”
cike da shagwaɓa take maganar tana son yin kuka.
gwaggo ta shafa bayanta “shikenan bazaki sake zuwa ba halilu ne zai rik’a ɗebowa”
rumgumeta mairo tayi tana murna. 

Story continues below


”’        * * *”’ 

_2:13pm…_
gwaggo ta kare dahuwar giɗar ta ta zuba a gwango.
ta kwalawa Mairo kira da sauri ta fito tana ɗaurin ɗankwali rabin fuskarta duk fodace da bata shafu ba.
“na’am gwaggo kin kare?”
saida ta kare lisafin sannan ta ɗago ta kalleta tace “ta ɗari biu da arba’ince”
ɓata fuska mairo tayi “gaskiya gwaggo saidai ace ta ɗari biu da talatin dai dan gaskiya zan ɗauki ɗaya
gwaggo tace “ɗauki ko nawa kike so mairo waya isa ya hanaki?”
murmushi tayi ta duka ta ɗauki turen tana faɗin “yau duka zan siyar”
“tho Allah bada sa’ah amman dai hodarki bata shafu ba mairo”
turo baki tayi “nidai gwaggo bana son haka bani na shafa ba nidai haka zanje”
hannu gwaggo ta ɗaga mata “jeki jeki Allah bada sa’ah inda yanzu kuma ban faɗa miki ba ki hauni da masifa”
batace komai ba ta ɗora turen samsn kai ta nufi kofa.
gwaggo ido ta sakar mata a ranta tana _Allah ya shirya minke mairo ya tsare_ 

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*3* 

tafe Mairo take ɗauke da turenta na giɗa saman kai tana yan wakewakenta.
saida tayi nisa da tafiya sannan ta tuno da ɓanɓaramar da tayi jiya da sauri ta chaja hanya harda haɗawa da ɗan gudu tana waigen bayanta. 
saida taga ta shanye kwana sannan hankalinta ya kwanta tafiya ta rik’ayi a hankali tana kwanɗalar giɗar tana ci. 

kashe kunne tayi tayi gefen dashi tana son ta tabbatarda abunda kunnuwanta suke jiyo mata.
wak’ar india ce _ghajiniguzarish_ ke tashi cikin wani kiɗan taushi mai daɗi 
taɓe baki tayi “tho wai wayasa wannan kiɗan mai ɗaɗi cikin ɗaji kodai buki ake?” magana take tana kallon giɗar dake hannunta kamar wata taɓaɓɓiya.
kara kasa kunne tayi har ta gano gefen da sautin ke tashi dariya tayi “Allah buki ne ake bari na leka na gani amman ba zan daɗe ba sai na dawo”
haka ta kunna kai daga wani ɓangare na hanyar ta rika tafiya tana bin inda taji sautin wakar na tashi harta iso wani guri mai kamada lambu.
tsayawa tayi tana kallon etacen dake gurin “lahhh ashe ma haka gurin yake ni kan ban taba zuwa ba sai yau”
rabon ido ta shigayi saida ta kare kallon gurin sannan ta cigaba da tafiya.
a hankali ta fara hango wasu mutane sanye da wani yadi kala ɗaya.
da sauri ta laɓe gefen ecce tana lekensu , 

duk kansu sanye suke da yadi kala ɗaya mai ja da kore (red and green) kana gani kasan fadawa ne in banda mutun biu dake zaune saman wani k’aton carpet na alfarma ɗayan sanye yake da riga da waddo na turawa ɗayan kuma sanye yake da riga doguwa mai kamada jalabiyar fakistan _golden color_ Mai kyau sai kyali take. 
ya dora wani ɗan kyale saman wuyansa daya sauko har saman rigarsa.
gashin kansa ya kwanta lum kamar balarabe ya lankwashe kafafunsa wata rekoda na gefensa tana bada sauti shi kuma yana fuskarta ɗayan suna karta ko wannensu kuɗi yake azawa in aka cinye ya kara wasu. 

        sosai abunda suke ya burge Mairo aje turen giɗar tayi tayi zaune tana kallonsu tana dariya amman baki rufe dan kar suji 
ta daɗe a haka can dai taji bazata iya jurewa ba ta ɗauki turenta ta nufosu tana Murmushi.
“Assalamu alaikum”
sallama tayi musu tana k’ok’arin k’arisawa kusa dasu
   da sauri suka tare wadda ke zaune saman carpet ɗin wasu kuma suka nufota rik’e da takobi.
tsaye tayi tana kallonsu kamar hoto har suka karaso kusa da ita,
wani zarare cikinsu ya ɗaga takobi zai sara mata ɗayan yayi saurin  rikewa yana faɗin “Yarima yace a dakata”
da sauri ya janye takobin yayi baya.
ɗaya daga cikin fadawan ya fisgota da karfi har giɗar dake saman kanta ta watse ya nufi gurin yarima da ita.
yana tsaye yana kallonsu har suka iso da ita kallo ɗaya yayi mata ya gane bata cikin hayyacinta ganin yadda idonta suka k’afe kuma bata motsi.
    ido ya ɗan tsura mata sannan ya bada umarnin a zuba mata ruwa, 

da sauri bafaden ya dauki ruwan gora ya watsa mata
sai a lokacin ta matsa alamar ta dawo hayyacinta zubewa tayi zaune ta ɗaga kai tana kallonsu
suma ita suke kallo har yarima saida ta kare kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan ta saki wata irin kara iya karfinta mai shiga cikin kwakwalwa faɗuwa yarima yayi zaune ya dafe kunnunwansa shida wadda ke kusa dashi.
mari daya daga cikin fadawan ya watsa mata saida ta faɗi can gefe ta fashe da kuka
     ɗagowa yarima yayi ya watsa masa wata mugunyar harara da sauri bafaden ya faɗi kasa “Allah ya huci zuciyarka Yarima banyi dan ranka ya bace ba”
kawarda kai yayi yana sauraren sautin kukanta dake tashi tare da sautin waka 

Story continues below


ya daɗe a haka sannan ya ɗago cike da isa yace “kashe sautin nan” da sauri ya tashi ya nufi rikodar sa hannu ya kashe ya dawo ya risina gaban Yarima yana faɗin “Allah karawa Yarima martaba na kashe”
ba tare daya kalleshi ba yace
“jeki ka rarrasheta”
“am gama Yarima” tashi yayi da sauri ya nufi gurin Mairo. 

tirgewa Mairo ta karayi tana kuka tana kiran gwaggo tana murza hannayenta da kafafunta cikin kasa,
yayita rarrashinta har ya gaji tak’i tayi shiru sai ma karawa take.
ganin tak’iyin shiru yasa Yarima yayi mata alamar tazo da hannun tashi tayi ta share hawayenta ta nufoshi tana murmushi kamar ba ita ba.
kallonta yake harta karaso kusa dashi tun kamin yayi mata magana ta zauna saman carpet ɗin kusa dashi. 
       da sauri ɗaya daga cikin bafaden ya unkuro zai mata magana Yarima ya ɗaga masa hannu nan dukansu suka ja baya kowa ya shiga harkar gabansa.
kallonta yayi a natse cikin isa yace 

“ya sunanki?”
washe masa hauru tayi 
“Mairo” 

“Mairo?” 

“eh sunana Maryam amman Mairo ake cemin kaifa ya sunaka?” 

bai amsa mata ba ya jefa mata wata tambayar “an garin kike?”
“eh kai amman dai ɗan birni ne ko?”
nan ma wata tambayar ya sake jefa mata batare daya amsa mata ba
“mi kikazo yi nan?”
“talla nake zan wuce sai naji kiɗi na ɗauka bukine ake shine nace bari nazo na gani saina koma shine na ganku sai na taɓe”
shiru ya ɗanyi yaɓa kallonta sannan yace
“tho miyasa kika fito?”
abunda ke gabansa ta ɗauka ta nuna masa “wasan da kuoe da wannan abun ya burgeni shiyasa na fito”
bai sake ce mata komai ba ya janyo wayarsa ya shiga danne2 

sai a lokacin Mairo ta tuno da giɗarta
hannu ta ɗora saman kai ta fasa kuka 
“wayyo na shiga uku giɗata”
wani mugun tsaki wadda ke kusa da Yarinan yaja yana hararta.
a hankali Yarima ya ɗago kai ya kalleta 
“ina giɗar take?”
“nima ban saniba ɗazu dai kamin nayi bachi nasan tana saman kaina”
kallon rashin fahimta yayi mata “bachi kikayi?”
“eh ɗazu da suka nufoni da takobi ba sai naji bachi dana farka sai naganni nan kuma banga giɗar ba”
murmushi yayi dan ya gane suma take nufi da bachi.
ɗaya daga cikin fadawansa ya kira da sauri yazo gabansa ya risina cikin isa Yarima yace 
“ina giɗar Yarinyar nan?”
“gata can kusa da ecce ta zubar”
“jeki ka ɗauko mata”
tashi yayi da sauri ya nufi gurin yana faɗin “am gama Yarima”
kallon Yarima tayi tana dariya “na gode”
kai kawai ya ɗaga mata 
ta sakar masa murmushi tace
“kai baka fada min sunanka ba?”
yi yayi kamar bai jita ba ya mai yarda idonsa wani gefen
nan mairo ta ɓata fuska ta buro baki 
“ni inna tambayeka saika kyaleni nima amsar da na baka ban yafe ba lafira saika biyani”
cikiciki take maganar amman hakan bai hanashi ji ba
dariya ce tazo masa da sauri ya mayarda ita murmushi ya kara kawarda fuskarsa. 

*© Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*4* 

suna haka nafaden ya kawo mata turen giɗarta ya aje yana faɗin “gashi Yarima Allah ya kara maka daraja”
hannu ya ɗaga masa bafaɗen ya tashi.
kallonsa Mairo tayi “na gode”
banza yayi mata kamar bai jita ba sun daɗe a haka sannan ya juya ya kalleta yace “amsar da kika bani zan biyaki lahira?”
shru tayi tana kallonshi dan batayi zaton yaji ba can tace “eh mana tunda kai baka banu amsar tambaya ta ba”
shiru ya ɗanyi sannan yace “mi kike tambayeni?”
“ba nace ka faɗa min sunanka ba”
ya ɗan daɗe kamin ya bata amsa “sunana Yusuf Usaini”
dariya tayi harda sa hannun baki “lahhhh shiyasa kake da kyau daman masu suna Yusuf suna da kyau”
murmusawa ya ɗanyi ya ɗauki enabi yakai bakinshi.
yatsa ɗaya Mairo ta ɗaga masa “sauran tambaya ɗaya”  
kai ya ɗaga mata yana tsusar enabi kamar mai shan minti.
tsaki kawai na kusa dashi keja haushi ya isheshi
harara Mairo ta watsa masa ta kalli Yarima tace “amman dai ɗan bunni ne ko?”
murmushin gefe yayi ya ɗaga mata kai alamar ‘eh’ waje tayo da ido ta shiga shafa mishi riga “lahhh nikan daman nace dan bunni ne kai inason yan bunni kuma…”
“ke! mahaukaciya
bata karasa maganar ba na kusa dashi ya katsa mata tsawa saida ta razana
hmda sauri Yarima ya ɗaga mishi hannu yana kallon fuskar Mairo data k’ara rik’e masa riga tana kallon mutunen.
tsaki ya k’ara ja ya kalli Yarima “haba Yarima ya zaka…”
dakatar dashi Yarima yayi ba tare daya kalleshi ba yace “enough yahuza plz excuse us”
tashi yayi cike da bachin rai ya nufi wta bishiya ya zauna. 

