TATTALINTA CHAPTER 11

Advertisement

TATTALINTA 

CHAPTER 11

*Ya* kyalkyale mata da dariya yana k’arasawa cikin kitchen d’in. Ba k’aramin haushin dariyar taji ba, toh ma wai me tayi da zai shigo ya dinga yi mata dariya, ta juya taci gaba da gyaran kyan miyarta tama fasa d’akko abubuwan. A bayanta ya tsaya bayan ya samu ya tsaida dariyar sa da kyar. Sak’alota yayi bayan ya sunkuya dai-dai tsawonta ya riko kugunta tare da kai mata pack a kumatunta yace. 
“Baby ya aka yi ne?!” 
Banza tayi mai ganin haka shi kuma yasa shi d’aukarta ta bayan ta ya fita da ita sai faman zillewa tak’e yi tana cewa ya sauke ta bata so amma yak’i har saida suka k’arasa kan kujerar parlor sannan ya direta yana dariya yace. 
“Baby me zaki yi a cikin kitchen ne..?” 
Cikin turo mai baki da yatsina fuska tace. 
“Ba girki zan yi mana ba, kuma duk an wani tashi an d’ora abubuwan a sama, kuna kazo kaga na kasa d’akkowa a memakwan ka d’akko min shine zaka tsaya yi min dariya.” 
   Kissing d’in lab6anta yayi tare da matseta a jikinsa, rarraba idanuwa yayi tare da had’iyar yawu tunowa da yayi yasan girkinta ya had’i yi yau yana jin bakinsa tamkar a lokacin ne yake cin abincin sabida yadda ya tuno da sanda bakinsa ya lalace da testing d’in gishirin girkin da tayi a gidan hajiya kaka. Yana manne da ita ta lafe a jikinsa yace mata. 
“Baby ki bari kawai na dinga yo mana takeaway bana son kisha wahala, kizo muyi zaman mu kawai…” 
“Amma Yaya gaskiya sai an sakko da kayan saman can sabida baxan iya d’akkowa ba yayi tsawo sosai.” 
“Baby kenan, toh za’a sakko dasu yadda zai miki sauk’in d’auka shikenan.” 
Cikin kwanakin da suka yi su biyu sunyi sune cikin mannewa juna, babu inda suke zuwa kullum suna gida a tare har Balqees ta saba idan bata jita a jikinsa ba jinta take yi tamkar mara lafiya har sai taji ta kusa dashi tukunna takejin relief. 
  Nadiya kuwa ana can ibadar ta kawai tak’e yi ko hotel bata fiye zuwa ba sai dai idan zata canza kaya amma kullum tana masallaci tana mik’awa Allah buk’atunta, sam bata gajiya da yin addu’a duk sanda zaka ganta a masallaci hannunta yana sama, idan ta shiga cikin rauda kuwa har sai taga an fara korowa tukunna take fitowa hakan yasa ko damuwa bata yi idan ta duba wayarta bata ga miss call d’in Sultan ba takan ce k’ila bashi da network domin a rana zai k’irata sau d’aya yace baya samunta ne tace karya damu itama wani sa’in tana kashe wayar. 
Bata ta6a bashi laifi kullum kanta tak’e d’orawa hakan ya fara sashi jin kunya da nauyinta sai ya dawo kiranta sau biyu sabida ta bashi time d’in da zai dinga kirin nata. 
Cikin sati biyun nan Sultan da Balqees sunyi wata muguwar shakuwa, wata sabuwar kauna ta kuma shiga tsakanin su duk da cewar be fiya kusantar taba dan yaga alamar bata son hakan shi kuma yana kiyaye duk wani abu daya san bata so ko zai 6ata mata rai, yana jinta har cikin kwakwalwarsa da magudanar jininsa. Soyayyarta a cikin jininsa take sam baya ganin duk wani laifinta komai za tayi a gurinsa dai-dai ne. 
Ranar da Nadiya zata dawo sun gyara gidan tatas yaje yayo masu ordern abinci da abinsha suka jerasu a dining table. Shiryawa suka yi kowannen su yayi kyau haskensu ya kuma k’aruwa sunyi wani fresh babu abin da yake damunsu sai dai kawai Sultan da yake son rage zafi shine kawai matsalarsa dalilin kuma da yasa ya k’agara da dawowar Nadiya, sai dai ko ta dawo bai san yadda zai yi ba sabida one month d’in da ta basu be k’are ba wannan ne kawai besan yadda zai tunkari ko waccen su da batun ba kasan cewar duk sun san akwai sauran kwanaki. 
Story continues below

Sai da suka gama shirin tafiya kawai yaga Balqees ta zauna a bakin gado, hannunta tasa a kugunta ta rik’e tana cizon lips tare da rintsa ido. Kallonta yayi tare da k’arasawa wajan ta cikin tashin hankali da damuwa da halin da yaganta ta shiga ya rungumuta tare da tambayar ta. 
“Baby meya same ki? Menene yake da munki?!” 
Hannunsa ta kamo tare da d’ora shi a saman mararta, tun kafin ya gama d’orawar tayi k’asa ta kwanta a k’asan bedside carpet tana murginawa sabida yadda taji tana tsira mata tamkar wata me yinkurin haihuwa. 
   Da sauri Sultan ya bita k’asan ya rik’ota tare da sanya ta a jikinsa gaba d’aya kwalliyar da aka yita dan d’akko Nadiya ta lalace domin gabaki d’aya shaddar dake jikinsa ta yakune garin rik’on Balqees d’in. 
Rasa yadda zayi da ita yayi gabaki d’aya ya susuce ita kuma axaba ta hanata yin magana sai juye-juye tak’e yi tana kuka. Ganin abin yayi yawa ne yasa shi fita da ita dan zuwa asibiti. 
Asibitin da Nadiya take aiki nan suka nufa cikin sa’a suka tarar da Huda k’awar Nadiyan suka wuce emergency room. Suna shiga Balqees ta fara amai tamkar kayan cikin ta zasu zazzago, tsabar tashin hankali Sultan ya kuma dad’uwa da kyar ya fito daga room d’in zuciyarsa na harbawa yana tsoran kar wani abun ya samu babyn shi. 
Hankalinsa be kwanta ba sai da aka tabbatar mai da cewar ciwon mara ne ke damunta sannan anyi mata allura ta samu bacci dan idan ba bacci tayi ba toh baza taji dad’i ba. 
  Ciki ya shiga ya samu guri ya zauna a kusa da ita tare da kamo hannunta ya rik’e duk tayi wani fayau da ita hancinta ya sake fitowa tamkar tsinin biro, gabaki d’aya ya manta da dawowar Nadiya wadda tunda suka sauka take faman k’iran wayarsa amma ba’a d’aga ba domin a gida ya manto ta dan tsabar shiga rud’ani. shiru Nadiya tayi a reception d’in airport d’in kasan cewar su Ummi basu samu damar zuwa saudiyan ba. Tunani ta dinga yi shin meya hana Sultan zuwa ko daman dan ya wulak’anta tane yasa da tace zata yiwa drive d’in gidan su magana yazo ya d’auke ta amma yace a’a ta bari zasu zo shida baby su d’auke ta. Tashi tayi tana jan trolley d’inta ta fito, taxi ta samu tayi shata aka kaita har bakin gate d’in su ta biya sannan ta shiga ciki mai gadi ya k’ar6i trolley d’in nan yake sanar da ita cewar ai oga sunje asibiti amarya ba lafiya. 
Sai da k’irjin Nadiya ya buga jin abinda mai gadi ya fad’a mata. Lallai Sultan shaf-shootar ne farar d’aya yake kwafd’e matan nasa. 
Tayi murmushi hakan yasa ta cire zargin da tayi masa na cewar yana sane yak’i zuwa d’aukar ta. Ciki ta shiga komai gashi nan a ajiye Nadiya tayi murmushi tare da shiga d’aki. Wanka tayi tayi sallolin kanta sannan ta fad’a kan gado dan rage gajiyar dake jikinta. 
  Sai wajan k’arfe biyar sannan aka sallamo su bayan Dr Huda tayi mata duk abunda zata yi mata sannan rubuto mata magunguna ya siya suka dawo gida. 
