Advertisement
Ruwa aka daura ma zarah ta sha na kusan rabin awa sannan ta dawo hankalin ta
“Ganin mumyn ta sosai ya girgiza ta tasan har duniya ta nade da kyar mumy zata sake dawowa dai dai in ma zata rayu kenan..
Tace na shiga uku wayyo Allah na” kukan takaicin duniya ya hadu ya mata yawa ta rasa me ke mata dadi
Ita kanta abubuwan da suka yi sun dame ta she need someone close to her amma in ta ce majeed tasan he wont even come zai ce baida lpya shima
Haka ta daure ta kira mum tana kuka wee wee ta gaya maga abunda ya same mumyn ta…
sai ta zaune tare da ita duk wani kulawa da lallami wanda zai bata karfin gwiwa tana bata har suka samu suna fuskantar mumy rabi da bata iya komai sai kuka da nadaman zuci..
Da kyar maganan ke fita sabida karkacewan bakin ta Ita kadai ta san hatsarin nan eznah ne musu ba wai haka kawai ya faru ba…
Advertisements
amma sam ta kasa furta wa sai rarrashin su mum keyi..
amma ai wannnan hatsari ne bai kamata ace ya bar zarah a wannan halin ba ..so ko gida bata kai ba ta sa aka kaita wajen sa . ..
Daga nan wajen su suhan kuma sai wajen 6.09na yamma motar su ya iso abuja motar baida kyau so duk jikin su yayi tsami sun galabaita ga shi sun kwana sun wuni ana tafiya
Ciwon ciki ke damun suhan amma tana kan daurewa Sai suka tsari keke napep zuwa anguwan su mum
kankat aka musu da kudin su sabida dubu daya ne da ganan kowani mutum dan dole suma bada 3k aka kaisu anguwar maitama…
“Da masifa mum ta shigo..tace kana bani kunya majeed yo ahakan Allah zai ji tausayin ka ya magance maka matsalan ka bayan kana take hakkin wata?
yayi shiru abun sa bai ce komai ba
Advertisements
mum don dole ta sauke murya tana duban mood din nasa tace” i know suhan is important amma let bygones please.. ai munyi bakin kokarin mu ko my boy ?sai ka jira sakamakon addu’ar ka bawai kana zama kan hakkin zarah ba .. 1
STORY CONTINUES BELOW
A sanyaye Yace toh naji mum ita zarahn suna ina yanzu?
Da kyar ya amsa don sam baijin karfin jikin sa ko kallon mum bai yi ba ya dau car key dinsa ya fice ya barta…
Su suhan na bakin gate din mum tasa riga da zani da mayafi amma baba majeh bai bari ta bude fuskan ta ba complete
Security ke interogating din su baba ibrahim na bada amsa…
Kirjin ta ne ya buga ganin Mace mai ciki kamar suhan tun kan mota ya tsaya ta soma bada direction ma driver bai gama parking ba ta fito agurguje tayo kansu
Ba tsayawa tambaya ko gaisuwa kan suhan taje direct ta yaye mayafin da take kare fuskan ta da shi ta watsar kasa
“In shock ta ta tsaya.. suna kallon juna tuni gangar jikin su ya amsa
“idon mum take ya kawo ruwa baki na bari ta soma cewa suhan..su..hannn.tana nuna ta da hannu cikin rudani
Itakan ta suhan gama rudewa ba abunda take illa numfashi sama da kasa””jin mum na dada ambatar sunan ta ya sa ta gaggawtawa a firgice ta fada jikin mum ta kankame ta tare da sake wani rin fitinannen kuka….
“Kowa ya tsaya yana kallon su mum na kuka suhan na yi..mum muryan ta har baiya fita wajen tambayar ta ena ta shiga ta barsu
cikin tsananin jimami da rudewa take shafo crying face dinta tana cewa ” na nemeki yata na kasa samun sukuni meya same ki waya dauke min ke?
Suhan Bata iya magana ita kam har su baba suka zo nan wajen da su mum suke..
Mum ta juya ta dube su da kyau sai yanzu ta ke gane kamar sa
…ta kamo suhan ta kankame ta daga gefen ta tace dama kaine ka sace min yata?
Fushi da bacin rai na so ya soma sauko ma mum don atsawace tafada tana hawaye”
tace kaine ka sace ta? ka gaya min ko na sa a harbe ka anan…
..da kyar mum ta kawo fahimta da sanyi ma zuciyan ta ta kyale su
Dam ta riko suhan ta hana kowa taba ta sai ma kokarin boye ta take ajikin ta kamar itama bata hankalin ta…
“Suka zauna a falo baba ibrahim ya daure sosai amma sai ya cigaba da dauriya don sai da yanzu hankali ta shigo masa yake jin kunyar Mum..