Story continues below


sai lokacin Mairo ta turo baki tayi kwafa “tho an taɓa shi zo kayi abunda zakayi mai k’aton kai”
murmushi Yarima yayi yace “baki tsoron ya dakeki?”
kai ta kaɗa “ni wlh bana tsoron duka nifa ko sheɗan bai kaini masifa ba”
faɗaɗa murmushinsa yayi “gaskiya ne tho tashi zaune”
tashi tayi zaune ta ɗauki ruwan dake gansa “insha ruwan bunni?”
kai ya ɗaga mata yana kakkaɓe rigarsa data bata da k’asar hannunta.
saida ta shanye ruwan kofin gaba ɗaya sannan ta dire kofin tana dariya tana faɗin “wlh na sha ruwan bunni” 
“birni ake cewa ba bunni ba” 
ya gyara mata 
washe hakora tayi ta sake cewa “bunni”
murmushi yayi yace “waya shafa miki hoda?”
“nice na shafa ɗazu da zanje tallah”
ta karasa maganar tana gyaran ɗankwalinta. 

can ta ɗauki abunda ke gabanshi ta kalleshi tace “minene kuke da wannan abun ɗazu naga kuna wasa dashi?”
saida ya ɗan daɗe sannan yace “chachace muke zakiyi?”
da sauri ta matso kisa dashi tace “eh zanyi dan Allah”
“tho mi zaki aza?”
“kamar ya mi ake azawa”
“duk abun mutum kr so yana azawa bakiga yadda muke yi ba ni kuɗi nake azawa”
kalle2 ta shigayi tana neman abunda zata aza can ta kalli giɗar ta da sauri ta ɗauko k’waya ɗaya ta aza “to ga giɗa nan na aza”
shafa kansa yayi yayi murmushi ya sa hannunsa aljihu ya ciro dalar amerika ɗaya ya aza.
bata fuska Mairo tayi ta turo baki “ni dai bana son wannan takardar da kuke da ita saida ka aza kuɗi ko wani abu mai daɗi”
ta karasa maganar tana lek’en lemun dake bayansa.
ido ya tsura mata yana mamakin wayonta wato shi ya aza (ɗora) kudin data sani ko abu mai daɗi ita kuma ta aza kwaya ɗaya ta giɗa
cikiciki yayi murmushi yace “ai kuɗi ne ba takarda bace in kika chaja kuɗi da yawa za a baki”
lak’e kafaɗa tayi “ban yarda ba kuɗi bane ai da na sansu saidai ka aza kuɗin k’warai”
“ba nida wayan can kuɗin da kika sani wannan ne kawai in kuma ba zakiyi ba shi kenan”
shiru tayi tana son masa musu shima shirun yayi yana kallonta.
da taga babu sarki sai Allah yasa ta kalleshi tace “na amince”
kai ya kaɗa mata ya ɗan daɗe sannan ya gyara zamansa suka fara.
yin kawai suke tana masa shirme dan bata iyaba ci kusan 10 yayi mata sai haushi take ji dak’er ta samu tayi masa ci biu koshi danya nuna mata yadda zatayi ne.
aiko murna kamar ta kasheta sai dariya take kwasa harda hawaye.
shidai kallonta kawai yana shakkun hankalinta. 

da taga ya kara mata ci biu ta ɓata fuska tace 
“nidai na daina kuma saika bana giɗata”
shiru yayi yana kallonta kamar ba zaiyi magana ba saida yaga ta fara turo masa baki sannan yace
“ni kuma kuɗina dana baki fa?”
ɗaukar kuɗin tayi ta kikkiresu tayi musu guntu guntu baiyi unkurin hanata ba saida ta k’are  ta watsar  ta kalleshi tace “ni bana sonsu”
“mi yasa kikayi haka bakisan ba kyau yaga kuɗi ba?”
“ai ba kuɗi bane takardace nidai bani giɗata”
banza yayi mata ya ɗauke kansa saida yagata soma yi masa kuka sannan ya ɗauki giɗar ya mik’a mata ta da sauri ta karɓa tasa a ture ta tashi ta karkaɗe jikinta ta ɗora turan saman kai tayi masa murmushi ta kama hanya. 

har tayi nisa sai kuma tayi juyo ta nufoshi.
kaɗan kaɗan take tafiya tana turo baki har ta karaso kusa dashi ta sauke turen ta aje masa ta fashe da kuka.
kallon kawai yake tun tana kuka ba hawaye harta fara hawayen tana shureshuren kafafunta cikin k’asa sai kallonshi take,
shima ita yaƙke kallo yana tsusar baki kamar mai mai shan minti.
sunfi karfin minti 30 a haka ita taki tayi maganar sai kuka take shina yaki yayi mata magana fadawansa sai satar kallonsu suke yahuza ko yasa earphone a kunne dan kar haushi ya kasheshi. 

saida yaji ta kara buɗe baki tana kiran Gwaggo sannan ya matsa ya rik’o fuskarta ya sakar mata manya idonsa yace “mi kike yiwa kuka?”
cikin kukan tace “ba kaine ba ka jani da wasa har lokacin komawa gida yayi ban siyar da giɗa ba kuma Gwaggo bazata bani kuɗin sawa asusu ba”
murmushi yayi yasa wani bafaden sa ya kira masa yahuza.
haka ya iso gurin yana hararar Mairo.
Yarima ya kalleshi yace “kuɗin nageriya nake so”
hannu yasa aljihu ya ciro yan dubu dubu ya aje masa gabansa.
nan ne yaga kuɗin da Mairo ta yaga kallon Yarima yayi yace “wayayi wannan aikin?” 
kallon Mairo Yarima yayi bai bashi amsa ba hakan ya tabbatar masa da itace ‘uhmmm’ kawai yace ya watsa mata harara ya koma gurin zamansa. 

Story continues below


Yarima ya kalli Mairo yace “ɗauki ko nawa kike so”
da sauri tasa hannu ta dauki dubu uku tana dariya tace “na gode”
kai ya ɗaga mata “sun isheki?”
“eh na gode amman dan Allah ka bani wacan abun”
juyawa yayi yana kallon apple ɗin data nuna masa.
hannu yakai ya dauki ɗaya ya mika mata tana karɓa takai baki “lahhh daman haka goribar bunni take?”
murmushin gefe yayi ya girgiza mata kai “ba goriba bace apple ne”
“minene apple?”
“tuffa”
“minene tufa?”
shiru yayi dan yanzu kam baisan mi zai ce mata ba.
kamin yayi mata wata magana ta sake rokonsa
“dan Allah karamin ɗaya na kaiwa Gwaggo”
kara ɗauko ɗaya yayi ya mika mata dariya tayi ta kara rok’onsa “na gode amman ɗan Allah kara min ɗaya na kaiwa k’awata jummalo (MANIRA Lol.) da Halilu hannu yasa ya sake ɗaukowa ya mika mata.
bata bar gurin ba saida ta lisafa masa mutum takwas ya bata sannan ta tashi ta ɗora ture tana dariya tayi masa godiya tare da sallama ta nufi hanyar fita gurin tana waigensa tana ɗago masa hannu shidai kallo kawai ya bita dashi da murmushi harta fice. 

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*5* 

tana tafe saman hanya tana cin apple ɗin tana ɗariya.
koda ta iso gida taci kusan guda 4 ɗayan ma da giɗa ta haɗashi ta ci a kofar gida ta tsaya ta karasa na biyar ɗin sannan ta shiga tana watsar hak’ora 

Gwaggo na zaune k’ark’ashi ecce durumi taɓa jan carbi Mairo ta shigo
“fuwan (gafaran) kudai masu gida”
murmushi Gwaggo tayi jin yau abunda Mairo ta shigo dashi sabanin sallamar data saba.
kusa da ita Mairo ta zauna ta eje mata turen giɗar gabanta ta zuba mata ido.
Gwaggo saida ta kai karshen carbin ta shafa sannan ta kalli Mairo da fuskar damuwa tace “yanzu Mairo tun fitar da kikayi giɗa ɗaya kika siyar?”
ɗariya tayi ta ɗauki apple takai bakinta tace “ɗayar ma cinta nayi ba siyarwa ba”
kai Gwaggo ta girgiza “yayi miki kyau yanzu ai saiki ce na baki na sawa asusu ko na siyen wani abu”
fashewa tayi da dariya harda buga k’afa ta ɗauki apple ɗaya ta mikawa Gwaggo “Gwaggo karbi ki ci goribar bunni”
banza Gwaggo tayi mata ta kara hade fuska.
nan Mairo ta ciro  kuɗin dake lak’ame a k’ugunta ta ajewa Gwaggo
“nidai ga kuɗinki nan har ma sun ninka na giɗar”
buɗe baki Gwaggo tayi tayo waje da ido “Mairo ina kika samu wannan kuɗin mai yawa haka?”
“wani ɗan bunni ne ya bani harda wannan goribar shine ya bani kuma fa kuɗin da yawa ne nice na ɗebo kaɗan”
kallon tsoro Gwaggo tayi mata “ina kika haɗu dashi Mairo”
kwantayi tayi saman k’afafunta ta soma bata labari tun farkon fitarta.
       
Mairo na kaiwa karshe Gwaggo ta ɗora hanu bisa kai tana salati
“Hasbunallahu wa ni imal wakil innalillahi wa inna ilaihi raji’un Mairo mi ya kaike mi yasa bakisan ciyon kanki ba Mairo mun shiga uku da wannan ‘ya mai ya kaiki shiga can?” 

Tashi Mairo tayi zaune tana kallon Gwoggo gabanta soma faduwa.
“minene hala Gwaggo?”
“Mairo kinyi gamo miya kaiki Mairo”
baki Mairo ta saki “gamon me Gwaggo?”
kamin Gwaggo tayi magana sukaji sallamar Halilu da sauri Mairo ta shige cikin Gwaggo tana fad’in “Gwaggo karki fad’a masa”
koda ya karaso Mairo yake kallon ganin yadda ta ahige cikin Gwaggo dan yasan ruwa baya tsami banza gashi kuma Gwaggo na kuka.
“Lafiya Gwaggo miya faru kike kuka?”
da sauri Mairo tace “bata da lafiya ne shine take kuka”
risinawa yayi yana fad’in “Subhanallah mi yake damunki?”
Mairo tace “ciyon kai ne da ciki yake damunta ko Gwaggo?”
Kai Gwaggo ta girgiza Alamar ‘ah ah’ nan cikin Mairo ya duri ruwa hannu tasa ta toshe bakin Gwaggo tana fadin “dan Allah Gwaggo karki fada masa dan Allah”
tsawa Halilu ya katsa mata “jaye mata hannunki kona miki duka yanzu”
da sauri ta janye hannun idonta cike da hawaye.
hannu Gwaggo ya rike yana fadin “dan Allah Gwaggo ki fada min abunda ya faru”
cikin kuka ta soma fada masa abunda ya faru.
raku6ewa Mairo tayi gefe tana hawaye. 

Halilu ya juyo yana harararta yace “ashe haukarki Mairo har takai kiyi wannan kasadar?”
Gwaggo tace “ni tsoro ma nake ji in basu shige mata ba”
Halilu yace “wane irin shige mata Gwaggo aini bako ta aljanu nake ba ya mutanen nan nake yan yankan kai ko yan iska tunda zamani yanzu ya chaja babu babba babu yaro inma aljanune ai da sauki”
sai a lokacin wannan tunanin ya zowa Gwaggo kallon Halilu tayi tace “kana da gaskiya Halilu tunda kaga harda goribar burni ya bata wata kila akwai abu a ciki”
Kallon apple ɗin dake saman ture Halilu ya kalla “ragowarce nan?”
“eh itace taci guda shida tace koma minene ai ta cinye shikenan”
da kuka ta karasa maganar.
Ayatul-kursiyu Halilu ya karanta sannan ya ɗauki sauran biu da suka rage ya jefar bayan gida ya juyo gurin ecce durumi ya kallo ya hau Mairo da duka. 

Story continues below


ihu take tayi ko ina ana jinta babu wanda take kira sai Gwaggo tana faɗin kasheta zaiyi.
wannan karon kan Gwaggo ba tayi unkurin hanashi ba dan itama ta tsorata da lamarin Mairo
mak’ota ne suka shigo suka caceta koshi daker dan mugun rik’o Halilu yayi mata saida bulalar ta kwanta mata a jiki.
kowa tambayar yake dalilin dokan da akayi mata Halilu dai baice komai ba ya fice Gwaggo ce take cewa kuɗin tallah ta zubar kuma an sata aiki taki tayi
wasu dai basu yarda ba dan sunsan yadda Gwaggo take son Mairo duk abunda zaisa ayi mata wannan dukan ta kyale batayi magana ba ba karami bane.
haka suka fice kowa da abunda yake faɗa, 

                 ”’*   *   *”’
kuka kan Mairo ta shashi har ta gaji tun tana iya ɗaga murya har ta koma kiran baba.
tausayinta ne ya kama Gwaggo tana cikin ɗaki ta fito ta nufi ta tadata zaune tana kaɗe mata jiki “dan Allah Mairo ki rika jin magana ki gyara halinki ki daina wannan halin”
kai Mairo ta ɗaga mata tana shisshekar kuka kamar zuciyarta zata fito idonta sunyi mugun ja.
hannunta Gwaggo ta rik’a suka shiga banɗaki wannanka tayi mata sannan suka fito,
Mairo na shiga ɗaki ko kaya bata saba ta faɗa saman gado ta soma wahalallen bachi 

_8:15pm…_
gwaggo ta tashe ta taci abinci.
da ciyon kai ta tashi saboda kukan da tasha gashi kuma tayi bachi hannunta Gwaggo ta riko suka fito.
saida ta wanke mata ido sannan ta nufo tabarma.
Halilu dai kallonsu kawai yake yan mamakin irin son da Gwaggo take yiwa Mairo
saida ta zauna sannan ta zaunar da ita saman cinanunta (cinyoyi) ta shiga bata abincin da hannunta.
kai Halilu ya girgaza yace “Gwaggo kinga irin wannan sagartar da kike nuna mata shi yasa take kara lalacewa tana rashin jin maganar nan”
tsaki Gwaggo taja ta watsa masa harara sai yanzu take jin haushin dukan da yayima Mairo.
bai sake ce mata komai ba harta kare bata abinci ta bata ruwa kamar wata jaririya ta zaunar da ita saman  tabarma tana k’ok’arin tashi Mairo ta rik’o hannunta tace “Gwaggo kin daina sona ko?”
dawowa tayi ta zauna tana shafa fuskarta tace “ina sonki Mairo inban so kiba wazan so  halinki ne bana so koshi kuma na rashin jin nan da kikene ina sonki Mairo”
saida ta kalli Halilu dake kallonta sannan ta sake kallon Gwaggo tace “tho miyasa kika bari Halilu ya dakeni ɗazin?”
“saboda abunda kikayi baki kyauta ba kuma inason ya zamo miki dalilin da zaisa bazaki sake irin abunda kikayi ba ko makamancinshi”
jikinta ta shiga nunawa Gwaggo da ko ina kwancin bulalane “amman Gwaggo ai kwarai dakeni dubi jikina kuma inata kiranki ki ceceni kika kyaleni”
“na daina Mairo daga yau babu wadda zai sake dukanki bazan bari ba kiyi hak’uri kinji”
kai ta ɗaga mata tana hawaye.
Gwaggo tace “amman fa ki rika jin magana kinji?”
“na daina daga yau bazan sake ba Gwaggo har na mutu”
tashi Halilu yayi ya nufi kofa yana faɗin “indai dukane tho yanxu kika fara shanshi har sai ranar da kikayi hankali” kukan shagwaɓa ta shigayi “Gwaggo ce ya kyaleni bana sonsa”
“a a ki daina cewa baki son sa amman dai dukakan bazan bari ya sake miki shi ba”
kai Mairo ta ɗaga mata tana share hawaye. 