Sai da Sultan ya kai Balqees d’aki yayi mata wanka ya sake mata kaya yasa mata marasa nauyi sannan ya kwantar da ita, sai lalla6ata yake yi tana faman yi mai rak’i da shagwa6a. Sai da yaji ana k’iran magriba sannan ya fita zuwa d’akin Nadiya wadda ke k’ok’arin shiga toilet. 
Jin motsin mutum ne yasa ta tsayawa taga ko waye nan taga Sultan, tunda suka shigo taji dawowarsu amma be shigo gurinta ba sai yanzu ta daure tare da k’ak’alo murmushi suna kallon juna. 
Wani irin shock yaji a cikin zuciyar sa, kura mata ido yayi tayi kyau wani kyalli ma yaga tana yi ya k’arasa da sassarfa wajanta tare da sanya ta a kirjinshi yana furta kalmar. 
“Oyo yo my Nadi, am so sorry kinji wallahi ba…” 
“Shhhhhh abban humaira karka ce komai naji ance kunje asibiti da fatan dai jikin nata da sauk’i…?!” 
Kasa amsa mata yayi sai faman jingina kanta yake yi a k’irjinsa wata muguwar sha’awarta na bijiro mai gashi jikinta ya kuma laushi wani dadd’an kamshi na fitowa a ko’ina na jikinta. 
Story continues below

“Abban humaira karfa a tayar da sallah kana nan kaji ka dawo.” 
“Tare zamu yi.” 
Da sauri ta d’ago tana kallonsa cike da mamaki, yaushe rabonta da suyi sallah tare tun ranar da Balqees ta tare a matsayin matarsa. Tunani ta fara yi toh me yasa bazai je suyi tare da ita ba kamar yadda suke yi kullum, bata yi k’asa a gwaiwa ba kuwa wajan yin magana tace. 
“A’a rufa min asiri kaje kuyi da ita na yafe hakkinta ne kuma.” 
“My Nadi baby tana off, kinga kuwa  dan munyi tare ai ba matsala bace. Oya muje muyi alwala.” 
Cikin toilet ya jata suka yo alwala yaja musu jam’i, ta dad’e tana addu’a shi har ya fara tsoran yawan yin addu’o’inta domin sai ta shafe awa biyu tana yi kuma d’abi’arta ce tun da suka yi aure haka takeyi yana kuma da tabbacin ta sabayi ne tun tana budurwa. 
Tashi yayi ya fita dan zuwa gano Balqees, kwance ya ganta da waya a kunnanta suna yi da Afrah. K’arasawa yayi kusa da ita tare da d’agota ya sanya ta a jikinsa yana kara kunnansa shima a jikin wayar Balqees tace. 
“Keni sai anjima ki gaida min dasu aunty Sa’a.” 
Tana kaiwa nan ta kashe wayar tana turo baki cikin sauri Sultan ya cafko lab6abta da bakinsa ya fara kissing d’inta ita kuma ta lumshe idanuwa bata hanashi kome zaiyi inda ba kusantar ta zai yi ba. A hankali ya zare bakinsa daga nata yana shafar gashinta cikin kulawa yace. 
“Menene kuma baby na waya ta6aki.” 
Cikin shagwa6a tana shafar fuskarsa tace. 
“Afrah mana.” 
“Toh me tayi miki..?!” 
Gyara kwanciyar tayi a jijinsa sannan ta kuma turo baki tace. 
“Wai ba ita bace ta bugo min waya ba, shine tace taji murya ta wata iri menene nace mata bani da lafiya wai wani kodai kodai nace mata mene wai ko ciki ne d’an baba ya fara damuna nace mata a’a, shine wai waya ganni da ciki harda cemin gudille! ni za’a gani ko cikin za’a hango….” 
Had’e rai shima yayi duk da cikin ransa dariya ce amma duk dan karya kuma 6ata mata rai yasa shi yin kicin-kicin da fuska yace. 
“Lallai ma Afrah wuyanta ya isa yanka, harke take kallo ta gyara miki haka? Allah ya kaimu gobe da kaina zan yi mata waya sai ta gaya min me take nufi.” 
Ganin yana fad’a ne yasa ta kuma kwanciya a jikin sa tare da shafar buturan jallabiyar sa ya sak’alo wuyan sa cikin nata bayan ya d’an zamu dai-dai jikinta yace. 
“Baby bakije kinyiwa auntyn ki sannu da zuwa ba.” 
Kallonsa tayi da dara-daran idanunta, so take ta gano da yanayin da yayi mata magana dan dama taga tunda ya fita ya dad’e be dawo ba, kasa hakura tayi tace masa. 
“Yaya zulkallain wai dani da Maman Ummi (humaira) wace kafi so…?” 
Da sauri ya kalleta jin abinda tace, sai kuma yaga idanunta sun fara kawo kwalla alamar hawaye na son zubo mata yayi saurin matso da ita yana kallonta sai faman turo baki take yi ya ce mata. 
“Me yasa ki kai min wannan tambayar baby?!” 
“Ba komai kawai so nake yi naji domin naga dama can kafi sonta tun kafin ma kuyi aure a kaina, tunda ni baka min soyayyar aure kawai tausayina kakeji hakan yasa kake bani kulawa da jikinka da lafiyarka da kuma aljihunka, yanzu kuma gashi zama ya had’a mu nasan babu abinda aunty Nadiya ta rasa dan haka dole soyayyar dukan mu ta banbanta a cikin zuciyarka.” 
_”Innalillahi wa’innailaihir raji’un, ni da nake shirin neman alfarmarki baby ki barni naje yau gurin ta tunda ke bazaki iya ba, shine kawai zaki yi min wannan tambayar..?!”_ 
Ya fad’a cikin ransa, kenan idan ya tambayeta zata sawa ranta cewar yafi son Nadiya akan ta. Nan da nan gumi ya tsatso mai baya jin yana kaunar wani abun kamar ransa a yadda yakejin Balqees, sai dai bazai iya nunawa wata a cikin su cewar ga wadda ya fiso ba yana ganin wannan shine kawai adalcin da zai iya yi musu. 
“Baby kiyi bacci bari zanyo sallan isha’i idan na dawo sai muyi magana kinji ko?!” 
Wani irin kallo tayi mai wanda yasa zuciyarsa bugawa, saurin janyo ta yayi jikinsa yana jin tamkar zuciyarsa zata fito. Da kyar ya samu nutsuwar ransa ya mik’e bayan ya sumbace ta yace. 
“Bari naje nayo sallah sai muje muci abinci.” 
Fita yayi tabi bayan nasa da kallo tanajin wani rad’ad’i na kishinsa a memakwan taje tayiwa Nadiyan sannun da zuwa sai kawai tayi likimo a kan gado, toh dama shima can d’akin Nadiyan ya shiga nan ya tarar da ita tana k’ok’arin…

Tana k’ok’arin sanya hijjab da alama alwala ta kuma yowa, kallon shi tayi tare da kawar da kai shima beyi magana ba ya hau kan sallayar ganin haka yasa tabi bayanshi ya suka yi jam’in tare. Suna idarwa ya juyo yana kallonta, wani irin tausayinta yake ji hak’ik’a yana son Nadiya sai dai ba kamar Balqees ba domin sai yanzu ne daya aureta ya gano irin narkakkiyar soyayyar dake dashi a cikin zuciyarsa. 
Yana son Nadiya domin nagartacciyar macace, uwa uba tasan ta kanshi gata da d’in bin ni’ima a jikinta yakan yi tunanin kodan ita tana karantar fanin kula da lafiya domin tunda suke be ta6ajin ta a kyafe ba, haka kuma duk a yanayin daya ganta sai yaji yana buk’atar ta yana jin wani feeling akan ta gashi yayi sa’a Nadiya akwai gyara tana son k’amshi. 
    (What do you mean Ahmad?auran sha’awa kenan kake yi da ita😏) 
Kamo fuskarsa tayi cike da kauna tana shafa mai girarsa murya a sanyaye tace. 
“Wai bangata ba ko jikin ne ya matsa mata?!” 