Ogah maje ne yayi bayani mai kama hankali cikin nitsuwa ma mum..
Har sai da tayi sanyi sannan baba ibrahim ya nemi garafa yayi kukan takaici da nadama
Sannan suka hadu suka bata labarin kalubale da tashi fadi da sukayi akan suhan Da kuma cikakken labarin abubuwan da suka faru da ita tun daga bacewar ta ..
“Majina da hawaye suka hadu ma mum suna sauka lokaCi guda idanun ta suka kumburo tsaban kuka da tausayin suhan..
“Ana labarin tana dada kallon ta tana tunanin duniya cikin kukan tausayi kaf saida zuciyan su yayi sanyi…
Mum ta sha mamakin da akace mata zarah ne tayi duk wannan abun she grow soo hot and angry
STORY CONTINUES BELOW
bata iya nuna fushin ta ba amma a ranar sai da ta nuna matukar bacin rai da debewar albarka a kan zarah…
Ganin suhan yadda ta jeme ta rame ba sai an gaya mata ta wahala ba jikin ta ya bata sosai….
Godiyan ta ma Allah daya sa suhan na dauke da cikin ta har yanzu tana tuno what if ta haihu wani wajen yaron ya bace?
“Kan kace kobo aka ba su baba masauki da duk wani convenince ta kama yar ta suka je chan daki…”
mum ta dube ta cikin tsananin tausayi tace ” majeed yana zuwa yata ki kwanta ki huta insha Allahu shi zai zo ya tashe ki uuhmm?…mum bata ma karasa rufe baki ba suhan ta mike ta haura gado ta kwanta ta rufe ido alaman baccin jiran majeed take
…mumy ta yi murmushi ta dan girgiza kai
Nan ta shirya tsaf zata koma asibiti don itama ta matsu ta sanar da majeed suhan na jiran sa a gida kuma ta samu ta gamu da zarah..
Shi kuwa tunda ya fice baijin komai aransa
yau ne rana na farko da ya soma jin zai sassauta tunanin suhan dinsa ya fuskan ci reality har Allah ya nuna masa ita…
har ya kai asibiti yana muhawara da zuciyan sa akan haka yana bata hakuri ta barshi yayi adalci..
An kashe wayar ma bata san ankashe ba ta daura a hannu akai ta na neman kwala ihu
Mumy rabi dake motsawa da kyar daga kan gado tace me ake ciki zarah?me suka ce miki yata. Da kyar maganan ke fita
Cikin masifa ta juyo tace i dont know just shut up mumy…kiyi min shiru ..
Tayi nan tayi chan tace” shikenan I lost everything sun cireni a matsayi na a companyn hadin kai da minister ..
Wani birkitaccen kuma kuntaccen kuka ta fashe da shi..sai da muryan ta yayi kamar ba nata ba
Kukan data keyi ya sa mumy shiga wani yanayin mai wuyan fassara
tace zarah dear ki nitsu ki saurare ni
A zuciye cikin kukan tace :bazan nitsu ba.. ba abunda zaki gayamin u started all this ..meyasa baki ce min ba hakan zan yi rayuwa ta ba u ruined my life mum.
Ganin hakan yasa Mumy ta dan kara sautin kukan ta itama tace tsaya mana zarah kiji abunda zan gaya miki ki saurarae ni dan allah…
Wani xuciyan yadada deben ta tace ni bana so naji komai” wannan bala’in da kike ciki bai ishe ki bane..bacin wannnan fitinan dake tare dake bai ishe ki ba kina so ki sake komwa gidan boka ko?me bokan naki ya tsinana min in banda asara.to ni na hakura yanzu mutuwan ma tazo ta dauke ni
STORY CONTINUES BELOW
Ni dai yanzu Ki daure ki nemi gafara ai naji boka da chan yana cewa idan har bamu yi confessing abubuwan damuka shirya ba toh bazamu gaji da ganin bala’i kala kala ba har mutuwar mu…
Ki tuba zarah kije ki gaya ma mijin ki komai
….a lokacin majeed na ji cos masifan da zarah ta yi dagon murya take tun daga bakin ward din ya soma tsinkayo muryan ta and the place is quiet cos exccutive ce ba mutane..