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*6* 

tun daga lokacin Gwaggo bata sake bari Mairo ta fita ba.
tallar da take ɗora mata ma bata sake ba kullum tana gida ko fita zatayi saida tare da Gwaggo, 

tun abun baya damun Mairo har ya fara damunta
tunani take ko ta saci hanya ta fita in kuma ta tuna da dukan da Halilu yayi mata saita tsorata duk da yake tasan Gwaggo tace mata ba zata sake bari ya dake taba.
tana zaune ta raffka uban tagumi tana tunanin karyar da zatayiwa Gwaggo da zata sa ta kyaleta ta barta fita,
can wata dabara tazo mata
tashi tayi ta koma kofar ɗakin gwaggo ta fasa kuka tana murgemurge
da sauri Gwaggo ta fito tana tamabayarta “lafiya Mairo mi nene?”
“ni gidansu Jummala nake son zuwa ba tada lafiya”
shiru Gwaggo tayi tana kallonta dan tasan rigimar ce ta tashi
“nidai babu ruwana kinsan halin Halilu in yanxu yazo bai ganki ba faɗa zaiyi”
“tho ai ba daɗewa zanyi ba kuma ai ba zaki faɗa masa ba”
Gwaggo bata sake cewa komai ba ta nufi tabarma ta zauna.
Mairo na ganin haka takara ɗaga murya tana ihu
cikin faɗa Gwaggo tace “tashi kije kuma duk kika daɗe babu ruwa daga can kuma karki biya ko ina”
tashi tayi tana dariya daman kukan kawai take ba hawaye.
“amman dai zan biya giɗan tsoho ko tunda kusa ne”
“nidai ba ruwana keda Halilu”
“eh na yarda”
da gudu ta fita gidan 

Story continues below


bata tsaya ko’ina ba sai gidansu jummala wuni sukayi suna shiririta basu can basu nan.
sai da bayan magariba sannan ko wannensu ya nufi gida
da fargaba ta shiga gidan tana lek’e2 
bakin k’ofar ɗakin Gwaggo ta hango Halilu zaune farin wata na haskashi.
faɗuwa gabanta yayi ɗan tasan ita yake jira zagi ta shiga zabga masa cikin ransa.
_hege mai katon kai mai kamada zabarmawa ni dai wlh ka takuramin Allah kasa ma ya mutu mai idon mage (mussa) mai kan ɓera_
ta daɗe gurin tsaye tana kallonsa wai ko zai tashi amman sai kara gyara zama yake. 
kamar ta fasa kuka ta shiga kwalawa Gwaggo kira _Gwaggo Gwaggo Gwaggo a dawo_ 
ɗagowa Halilu yayi yana kallon k’ofa yace “to shigo mana aike ake jira”
k’in shigowa tayi ta cigaba da kwalawa Gwaggo kira “Gwaggo ke ki taho mana gani”
ta daɗe tana kiranta sannan ta fito sanye da hijab da alama sallah ta k’are,
har kofar gida tazo ta kama hannunta suka shigo.
tashi Halilu yayi yana k’ok’arin rikota Gwaggo ta tare “kyaleta Halilu ni na aiketa”
“Gwaggo ki daina goya mata baya tana k’ara lalacewa”
“tho mi nayi da zakace na goya mata baya bana son raini fa Halilu”
“wane irin aikene zaki mata tun da maraice sai dare zata dawo”
Mairo ta turo baki tana watsa mata harara “ai bada maraice bane da rana ne”
buge mata baki Gwaggo tayi “ke yiwa mutane shiru dake ake ne”
kai Halilu ya girgiza “yayi miki kyau ai kamaki zanyi saiki faɗi wadda ya aikeke”
kuka Mairo tasa “Gwaggo kinji ko dukana zaiyi”
“ba zai dakeki ba bani na aikeki ba”
“hmmm Gwaggo ina miki tsoron wata rana ki daina goyawa Mairo”
“wai miyasa ka rai nanine Halilu karya zan maka kenan na faɗa maka aikenta nayi”
taɓe baki yayi ya girgiza kai ya fice. 

kwafa tayi da taga ya fice “kai mugu bakin azzalumi to zo ka dakeni ɗin”
sakin hannunta Gwaggo tayi ta shiga mata masifa “ban rabaki da rashin kunya ba kuma kinsan saida mukayi dake bazaki daɗe ba kikaje kika zauna har dare”
turo baki tayi “to ba shine daren yayi saurin yi ba kuma kinsan na daɗe ban fita ba kuma…”
bata karasa maganar ba Gwaggo ta katsa mata tsawa “ke dan Allah rufe min baki ‘yar rashin ji kuma ki wuce kije kiyi sallah kici abinci”
da ture2 ta nufi ɗaki tana gunguni. 

_Washe gari…_
tun safe Mairo tasa Gwaggo gaba tana rokonta tayi mata giɗar siyarwa,
sai faman rantsuwa take mata wai bazata sake yin abunda tayi ba.
sam Gwaggo kin yarda tayi duk da magiyar da tayi ta mata
Mairo na ganin haka ta sawa Gwaggo kuka ba k’akkautawa harda su shak’ewa tana murje murje cikin kasa duk ta bata kayan jikinta.
banza Gwaggo tayi da ita duk da bata son kukanta amman ta daure.
haka ta wuni tana kuka ta kuma yi sa ah Halilu bai dawo gidan ba tun fitar da yayi da safe.  
          saida ta gaji dan kanta ta shi ta dawo kusa da Gwaggo dake tukin tuwo ta zauna tana ajiyar numfashi, 

    Gwaggo saida ta gama kwashe tuwon ta kai ɗaki sannan ta riko hannunta suka shiga banɗaki tayi mata wanka.
har suka fito bata daina ajiyar zuciya ba idanuwanta duk sun kunbura sunyi ja
saman gado Gwaggo ta zaunar da ita ta ɗauko doguwar rigar atamfa tasa mata,
ta kwantar da ita saman jikinta tana shafa bayanta
lafewa Mairo tayi in banda ajiyar zuciya babu abunda take sauke
sun daɗe a haka Gwaggo sai buga mata baya take tana son tayi bachi ita kuma taki tayi bachin sai faman sauke wahalallen numfashi take.
kai Gwaggo ta girgiza tace “ni kan Mairo kina bani mamaki ace bakida aiki sai kuka sai ja magana sai masifa haka kawai ki wahallarda kanki dubi yadda kika wuni kina kuka”
nan sabon kuka ya zo mata “to bake bace kika ki yarda kimin giɗa ba kuma na faɗa mki bazan sake ba”
da in’in niyar kuka take maganar tana numfashi da karfi kamar zuciyar zata fito 

bubbuga bayanta Gwaggo ta shigayi tana faɗin “halinki nake tsoro Mairo karkije ki sake yin wani abun kuma kina ganin yadda Halilu ya sa miki ido jira kawai yake kiyi wani abun bama hHlilu kaɗai ba harda makota jiraye suke dake Mairo ke kuma gaki baki jin magana”
ɗagowa tayi idonta cike da hawaye tace “wlh Gwaggo na daina na faɗa miki bazan sake ba in kuma na sake Allah yasa na mutu”
rufe mata baki Gwaggo tayi “Subhanallahi Mairo miye haka karki sake faɗan irin wannan maganar kinji”
kai ta ɗaga mata “na daina Gwagho zaki doramin ko gobe zakimin giɗar?”
shiru Gwaggo tayi tana tunani dan tasan Halin Mairo in kuma bata dora mata ba wata sabuwar masifa ce.
kallonta tayi tace “kinmun Alkawari bazaki sake ba bazaki yi abunda zaisa a dake kiba?”
da sauri tace “eh nayi”
“shikenan zn dora miki”
“gobe ko Gwaggo?”
“eh Allah ya kaimu”
“amin”
rumgumeta tayi “na gode Gwaggo”
“Allah yayi miki Albarka”
“amin gwaggo zaki sayamin hancin ligidi?”
“eh  shi kike so?”
“eh”
“to bari na bada a siyo miki”
kwantar da ita Gwaggo tayi ta nufi kafit (wadurup ta da tsohuwar yayi) ta bude fanteka (kwala) ta ɗauko kuɗi ta sa hijabinta ta fice. 

Story continues below


© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*7* 

_Washe gari…_
tun da asuba Mairo ta tashi tana yin sallah ta shiga karatun gajerun  surorin data iya inta kare ta sake maimaitawa har rana ta fito. 

_8:14pm…_ 
Gwaggo na motsa kunu (koko) Halillu ya shigo gaishe ta har lokacin Mairo karatu take.
mamaki yayi sosai bayan sun gaisa da Gwaggo yace “yau yarki abun k’warai akeji?”
murmushi Gwaggo tayi “ai daman tana abun k’warai indai karatu ne ai kasan Mairo ba baya ba”
“a makarantan ba agida yaushe rabon da tayi irin wannan karatum tunfa da asuba nake jinyo ta ɗakina”
“to ai daman Mairo abunda take ai kuruciya ce data girma dainawa zatayi”
“ai da girmanta Gwaggo yanxu inta kara kaɗan ai aurarda ita za’ayi” 

kuka Mairo ta fara wadda ba hawaye ta daina karantun “wlh Gwaggo bana son aure ba zanyi ba”
dariya Halilu yayi “au daman ba karatu kike ba kunnenki na kanmu ai daman nasan karatun munafirci ne”
kamar ta fasa kuka ta kalli Gwaggo “kice ya kyaleni ya tashi ya bar miki ɗakinki”
kofi Gwaggo ta janyo ta zubawa Halilu ta mika masa “karɓi ga kununka kosai na can gindin murhu a kwano”
dariya yayi bayan ya karɓa yace “dan tace ki koreni shine zaki koreni Gwaggo?”
“to naga fitina kake son jami muna zaman mu lafiya”
“ai ni gaskiya ce na faɗa kuma Mairo da kike gani aurene kawai zaiyi mata hankali ta daina abubuwan nan da take”
haɗashi da Allah Gwaggo ta shiga ganin Mairo nason yin kukan da gaske daker ta samu ya fita.
juyawa Mairo tayi zata cigaba da karatu Gwaggo ta shafa bayanta “taso haka yar Gwaggo ki karya (breakfast) ai kinyi karatun da yawa”
murmushi tayi “to gwaggo aI zaki mun giɗar ko?”
“sosai ma ai dole nayi miki bana miki alk’awari ba anjima kaɗan zanyi miki”
daɗi ne ya lumluɓe Mairo da sauri ta ɗauki kayan karatun ta aje gefe ta kwanto jikin Gwaggo ta soma bata kunun tana sha cike da jindaɗi. 