Zame jikinsa yayi tare da jire rigar jikinsa, rungumuta yayi tare da cewa. 
“Tana can kwance a d’aki amma dai da sauk’i, me zan samu yanzu tsarabar me kika yo min…?!” 
Murmushi tayi mai sauti kafin tace, 
“Abban humaira kenan ni wallahi sai shekaran jiya na shiga kasuwa banje nayi wani siyayya ba dan na d’auka su Ummi zasu je sai ta ce min ba’a samu viser ba hakan yasa na maida hankali na wajan yin abinda ya kaini.” 
“Naji toh amma ni basu nake nufi ba tsaraba nakeso naga kinyi wani kyau meye sirrin?!” 
Nadiya tayi dariya kawai dan ta gano abinda yake nufi, cikin bagarar da zancen ta fara k’ok’arin zame jikinta tana cewa. 
“Tashi muje nayi dubiya wannan ciwon dai ya takura mata yanzu tunda tace ada bata yi sai daga baya, ya kuma kamata abban humaira akaita asibiti a duba lafiyar ta.” 
Sam ji tayi tana jin zafi cikin zuciyarta, tana hango yadda zai yi mata haka yake yiwa wata d’iya macan bayan ita babu wanda take kulawa sai shi. Tana can tana kishi kawai taji sa har ya samu abinda yake so, ba yadda ta iya haka ta hakura ganin kamar a matse yake sai dai tasha kuka kamar ranta zai fita, ko daran farkonta bata yi mai kukan da tayi yanzu ba hakan ya d’aurewa Sultan Ahmad kai ya janyo ta jikinsa yana bata hakuri. 
Story continues below

Al-ajabi, mamaki, tunani, da sak’e-sak’e duk suka dabai baye zuciyar Balqees ganin yadda yake mata tamkar wanda aka ce jeka an baka aljanna. Cikin had’e rai ta turesa tare da kallonsa cikin mamaki, kuma kai hancinta tayi jikin fatarshi tace. 
“Yaya zulkallain ina kaje harda su wanka?” 
Da sauri ya tashi yana janyo ta tare da kallon fuskarta yace. 
“Baby na me kika ji kika yi min wannan tambayar??” 
“K’amshin sabula naji wanda bansan shi ba.” 
Tayi maganar cike da shagwa6a gashi ta kura mai ido tana jiran jin amsa, shafa kai yayi tare da lasar lips d’insa yana kuma cizon lips d’in duk a lokaci d’aya. Numfasawa yayi tare da kwanciya ya d’ora kansa akan cinyarta yana shafo round face d’inta yama rasa me zai ce mata wanda ba zai 6ata mata rai ba ko taji babu dad’i dan haka yayi k’ok’ari wajan cewa. 
“Naje d’akin Nadi ne shine na ganshi tazo dashi daga saudiya nima naji k’amshi yayi min me yasa kika min wannan tambayar baby?!” 
Fuskarta ta d’aura akan tasa yana kan cinyarta, wata k’atuwar ajiyar zuciya ya sauke ganin bata koma tado mai da zancen ba. Murya k’asa-k’asa take mai magana saitin wajan bakinsa tace. 
“Yaya yinwa nakeji fa.” 
Idanuwa ya bud’e yana kallon fuskarta, cikin kulawa yace. 
“Toh oya tashi muje parlor ai muna da abinci acan.” 
“Toh goya ni mana.” 
Tayi maganar tana turo mai baki, kamo shi yayi da yatsunsa ta d’an saki ‘yar k’ara yayi dariya tare da sunkuyawa caraf ta haye suka nufi zuwa parlor. Nadiya kuwa bayan ya fita pillow ta d’akko ta cusa kanta a ciki tana sakin wani marayan kuka wanda babu mai lallashinta, ya samu abinda yake muradi shi yasa ya tafi alhalin da ba haka yake mata ba sai ya tabbatar sunyi wanka tare sannan. Ta dad’e kwance tana kuka kafin daga bisani ta mik’e da kyar ta shiga bathroom, sai da ta ciki ruwa cikin kwamin sannan ta shiga, duk da cewar bata tsarki da sabulo yau kam da ta sameshi sai da ta kusa k’arar dashi sabida wanke gurin da ta dinga yi tana hawaye. 
Sai da suka zauna a kan kujera sai kuma Sultan ya mik’e tare da kallon Balqees yana rik’e da hannunta yace. 
“Baby bari naje na kira Nadi naga ba’a ta6a abincin ba, da alamun itama bataci komai ba.” 
D’aga mai kai tayi ya mik’e tare da shafar kuncinta yayi hanyar d’akin Nadiya, yana shiga d’akin Nadiya. Kwance ya tarar da ita tayi ruf da ciki idanunta a rufe yayinda gefenta kuma iPad d’inta ce a bud’e da alama abu take son yi amma ta kwanta. A gefenta ya zauna yana kallon kyakyawar fuskarta da tayi fayau, da alama ta samu bacci duba da yadda take sauke numfashi ahankali hakan yasa shi mik’ewa ya fita tare da janyo mata k’ofar d’akin. 
“Zo nan na baki da kaina baby.” 
Sultan ya fad’a bayan ya k’arasa ya zauna akan kujera, Balqees ta mik’e tare da komawa kan cinyarsa. Da kanshi ya zuba abincin sannan ya fara bata a hankali tamkar wata yarinya, yana bata shima yana cinye ragowar da ta bari a cokalin ta turo baki tana yatsina fuska tace. 
Story continues below

“Yaya yanzu ranar Monday zamu koma school?!” 
Kallonta yayi yana dariya ganin yadda tayi da fuska da alama bata son komawar ya kuma janta jikinsa yana cewa. 
“Toh baby bakya son ku koma ne?kunsha hutu fa ai gara ku koma kinga wannan samistern zaku kwalo dan babu mai rangwanta muku gara ma ki tsaya kiyi karatu.” 
   Shiru tayi sai faman 6ata rai takeyi, sam bata kaunar wannan school d’in ta gaji da ita musamman da ta d’an dad’e a gida bata fita ko nan da can, kan k’irjinsa ta kwanta tare da rungume shi tamkar zata koma cikinsa. Wani nishad’i yake ji zuciyarsa wasai yau dai-dai yake jinsa, sai da ya tabbatar sun k’oshi sannan ya d’auke ta suka nufi d’akinsa. Kwata-kwata baya jin wahalar d’aukar ta ko dan ya ganta daf da k’asa ne oho, ya kaita kan gado nan fa suka hau wasa kamar wasu k’anun yara hardasu cakulkuli da tsunkuli su cizon wasa duk suka yi kafin suyi bacci. 
Haka suka ci gaba da rayuwa shidai ta ko’ina yana jin dai-dai sai dai tun ranar da Nadiya ta dawo ya nemeta bata sake bashi kanta ba sai da kwanakin da ta bawa Balqees suka k’are. A cikin kwanakin suka saki jiki da juna rsakanin Balqees da Nadiya dan sukan zauna suyi hira lokacin da aka koma school Balqees bata koma ba sabida sultan yace ta bari sai lectures sun kankama. A ranar da zai koma d’akin Nadiya ita bata nan ma tana asibiti ranar aikin rana take dashi bayan Sultan ya dawo daga wajan aiki ya tarar da ita a kwance a d’akinta suna waya da k’awarta sdy akan harkar makaranta ya shiga ya tsaya yana kallonta. 
Murmushi yayi a duk lokacin daya ganta yakanji wani nishad’i da farin ciki, zuciyarsa kan samu nutsuwa idan ya tuna cewar ita d’in mallakinsa ce, sanye take cikin riga da wando english wears rigar yellow mai guntun hannu da dark pink d’in wando ta sanya pink d’in hair band sai tayi tamkar wata baby ‘yar 12years d’in nan. Sam bata ganshi ba kasan cewar ta bawa k’ofar baya sai dai hanci da take ta bud’ewa kasan cewar tana jiyo k’amshin turare irin wanda yake sawa. 