Amma da yaji fa abun yar tone tone ake sai ya dakata daga bakin kofa musamman ma daya ji sunan sa…
mumy tafara right from storyn yadda suka shayar da shi maganin ya so zarahn ya aure ta har badagalar da zarah tayi da maza …lesbianism… da ma abubuwan da bai taba tsammani ba na badala wanda take yi in taje businesa trip kan tayi achieving career ta uwa uba abunda suka ma suhan” tas tas sai da ta tuno ma zarah tana mata nasihan akan ta je ta nemo gafara ko zasu samu sauki a al’amuran su jar su mutu da atrocities kamar yadda boka ya fada …
“zarah ta rude gaba daya Kuka ta fashe da shi a sanyaye tana cewa na shiga uku mumy “”….duk wannnan nina aikata su ba karya amma yanzu i lost evrything babu ko daya daga cikin su sai mummunan sakamako ta yaya zan neme gafaran to? What am going trou is already a torture to me …zafin mutuwa ne kawai ban dandana ba….
“dum Majeed ya tsaya kunnen sa har na masa wani choiii duk ya gama tsimewa cikin matukar mamaki, rudani, razana da firgici bai bata lokaci ba yayi yunkuri a haukace ya banko kofar ya bankade ya shigo saida suka tsorata
“fuskan sa babu alaman rahma ya tsaya yana maida nishi a hankaki “Jikin ta ya bata kamar yaji su cos idanun sa da yanayin sa duk sun nuna…
Ta soma ja da baya a tsorace tana sum sum da ido tana waige waige jikin ta ya hau karkarwa…
“da sauri Ya kamo ta a firgice ya dadaa tsorata ta da very furiuoss and angry voice dinsa yace ” zarah,.. karya kike gaya anan ko gaskiya?duk ke kika aikata wannan abubuwan right” toh ena suhan?.ya girgiza cikin bacin rai yace nace ena suhan ena kika kaita tell me or i will kill you..ta razana sosai sabida muryan sa ma kadai ya isa ya sa hanji tafasa sai ta danna ihu….
Mumy ita kanta ta tsorata da yanayin su amma majeed baima jin su baki daya
…ya shakuro zarahn bai damu ba yana mata tambayar ena ta kai masa suhan…
” tana so tayi magana amma tsawan da yake mata ya gama firgita ta…Ta shiga kukan razana da firgici tsaban damkan tsanani da ya mata hannayen ta duk suka koma ja da zanen yatsun sa sun bayyana boroboro…ta bude bakin cikin shakurarren kuka tace majeed pls listen, ure hurting me pls stop it.. boka..boka ne ya san inda take ni wallhy ban sani ba ..wallhy i swear pls kisten to me maj..ee..sai tasssss tasss tasss maruka ke binta ko ena shikan sa baisan sau nawa ya aika mata marin ba earings din kunnen ta saida suka sinke suka watsu kasa
“Ta kasa zubewa akasa don radin yana sake ta ta hau jeka ka dawo cikin rudaden kuka
…shikam bai ya hankalin sa ko kadan ji yake kamar bai san zarah ba.
STORY CONTINUES BELOW
“har Sai da ta samu karaya a hannu da mummunan gurdewa a dunduniyar gwiwar ta.
Gashi ya buga mata ciki ko iya tsayawa bata yi ta dugun kune tana wayyo wayoo”muryan kukan ma ya tafi sai gurnanin azaba kanta na bugawa cikin azaban radadi tana karkarwa kamar kaza data ji dukan ruwan sama
Yana tsaye yana huci ko don kadan baiji ya kai geji ba ya kuma sa a ransa shi dai yau sai sun masa providing din matar sa kafin ya kyale su
‘Mumy tayi tattaki tana kan zagin sa tana kwashe masa albarka tace agaba na kake jibgar yata? Ashe baka da mutunci majeed ai ko mutuwa na jin kunyar idon mahaifiya Allah ya tsine maka… dan iska dan marasa tarbiya.. Da kyar take maganan amma sai ta dage tana kai …..to gashi ya zo zai kashe ki..na ma rasa me kika gani jikin wannan marar hankali,. mahaukaci dakika nanike masa duk shi ya samu a halin da muke ciki..
Allah ya tsine maka shege ja’irin yaro mugu azzalumi yata tafi karfin ka..
Ko kallon ta baiyi ba ,don it seems like saida aka fito fili da maganan yake jin sabon feeling din tsana mai tsanani a zuciyan sa ma zarah…
Bai sani ba asirin ne ya ke warwarewa a hankali sai yayi tunanin ko fushin da yake damun sa ne….
“da abun ya kaishi makura ya juya kan mumy yace mata “wallhy baku ga komai ba sai kun fito min da matata….