_2:00pm….._
Mairo ta fita tallar giɗar k’inbi tayi hanyar da tabi ranar duk da zuciyarta na raya mata ta ɗan lek’a taga ko yana nan gashi har k’anshin goribar birni takeji tana tuna yadda take cinta. 

haka dai ta daure ta nufi bakin kasuwa gurin data saba zama tana siyarda giɗar. wata yarinya na zaune a gurin tana ganin Mairo ta tashi da sauri ta koma gefe dan tasan halin Mairo indai matsifa ce saida ka barmata balle yau da fuskarta take a haɗe kamar anyi mata mutuwa. 

koda la’asar tayi Mairo siyar da bakin rai ta nufo gida tana tureture baki kamar ta fasa kuka sai wata tafiya take kaɗan kaɗan.
haka ta ido gida ko sallama babu tun a bakin kofa tayi jifa da turen ta ta karaso idonta ciki da kwallah ta zauna kusa da Gwaggo dake Sallah, 

tana sallamewa ta kalleta “lafiya Mairo waya taɓa ki?”
soshe soshe ta shiga yi tana tunano karyar da zatayi “ni..ni…ni….ɗan ta malele zan siya?”
shafa kanta Gwaggo tayi tana murmushi “haba Mairo sai kace wani abu harda su kwallah? ɗauki kuɗi kije ki siyo ki haɗa da kifi yadda zaki jidaɗin cinsa”
kai ta ɗaga “tho amman sai in zanje makaranta”
“tho inkin huta ki watsa ruwa sannan kije makaranta kinji”
kai ta ɗaga mata ta mika mata kuɗin giɗar.
“eyeee Mairo yau duka aka siyar gaske naji kin jefar da ture tun kofa”
murmushi Mairo tayi “yau nawa zaki ban?”
“hamsi zan baki ashiri kisa a susu talatin ki siye ɗan ta malele”
ta karasa maganar tare da mika mata 50 ɗin., 

da zumuɗi ta karɓa ta tashi ta nufi ɗaki da guɗu yau an sami abun sawa a susu mai tsoka. 

    ”’*** *** *** *** *** ***”’
     tun daga lokacin kullum sai Gwaggo tayiwa Mairo giɗa ita kuma bata fashin zuwa gurin siyarwa so ɗaya ta je gurinda aka bata goribar birni koda taje bata tararda kowa ba tsoro taji sosai babu abunda take rayawa a ranta sai aljani ne 

Story continues below


“kai aljanine wannan mutunen da gaskiyar Gwaggo tunda gashi ban sake ganinshi ba kuma duk goriba karfine da ita amman tashi taushi ne da ita kuma na riga naci” 
a fili take wannan maganar can ta tsaya tana tunani “inda ba aljani bane ai bazai zo cikin dajin nan ba har ya zauna kuma fa….” 

bata karasa maganar ba ta watsa da gudu saboda motsin da taji cikin itacen dake gurin tana faɗin “karku biyoni na daina bazan sake zuwa ba wayyoh Gwaggo”
ihu take tayi da kuka tana gudu rabin giɗarta na zubewa,
har tabar gurin bata daina kuka ba dan gani take kamar sun biyota saida ta isa baki kasuwa sannan ta ɗan natsu ta soma numfasawa daidai, 

tun daga lokacin bata kara tunanin zuwa gurin ba
duk ta ɗauko tallar giɗarta sai dai ta nufi bakin kasuwa inta siyar ta tayi ta shiririta ita da abokanin talla ko inta dawo ta biya gidansu jummala suyi gantalin da suka saba daman haka take so, 

fagen neman magana da matsifa ba babba ba yaro kowa ta raina musamman inta ga ta girmeka ko kana tsoronta,
        Gwaggo in banda goya mata baya babu abunda take.
Halilu yayi faɗa harya gaji amman a banza kamar ma kara turata yake, 

gashi Gwaggo ta hana ya daketa sai in ya faki idonta ko ya haɗu da ita can waje.
harta saba inta ganshi saita chanja hanya haka suka rika wasan ɓoya ita dashi. 

*_3 months later….._*
yau da wuri Mairo ta siyarda giɗarta kuma yau bata jin wasa saboda dukan da Halilu yayi mata jiya dan yanzu har bakin kasuwa yake zuwa da ya tarar tana wasa ya fatattaketa da duka har gida, 

duk yadda abokanin shashacinta sukaso ta tsaya kiyawa tayi dan tsan sai yazo gurin kuma Gwaggo tace mata da ta siyar ta dawo gida dan kar halilu ya daketa,
sallama tayi musu badan sunso ba dole suka kyaleta wasu kuma suka wuce gida dansu inba da Mairo ba basa jindaɗin wasa, 

_Aysha adon gari ga Hajara adon gari ni Maryam adon gari inba ni ai ba gari Khadija Abubakar nake Candy kunji laqani gani tafe da’ayari yan mata a dandali_(MY UP COMING SONG INSHA ALLAH)
Mairo na tafe tana rera wak’a mak’ale da turenta na giɗa. 

tunda kamin ta k’araso ta hango wata kafirar mota baqa mai shek’i fake kofar gidansu yara sun zagayeta sai shafa suke. 

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*8* 

da gudu Mairo ta karaso gurin ta shiga korar yaran duk da bata san mai motarba ɗan kawai ta ganta kofar gidansu ne kuma taga yara sun zagayeta suna shafa ita yar neman masifa, 

shafa motar itama ta shigayi tana dariya tana kallon kanta ta madubin motar harda zira halshe tana lasa glass tana tale idanunta (fitar da ido)
tafi kafin minti 3 ahaka sai fana dariya take kamar wata taɓaɓɓiya, 

yaran sai kallonta suke suna son su kwakwayeta suna tsaron tayi musu masifa tunda taɓa motar ma ta hana su. 

can ta juyo ta kallesu ta hade rai taja tsaki “mtssss ku dan Allah ku ba mutane guri kauyawan banza kawai kowa ya bar mana k’ofar gidan mu ko naa muku hegen duka”
maganar take tana wani ɗageɗage da marmaɗen ido.
          duk ja yaran sukayi da baya dan sunsan halin Mairo indai masifa ce ba baya ba
yarinya ɗaya aka bari tana watsawa Mairo harara harda kai hannu ta shafa motar tana faɗin “an shafa kema ai yar kauyece da hegen kanki”
kai Mairo ta girgiza tana dariya “hee ni kike faɗawa wannan maganar  zaki ko ci ubanki yanzu”
ɗankwalinta ta cire ta k’ulle kuɗin giɗar dake hannunta ta ɗaura ɗan kwalin a k’ugunta (kwankwaso) tayi cikin yarinyar suka hau faɗa da juna, 

kaye huɗu yarinyar tayiwa Mairo dan ta fita girma kuma k’arfi ba ɗaya ba gashi  daman can  Mairo ba wani k’arfi ne da itaba sai yar banzar masifa.
ɗukan k’warai Mairo tasha a hannun yarinyar tun tana iya jurewa har takai ga fasa kuka tana faɗin “azzaluma wlh sai naci ubanki hegiya-”
Mairo bata rufe baki ba yarinyar ta kai mata wani mugun shuri.
nan Mairo ta faɗi ta fashe da kuka
da gudu yarinyar tabar gurin gudun kar Gwaggo ta ji ta fito. 

Story continues below


kuka Mairo tayi tayi tana kallon kofar gidan ganin babu wadda ya fito yasa dole ta tashi rik’e da ɗankwalinta a hannu kanta kuma duk k’asa ta shiga gida,
da kuka ta shiga gidan ta nufi gurin Gwaggo dake bakin murhu tana eza wuta.
da sauri ta ɗago ta rikata “lafiya Mairo Halilu ne ko?”
kai ta girgiza mata ta shiga faɗa mata abunda ya faru,
ɗankwalinta Gwaggo tasa tana share mata hawaye “haba Mairo miye na wani korar yara dansun taɓa mota kuma in banda fitina inake ina faɗa da wannan yariyar?”
turo baki Mairo tayi ta ɓata fuska kamar ta fasa kuka 

“shigar mata kikayi ko Gwaggo?” 

“a’a wani nan na shigarwa wata na bar Mairo dukan da ta miki ne ban jidaɗiba” 

“kuma harda wani mugun shuri tayi mun ina jin zafi har yanzu” 

“barta da Allah kijin”
kai ta ɗaga “Gwaggo motar wace kofar gida?” 

“yan birni ne suka zo ganin gida” 

kusa da ita Mairo ta matso “yan bunni Gwaggo gurin wa sukazo ina suke” 

“sun tafi ganin sauran dangi”
“lahh daman Gwaggo kina da yan uwa yan bunni?” 

“eh kema ai en’uwanki ne tun kima karama marabinsu da nan”
risinawa Mairo tayi zatayi magana sukaji Sallama. 

Gwaggo ce ta amsa masa Mairo kan ido ta sakar masa kamar bata taɓa ganin mutane ba, 

harya karaso tsakar gidan shi take kallon tana masa dariya shidai kallon kawai yake kamin ya kalli  Gwaggo yace “Sannu da aiki Gwaggo”
“yauwa sannu qasin kai kaɗai ka dawo?”
“eh ina gabansu ne suna hanya suma”
tabarmar dake shinfiɗe k’arkashin ecce ya nufa ana k’ok’arin zaunawa yayiwa Mairo magana
“ke baki eya gaida mutane ba?”
tasowa tayi da gudu tazo kisa dashi ta zauna. 

“na eya ina wuni?”
“lafiya kalau ya sunaki?”
saida tayi dariya sannan tace “Mairo sunana Mairo”
murmushi yayi ya kalli Gwaggo “Gwaggo ni bansan wannan yarinyar ba yar gidan nan ce?”
daga can Gwaggo ta amsa mishi “eh gidan nan take ear uwarka ce ai yar wajen margayi ce”
“wane margayi?”
“malam tanimu wadda koda kukazo gaisuwarsa bakayi aureba ita kuma tana k’arama”
shiru yayi yana kallon Mairo data washe masa hak’ora, 

“na ganeta Gwaggo daman ke kike rik’onta?”
sallamar dasu Abbah sukayine ya hana Gwaggo amsa masa tambayarsa.
“amin wa’alaikassalam alhaji harku dawo?”
“eh wlh kinga kara mu kama hanya da wuri tunda munga dangi”
momi ce ta amsa mata.
bayan sun xaune Gwaggo ta nufosu tana faɗin 

“ai nikan ban yaba miku ba ace mutum shekara ds shekaru rabonsa da gida amman yazo ɗai rana ai kamata yayi ace kuzo ko sati ɗaya kuyi ko biu” 

ɗariya sukayi Abbah yace “har yanzu dai Jamila baki chaja ba halinki nanan na masifa” 

“yau ni wani haline dani daga faɗar gaskiya”
momi tace 

“karki damu jamila insha Allahu zamuzo muyi sati anan yanzu bamuzo.da shirin kwana ba kuma kinga sauran yara suna makaranta sai anyi hutu tukuna” 

taɓe baki Gwaggo tayi “nidai nawa idone ai rana bata karya”
dariya suka sake yi har Mairo sai a lokacin ta gaishesu.
duk suka amsa Abbah ya shafa kanta “Maryam am girma ko?” 

“ashe zaka iya gane ta ai ɗaukar ka manta”
cewar Gwaggo 

murmushi yayi yace “haba dai yar tawa zan manta ko yanzu da mukaje gurin tsoho saida mukayi maganarta”
mansura ta kalleta tana murmushi tace “oh Abbah itace yarinyar da ake magana” 

momi tace “eh itace yar marainiya”
“Allah sarki Allah ya jikan mahaifa”
duk suka amsa da Amin. 

sun ɗan juma suna fira daga bisani Gwaggo ta kawo musu abinci.
gudun masifar Gwaggo yasa dole suka ci badan sunso ba koshi kaɗan sukaci dan tuwon dawane ba wani sonshi suke sosai ba. 

Story continues below


kuɗi Abbah ya ciro aljihunsa masu ɗan ɗama ya ajewa Gwaggo “gashi ayi wata lalurar”
“haba Alhaji bancin abin alkharin da aka kawo?”
“babu komai jamila a daici da hak’uri”
godiya sosai Gwaggo tayi masa momi da mansura sukayi mata sallama.
suna shirin fita Mairo ta laqe kafaɗa ta bata fuska ita saita bisu. 