A hankali ta waigo karaf suka had’a idanuwa, da gudu taje ta d’ane shi shima ya d’auke ta yana juyi da ita dan ba wani nauyi gareta ba. K’arasawa yayi bakin gado tare da k’ar6ar wayar ya kashe ta dan har lokacin sdy na jinsu, ta kalli cikin idanunsa tare da lumshe nata tace. 
“Kai Yaya wannan school d’in dad’ar da kai takeyi wallahi, jiba fa sai yanzu ka dawo.” 
  Saman hancinta ya sumbata tare da sauke ta ya d’ora ta akan gado, rungumota yayi yana shak’ar turaran jikinta tare da sanya hannunshi cikin rigarta yana shafarta yace. 
“Toh baby ya zanyi, kema gashi kin kusa komawa dan naga d’aliban sun dawo sosai har an fara lectures dan nima yau nayi.” 
Sake lafewa tayi ajikinsa ya d’ago ta yana kallonta tamkar zai lasheta dan tsananin so da yadda yaji zuciyarsa na k’ara mannuwa da tata, murya k’asa-k’asa yake cewa. 
Da sauri ta kallesa cikin tsananin mamaki, had’e rai tayi tana turo mai baki yayi saurin janyo ta k’irjinsa yana shafa tsakiyar kanta tare da hura mata iskar bakin shi a cikin kunnanta wai duk dan kar ranta ya 6aci, amma ina sai butsare mai take yi ya janyo fuskar ta tare da d’ora goshinsu guri d’aya hancinsu na gogar juna yace. 
“Baby na ya akayi ne?!” 
Tayi maganar hawaye na fito mata daga cikin ido, har cikin ranta takejin zafin zai tafi ya barta tamkar ance mata sun rabu rabuwa ta har abada. Jikinsa a sanyaye yana sanya harshensa akan tattausan kumatunta yana lashe hawayen da take yi, shi kanshi baya son rabuwa da ita domin yana matukar son rigimarta, shagwa6arta da rakinta hakan sam baya 6ata masa rai amma ya zai yi da Nadiya?tana da kawaici tana kuma da hakuri sai dai idan yace zai zauna a gurin Balqees to lashakka alhakinta bazai ta6a barinshi ya rintsa ba kuma ma yana da buk’atar ta dan Balqees da kuka da rigima su yakushi yake samu a gurinta kuma duk sai sun sha wahala, yana tunanin ma sai ya kaita asibiti an duba ta dan yana tunanin tana da matsala idan kuma ba aljanu bane. 
“Kayi hakuri kinji baby,ai gobe muna tare nima ba’a son raina zan barki ba, wannan yana d’aya daga cikin abinda yasa nace kuyi kwanaki d’aya-d’aya hakan ne kawai zai sa baxamu dinga nisa da juna ba kiyi hakuri.” 
Hawaye ta share tana faman sauke ajiyar zuciya, ya zai yi wajan ganin ya tafi ba tare da ya barta cikin damuwa ko zargi ba, sam baya son 6acin ranta ya fison kullum ya ganta cikin farin ciki hakan shine kawai zai kawar mata da tunanin cewar ita d’in marainiya ce gaba da baya, ta gane cewar shi mai son farin cikin tane yana son ya ganta kullum cikin dariya da walwala yana da burin Tattalinta tamkar yadda uba zai yiwa ‘ya’yansa, tamkar kuma d’a a cikin mahaifiyarsa. 
Cikin da bara da son kawar mata da damuwa yace, 
“Tashi muje ki rakani gurin Umma mu d’akko Humaira.” 
Ai kuwa sai ta mik’e da sauri cike da murna ya bita da kallo yana jin zuciyarsa cikin nishad’i ganin ta ware tana murna. Doguwar riga ta d’aura tare da yane kanta da vail tasa wani ubansun hill mai shegen tudu ta kalleshi tace. 
“Yaya tashi muje.” 
“Amma baby wannan takalmin ai kada ke zai yi gaskiya kisake wani.” 
Kallon takalmin tayi dan ba k’aramin kaunarsa take yi ba, duk cikin kayan lefenta tafi son takalan sabida Nadiya ta za6o mata dai-dai wanda takeso, had’e rai tayi tana tsuke baki ya tashi tsaye tare da kamo hannunta yace. 
“Idan yayi miki dai-dai da son ranki to shi kenan mutafi but sai kin saki fuskarki kinyi dariya.” 
Da sauri tayi murmushi tare da rungume shi, ta d’an wuce cibiyarsa dan har dafa kafad’un ta yayi sa6anin da dasai dai ya riko hannunta ko ya d’ora hannun saman kafad’ar ta kanar tana yi mai jagoranci da haka suka fita ba mota sai mashin d’insa suka hau. Sun a zuwa basu dad’e ba Umma ta basu humaira suka juyo gida ana kiran sallan isha’i Nadiya ta dawo gida a gajiye tib’isss..
   Ciki ta shiga hannunta rik’e da handbag d’inta sai jarkar faro a hannun ta shiga bakin ta d’auke da sallama. Zaune dukan su suke a parlor Sultan daga shi sai boxer shorts da singlet yana faman aiki a cikin laptop d’insa shi koda can baya zaman majalisa kulluma yana gida daga gurin aiki sai gidan hajiya kaka ko gidan Umman shi sai kuma gidansa sam be yadda da zama a waje ba. Amsa mata suka yi yayin da humaira ta ruga da gudu tare da d’are ta, ada kafin Sultan ya auri Balqees idan ta dawo su duka biyun zasu zo su yi mata oyo-yo amma yau sai Nadiya taga sa6anin haka tayi murmushi kawai tare da shiga ciki bayan ta d’auki humairan tana cewa. 
“Ah abban humaira ashe kana gida? gashi can za’a fara kiran sallar magriba kuma.” 
Kafin ya bata amsa ta kalli Balqees tana murmushi tare da sauke humaira a k’asan carpet tana cewa. 
“Mamman humaira hutawa ake yi ne?!” 
Sai kuwa Balqees taji wata kunya ta lullu6eta, tabbas kamata yayi ace itace ta fara yi mata magana ba wai itaba amma tunda suka had’a abu d’aya takejin wani d’agawa takejin sunyi dai-dai da ita, a d’in kunya ce kuma cikin basarwa Balqees d’in tace. 
“Sannu da dawowa aunty Nadi.” 
“Yauwa Maman humaira ya jin dad’i da kuma abban humaira?hope dai bakwai damunsa dan nasan ku…?!” 
Murmushi kawai Balqees tayi tana satar kallon Sultan sai taga shi humaira ma yake yiwa wasa, Nadiya ta kalleta ganin kamar bata cikin walwala yasa tace. 
“Bari na shiga ciki yau duk na gaji da yawa.” 
“Toh.” 
Haka kawai Balqees ta fad’a shima Sultan ya mik’e tare da cewa, 
“Nima bari nayo alwala kuje kuyi kuma yau tare duk zamu yi sallan.” 
“Ahh Masha Allah toh bari nayi sauri na d’an watsa ruwa.” 
Nadiya ta fad’a tare da shigewa cikin d’akin ta da sauri, kai da ka ganta kasan maganar shi ba k’aramin dad’i tayi mata ba hakan kuma yasa ya bita da kallo yana murmushi wanda besan ko na meye ba har ta shige. Juyawa yayi gurin Balqees wadda humaira ta hau kan ruwan cikinta tana doki yaje ya d’auke humairan tare da d’ago Balqees d’in ya d’an yi k’asa-k’asa ya had’eta da k’irjinsa yana kallon fuskarta yace. 
“Oya muje kiyo alwala muyi sallah gabaki d’ayan mu.” 
“Toh..” 
Ta fad’a tare da watsa mai wani kallo wanda ya fassarashi da ma’anoni masu yawa, kissing d’in lab6anta yayi kafin ya cika ta, humaira ta d’auka suka shige cikin d’akin ta. Dukan su cikin shirin yin sallah suka fito ya shimfid’a musu k’atuwar darduma suka jeru Balqees da Nadiya shi kuma ya shaga gaba yaja musu jam’i. Suna idarwa cikin farin ciki da jin dad’i Nadiya ta mik’awa sultan hannu tace. 
“Oga Happy family..” 