Mum din sa tun daga bakin kofa taji hayaniya tsakani da Allah ya zage yake ma mumy rabi rashin kunya…
Duk zagin da ta masa sai da ya ya rama,, a lokacin ma ta tsine masa shima ya tsine mata yace “kuma sai ya daure su idan basu fitar masa da matar sa….
Mumy rabiatu da ke kukan fitar rai tace ” ba zamu fitar ba Allah ya sa ta mutu namumin daji suyi gutsil gutsil da naman ta su wulakan ta ta…
Mum ta na bude kofa ta ga yana shirin dakan ma mumy rabiatu wani tsawan”
mum ta yi saurin wanka masa mari cikin tsawa tace queittttt…kamin shiru kana ji na.
Ya dauke kai
Mum”tana lura da yanayin dakin ga zarah a kasa kamar mutacciya tana wash wash..
Ta san yayi fushi sosai sai ta sa hannu zata jawo sa suyi magana ya bangaje ta cikin fushi..
ta soma kuka tace majeed meyasa baka ji ne wai kenan ba zakayi hakuri ba ?
Meyasa ka zo nan ka daga musu hankali ba gashi nan kasa marar lpya kuka ba? Ita meye laifin ta
Bai juya ba ya kalle mum ba amma kukan yake kokarin tarewa a hankali yace ” ita ta batar min da matata na mum..sun cuce.. ni kawai su gaya min inda take if not wallhy Bazan yafe musu ba.
In aka same nin me za’ayi dani i was once there for zarah mum
ya juya ya kalle su duka yace” im giving you just 1hr to provide her or else zuriar ku kaf sai na kulle ku sai na wulakanta ku ya juya ya fice abunsa ….
Abubuwan sun matukar damun mum sa ta juya cikin jimami ta karasa ta dago zarah dake nishi sama sama tana kiran sa yana ji ko ya juya…
“Tace zarah ya akayi haka?.why must you do all this to us me muka miki haka. Yau kinsa naji na tsane ki da naga suhan ahalin da kika jefa ta aciki…
Zarah me ye ban miki ba a duniya ki gaya min?meyasa zaki mana haka..why zarah…
Mum na kan magana ta hada har da da mumy rabi’atu dake ganin duhun mutuwar ta sama sama hankalin ta ya tashi sosai
wani karfin hali ya zo mq zarah su oan su ba su san ta rarrafa ta daddafa tayi waje ba
Yana daf bude car dinsa ta fado kasa haka ta kokarta dai ta sake ta shi tana dingishi
a Gaban sa ta zube a ragwabe ta kamo sa duk jikin ta na karkarawa gwanin tausayi
A chan kuma Ganin babu zarah ya sa mum fitowa da sauri tana dubawa cos a yadda take in akace zata iya motsi mai kyau mutum mai hankali bazai yarda ba
“..tace im sorry majeed ka yafe ni…i love you soo much wallahy ena son ka..pls listen to me i wil explain everything.
Bai jira ba ya daka mata tsawa
Dariyar takaici yayi yace “u want to explain ok, go on is it about my wife? Kin tuna inda kika kai min ita ko say it now
Cikin tsumayin kuka ta girgiza kai alaman ah’a..ita dai burin ta ya saurare ta
Tsaban takaici sai Ya lumshe ido yace ki tashi min anan kar na kashe ki na kashe banza ure very stupid….
Nan mum ta iske su daga nesa ta dakata
Daf fuskan ta ya zo yace i hate you… I hate you sooo muchhhhhhh zarah i cursed the day i met you muguwa azzaluma…
Kinci amanan kanki ur atrocities wull surely kill you..
maganan yayi mata zafi a raunane ta dago ta kallesa tace “majeed kar kace hakan nifa matar ka ce.
Yace “na sake ki…
Na sake ki saki uku”get out of my life i hate you
Zatayi magana ya hankade ta gefe cikin masifa yace “ohh wannan ya dame ki ne? Wait nooo ..actually it shudnt’ don dama ke a ba mata ta bacee u got ur lesbians friends ur businesss sexual secrificess kuje chan ku karata zasu baki rayuwan da kike so amma nafi karfin ki …
Kuka take a kasa a zube.. mum ta zo itama ta bi bayan sa ba bata lokaci
Ko tsayawa bai yi ba yana tuki tana binsa har gidan ta suka kai don raki barin sa ya sha kwana.
he tot ko zata masa fada akan ya sake zarah ne..