Gwaggo ce ta shiga lallasarta “haba Mairo wane irin binsu kuma bunni fa zasuje”
“eh ina son zuwa bunni nidai saina bisu”
“kinason ki daina ganina?”
“a a ai dawowa zanyi”
Abbah ne ya dafata “kiyi hakuri Mairo kinga Jamila bata so kije ki bari har wani lokacin inmun dawo sai muje dake kinji?”
kuka ta fasa “a a ni saina biku yanzu”
Qasin ya kalli Gwaggo yace “Gwaggo ki bari aje da ita tunda tana son zuwa”
faɗa Gwaggo ta soma “babu inda zataje ita kenan ina ganinta ina jindaɗi saiku ɗauke ta to baza taje ba”
juyowa Gwaggo tayi gurin Mairo ana lallasarta ba 

aiko.kamar tana kara turata sai uhu take kaar wadda aka yiwa wani abu.
Abbah tsaye yayi yana lallaɓata shima
duk yadda Momi taso su tafi kiyawa yayi dan bayason barin Mairo tana kuka gashi Gwaggo ta hana aje da ita. 

suna Halilu ya shigo aiko da gudu Mairo ta tashi tayi bayan Gwaggo tana kuka,
nan ya shiga tambayar abunda akayi mata momi ce ta faɗa masa, 

nan ya hau Mairo da masifa “Allah in baki yiwa mutane  shiru ba saina miki shegen duka yar iskar yarinya”
kara buɗe baki Mairo tayi tana kuka kamar wata karamar yarinya, 

Gwaggo ta kalli Halilu “kaga ko ana neman tayi shiru kaxo kana mata masifa ko” 

“to Gwaggo in tana son xuwa ki barta taje mana in kuma ba zataje ba su su kama hanya kar dare yayi musu” 

“to waya hanasu tafiya ai sune suka hure mata kunne tace saita bisu” 

Qasin yace “a a Gwaggo karkiyi zargin kowa itace kawai dan kanta tace saita bimu”
momi dai haushine yasa ta fice ita da mansura suka bar Abbah da Qasin. 

Halilu yace “ni wlh da kina yarda da kinbarta taje su da kansu zasu dawo da ita dan mugun halinta” 

kin yarda Gwaggo tayi saida taga su Abbah zasu wuce gashi Mairo na kuka kamar ranta ya fita sannan ta amince.
aiko Mairo kamar ta zuba ruwa k’asa tasha da gudu ta nufi ɗaki ta shiga haɗa kayanta cikin bakko (ghana most go). 

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*9* 

bayan Amimcewar Gwaggo saida akaje gurin tsoho tare da Mairo aka faɗa masa shima kin amincewa yayi saida yaga abun na Mairo bana wasa bane sannan ya yarda sosai Abbah ya jidaɗi daman tun rasuwar kanensa yaso a bashi ita Gwaggo ta hana, 

sai goshin magariba (kusan magariba) suka kama hanya
so huɗu ana tsayawa Mairo nayin amai jikinta sai rawa sanyi yake nan da nan zazzaɓi ya rifeta saida aka kashe ac ɗin motar, 

*_9:37pm….._*
suka isa Sokoto koda Qasin yayi farkin Mairo na rungume jikin momi tana bachi.
saida kowa ya fita sannan momi ta tasheta 
a firgice ta fito motar tana ɗaga kanta hankes ya cika mata ido,
gidan sama ne mai hawa ɗaya ko ina an manna gulof murza ido Mairo ta shigayi dan gani take kamar mafarki take. 

bayan momi ta fito Qasin ya rufe motar shida Mansura suka nufi part ɗinsu daman Abbah tuni ya wuce nashi part ɗin, 

Mairo na tsaye tana kalle2 momi ta rik’a hannunta zasu shiga ciki Mairo tayi tsaye tana kallon kofar farlon da alama tsoro take ji, 

faɗuwa gaban momi yayi tana tsoron kar kuma tace bazata shiga ba.
“lafiya zomu shiga ciki mana”
shiru Mairo tayi ta lakkafe kafaɗa
saida Momi ta maimaita sannan tace “nan ne gidan?”
“eh nan ne zo mu shiga ciki”
tsaye tayi kamar bazata shiga ba
momi bata bi ta kanta ba taja hannunta suka cigaba da tafiya.
jiki a sanyaye Mairo ta shiga farlon tayiwa hannun momi mugun rik’o Usman na kwance saman doguwar kujera yana bachi siraj kuma na kallo, 

Story continues below


shine ya taso ya tari momi da far’ah “sannu da zuwa momi” 

“yauwa sannu siraj baka kwanta ba?” 

kayan dake hannunta ya k’arɓa yana faɗin “eh ban kwanta ba wacece wannan momi?” 

kallon Mairo momi tayi “qanwarka ce” 

“daga can aka zo da ita?” 

“eh bari na shiga ciki” 

Up stairs momi ta nufa Mairo na rik’e da  hannun Momi,
suna shiga bedroom Momi ta faɗi zaune saman bed ita da Mairo,
har lokacin tana  rike da hannunta 

bayan sun ɗan huta Momi ta nunawa Mairo tawel “jeki ki ɗauki ga tawul can ki ɗaura sai kiyi wanka kici abinci ki kwanta”
kai Mairo ta girgiza “a’a nidai Gwaggo wanke min kafafu kawai take in zan kwanta bata min wanka”
“to mu wanka muke in zamu kwanta tashi ki cire kayanki”
tashi Mairo tayi ta nufi gurin da Momi ta nuna mata.
itama Momi tashi tayi ta shiga cire kayanta 

saida ta gama wanka sannan ta kira Mairo tayi mata
tare suka fito  Mairo bata tsaya jiran komai ba ta faɗa saman bed
Momi kuma ta nufi waduraf tasa kayan bachi ta ɗaura zane sama bayan tasa hijab ta kabbarta sallah. 

koda Momi ta gama sallah Mairo tayi bachi.
tana cire hijab ɗinta ta nufi down stairs.
bata daɗe ba ta shigo ɗakin da plate din abinci a hankali ta shiga tada Mairo amman hakan bai hanata farkawa a firgice ba.
“k’arɓi ga abinci kici saiki kwanta”
kin k’arɓa tayi ta tsurawa Momi ido can kuma ta mayarda su gurin abinci. 

sakwarace da miyar agutsi da namomi hannun tasa ta k’arɓa “ni bazan iya cinyewa duka ba”
“ci kibar saura”
kusa da ita Momi ta zauna tana amsa waya. 

saukowa Mairo tayi kasa ta hau cin abinci
cikin yan mintuna ta kare ta tashi tana suɗar miyar dake plate ɗin duk ta ɓata gurin da miya kamar mai ɓararen baki.
nunawa Momi hannunta tayi “na kare ina zan wanke hannuna?”
toilet Momi ta nuna mata
tana gyaran ɗaurin tawul ta shiga toilet ɗin 

koda ta fito Momi ta gyara gurin tana mopping
tsaye tayi har momi ta kare ta nuna mata gado “hau ki kwanta”
ba musu ta hau Momi taja zanen rufa ta lulluɓa mata.
ta kashe wutar ɗakin ta kunna ta bedside lamp ta nufi kofa,
Mairo na ganin zata fita ta tashi da sauri “ni kaɗai zaki bari nan?”
Momi daga gurin da take tsaye tace “tsoro kike jine?”
“eh bazan iya kwana ni kaɗai ba”
“babu abunda zai sameki ki kwantar warki kiji?”
“aa ni bazan yarda ba”
saukowa tayi ta nufo Momi.
Momi tace “to bari na kunna miki wutar saiki kwanta kamin nazo yanzu zan dawo jeki kwanta”
lake kafaɗa tayi “a a ni bazan yarda ba”
tsawa momi ta katsa mata “wuce kije ki wanta nace”
jiki na ràwa Mairo ta faɗa saman gado ta ɗanne fuskarta cikin katifa,
Momi na ganin haka ta taja kofa ta fice 

kuka Mairo tayi tayi kaɗankaɗan kuma ta kasa ɗago kan dan tsoron kar taga wani abu har bachi ya ɗauketa. 

*_washe gari….._*
tunda asuba Momi ta tada Mairo
a firgice ta farka jikinta sai rawa yake hannun momi ta rika suka shiga banɗaki tare sukayi alwala.
bayan sun fito Mairo ta nufi yar zakarta ta zazzage ta ɗauki wata atamfar kauye tasa tare da hijab ta fara sallah, 

tana sallamewa komai bata tsaya yiba  ta koma bachi.
sai 8 da minta ta farka koshi dan siraj ya tada tane.
da murje murjen ido ta tashi tana mik’a idonta a lumshe tana soma kiran gwaggo.
“ke tashi momi na kiranki nace”
‘to’ tace tana turo baki kamar ta fasa kuka
shidai bai tsaya jiranta ba ya fice, 

saida ta gama gunguninta sannan ta tashi ta nufi kowa duk jin take bata son gidan,
tana fitowa ta hango farlo down stairs.
wani irin ihu ta saki saboda juwa data gani tayi bayabaya tana kiran “na shiga uku wayyo Gwaggo na bani mutuwa zanyi” 

Story continues below


duk kai suka ɗago sun Kallonta daga dining area siraj ne ya fara tambaya “lafiya?”
cikin kuka tace “na bani bazan iya saukowa ba na shiga uku Gwaggo”
duk fashewa sukayi da dariya banda siraj da yaja tsaki sai kuma Momi data hau mata faɗa “ke wai wane irin iskancine dake haka haka kawai zaki rika yiwa mutane uhu”
Qasin dake tsaye ya kalli Momi yana murmushi “tsorone taji momi kinsan yar kauye ce”
“to dan taji tsoro sai tayiwa mutane ihu iskancin da takeyi can kauye nan bazan ɗauke shiba”
tea cup ɗin dake hannunshi ya aje ya nufi up stairs. 

hannunta ya riko ta rumgumeshi iya karfinta ta kulle ido gam sannan suka sauko.
har suka isa dining bata buɗe idon ba saida taji an zauner da ita sannan ta buɗe ido tana kare musu kallo, 

da Qasin ta fara sannan Usman, Siraj sai kuma ta juyo gun Nura.
kofin tea Momi ta aje mata idonta cike da hawaye ta ɗauka ta kai baki
bata ajeba saida tasha rabin kofin Siraj da Nura da Usman sai dariyarta suke Qasin Murmushi yayi ya kalli agogon hannunsa yace “Momi ni bari na wuce gurin aiki”
“to Allah ya tsare”
“Amin”
saida ya kara kurɓa tea ɗin sannan ya fice. 

Usman ya kalli Mairo yana driya yace “bakison bredin hala?”
banza ta masa har Momi ta kare cin abincinta da Usman suka tashi.
sannan ta ɗauki bredin tana hawaye ta rika somawa kamar turo da miya tana ci. 

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*10* 

Siraj dai sai kallonta yake can yaji bazai iya zurewa ba yace “wai mi kike yiwa kuka?”
cikin kukan tace 
“ni gida nake so”
dariya yayi “gida?”
“eh”
“mi aka miki to?”
“bana son gidan nan bana son gida a sama kuma mumi faɗa take min”
fashewa sukayi da dariya Nura yace “hala baki taɓa ganin gidan sama ba?”
“eh nidai bana sansa”
tashi nura yayi yana faɗin “amman gaskiya kauyancinki yayi yawa”
k’ara turo baki tayi kuka nason fito mata fili Siraj dai kallonta kawai yake har ya kare cin abinci ya tashi, 

Mairo tasowa tayi ta dawo kusa da doguwar kujera dake parlour ta zauna har lokacin hawaye take.
jin tafiyar momi yasa ta ɗago kai tana kallon up stairs “lafiya kike kuka?”
fuskar momi a haɗe take mata tambayar
“gida nake so gurin Gwaggo”
murmushi momi tayi “karya kike yi ai ke kika dage saikin biyomu jiya jiya muxo yau kice a kaiki gida babu yadda bayiba akan ki zauna kika ki”
hannayenta ta haɗe tana rokon momi 
“na daina mumi bazan sake cewa a zo dani ba”
“uhmm tashi muje kicin kiyi wanke wanke”
lake kafaɗa tayi “ni ban iya wanke wanke ba”
kunneta momi ta kamo “ke bari kiji na faɗa miki iskancin da kike can kauye nan bazaki min shiba”
kuka Mairo tasa sai kiran Gwaggo take. 

haka momi taja hannunta suka nufi kicin.
gurin wankewanke momi ta nuna mata ta “oya sa hannu ki wanke” kallon momi tayi idonta cike da hawaye tace “wlh ban iya wanke wanke ba”
“dukanki dai kikeso nayi kamar zakice baki iya wanke wanke ba kuma rikon kauye ba birnin ba koki wanke shi ko na miki dukan tsiya” momi na kaiwa nan ta juya tabar kicin ɗin, 

haka Mairo ta hau wankewanke tana kuka
sama take wankewa dan har ga Allah bata iya ba tunda Gwaggo bata sata aikin komai inba sharaba koshi inta ga damane take yi.
haka ta wankesu samasama kofukan da akasha tea ma ɗaurayisu kawai tayi ta aje,
koda ta kare ta fashe tea cup ɗaya kuma duk ta ɓata gurin da ruwa ɗan kwalinta tasa ta goge ruwan ta jefashi bayan firjin.
jikinta a sanyaye ta nufo parlour tsaye tayi tana kallon momi dake zaune saman kujera.
ganin bata kula taba yasa ta karaso kusa da ita “na kare”
sai lokacin momi ta kalleta “to wuce kiyi wanka”
“ina?”
“inda kika ga na miki jiya”
lake kafaɗa tayi tayi baya baya “ni bazan hau sama ba gaskiya”
taɓe baki Momi tayi ta cigaba da kallon tv. 