A hankali yabi zanan lallen hannunta da take mik’a masa da kallo, jikinsa a sanyaye shima ya mik’a mata suka yi shaking sannan ta cire tare da mik’awa Balqees ma tana murmushinta mai burgewa tace. 
“Happy family Maman humaira, Allah ya k’ara mana zaman lafiya.” 
Balqees ta sunkuyar da kai cikin sanyin jiki tace, 
Story continues below

“Amin aunty Nadi.” 
Wani nishad’i da jin dad’i ya mamaye Sultan Ahmad yana kallonta, wani abu ya kuma sukar shi akan Nadiyan tausayinta da ganin darajarta suka sake ninkuwa a cikin zuciyarsa ya mik’e bayan ya ce musu yana zuwa su kuma suka zauna suna d’an ta6a hira. 
   Fita yayi ba jimawa ya dawo suna nan inda ya barsu ya ajiye ledan hannunsa suka yi sallar isha’i, bayan sun idar da kanshi yaje cikin kitchen ya d’akko tray da kofuna ya kawo inda suke. Ledar da ya shigo da ita ya d’akko yana k’ok’arin bud’ewa ya zuba Nadiya tayi saurin mik’a hannu ta kar6a tana zazzagewa cikin tray d’in tana fad’in. 
“Karufa mana asiri abban humaira kana da mu ace kaine zaka yi komai ai sai kaja mana fushin ubangiji.” 
Murmushi ya kuma yi yana kallon Balqees tayi kamar bataji suba, balqees kam gani take kamar Nadiya ta fiye shisshigi da yawa ne akan abinda ba’a saka ta, yya maida kansa gurin Nadiya tare da fad’in. 
“My Nadi ina cikin farin ciki ne shi yasa, kuma duk abinda nayi muka na jin dad’i ne dan da ace tun farko kina juyan baya akan auran da nayi da na san bazan dinga samun farin ciki da jin dad’in da nake samu a kowace rana ba, Nadi Allah yayi miki albarka..Allah yayi muku albarka baki d’ayan ku ya k’ara had’e min kanku.” 
Nadiya ce still ta amsa yayin da Balqees ta sanya hannu ta d’akkowa humaira tsokar naman ta bata ita duk ganin zak’ewar Nadiya take gani gabaki d’aya haushin su takeji gashi yayi ma Nadiya addu’a ita kad’a ya kuma zo ya yi musu su duka. Madarar daya shigo da ita ya zuzzuba musu a kofuna suka fara cin naman wanda Balqees da kyar take sanya baki a cikin hirar, ganin haka yasa yake gutsorowa yana sanya mata a baki amma Nadiya bata nuna ko mai ba hirar ta kawai take yi babu abinda ya dameta zuciyar ta ma tazbihi kawai takeyi har suka kammala. 
“Toh ni zan shiga ciki sai Allah ya tashe mu lafiya zan d’an yi wani aiki.” 
“Toh sai da safe.” 
Cewar Balqees Nadiya ta amsa tare da shiga cikin d’aki lokacin humaira tayi bacci a cinyar Balqees sai ta kasa cewa a bata ita dan haka ta shiga d’aki, sai da suka gama soyayyar su ya rakata d’akinta tana ta faman kuka duk ta rikita shi da kyar ya samu ya kai zuciyar sa nesa ya tafi d’akin Nadiya ya tarar ta idar da sallah lokacin sha biyu da minta goma na dare ya kalleta yana daga bakin k’ofa yace. 
“Ki shirya ki taho d’aki na kin san yau kin k’ar6i girki.” 
Kwance ya shigo ya tarar da ita tayi d’ai-d’ai akan gado rigar jikinta mai yauk’i wanda iya karta cinyarta, bin santala santalan k’afafuwanta yayi da kallo nan da nan ya cire kayan jikinsa ya hau gadon tare da janyo ta jikinsa amma fur ta dak’ire tayi mai tamkar a cikin bacci, ya kuma wulkito ta, wani irin juyi Nadiya tayi gaba ki d’aya ta koma jikinsa tare da sauk’e wani shu’umin numfashi hannunta sakale ta bayan shi ta ci gaba dayin likimoniyar ta tamkar mai yin bacci. 
   Ta d’auki alwashin nunawa Sultan ko wace mace fa da nata iya shegen, sai ta gano shin wani irin rainin wayo ne yake yi mata dan ta lura akwai abinda yake d’i mauta shi, ta fara gano cewar a kanta yake samun nutsuwa irinta auratayya sa6anin Balqees da ta rasa gano silar mannewar su amma ta tabbatar akwai matsala dan be dace ace kana da mata biyu amma kana shiga irin wannan yanayin ba. 
Ahankali ya gyara ta daga jikinsa tare da sanya hannu ya su6ale mata rigar jikinta a haukace ya fara bata wasu zafaffan sakwanni masu shiga cikin kwakwalwa, abinku da lafiyayyar mace ai sai ta kasa jurewa nan da nan itama ta fara taya shi da nata zaffafan wanda ya sake rikita shi sai da taga yana shirin wucewa tayi saurin zame jikinta hankalin Sultan ya tashi yayi saurin rik’ota tana hawaye, jin yadda jikinsa ke rawa gashi da alama ya kasa magana kawai sai ta juya ta mik’a masa kanta da jikinta gabaki d’aya. 
    Tana son shi sosai, soyayyar sa tayi mata yawa baza ta iya yi mai abinda yake cikin ranta ba gashi tana tsoron fushin ubangiji akanta dan tana tsoron ta mutu a lokacin da mijinta yake fushi da ita akan wani abun dan haka ta bashi hakk’insa tana kuka bakinta da zuciyarta far addu’ua. (Gaskiya Nadi tafi Balqees zafin kishi kata’i😳) 
Tare suka yi wanka sannan suka kwanta, sai da ta tabbatar yayi bacci sannan ta tashi tayo alwala, d’akin ta tawuce ta d’akko kayan da zata yi sallah dasu ta dawo. Salloli ta dinga yi tana neman sassaucin zuciyarta har wajan k’arfe uku sannan ta samu ta kwanta tayi bacci ita. haka suka ci gaba da rayuwa Nadiya tana iya k’ok’arinta wajan ganin ta kauda kai akan Balqees da Sultan domin su yanzu kullum tare suke fita school baya dawowa kuma sai duk ta gama lectures d’inta haka yasa Nadiya ta samu suka yi exchange na duty ita da Dr badiya zata ci gaba dayin na rana bata dawowa sai shida da ‘yan mintuna. 
Watanni uku Yusif yayi a k’asar India ya dawo gida Nigeria, yayi fresh dashi yayi k’iba fuskarsa babu ta6o ko d’aya sai dai daka ganshi zaka san yayi sanyi ya zama slient sai sandar dake hannunshi yana kuma d’an d’in gisa k’afarsa ta dama wadda da alama ya samu matsala a ita. Kwananshi biyu da dawowa hajiya kaka tace da Sultan yazo suje zata dubo shi, shida Balqees da Nadiya suka shirya yau zasu fita dan tunda ya auri Balqees basu ta6a fita gabaki d’ayan su ba sabida sa6anin zama da suke samu yau wannan na lecture gobe wannan na asibiti haka suke tayi sai yau Sunday Allah yayi suka zauna a gida. 
   Shiyawa suka yi gabaki d’aya ranar girkin Balqees ne dan haka da sauri ya shiga d’akin dan yasanta da shegiyar rigima ya tarar da ita tana sanya hijja dan cewa yayi duk shi zasu saka gashi matan nasa sarakan yafa mayafai ne yaje ya janyo ta suka zauna a bakin gado ta bishi da kallo ya kashe mata ido d’aya tare da kamo hannuwanta duka biyun yace. 
“Babyy kinga fita zamu yi gabaki d’ayan mu ko?!” 
Tace “eh Yaya.” 
“Good ina son ki bawa Nadi girmanta wajan shiga mota, damun fita direct kawai ku shiga baya keda angel(humaira) kinji ko…?” 
Ya tsina fuska tayi tare yin kwalkwal zata yi kuka ya janyo ta jikinsa yana bubbuga bayanta, murya k’asa-k’asa tace. 