“amma ya riga yayi so bai damu ba don yanzu ba abunda ke turirin a ransa illah masifan sai an fito masa da matar sa…
Suna isa gidan yayi parking kan ta karasa ya fito ya tsaya bakin car dinsa ya daure fuska ya harde hannu…
Ya daure fuska yace mum”
Tace” hey,don talk to me like that have u lost ur senses?
yayi shiru ya sunkuyar da kai kasa idon sa suna so su ciko da hawayen takaici.. he just felt cheated and pained zuciyan sa na masa zafi sosai…
“majeed Answer me baka da hankali ko ..u dont shut am talking nace karasa hankalin ka ko?
Meyasa zaka sake ta just like that na so abi abun a hankali..
ya dago ya kalle ta a raunane yace zarah ba matata bace mum..ko na zauna da ita ma is still the same
I heard everything she was saying kuma na tambaye ta tace ya faru to me zan yi da ita….
kallo cike da kulawa mum ke masa amma sai ta daure tace me kaji?
Me ta gaya maka wanda har zai kai kayi saki uku one time majeed…
i mean nima sam bana kaunar wannan zaman naku but yin haka cikin fushi is not a good idea “a ranta tace and with the way she treated suhan i also feel same hatred for her amma we dont let anger control us hakuri ake yi …
Ya mata shiru gani yake har yanzu mum bata san wacece zarah ba..daga bisani ya soma bata labarin abubuwan da yaji a bakin su a asibiti a tsanake yake maganan cikin nitsuwa
mum…ta kawo salati don ita kam ta dauka zallan matasalar kishin ke damun zarah tayi hakan ashe abun ya wuce tunanin ta ,zina noo bazan taba bari dana ya zauna da mazinaciya ba
….now she know why majeed bazai taba iya hakuri ba..sam abun baiyi dadin ji ba
She cundnt say a word anymore ta shiga bashi baki tana kawo masa nasiha still akan yayi hakuri….
Ta sa shi don dole ya sauya yanayin fuskan sa suka shige ciki akan cewa tana so ya gaisa da baki ,bai san suwaye ba amma kawai sai yabi bayan ta afterrol yasan in yafita nan tunanin abunda zaima zarah da uwarta bazai barshi yaji kunne ba..
Suka zauna a falo dake kusa da site din mum sai ta sa aka kira su baba ibrahim da ogah majeh..
Tun Daga shigowar su yake binsu da kallo
Shikam ma ya mance da kamannin baban suhan gaskiya
amma baban suhan tsaf ya gane sai dai abu daya ya iya dagowa daga gare shi” tashin Hankali da uneaseness dake tattare a mood din sa don koya boye ana gani..
Suka zauna mum na gefen sa…
Yana shiru sai da Ta dan tsakure sa ya rusuna a ladabace yayi musu sannu da zuwa ita kanta mum ta gane bai dago su ba…
tace mahaifin suhan ne da aminin sa suka taho…
A dan rude ya sake kai kasa ya musu gaisuwa yana tuno face din baba .
STORY CONTINUES BELOW
shikuwa baba na ta jin kunyar sa amma shikam bai damu ba he tots ma akan maganan batar ta suma sukazo.
Already mum ta sanar ma anty jamila so tana hanyar zuwa daga inda taje yawon neman suhan…
Mum tace tun da zu suka zo daga lagos majeed ..
ba wani boye boye ta soma bashi labarin kafff halin rayuwar da suhan ta tashi ga ta san a bakin ta ne kawai zai iya nitsuwa yaji ba tare da yayi reacting ba…
Su baba ke dada sa baki suna masa bayani cikin nasiha burin su ya mance da komai azauna lpya
…take jikin sa ya hada zafi,sai kukam zuci yake cikin ransa Yace an haukatar masa da mata da ciki an wulakanta masa matar sa kamar wacce bata da gata a duniya an cuce sa”
bai ce komai ba amma yadda yake binsu da wasu irin Kallo yasa suke dada zafafa tatausasan kalaman su… its like yana shirin fashe musu da kuka ne amma sai ya cije idanun sa sun gauraya har sun hargitse da wutan rudani ji yake kamar ya je ya kashe zarah da hannun sa taji azaban da ta dandana Masa….
Baba yace ka yafe mini dana”.nasan duk abunda zanyi bazan wanke wanda nayi da chan ba.
na tafi na barku duka a lokacin da kuke matukar bukatata
Anan ne Majeed ya sauke nannauyan ajiyan zuciya shikan sa ogah maje daya ga yadda mum ke kokararin calming dinsa witout saying a word yasan lallai an taba zuciyan soja….altho ba komai suka gaya masa ba don wani abun sunsan bazai taba cirewa aransa ba
bayan baba yayi magana ne ya samu ya juyo
Anan ya maraice musu yace masa Kun bani labarin suhan amma baku zo min da ita ba kuke nufi ko?..
to ni ku gaya min inda take wahalan ya isa haka zan dauko ta da kaina
ena dai baku so ne nayi komai ma wanda suka cuce ni to kubani matata kawai zan hakura.