*****
ranar Mairo wuni tayi tana kuka saboda faɗan da momi tayi mata kuma ta hana mata abincin rana saboda takiyin wanka. 

da magariba Mairo na gefen kujera zaune Momi ta nufi kofa da sauri Mairo ta tareta tana “ni ki bani abincina yunwa nake ji”
tureta momi tayi saida ta faɗi wani mahaukacin ihu ta saki momi saida ta rufe kunnuwanta ta hau shurenta.
“lafiya?”
Qasin na shigowa abunda ya fara tambaya kenan 

momi ta nunata da yatsa “rainin wayo ne da ita so nake na gyara mata zama”
karasawa yayi ya tada ta “mi tayi momi?”
“iskancin da take can kauye ne take son tamun”
kallon Mairo yayi “mi kika mata?”
cikin kuka Mairo tace “ban mata komai ba muguwace azzaluma ƙk’atuwar banza kuma ban yafe miki b-”
da sauri Qasin ya rufe mata baki “ke karna sake ji ba mamanki bace”
kai ta girgiza tana hawaye “ni ban sonta ba mamana bace”
kwafa momi tayi “aiko kashinki ya bushe cikin gidan nan”
“wai minene mafarin wannan abun ne momi?”
momi tace “rantsuwa nayi duk batayi wanka ba bazan bata abinci ba”
kallon Mairo yayi “ke mi ya hana miki wanka maryam kin fi son ki zaina da k’azanta?”
“a a itace tace saina hau saman sama sannan nayi wanka ni kuma tsoro nake ji”
kallon momi yayi yana murmushi “kinji momi tsoro take ji kinsan ko ɗaxun saida aka saukarda ita”
“ba wani tsoro iskancine kawai”
“ba iskanci bane ko?”
ya tambayi Mairo kai ta ɗaga yace “bata hakuri sai kuje tayi miki wanka kuma karki kara rashin kunya kinji”
saida ta daɗe sannan ta kalli momi kasa2 tace “yi hakuri bazan sake ba”
da ita da dashi duk tsurawa momi ido sukayi sunajiran abunda zatace 

saida ta watsa masu harara sannan ta fixgi hannun Mairo suka nufi up stairs.
kankame momi Mairo tayi ta rumtse ido nan momi ta sakar mata hannu “wuce da kanki”
kuka tasa nan momi ta katsa Mata tsawa dole ta rike karfen ta rika hawa da rumtsen ido har ta haye.
momi ce tayi mata wanka Mairo kan ana mata wanka tana tunanin yadda za ayi ta tsera ta gudu ta bar gida,
bayan sun fito momi ta wulgo mara kayanta ta sauka downstairs ta ɗebo mata abinci. 

*_washe gari….._*
tun asuba momi ta tada Mairo bayan sunyi sallah bata barta ta koma bachi ba suka nufi kicin.
tare suka haɗa komai na breakfast ranar momi batayi mata faɗa ba dan tare sukayi komai duk da ba wani iyawa tayi ba daman momi abunda bata so ta saka aiki kaki da kuma kuka. 

*_8:30am….._*
suka kare hada komai momi ta nunawa Mairo gurin da zata jera.
ba musu ta rika jera abinci badan ranta yaso ba sai dan gudun matsifar momi aranta kan ɗebima momi albarka kawai take tana aiban ta’ta.
Mairo ce ta fara zama bayan ta jere breakfast ɗin sannan momi,
Usman da Nura dake zaune saman kukera suka nufo dining.
Siraj sai janta yake ita kuma ta wani haɗe fuska kamar ta fasa kuka .
momi da kanta ta zubawa Mairo breakfast su kuma suka shiga zubawa kansu.
Nura ya kalli Momi yace “yau yaya ba zai karya nanba ?”
momi tana k’ok’arin zuba ma kanta tace “zaizo mana ai kasan nan yake karyawa kila bai tashi bachi bane” 

kamar daga sama sukaji an banko kofar parlour duk juyawa sukayi suna kallon Qasin daya shigo fuska a haɗe.
yana karasowa momi tace “lafiya?”
takardun dake hannunsa ya nunawa momi cikin zafin rai yace “kwangila ce Yarima yakai a kanfaninmu”
murmushi momi tayi “wow…-”
tare numfashinta yayi ya juyarda fuska “haba momi kamar bakisan Yarima ba he just want to ruin my life kuma deal ne between me and him saina gani tsakanin ni da shi who is going to be loser”
tashi momi tayi ta daga hannunta da niyar yi masa magana sai kuma ta kasa jefarda takardun yayi ya fice cike da bacin rai.

sanyi jikin momi yayi ta kasa kai komi bakinta Nura da Usman ne kawai suke cin abinci shima Siraj ya damu sai kallon momi yake, 

tashi momi tayi ta nufi gurin daya watsarda takardun ta shiga haɗawa.
saida ta haɗesu guri ɗaya sannan ta kalli Siraj daya juyo yana kallonta tace “Siraj jeka kiran min yayanku”
kai kawai ya ɗaga mata ya tashi ya fice.
Mairo dai sai satar kallonsu take tana tsomen beredi, 

guri momi ta samu ta zauna dafe da kai kamar mai mata ciyo.
tana haka Qasin da Siraj suka shigo dining Siraj ya nufa Qasin kuma ya nufota yana faɗin “gani momi”
kujera momi ta nuna masa har lokacin tana ɗafe da kai.
bayan ya zauna ta kalleshi tace “Qasin ka rika hakuri kasan da wadda kake zama Qasin ni bana tunanin saboda ɓata maka suna ko karyarda kai Yarima ya ɗauki kwangila ya baka” 

kawar da kai yayi alamar bai jidaɗin maganar ba.
ganin haka yasa momi ta taso ta dawo kusa dashi ta zauna “Qasin ni a ganina kamar ma Yarima yana son ɗaukaka kanfaninku ne”
juyowa yayi ya kalleta “a a momi so yake ya karya ni kawai kuma bazan taɓa yarda da wannan kwagilar ba ba zai taɓa cinma burinsa a kaina ba” 

kallon momi yayi yana nazarin kalamanta can ya lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya ya sake buɗe idon yace “momi banida mafita sai wannan momi bana son Yarima yayi nasara a kaina momi ki duba min plz”
itama Momi ajiyar zuciya ta sauke tace “baka ganin mayarda kwangilar zai zame maka matsala?” 

“zai iya zama kan dan lokacin da zai bada kwangilar tare da yan jarida yazo”
“to karka kuskura ka mayarda kwangilar zai zubar muku da mutuncin kanfani”
“momi ba nida wata mafita sai wannan”
“haba Qasin sai kace kai ba namiji ba kai bakasan yadda zaka sarrafashiba ka bashi kunya ka taka abunda ya taka Qasin ka zama gawurtaccen namiji ba rago ba” 

Siraj da tunda ake maganar hankalinsa na gurin tasowa yayi yana faɗin “yes yaya kaima namijine ka ya k’eshi ks kara ɗags martabar kanfaninka kabi shawarar momi plz” 

ajiyar zuciya Qasin ya sauke a karo na uku ya kalli momi “momi ba hannuna da nasa ya bani kwangilar ba PA ɗina yaba kuma banida tambas dan zai iya haɗa kai dashi ya cutar dani”
Siraj yace “ka chanja PA kawai” 

“haba Siraj how many PA I have to change just because of him? PA 4 na chanja akanshi bazan sake chanja wani ba not anymore”
cikin faɗa yake maganar jijiyar wuyansa na tashi da sauri Usman da Nura suka juyo suna kallon su, Mairo kara sakin baki tayi tana kallonsu daman hankalinta yana gurin, 

dafashi momi tayi “ga wata shawara Qasin”
kai ya ɗaga mata ba tare daya kalletaba ‘uhmm’
“mi zai hana ka karɓi kwangilar kayi da kanka?” 

murmushi yayi mai cike da jin haushi “haba momi ai zubarda kai ne daɗi zaiji na k’arɓi kwangila da hannuna masa”
“ba faɗuwa kayi ba Qasin cigabane a gareka da kuma ɗaga darajar kanfaninku”
kai ya girgiza “momi ba zaki gane ba” 

“kaine baxa ka gane ba Qasin idan kayi haka mutane zasu yaɓeka suce bakada girman kai sannan kodan kwangilar tayi ya kamata kayi haka kuma idan tayi kyau zaka jawowa kanka customers ayaba maka ka kara samun ɗaukaka”
Siraj yace “gaskiya ne yaya ka ɗauki shawarar momi” 

ya daɗe zaune gurin kamin ya ɗago kai ya kalleta “shi kenan momi zanyi yadda kikace” 

murmushin jidaɗi Momi tayi ta shafa kansa “Allah ya maka albarka ya shige maka gaba”
shida Siraj suka amsa da ‘amin’
tashi yayi ya nufi kofa yana sauke ajiyar zuciya, 

Story continues below


da gudu Mairo ta taso ta nufo shi tana faɗin “dan Allah ka je dani yawo inson fita”
fuska a haɗe ya shafa kanta yace “ba yanzu ba” ɓata fuska tayi idonta suka cika da hawaye shirinta na guduwa ya rushe .
juya tayi  tana kallonsa har ya fice. 

tashi momi tayi ta nufi up stairs tana faɗin “Maryam in kuka k’are ki haɗa kayan ki kai kicin ki wanke kuma ki share parlour nan ki goge”
kara ɓata fuska Mairo tayi abunda ta rsana kenan hawayen dake makale a idonta suka zubo.


© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*12* 

bachi Mairo take saman kujera ta wani turo baki sai numfashi take da k’arfi, 

Momi na saukowa ta tadata “ke ke ke Maryam”
a firgice ta farka ta kara turo baki fuskartar momi ta rik’o “kinyi wanke2?”
kai ta ɗaga tana murza ido momi tace “tashi kije kiyi wanka”
tashi tayi kamar ta fasa kuka ta nufi up stairs zuciyarta cike da tsoro, 
rik’e k’arfin tayi ta rumtse ido tana tafiya a hankali har ta haye. 

        ”’*  *  *”’
Momi na kicin tana girki taji uhun Mairo da sauri ta aje robar dake hannunta ta nufi up stairs.
tsakiyar ɗaki ta tararda Mairo sai juye2 take tana kuka jikinta ba kaya kikata momi tayi “ke lafiya miya faru?”
kasa magana tayi sai toilet take nunawa momi tana tuma, 

da sauri momi ta nufi toilet ɗin,
kalle2 ta shiga ta rasa dalilin dayasa Mairo kuka hankalinta bai kai gurin shower da take kunne ba sai gab da zata fita sannan idonta suka kai gurin juyowa tayi ta nufi shower da niyar kashewa,
nan hannunta ya taɓo ruwan dake zuba da sauri tayi baya baya da yar k’ara saboda ta fasasshin ruwan da suka taɓa mata hannun, 

ta daɗe tsaye cikin toilet ɗin tana duba hannunta,
sannan tasa hannun hagu ta kashe shower.
koda ta fito duk’e ta tararda Mairo sai faman kuka take tana kiran ta bani ta shiga uku ta data momi tayi tana faɗin “sannu Mairo ni wlh na manta da yadda shower take mantawa ma nayi na haɗa miki ruwan da kai na yi hakuri kinji”
kai ta ɗaga tana kuka tace “ni a kaini gida gurin Gwaggo”
hakuri momi tayi ta bata daker tayi hakuri momi ta haɗa mata wasu ruwan tayi mata wanka ranar har kanta saida momi ta wanke, 

da suka fito momi ta rasa kayan da zata saka mata dan ita bata ga wasu kayan kwarai da zata sa mata ba haka dai momi ta ɗauko wata tsohuwar a tamfa tasa mata,
momi ta kalleta tace “hau gado ki kwanta”
da sauri ta nufi gadon ta faɗa rub da ciki, 

momi na gab da wucewa Mairo ta ɗago da jajayen idanunta ta kalli momi “mumo ko zaki aikeni?”
juyowa momi tayi “aike kuma Maryam kamar ya?”
tashi tayi zaune “in siyo miki wani abu ko aike”
murmushi momi tayi tace “a a ni babu abunda za’asiyo min koma abu zan siya saidai na aiki direba ko yara su siyo”
komawa tayi ta kwanta tana zubarda hawaye.
kai kawai momi ta girgiza ta fice. 