“Amma Yaya dan kawai motar tace za’a wani ce na koma baya, ai yau a wajanka nake ni ya kamata na shiga gaban.” 
“Noh baby na ba zancen dan tata bace kinga itace babba be dace ace munyi haka ba kiyi abinda na saki ni dai kawai.” 
“Toh wai kai meya hanaka siyan taka bayan kana da kud’in ba wai babu ba..?” 
“Ya akwai kud’i amma akwai  abinda nakeson yi dasu kedai kawai yanzu kiyi abinda nace, idan muka dawo akwai special abu dazan miki muuuchh.” 
Ya fad’a tare da bata wani kyakyawan hot kiss a saman lab6anta da suka shi red d’in janbaki, sannan ta d’aga mai kai taja hannunta suka fito. A zaune suka ga Nadiya tana gyarawa humaira skirt d’in jikinta Sultan be saki hannun baby ba yace ma Nadi. 
“Mu tafi ko?!” 
“Ok tom dama ku muke jira.”
    K’ofar gidan hajiya kaka yayi parking yace su bari yaje ya fito da ita dan karsu shiga su zauna. Yana shiga ya tarar da ita a shirye tayi kicin-kicin yayi murmushi dan ya san gajiya tayi da jiran shi, tun kafin yayi magana ta fara mai fad’a. 
“Banda kaima yanzu ka raini ni Muhammadu tun jiya na sanar dakai lokacin da zaka zo shine baka ga dama ba sai yanzu ko…?!” 
“Yi hakuri hajiya kaka ta! ba haka bane kin san tafiya da mata sai hakuri duk sune suka 6ata mana lokaci kiyi hakuri.” 
“Kaka kiyi hakuri kinga mutuwa ake yi wallahi ni dai na yafe miki.” 
Dama ya riga ya  san bata son zancen mutuwa duk sanda aka ce mata mutuwa ake sai tace toh ko kaine walakirin ai ayi shiru a jira ta Allah. Hannun shi ta kamo ya taya ta tamik’e sannan suka fita dama da mayafin zaninta a kanta dan haka fita kawai suka yi ya kullo mata k’ofar ta. 
“Oyo-oyo my hajiya kaka ta I miss you wallahi.” 
Balqees ta fad’a bayan hajiya kaka ta zauna a cikin motar, ta6e baki hajiya kaka tayi tana kallon humaira tace. 
“Kinibabbiya kawai, wai yarinyar nan kinyi aure tunda aka kai ki gidan nan ban sake sanya ki a idona ba sai yanzu.” 
“Hajiya kaka ina wuni, ya gida da k’afar ki kuma?!” 
Baki wangale hajiya kaka take amsawa Nadiya gaisuwar da take yi mata harda zura hannu ta kamo nata kamar zata janyo ta bayan. Balqees ta saki baki ido waje tana kallon hajiya. Sultan na kallonta ta cikin madubi, murmushi kawai yake yi dan yasan haushi taji, shi kanshi yana mamakin yadda yake jin ‘yan uwan shi kowa Nadiya duk gidan daya shiga sai sun fad’i alkairin da Nadiya take musu, yana kuma yin alfahari da hakan dan kanshi har girma yake k’ara yi. 
“Allah yayi miki albarka kinji ‘yar nan.” 
“Amin hajiya kaka na gode da addu’arki gare ni.” 
Motar Sultan yaja fuskar sa fal murmushi yayin da hajiya kaka ke tayi mawa Balqees mita tun tana ramawa har tayi shiru ta dena kulata. Suna shiga gidan hajiya kaka da Nadiya suka jera wajan shiga ciki yayin da Balqees ta tsaya d’akko humaira Sultan yayi saurin shiga bayan motar ya kamo hannunta yana k’ok’arin sanya kwayar idonshi cikin tata amma tak’i sai faman tsuke fuska take yi tana fusge hannunta daga rikon daya yi mata shi kuma ya rik’eta gam yana had’e fuska. 
“Ba zaki dena ture ni ba baby.” 
Kicin-kicin tayi da fuska sabida haushin yana ji hajiya kaka na yada mata maga amma yayi shiru be shigar mata, ra6awa yayi tare da janyo ta yana tambayarta. 
“Baby na menene kuma?!” 
“Ni babu komai.” 
“Toh naji amma ki saki ranki dan bana son ganinki cikin wannan yana yin.” 
Story continues below

Sakin fuskar tayi amma still a cikin ranta ba haka bane yayi mata kiss a saman lab6anta sannan ya fito daga cikin motar bayan ya d’akko humaira. Cikin gidan suka nufa duk suka gansu zaune a parlor Aisha na kusa da Nadiya dan yanzu ba k’aramin d’asawa suke yi da ita ba sai kus-kus d’insu suke yi suna dariya yayin da Fateema kuma ke zaune tana matsawa Yusif hannun shi daya ce yana mai ciwo. 
   Sultan na gaba Balqees na baya suka shigo Fateema sai yafito Balqees take yi amma ta share ta sabida ta ganta gurin Yusif, sai da suka k’arasa suka zauna sannan ne Yusif ya kallesu fuska ba yabo ba fallasa kafin ya d’auke kanshi ya mayar kan screen d’in wayarsa yana daddannawa. 
“Mommy ina yinin ku?!” 
“Lafiya k’alau Ahmad ya gida da iyalin?!” 
“Lafiya lau Mommy ya mai jikin?!” 
“Gashi nan da sauki alhamdulillahi.” 
Juyawa Sultan yayi yana kallon Yusif sai kawai yayi murmushi tare da cewa, 
“Sufee ya jikin naka?!” 
Tamkar beji ba yayi mai banza Sultan ya kuma murmusawa tare da kad’a kai, hajiya kaka tayi caraf ganin yak’i amsawa cikin fad’a tace. 
“Yanzu kai dan rashin mutunci muzo k’afa ya k’afa dubaka amma kanaji ana yi maka sannu shine babu wanda ka kula?wannan ba halin annabi bane ba sam Yusif baka koyi dashi sakarai kawai.” 
   Still yayi mata banza haushi ya kuma kama hajiya kaka itama tayi watsi dashi tare da juyawa su ci gaba da hira da Mommyn shi. Balqees kuwa ko gaida shi bata yi ba ganin yadda yake wani basarwa. Sun dad’e a gidan kafin suka tashi suka tafi Yusif sai satar kallon su yake yi. 
Sai da suka fara kai hajiya kaka sannan suka wuce gida. Suna zuwa kowa ya wuce d’akin sa sai da duk suka rage kayan jikin su sannan Balqees ta fito ta wuce d’akin Sultan domin shi k’a’idarsa duk wadda take dashi toh d’akin sa zata bishi haka ya tsara rayuwarsa sabida baya son ya tara ‘ya’ya yazo ya rasa yadda zai yi bayan su kuma matan sun saba da sai dai ya bisu. 
Tsaye ta tarar dashi yana kallon quarter million d’in fuskarshi daya fara yi mai yawa yana tunanin askewa, k’arasawa tayi sai wani fad’in rai take yi (kunsan gajeru akwai😜). A hankali ya juyo yana kallonta, sanye take cikin kayanta na d’azu doguwar rigar ta kawai ta cire sai hula da ta sanya a memakwan band ya k’araso gurinta a ranshi yana cewa. 
_”Baby har baby amma bata yadda ya kusan ce ta.”_ 
Janta yayi zuwa jikinsa sai tayi tsumu tsumu da ita yayi hanyar zuwa toilet da ita, ganin haka ne yasa ta saurin yin magana. 
“Yaya ya haka kuma?!” 
“Ya what?!” 
Shima ya tambayeta yana d’aga mata girarsa, Balqees ta cono baki tana juyar da kai tace. 
“Gani nayi kana k’ok’arin kai ni toilet.” 
“Wanka zamu jeki taya ni yi.” 
Zaro ido tayi tana faman girgiza mai kai alamar ba zata yi ba, shi kuma ya kad’a mata kai alamar sai fa tayi kawai suka fara jan juna yaja ta itama tajashi daga k’arshe ya rinjaye ta suka shiga, kallonta yayi a marairaice yace. 