Mum ta dan ja kunne sa tare da sake karamin murmushi mai dauke da hawaye tace majeed bazaka dawo hankalin ka bane..” shiyasa taki gaya masa end of the story da yasan suhan na gidan bazai ma saurare su ba
Shi dai su baba yake kallo …yana jiran yaji mai zasu ce.
Baba majeh yace ai na gaya maka dana bata gama warkewa bane
mum Tace amma ena mai tabbatar maka daga nan in Ka kirata ma zata amsa maka….
Yayi dan karamin murmushin mamaki bazata ya mike tsaye yace da gaske kike yi mum?.ta gyada masa kai tana taro hawayen ta tana ganin yadda danta yake neman fita hankalin sa lokaci guda.
da sauri ya ja gefe ya shiga kira..yace suhan”
Ya soma tafiya a hankali yana kiran ta da dan karfi duk suka mike tsaye cikin fargaba suna so suga ko aikin zai warware da gaske
majeed sai duruwa yake kamar an masa kwatance yana kiran suhan…
Ta tashi a baccin amma tana kwance qamshin sassanyar turaren da mum ta fesa mata ako ena ajikin ta take shaka …
Can ta soma jin wani iri duhu duhu kamar bata duniya har sai da duhun ya mamaye ta sosai sannan ta soma jin muryan sa aciki ..
a zauce ta soma firgici tana motsa lips dinta zata amsa kiran sa shikuwa
Room by room yake bude kofa yana kiran suhan
…ai mum bata taba mun karya ba so suhan zata amsa ni…
Ya dada kwala mata kira
Daga inda take ta shiga numfashi sama sama tana girgiza kai a haukace
…tace innalaihhi wa enna ilaihi rajiun ta rike kanta da hannu bibbiyu idanun ta basu bude ba…
Yana sa hannu kofar data ke ciki ya tura tare da cewa suhannnnn” a firgit ta mike tare da amsawa tana sauke nishi da nunfashi kamar wacce ta tashi daga mummunan mafarki…..
STORY CONTINUES BELOW
1 seconds bai kara ba ya shigo, he wants to run and come to her but yana contampleting ita ce ko gizo yake gani….
Ta soma karkwarwa tana matukar so ta tashi amma nakuda mai zafi da radadi ya rike mata baya….
” shikam jikin sa yayi sanyi ya zuba mata raunannun idanun sa..Ta soma hawaye tana ganin sa yana tahowa a slow yana bata close looks mai dauke da tausayi da shakin kewa
Cikin kuka da shagwaba ta marairace tace sweetlove?
Bai amsa ba har Ya zauna gaban ta a da skare ya kamo fuskan ta yana kallon ta tana masa kuka”
Kan tace zata sake magana ya yi wani wana wawan yinkuri ya rungume ta tsam ajikin sa….
Yace suhan Ena kika je kika barni why did you leave meyasa kika kashe ni tun ena raye u know i can bear all this.. Suka dada kankame juna
Shiru ne ya dan ratsa wajen in banda muryan kukan ta ba abunda ke tashi
..ta shige kirjin sa sosai ya sa kan sa agefen wuyarta yana shunshuno qamshin ta yana dada cusa kansa cikin jikin ta
Duk jikin sa na bari itama sai dada cusa kai take kan kirjin Sa tana feeling dinsa ..ya matso ta gam kamar mai matukar jin tsoron za’a kwace masa ita..
tausayin kanta dana mijin ta ne ya lullube ta lokaci guda..
Ajiyan zuciya yake sauke wa a hankali yana shafo ta yana kuma dada jin yadda gangar jikin sa suke komawa dai dai”
yana hawaye a gefen Kafadar ta yace ” kiyi hakuri preety na kinsha wahala, i wont ever allow anything to touch you ni zan dauke ki na tafi dake har abada ba zasu sake taba min ke ba…
Ta kankame sa tana kan kwanciya jikin sa sai yanzu take jin ma ashe zata iya daure zafin nakudan dake damun ta cos she dont even wanna let go…
ya dago ta suka hada ido ya shiga share mata hawayen ta a tsanake ya hade bakin su waje daya yana sauke mata wasu lafiyayayun kisesss idon ta a lumshe ta tamke sa gam gam bayan ya zame lips din sa”yace kin yi hakurin?