Mairo tunda ta kwanta take wahalallen bachi sai uku da rabi ta farka koshi dan momi ta tadata ne.
hannunta Momi ta riko ta suka nufi bathroom kin shiga tayi ta lak’e kafaɗa “ni bazan shiga ba”
“yi hakuri ni zan haɗa miki ruwan ba zakiji zafi ba”
daker momi ta lallaɓata ta yarda suka shiga, 

brush momi tasa tayi tare da alwala sannan suka fito,
tsareta momi tayi saida tayi sallah sannan ta riko hannunta suka nufo downstairs. 

zaune suka tararda Qasin yana cin abinci laptop na gefensa yana aikin danne2.
tsaki momi taja bayan ya jama Mairo kujera ta zauna,
ɗagowa yayi yana kallon Momi “lafiya dai momi?”
saida ta zauna sannan tace “hala baka ci abincin ba?”
sosa kai ya ɗanyi yayi murmushi “indomi ce ta ɗafa”
taɓe baki momi tayi “to Allah ya kyauta ya sawwake”
kasa amsawa yayi saima kallon Mairo da yayi yace “bakida lafiya ne hala?”
kin masa magana tayi saima faman cin abincinta da take tana sauke ajiyar zuciya, 

Story continues below


momi ce ta kalleshi tace “k’onewa tayi da ruwan zafi shine take fushi”
“ayyah sorry kijin injin bata jimu ba?”
“bata jimuba zafin daine ya raɓeta”
kanta ya shafa “sannu kinji?”
kai ta ɗaga masa tana aika lomomi, 

suna haka Usman ya fito ɗakinsa ya nufi kofa.
kiransa momi tayi “Usman”
“na’am Momi”
“dan Allah jeka ɗaki ka ɗauki ATM ɗina kaje nan Damary plaza ka siyo ma Maryam kayan sawa”
“owk momi”
da sauri ya nufi upstairs. 

tashi Mairo tayi jikinta na rawa tace “zan bishi mumo ina zuwa”
momi kamar tasan plan ɗinta ta zauner da ita “a a ba yanzu ba ba kasuwa zaije kuma ba daɗewa zaiyi ba” 

da kuka tace “thom”
ta sunkuyarda kanta tana hawaye.
Qasin ya shafa kanta yana murmushi “yi hakuri bari ranar da nake free sai muje yawo ko ki zaga gari?” 

kai ta ɗaga mishi ba tare data kalleshi.
murmushi momi tayi ta kalli Qasin tace “Qasin ya akayi da batun kwangilar?”
“na karɓa ni da kaina zanyi kuma baza a samu matsala ba insha Allah”
daɗi sosai momi taji “Allah ya taimaka ya shige maka gaba” 

tashi Qasin yayi ysns faɗin “Amin momi bari naje part ɗina nayi wani aiki”
kai kawai momi ta ɗaga mishi ya fice rik’e da laptop.

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*13* 

da ɗare Usman ya kawoma Momi kayan (tufafi) data aikeshi ya siyo,
aiko murna gurin Mairo ba’a magana sai tsalle take tana wani shafar tufafin tana jefasu sama tana rawa.
duk wani bachin rai dake ranta ranar gushewa yayi sai faman godiya take yima momi.
tun abun naba Momi dariya har ya koma bata tsoro ganin irin murnar da take kamar zata haukace sai faman uhu take, tana daredare harda hawaye, 

momi dai da taga ba kanta baro mata ɗakin tayi ta sauko k’asa,
nan ta tararda Qasin yana aikin rubuce2,
guri ta samu ta zauna suka soma fira. 

Mairo na jin muryarsa ta kwaso tufafin ta nufo downstairs da gugu tana faɗin “Qasin kaga tufafina da-”
kasa karasa maganar tayi saboda wani mugun kaye da tasha saman tile aiko nan kuka ya chaja salo ta koma yin na gaske, 

dariyace tazo ma Qasin haka ya matseta ya nufeta ya tadata tsaye yana bata hak’uri yana murza mata gurin data gimu. 

momi kan faɗa ta hau yi mata “yarinya ba kai sai bak’ar hauka tun ɗazu take murnar tufafin nan kamar mahaukaciya kekan kauyenciki yayi yawa Maryam”
Qasin na dariya yace “haba momi koni ai murna zanyi inna samu sabon tufafi zuwa fa tayi ta gwada min ko?”
kai ta ɗaga masa tana kuka, handkerchief ɗinsa ya ciro yana share mata hawaye.
“ya isa haka jeki gwada tufafin mugani suna miki kyau”
da ininniyar kuka tace “thom”
ta nufi ɗaki. 

       ”’ *   *   *”’
tun daga lokacin Mairo bata k’ara saka tufafinta na kauye ba saidai wayanda momi ta siya mata,
kuma ba laifi Usaman ya iya zaɓi dan duk tufafin data saka saisun yi mata kyau sun k’arɓi jikin ta,
kyau ta ma ba laifi da farinta sai kara fitowa yake ga gashin kanta kullum sai momi ta gyara mata shi, 

taci maikyau tasha maikyau tasa maikyau wasa wasa cikin wata 2 tayi bulbul kamar ba itaba,
aiki kan yanzu Mairo ta ɗan fara sabawa dan kullum tare da momi suke haɗa breakfast kuma duk wani karamin aiki ita momi take sawa tayi tun tana fushi har ta gaji ta daina sai in taje ɗaki ta rika kuka tana zagin momi da cire mata albarka, 

Story continues below


zancen guduwa yanzu ta daina tunda taga momi bata bari a fita da ita kuma in zata fita bata zuwa da ita babu yadda batayi ba momi tak’i yarda duk wata dabara ta ta saita rushe ta daina ma yima momi zancen ta hakura, 

*_3 months later….._*
yau da far’ah Mairo ta tashi saboda tayi markin Gwaggo,
koda Momi ta shigo ta tasheta zaune ta tararda ita harma tayi alwala tana sanye da hijab,
da mamaki momi ta shiga bathroom bayan ta ɗoro alwala ta fito ta nufi waduraf tana faɗin “Maryam ya akayi yau kika rigani tashi?”
carbi ta nunawa momi tana wani gyaran murya kamar wata babbar mace wai ita mai tasbihi ba a magana, 

“hmm Maryam manya”
momi ke faɗar haka tana k’ok’arin ɗaura zane,
hijab tasa ta shimfiɗa carpet ta rik’a carbin tana salati har aka tada sallah sannan suka bi zan’in masallacin dake kusa dasu,
suna karewa bayan suyi yan addu’o’e suka nufi kicin. 

*_8:45am_……*
Mairo ta shiga jera breakfast a dining sai tsaki take tana faɗin “mumo yau munyi rana”
tsayawa tayi tana kallon agogn dake manne gefen gurin tana tunani yadda momi ta koya mata, 

ta daɗe a tsaye tana kallon agogon ganin bata tuna ba yasa ta shiga shirmen ta “kinga fa mumi har wannan mai laulaye tayi (8) da mai k’afa ɗaya (4) da mai kai sama (9) gaskiya munyi rana yau”
da dariya momi ta fito kincin ta nufo dining tana faɗin “waike Maryam yaushe zaki daina wannan shirmen naki ne? ke kullum ana koya miki abu amman kamar kara toshe miki k’wak’walwa ake”
turo baki tayi ta nufi kujerar data saba zama ta zauna,
momi bata sake cewa komai ba ta shiga zuba mata abincin harsu Usman da Nura da Siraj suka fito suka nufo dining, 

bayan sun zauna kowannensu ya shiga zubama kansa,
har suka fara ci Mairo bata ci nata ba sai kunbure2 take tana harararsu duk da momi ce take son ta harara amman ba dama.
babu wadda ya tanka mata sai Siraj dake k’ok’arin zaunawa,
“waike lafiya kike hararar mutane?”
saida tayi kwafa sannan ta kalleshi tace “ina ruwanka dani”
tashi yayi da niyar ya doketa momi ta tareshi “ai tace maka ina ruwanka da ita bai isaba?”
“tho momi baki ganin yadda take hararar mutane”
“ba da kai take ba ni take son harara bata da dama saboda nace bata gane agogo”
komawa yayi ya zauna yana dariya “LOL yarinya aike kullum liki minandak’u ce kulli yaumin ɗifɗif”
kifa kanta tayi da dining tana kuka, 

momi ta kalleshi da siffar masifa “wai Siraj mi yasa kake wasa da ita ne bafa tabashiyarka bace mahaifinta da naku uwa ɗaya uba ɗaya suke”
hannu ya ɗaga “tho momi kice ta daina wasa dani”
“ai kai ka soma wasa da ita gashi har sauran suna son yi”
jan zib yayi a bakinsa alamar bazai kara cewa komai ba,

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*14* 

sai a lokacin Mairo ta ɗago kai ta soma cin abinci, 

_GOOD MORNING EVERYONE_
yau da abunda Qasin ya shigo dashi kenan fuskarsa ɗauke da murmushi ya ware hannayensa hannunsa ɗaya rike da wasu file.
duk juyowa sukayi suna kallonsa rabon da suji muryar irin wannan ta farinciki daga gareshi harsun manta,
wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar momi dan tasan duk yadda akwai abun farincikin daya faru, 

yana karaso ya mika ma momi file ɗin yana faɗin “lafiya kuke kallona hakane?”
murmushi sukayi suka ci gaba da cin abincisu dan sun san ko minene dole a fasa kwai suji, 

a rikice momi take karanta har tana tsalleke wasu saboda daɗi tana kare karantawa ta mike tsaye ta rumgumeshi idonta cike da hawaye
“ai daman na faɗa maka Qasin duk ka ɗauki hawarana bazaja taɓa jin kunya ba kuma ka gani”
rumgumeta yayi yana dariya “haka ne momi na”
ko wannensu kasa cin abincin yayi sai murna suke suna yaba masa suna rumgumarsa, 

Story continues below


Mairo kan ido ta sakar musu kamar tana cin abincinta dan ita mahaukata ta ɗaukesu tunda bata gane abunda suke yiwa murna, 

saida tayi tsaki sannan suka tuna da tana gurin 
ɗagata momi tayi saboda murna ta tsayar da ita saman dining tana faɗin “me kike yiwa tsaki yata? yau ranar farinciki cefa”
“to ba duk kunata murna ba kuma kunk’i ku faɗa min dalili”
“ayyah to yi hakuri bari na faɗa miki yayanku ne yaci nasara akan kwangilar da aks bashi har mutumen ya yaba masa da kalamai masu daɗi”
“to minene kwangila?”
“sashi akayi yayi gini sai kuma yayi sa’ah shine muke murna”
fashewa tayi da dariya “hahaha nima Qasin nayi murna”
“to ai ba haka akeba uhu ake ana tuma”
aiko kamar jira take ta soma yin sama tana yin kasa saman dining, 

juyawa momi tayi tana kallon Usman da yayi maganar “kasanfa bana son iskanci dan ba hankaline da ita ba”
juyowa tayi ta sauke Mairo tana faɗin “ke kuma kinsan na rabaki da kiran sa Qasin ko to daga yau karna sake ji”
bata fuska Mairo tayi ta soma kuka, 

dafata Qasin yayi “haba momi miyasa zaki sata kuka yaufa ranar farinciki ce”
share mata hawaye ya shiga yi yana faɗin “yi hakuri yi shiru kinji?”
makkale kafaɗa tayi “ni bazanyi shiru ba”
“aiko in bakiyi shiru ba ba zanje dake yawo ba kindai san kinfi kowa son yawo ko kina so naje dake?”
kai ta ɗaga tana share hawaye.
Qasin yace “good to ysu zanje dake kodan farinciki danake”
da far’ah tace “yanzu ko?”
“a’a sai an jima inna shirya harda tufafi ma xan saiya miki kiyita tsalle”
wata irin dariya ta saki tana tunowa da momi yasa ta karasa ba ta rufe baki, 

ɗagowa yayi yana murmushi ya kalli momi “thank you more. momi”
“ur welcome Qasin nafika farinciki”
“momi ai har a tv aka nuno dan da yan jarida yaje dan yayi zaton zan to zarta”
“kwata2 yau bamu kunna tv ba bamu gani ba”
“ai tun jiya ne da dare ai”
hannu momi ta daga “oh nidai Alhamdulillah ai tunda anyi nasara” 

     ”’ *   *   *”’
ranar wuni sukayi suna farinciki momi harda rabon kuɗi ta rikayi ko abincin rana ma kasa ci tayi saboda farinciki, 

*_2:30pm……_*
Qasin ya shigo sanye da kananan kaya,
zaune ya tararda Mairo tasha doguwar rigar fakistan momi ta mata farkin ɗin kanta kamar wata balara sai ɗan gyale na abayar da take rike dashi,
ta wani hakinci kamar wata princess ga bakinta yasha mai yar girace kawai momi batayi mata ba, 

tsayawa yayi yana kallonta kamin ya kai hannu yaja hannunta su taɓe “eyye yarinya haka momi ta gyara ki?”
da sauri ta tashi tsaye “eh daman kai nake jira tun ɗazu”
murmushi yayi “to yayi kyau bari naga momi sai muje kinji?”
kai ta ɗaga masa ya nufi stairs. 

bai daɗe ba ya fito ba mairo ta mika masa hannu ya rika suka fice yana yaba kwaliyarta,
suna kaiwa parking space ya buɗe mata giɗan gaba ta zauna shi kuma ya shiga driver seat. yayima motar key suka fice, 

wuni sukayi suna yawo duk gurinda suka ga wani abun kwadayi sai ya tsaya ya siya,
Qasin yasha dariya saboda Mairo take murna kamar wata taɓɓabiya. 