“Baby please inyi baza kiyi kuka ba?!” 
Ai Balqees bata san lokacin da ta rafka mai wata muguwar harara ba tamkar kwayar idonta zata fad’o. Da mamaki yake kallonta dan shi bega abinda yayi na hararar ba ya janyo ta suka fito daga toilet d’in zuwa bakin gado yana kallonta danjin dalilin canzawar ta, ta yatsina fuska tare da rungume dogon hannunshi tace. 
“Lallai ma Yaya, kawai sai naje na cewa kishiya ta ga abinda yake damu na ko?ni bana son wannan abun wallahi ina shan wahala gara idan asibitin zamu ka kaini wani daban amma ba wadda ma aunty Nadiya zataji matsala taba.” 
“Ikon Allah baby kishi kike da Nadiya?!” 
Ya fad’a yana mamaki ta ta6e baki tare da yatsina fuska, sam be san abin Balqees ya kai haka ba sai yanzu. Tabbas ya san Nadiya bazata cutar da ita ba, yasan halinta yasan abinda zata yi mai kyau da marar kyau, ko kaffara ba zai yi ba yasan idan ta sanar da Nadiya baza ta ha’ince ta ba ko rantsuwa yayi ba zai yi kaffara ba amma tunda ba ta so zai bari suje wani asibitin. 
    Lokacin da Balqees ta cika wattani biyar a gidan Sultan Ahmad lokacin ne ita kuma Nadiya Allah ya k’ara azurta ta da wani cikin, sam bata gano ba sai jiya gashi sauran sati biyu a fara azumi. Tashi tayi da wata iriyar kasala har lokacin tafiyarta aiki yayi amma ta kasa tashi gashi su Sultan basa nan sun tafi makaranta ta mik’e da kyar ta mik’e taje cikin aid box d’inta ta ciro test trip tare da shiga bayi ba jimawa sai gata ta fito tana murmushi fuskarta da alamun ruwa tayo alwala. Sallaya ta shimfid’a. sallah tayi raka’a biyu ta dad’e cikin sujadar ta kafin ta d’ago ta kuma yin addu’a. Saurin tashi tayi ta shiga bathroom tayi wanka ta shirya itama ta fita gurin aiki dama humaira na gurin Ummi an sanya ta a day care hakan yasa komai yake zuwa mata cikin sauk’i.
   A sannu sannu Nadiya take tafiyar da harkokin rayuwar ta, sam bata bari ta nuna musu cewar ga abinda yake jikin ta sai dai a lokacin ne kuma Sultan ya matsa mata, duk sanda aka ce yau itace take dashi to ranar babu sukuni indai tana gida yana gida. abin yana bata mamaki tamkar ita kad’ai gare shi. 
Ana gobe za’a fara azumi suna kwance bayan ya samu nutsuwa tana jikinsa duk ta nanik’e mai, so take tayi mai magana shin wani abun yake sha ne ya k’ara mai k’arfin sha’awa ko kuwa dai Balqees bata bashi sai yazo gurinta, ko kuma yanzu haka ya dawo tamkar wani mabuk’aci, amma ta rasa ta ina zata fara dan kar yayi mata wata gurwar fahimtar. Cike da dakewa tace, 
“Abban humaira.” 
Nadiya ta kira shi a hankali tana faman lankwasa mai yatsun hannun shi, ya sake manna ta a jikinsa domin k’amshi ta yana matuk’ar ratsa zuciyar sa yace. 
“Na’am my Nadi ya aka yi…?!” 
Tace, 
“A’a abban humaira gani nayi yanzu ka zama wani harj duk da dai a dama haka kake amma yanzu tamkar ba mata biyu gareka ba meye sirrin?!” 
Juyo da ita yayi tare da sanya hannu ya kunna fitilar gefen gado haske ya kauraye d’akin kalar green, hancin ta yaja tare da kashe mata ido d’aya tayi murmushi tana kallon kyakyawar fuskar shi. soyayyar sa da kaunar sa suka k’ara bijiro mata tana jin shi har cikin k’ahon zuciyar ta. Tana son shi so mai matuk’ar girma tare da kishin sa mai tsananin zafi sai dai takan yi addu’a Allah ya sassauta mata ya dinga bata ikon dannewa tunda yanzu ba ita kad’ai bace dashi karya wahalar da ita duk da cewar ya riga yayi dashin da ko beyi mai ban ruwa ba toh baya bushewa. 
“My Nadi gajiya kika yi dani ne kike tambaya ta..?!” 
Da sauri ta kalleshi tana girgiza mai kai alamar a’a kafin takai bakinta saman goshinsa ta sumbace shi tare da cewa. 
“Ban ta6a jin ka ginshe ni ba abban humaira koda a cikin mafarki ne, kuma idan ba’a gurin mu ka samu ba a ina zaka samu? kayi hakuri idan maganar tawa ta 6ata maka rai kaji mijina.” 
Janyo ta yayi jikinsa sam bata son 6acin ranshi kullum burin ta yaji dad’i tasa shi farin ciki da walwala, baya jin ta ta6a yi masa wani abun na rashin dai-dai a cikin sanin ta sai dai sa6anin haka. shine ma kullum yake cutar ta yake sata damuwa yake mata abinda bata jin dad’in sa, shin me zai yi mata a rayuwarsa wanda zai sata cikin farin ciki da nisha d’i kamar yadda yake ji idan tayi mai? idan ya sai mata mota yana ganin ba wani burgeta zai yi ba domin tun kafin ya auro ta take da mallakinta, gold shine abin sawar ta koda yaushe, ko ya sai mata ba wani sabon abu bane a wajan ta. kai ta hajji taje ta kuma zuwa ko yanzu taga damar zuwa za taje dan haka idan ya biya Mata ba wani sabon abu bane a gurin ta shin me zai yi mata…?” 
“Me zan miki ya saki nishad’i kamar yadda kike bani nima Nadi..?!” 
Ya fad’a a bayyane ba tare da ya san maganar ta fito fili ba, ji yayi tana shafar k’irjin sa tare da cewa. 
“Ka bani soyayyarka, kulawarka, da tattalinka sune kawai zasu sanya ni cikin farin ciki a rayuwa ta, karka wulak’anta ni ko ka guji ni yin hakan a gareni shine zai iya tarwatsa duk wani farin ciki na da jin dad’ina. ina sonka Ahmad so mai tsafta mai tsanani, please karka wulak’anta ni aduk yana yin da zan tsinci kaina..” 
Story continues below

Tashi yayi zaune tare da janyo ta ya sanya ta a jikin shi, zuciyar sa ta k’arye sai kawai kwalla ta fara zubo mai tana sauka akan kafad’unta. Nan da nan ta rikice tana k’ok’arin juyawa ta kallesa amma ya hana hakan ganin yana hawaye yasa ta fara bashi hakuri itama kawai sai ta fashe da kukan suka had’u suka yi tayi babu me lallashin wani. 
   Murya na sark’ewa jikinsa duk yayi sanyi tausayin ta da darajar ta suka k’aru a cikin ranshi yace. 
“Dan Allah Nadiya ki dinga nuna min 6acin ranki ko yayya ne ina gani, wannan hakurin naki da kawaicin naki zasu iya jefani a wuta domin zan tayi miki abubuwa ba kya nuna min bare na gyara kuskure na please Nadi please.” 
Sultan kuwa jiyayi kanshi na wani irin juya mai ya dafe kai tare da rintsa idanuwa yana k’ara matseta a jikin shi, 
“Anya idan ya rasa Nadiya zai samu wadda zata maye mai gurbinta?” Balqees ce, no baza ta iya ba dan abu k’alilan yake had’a su zata yi kicin-kicin ta 6ata rai. 
“Allah yayi miki albarka matata, Allah ya baki aljanna mad’aukakiya, in dai har miji yana bawa matarsa aljanna toh Nadiya na baki aljannatul Firdausi, Allah ya zama gatanki ni dai babu abinda zan iya nunawa nace nayi miki sai ma bakanta miki da nayi ta hanyar auran wadda kika san ina matuk’ar so, kiyi hakuri ki yafe min wallahi ina sonki ina alfahari dake.” 