Ta sunkuyar da kai Cikin sanyin murya tace” i miseed you ..bamu tare nayi kewar ka sosai zuciyana tana min ciwo in ka tafi ka barni.. he knows tana gayan abunda take ji yanzu ne”
. Duk tausayin ta ya kashe masa jiki ya cigaba da shafota yana matso ta yana kissing dinta ko ta ena…
Wani sabon salon kwanciyar hankali yake ji sai sauke ajiyan zuciya yake kamar yaron da yaga mahaifiyar sa bayan tsawon watanni hudu…
Shiru su kayi dukan su manne da jikin juna ..yayi yunkurin daga ta ya tambaye ta wasu abubuwan kuma yaga lpyar babies din sa..
Ko motsi mai kyau bata iya yi ba ta sa ihu mai dauke da radadin azaba tana riko kwankwason ta ..
a rude ya mike yace meye ne kuma suhan?meya same ki yana neman birkicewa.. ta damke hannun sa tana nishi sama sama tace ciki na ke min ciwo..hasbiyallah wa eneemal wakeell wayooh Allah na zan mutu….ta cize bakin ta …
Ya rasa meke masa dai dai nishin data ke yi akai akai ya sa kawai ya dauko ta a hannu duka suka ririrota kasa yana kiran mum…
Su mum Duka suka mike tsaye suna kallon suhan a hannun sa Na wash wash nakudan ne gadan gadan Ba bata lokaci sukayi kansu duk ya birkice yana mata sannu mum ne ta tallafo ta ta taya sa suka sa ta a mota
Ba bata lokaci sukayi asibiti da ita..
Tun a motan ta soma yunkurin haihuwa saboda haka minti 10 bata yi akan gadon haihuwar ba yara suka soma fitowa daya bayan daya farare sol da su manya manyan baby boys..
Daga waje majeed ko zama baiyi ba don Kamar baza’a fito ba haka yake ji
amma saida suka kimtsa ta babies din ta tsaf sannan aka sanar da kowa, su mum da anty jamila wanda ke faman fushi da baba ibrahim don sam taki amincewa da tubar sa sosai tayi fushi da shi..
STORY CONTINUES BELOW
Wajen majeed ena ka saka hakuran sa sun kasa rufuwa sai hamdala yake kaiwa wajen ubangiji.. today is suposed to be the worst day of his life amma sai Allah ya sauya masa da mafi alkhairin al’amari
lokaci guda ya dawo normal ya soma zumudin sa yayi nan yayi nan sam shikam baijin kunyan kowa
..murna yake an haifa masa har yaya biyu 2 more soldiers..
Tsakanin baba da anty jamila Har sai da aka kai wajen suhan kan anty jamila ta yafe ma baba ibrahim
kowa na mata son barka tana rike da hannun majeed a kunyace tana maida murmushi
su mum na tare da babies don har hawaye sai datayi musu tana zuba musu addua cike da albarka
ana hidiman musu hotuna da videos tana turawa ma yan uwan su kan kace wani abu atmosphere wajen ya sauya da kire kire da vedio calls cos yawancin wanda suke abroad alokacin suna zumudin ganin babies ..so funny and happy moments kowa na dariya..
A cikin sati guda zarah ta shiga wani irin yanayin rayuwa saboda duk inda ta zauna sai wajen ya cinye da wutar gobaran aljanu na ban mamaki,,
har sun kona mata wadrobes da muhimman safe din ta wanda ke boye kuma ita kadai abun ke shafa a hankali sai da suka kona mata sauran suturan ta kaf tq dawo empty in zata sa sai dai ta nema na mumy ga rauni da bandages na ciwon da majeed yaji mata ga yanayin sabon sauyin rayuwar ya zo da babu kudi babu kowa
Tuni board members suka karbe dukan qaddarorin zarah bai isa ba ma sai da ta hada da na mumy rabiatu hatta gidajen ta duk sun sayar sun biya board members millions of naira data gwasa
Duk dama ta so ta sauke dan sauran girman kai ta koma ma su faiza su taimake ta ko da da jinyar mumy ne amma hakan bai yuwa ba sai shiru sai su kayi ma kamar basu san ta…
Tasha mamaki sosai da mutanen duniya nadaman rayuwa da asara ya hau kanta lokaci guda ta dawo baka ta soma nuna alaman jemewa tsaban damuwa da tunani ga hannun mumy ya gama rubewa yana wari sosai kullum sai si zauna suna zage zage tana blaming mumy ..they both live frustrated and unhappy har Allah ya karbe rayuwan mumy..