*_4:52pm….._* 
suka nufo gida Mairo sai surutu take masa shidai tun yana dariya harya koma murmushi, 

daf ta zasu shiga gida ta tuno da Alkawarin da yayi mata na siya mata kaya,
aiko nan tasa mai kuka dole ya juya ya nufi Dubai mall. suna isa ta shiga k’ok’arin rigansa fita amman ta kasa dan bata san yadda ake buɗewa ba, 

saida ya fita sannan ys buɗe mata kofar ta fito sai dariya take tana yaba kyaun gurin,
suna shiga ta nufi wani gurin saida ya riko hannunta suka nufi sashen yara,
sannan ya saketa ya ɗauki basket ya mika mata ya riko kunnenta “karki kuskura wuce ɗauko kala uku uku kawai zaki ɗauko kinji ni ai?”
kai kawai ta ɗaga mishi badan ta fahimci mi yake nufi ba dan hankalinta nacan gurin kayan data gani, 

Story continues below


haka ta nufi kayan tana wani leko harshe kamar karya tana shafa kayan.
tafi karfin minti 20 tana duba kayan sannan ta ɗauko kala biyar ta nufoshi tana dariya “duba kaga suna da kyau sosai”
ɗaya bayan ɗaya ya rika dubasu “haba Maryam har huɗu keda nacewa uku?”
“nidai su nake so”
“a rage kinji?”
lake kafaɗa tayi “a a nidai duka” 

bai sake cewa komai ba ya nuna mata gurin biyan kuɗi “ɗauki ki kai can”
da sauri ta ɗauki kayan ta rigashi isa,
ana cikin lissafi ta ɗauko wata riga ta ɗora “harda wannan inaso”
bakin baki Qasin yayi yana kallonta can dai yaji tsoron ta sake ɗauko wani abun ya nuna mata kofa “Maryam jeki gurin mota ki tsaya harna fito kinji?”
ba musu ta fice ta barshi, 

tsaye tayi jikin motar tana wasa da hannayenta duk wadda zai shiga saita faɗa masa akwai kaya masu kyau a ciki,
wasu basa kulata wasu kuma suyi ta dariyarta,
tana haka Yarima yazo shiga cikin wasu tufafi na alfarma fadawansa na take masa baya,
nunashi Mairo tayi tana faɗin “kai ma kayi sa’ar zuwa nan kayan suna da kyau”
kwatakwata bai lura da itaba sai a lokacin ya juyo ya kalleta a ransa yana _wani sabon tsari suka samune nasa yara sunayiwa mutane welcome_
suna haɗa ido Mairo tayi waje da ido “lahhhh kaine”
kayanshi ta shiga shafawa tana ɗaga masa gira.
can ta shaa nata kayan tana juyi tana rawar kai “ni ka gani yanzu kaya masu kyau nake sawa” 

shikan kallonta kawai yake yana tunanin gurin daya santa. dan jikinshi yana bashi ya santa,
saidai ta ɗan kwanta masa lumshe ido yayi yana tsusar hot pink lips ɗinsa faɗawansa dai sai kallonsa suke da k’warorin mutanen dake guri 

bai buɗe idon ba sai da ya tuna da murmushi ya rika fuskarta “ya akyi kikayi kyau haka? waya kawoki nan?”
saida tayi dariya sannan tace “yaya kuma momi ce tamun kwaliya”
“wane yaya?”
kamin ta bashi amsa Qasin ya fito ya nufosu fuskarsa ɗauke da mamaki. 

nunashi Mairo tayi “gama shi nan”
kai ya ɗaga mata yana wani shu’umin murmushi.
Qasin na karasowa Yarima ya mika masa hannu “thanks to yhu once again My Men for the contract”
kallon hannun kawai Qasin yayi fuskarsa babu yabo ba fallasa ba tare daya amsa ba yace “ur welcome the perfect one”
murmushin fuskar Yarima ne ya kara faɗaɗa,
Qasin bai saje kylashi ba buɗewa Mairo mota “ke shiga muje”
da sauri ta shiga tana ɗagawa Yarima hannutana sama byebye. 

da wani irin karfi Qasin yaja motar har saida Mairo taji tsoro,
Yarima yayi tsaye yana kallon motar har suka bace masa.

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:40 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡* 

*BY*
  
    *_KHADEEJA CANDY_* 

*15* 

tunda suka shiga motar Mairo kasa magana tayi saboda tsoro saima rike bel ɗin motar da tayi,
shima bai tanka mata ba saida suka kusa isa gida sannan ya soma magana ba tareda ya kalleta ba “ina kika sanshi Maryam?”
shiru tayi kamar ba zata amsa ba saida ya sake maimai tawa sannan tace “can gida na sanshi harda kuɗi yake bani da goribar bunni ba na taba faɗa maka wani yaban goriban bunni ba?”
kai ya ɗaga mata “eh ina ya haɗu dake?”
“can gida”
“gida ina?”
daidai nan suka iso gida yana yin parking ta yinkura zata taji bazata iya buɗewa ta juyo ta kalleshe “buɗe min zan fita”
yana kallon kallon fulawoyin gidan yace “sai kin faɗa min gurin da kika sanshi?”
kamar ta fasa kuka tace “bana ce maka can gida ba”
sai a lokacin ya kalleta “to ai baki min bayani yadda zan gane ba”
ganin babu sarki sai Allah dole tasa ta faɗa masa tun farkon haɗuwarsu, 

“to tun daga lokacin baki sake ganin shi ba sai yanzu?”
“eh nidai buɗe min na fita”
“to ya akayi ya ganeki?”
“nidai ba shine ya ganeni ba ni ban saniba”
bai sake ce mata komai ba ya buɗe motar ya fita,
ya zagayo gefenta ya buɗe mata ta fito da guɗu ta nufi parlour. bayan ya rufe motar ya rufa mata baya, 

parlour suka tararda momi da gudu Mairo ta faɗa jikinta “kinga yaya ya simin mai kyau”
dubawa Momi ta shigayi tana yabawa “eyyye yar yayanta duk ke kadai?”
“eh ni kuma na zaɓo kuma mukaje yawo”
“amman gaskiya yana ji dake to injin kin masa godiya?”
“eh na masa ko yaya?”
kai ya ɗaga mata yana murmushi
“eh kinyi bama iyaka”
“naji je ɗaki ki aje”
“to”
tashi tayi tana dariya ta nufi ɗakin. 

momi ta kalli Qasin tace “magana nake son muyi dakai Qasin mai muhimmanci”
agogonsa ya kalla “owk momi amman fa kamar lokacin Sallah yayi”
agogon ɗakin momi ta kalla “inaga ma an soma sallar wani gurin jeka masallaci kawai nima bari na tashi nayi sallah gobe mayi maganar”
‘to’
kawai yace ya tashi ya fice jiki yake baya son maganar duk da bashi da masaniya akan abunda zasu tautauna, 

*_washe gari….._*
da safe Qasin bai lek’a part ɗin momi ba ya wuce gurin aiki,
bai shigo gidan ba sai dare part ɗinsa ya fara wucewa saida yayi wanka ya sauke gajiya sannan ya nufo part ɗinta,
zaune ya tararda momi tana hamma Mairo na kasan carpet tana bachi Usman da Nura ma duk bachi suke saman kujera,
ta dasu Qasin yayi yana faɗa “momi sai ki rika barinsu suna miki bachi saman kujera manya dasu kuma maza”
“ai nasha musu magana har na gaji”
masifa Qasin yayits musu da suka farka basu dai ce masa uffan ba daya kare suka tashi kowane ya nufi ɗakinsa, 

tsaki yaja ya zauna yana faɗin “shi yasa Siraj yake burgeni wlh shi halinsa da ban yake”
momi tace “ai Siraj yasan kansa gadai wata nan da take son biye musu”
kallon Mairo yayi “gaskiya momi ya kamata asa maryam makaranta dan inaga Gwaggo ba k’arɓarta zatayi ba”
“eh ai inaso ma maka maganar daman jira nake naga yadda zaman zai kasance dan kar asata daga baya tace abata yarta amman kaga yanxu tunda bata tambaya ba ai sai a sakata”
“ina gafa Gwaggo fushi ne tayi kinga ai ko waya bata kira duk da son da take yiwa Maryam”
“fushi kan ai da gani” 

momi na yunkurin tashi Qasin yace “momi wace magana ce kikace zamuyi jiya?”
da idon bachi momi ta kalleshi “bachi zanyi ba wani magana yanzu yau ma ko leko nan bakayi ba bakayi breakfast ba ka fita”
“eh kirana akayi shiyasa kuma tunda naje nake aiki sai da magriba na samu kaina”
“to nidai bachi zanyi kuma ko gobe bani da time dan gobe abbanku zai dawo”
tashi yayi yasa hannayensa aljihu yana faɗin “Allah kawoshi lafiya ni bari naje na kwanta”
“to saida safe ta damun maryam kamin ka wuce”
ɗaki momi ta nufa tana hamma, 

a hankali Qasin ya shiga data ita ganin bata motsaba yasa shi girgiza ta. ciki magagin bachi ta rika faɗin “mumi kinga Siraj ko”
“ba Siraj bane nine tashi kije ɗaki ki kwanta”
sake komawa tayi bachi haka yasashi data ita tsaye yana girgizawa “ke momi tace kije ɗaki ki kwanta”
“aa barni ni nan zan kwanta”
girgizata ya rikayi da karfi daker ya samu ta buɗe ido aiko tana ganin shine ta kara zube masa, dole ya ɗauketa ya kaita ɗakin yayiwa momi saida safe ya fuce. 

*_4:21pm….._*
momi na zaune ita da Siraj suna fira sukaji an buga k’ofa. kofar momi ta kalla tace “waye?”
shiru akayi ba amsa nan ta kalli Siraj “jeka duba”
tashi yayi ya nufi kofar yana buɗewa yaga Yarima tsaye cikin kananan kaya yasa hannayensa ciki aljihu sai kanshin turare yake fuskarsa na kallon wani gurin.
kasa masa magana Siraj yayi shima kin juyo fuskar yayi ya kalleshi,
juyowa Siraj yayi ya nufi ɗakinsa tambayarsa momi ta shiga “lafiya wanene?”
yana gaf da shiga ɗakin yace “gashi nan waje nima ban sanshi ba”
tashi momi tayi ta nufi kofar, yadda Siraj haka ita ta tararda shi tsaye murmushi momi tayi tace “Yarima ne yau a gidan?”
sai a lokacin ya juyo ya kalleta shima fuskarsa ɗauke da murmushin “nine Momi”
“kuma ka tsaya a waje”
“to ai ba amin iso bane”
kai momi ta girgiza “Yarima ai naga gidan ba bakonka bane gidan nan ai gidanku ne tunda kai ɗana ne”
momi na cewa haka ta juyo ta dawo cikin parlour.
kai ya ɗaga yana karewa bakin kofar kallo kamar sannan ya taka kafarsa ya shiga cike da takama, 

yana zaunawa momi ta dire mishi drinks.
“yau Yarima an tuna damu? kodai wani abun ne ya kawoka?”
da kanshi ya shiga zuba drinks ɗin yana faɗin “ziyara ce na kawo muku momi”
momi tayi dariya “aiko ka kyauta ya aiki to ya kuma gida?”
saida ya kurɓa drinks ɗin kusan so uku sannan yace “Alhamdulillah”
kallon parlour yake ta ko ina kamar mai neman wani abu.
can ya kalli momi yace “gaskiya momi Siraj bashi da tarbiya”
ko kaɗan momi bata jidaɗin maganar ba amman haka ta haɗiye tayi murmushi “yayan zamanine sai hakuri kannen naka”
taɓe baki yayi ya juyarda fuskar wani gefe.
momi zatayi magana Mairo ta fito kicin rike da abu a hannu tana faɗin “mumi kinga ni duk na wanke shuwakar kuma ta fita” maganar take tana kallon kujerar da Yarima yake zaune dan bata gane ko wanene ba,
momi tace “thom naji jiki gani nan zuwa” 

yana juyowa suka hada ido murmushi ya sakar mata.
waje Mairo tayo da ido ta buɗe baki ta nufoshi da gudu rike da shiwakar da sauri momi ta tashi tsaye kamin ta rikota ta rumgumeshi har cup ɗin dake hannunshi ya faɗi.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like