Lokacin an gama hidiman sunahn babies din suhan sunci suna shaheed da mujaheed
A hidiman al’adan shamud karo na karshe
Yadda aka a zurta suhan lokaci guda haka aka ba yaran nan tarin dukiya da qaddarori…. 1
Majeed dama da kyar ya bari akayi sunan anan don duk yadda mum ta so ya hakura ya zauna a nan nigeria amma sam yaki yace shi bazai zauna anan kasar ba…
Da shike kaff su anty maimah da sauran yan uwa sun bashi Goyon baya akan is risky ya cigaba da zama anan tunda irin abubuwan dake faruwa kenan don dolen mum ta hakura majeed ya tattara shi da suhan a satin ta na biyu da haihuwa suka koma chan USA da zama..
Baba ibrahim da aminin sa baba majeh suke a gidan ummah
Suna running business tare cikin amintaka wanda suhan ta daura masa capital mai karfi a garin kaduna
Anty jamila tayi aure taje as second wife na daya daga cikin abokan uncles din majeed mai suna sadik ita ma yanzu tana rayuwan ta mai tsafta mai dadi a garin Abuja.
*After 5years..*
Zarah duniya tayi mata zafi rashin dukiya da atrocities duk abunda ta sa hannu akai sai ya zame mata babban asara ko mummnan jafa’i”
Wata uku da barin su suhan nigeria ta yi cikakken nadama bayan taga duniya duniya ya gan ta..tayi tattaki tajee neman su amma babu su
Bata yi tsammani ba kuma ta sha mamakin ganin aikan da majeed ya bar mata
kudi ne mai yawa da signed papers na marriage alimony
Kuma ya tabbatar mata da ya yafe mata amma bashi ba ita har abada..
Da kyar tayi fama da ciwon zuciya don tunda suka rabu take fama da kaunar sa na asali a zuciyan ta,
But She knew how majeed is, tunda har ya ce bazata sake ganin sa toh ba shakka hakan ne…
Sai Ta hakura da kudin ta daura tana neman aiki ga aikin amma ba karamin wahala take sha ba a hannun mutane karshe ma yan zauna gari banza suka shigo mata cikin dare suka kwashe sauran kudin sai da ta bar garin abuja ta koma kano da zama ta samu sukuni
Kusan abubuwan data ma mutane su ake mata she had no choice than ta koma ma Allah ta tuba …
Anan Ta hadu da alhaji sunusi mai sugar baki ne irin cikakken dan kanon nan kato ne kuma mummana
Shi kadai ya nami auren ta cos of sabon salon bakin jinin da take da shi a idon mutane so she had no choice sai ta aure sa ta zama masa mace na uku a jerin matan sa sati guda tayi agidan sa ya auro wata suka cika ..
A Hakan take zama a gidan ba korafi ga arziki kam dai dai gwargwado kuma za tayi aiki amma da sharadi “duk salaryn ta alhaji sunusi yana da kashi 70 aciki idan kuma ba za ta bayar ba toh yasa mata doka sai dai ta bari gaba daya
but she cant shike rufa mata asiri saboda duk barikan cin ta matan sa babu wacce take ragar mata a dole ta koyi zama da su….
Suhan takoma makaran ta after giving birth to a baby girl Najnah @ just 1year interval da haihuwar su mujaheed duk dama da kyar aka rike cikin saboda laulayi da rainon twins Lokaci guda a karshe ma saida mum ta taho US cos cikin ya shigo ne bazata kuma yaran suna da fitina sosai ride and die fans din majeed ne..
After then ,suka soma taking planning measures don tayi karatu she is now a member of the most reputable university in the world wato ‘avard university tana karanta couse mai taken international relations tana aji biyu.
1
HAKA _SAKAMAKON_ Kowa ya kasan ce”.
Quotes🌹
We dont always know who is our soulmate”but Its takes just one moment to love the the right Person, open your heart to feel and live freely#MAJEED
‘wake up to the call to the sound around you …live your dreams ur destiny awaits#SUHAN
the world is an echo what you send to it will be sent back to you in double return:#BABA IBRAHIM
..one wrong turn too many pitch blunders ” follow excellence and success will chase you#ZARAH
Sow the seed of patience and die today cos the whole world shall feel the serenity of ur soul
#UMMAH MARYAM.
+
majeed suhan da yaran su mujahed shaheed and najnah..happily eva after😃👌🏼
ALHAMDULLIH Anan muka tsaya godiya ta na musamman ma ubangiji ne
GIPHY App Key not set. Please check settings