“Amin mijina ka bani aljanna naji dad’i ko yanzu Allah ya d’auki raina na san bani da haufi.” 
Ranar basu rintsa ba ko wanne da tunanin d’an uwansa a ranshi, har wajan k’arfe uku sannan ta shiga bayi ta had’a musu ruwan wanka suka yi tasa shi suka yi nafila ta kalleshi cike da kulawa tace. 
“Abban humaira jika tashi babyn ka muyi sahur bari na dafa mana indomi shaf-shaf.” 
Kasa kallonta yayi sai yayi ma kamar gyangyad’i yake yi kuma tasan k’arya ne, murmushi tayi tare da jan hancinsa sai ya bud’e ido k’ad’an tare da cewa. 
“Na’am magana kike?” 
Tace 
“Cewar nayi kaje ka kira Balqees muyi sahur zan dafa mana indomie.” 
“Oh toh kije ki taso ta mana tunda fita zaki yi.” 
“A’a kazo muje ka wuce d’akin ta ka tashe ta domin ko wace mace tana jin dad’i idan taga mijinta yana tashinta ni kuma sai na shiga kitchen.” 
K’in tashi yayi duk da yana son zuwa, ganin haka yasa ta mik’ewa tare da kamo hannunsa sannan ya tashi suka fita ta wuce kitchen shi kuma bedroom d’in Balqees. 
   Kwance ya tarar da ita tasa pillow a bayan ta tasa wani a gabanta ta rungume sai shak’ar baccin ta take yi, ya k’arasa wajan gado tare da d’auke na bayan ta ya zauna a gurin yana lek’en fuskar ta. A hankali ya zare wanda ta rungume d’in ai kuwa cikin baccin ta fara k’ok’arin kwace abinta yana ja tana ja can dai ya sakar mata tare da d’ago ta baki d’aya ya zaunar da ita sai a sannan ta bud’e ido a hankali tana kallonsa.
Story continues below

“Tashi muje ayi sahur.” 
Da kyar ta farka sai da tayo bursh sannan suka fito zuwa parlor, cikin sauri Nadiya tayi musu suka ci sannan Balqees ta shiga d’aki suma suka koma ran Sultan fari kal. 
Haka rayuwa taci gaba da garawa a gidan sultan ko wacce yana iya k’ok’arin sa wajan ganin ya bata kulawa ta musamman tare da matsayi mai girma. B’an garan Balqees sai dai hamdala takan d’an sakar masa jiki amma fa bawai dan taji sauki ba, gashi sai kashe kud’i yake yi akan matsalar ta. lokacin abba ya k’irata suka sanar da ita yawan gadon dan iyayanta suka bar mata. Tasha kuka a ranar da kyar Sultan ya lallasheta. Da sallah da kan shi yaje ya siya musu kaya iri d’aya kud’i kawai ya basu na d’inki dana takalma sabida ko wacce akwai irin wanda yafi kwanta mata a rai. Duk aiyukan sallan nan tare suka yi shi sai dai duk Nadiya ce karfin yin domin tafi Balqees kazar-kazar da kuma kwarewa takan nuna mata yadda zata yi wasu abubuwan. 
Kwana biyu da yin sallah suka shirya tsab zasu je gidajen abokan sa, d’akin Nadiya ya fara shiga ya ganta tana shiryawa ya k’arasa har inda take. Sosai yaga ta kuma yin haske jikinta ya kuma cika tana sanya awarwaro ya sak’alo ta jikin sa tare da shak’ar kamshin jikinta a hankali yace. 
“Wai my Nadi meye sirrin ne? Ta ko’ina k’ara kyau kike yi kina kuma yin sweet gaya min.” 
Tayi dariya tare da cewa. 
“Kai ne sirrin abban humaira.” 
“Ah haba dai kice na kuma bige wani aiki…?” 
Ya fad’a yana k’ok’arin zura hannu cikin rigar ta zai shafo cikinta, tayi saurin tankwa6e mai tana dariya tace. 
“Ni ba haka nake nufi bafa, kaga ai kwanciyar hankalinka shine nawa toh kaga kuwa dole ka dinga ganin canji, duk lokacin da kake cikin damuwa shima zaka ga hakan a tare dani.” 
“Wow Nadi idan ina sauraran maganganunki nakan jina tamkar wani d’an bawai, suna sani cikin nishad’i sannan ina alfahari dake a cikin rayuwa ta I love you.” 
Rungume juna suka yi cike da shauk’i sannan ya d’ago da ita yace. 
“Kin yi kyau kamar karki fita na zauna nayi ta kallonki.” 
Kamo fuskarsa tayi tana kallonsa da hannu biyu ta rausayar da kai tare da cewa. 
“A’a abban humaira kafini yin kyau domin a lokacin da ka shigo sai da naji wani kishin ka kar wata ta ganka kayi kyau tamkar baka ajiye mata biyu ba.” 
“Allah my Nadi kice nan gaba ba zan sha wahala ba wajan yo ta uku? dama gashi ‘yan mata sunyi min yawa zan yi k’ok’ari naga mayo ta ukun nan.” 
Ya fad’a yana kallon kansa a cikin madubi, wani kululun abu ya tukare ma Nadiya ta dad’e bata ce komai ba sai faman kallonsa takeyi kirjinta na bugawa. Jin tayi shiru ne kuma tana tsaye yasa shi juyowa sai yaga ta saki dariya tare da k’arasawa wardrobe tana cewa. 
“Toh idan da alkairi Allah ya baka ikon yi aini bana tsoran kishiya.” 
Nan kuwa ta ciki na ciki ya kalleta tare da turo baki kamar wani k’aramin yaro, tana waigowa ta ganshi sai ta saki murmushi dan ba k’aramin burgeta yayi ba dayayi hakan taje tana gyara mai ma6allansa tare da cewa. 
“Toh meye kuma na shagwa6a ba addu’a nayi maka ba…” 
Kamo ta yayi ya rik’e cikin muryar ta6ara irin ta yara yace. 
“Toh bake bace kikak’i nuna kishi na ba, wato ma so kike nayi wani auran ko?!” 
“Abban humaira ke nan ina kishin ka mana kawai dai na san bazan iya ja da ikon Allah bane idan na nuna kishi bashi zai hanaka k’aro aure ba dan haka ni koda yaushe fatana Allah ya baka yadda zaka iya karya baka abinda ba zaka iya ba amma ina kishin ka wallahi.” 
D’aukar ta yayi yana juyi da ita a tsakiyar d’akin, dai-dai lokacin Balqees ta shigo d’akin Nadiyan dan tana son ta nuna mata yadda d’ankunnanta yayi taji ko duk haka suke, sultan ta gani yana juyi da Nadiya tana cewa ya sauke ta amma yak’i sai da suka ga Balqees karaf sannan cikin dakewa da basarwa ya direta a hankali yana kallon k’ofa yace. 
“Baby shigo mana.” 
Da kyar ta sai-sai ta kanta dan ji tayi hajijiya na k’ok’arin kaita k’asa, kallon Nadiya tayi wadda ta juya tana warware mayafin ta jiki a sanyaya tace. 
“Dama zuwa nayi kinga d’ankunnan nan ya babu nan gurin ko duk haka suke??” 
Juyawa tayi ta kar6a tare da dubawa tace. 
“Oh eh haka suke nima kinga nawa.” 
   Ta fad’a tana nuna mata kunnan ta, kar6ar nata Balqees tayi tare da ficewa daga d’akin, haushin Sultan ya cika ta fam, duk fa a cikin girkinta ne dan sai da yamma tukunna zai koma gurin Nadiya amma dan bak’in munafinci yaxo yana ha’intar ta. (Kunji fa! Bafa haramun bane dan miji ya kula d’ayar matarsa dan ba kwannanta bane in dai ba saduwa suka yi ba wannan tabbas hakkinta ne amma wasa da dariya da sauran abubuwa duk zai yi da uta. kai Allah ya rabamu da wahalallan kishi kana yi ana jin haushin ka). 
Sosai yaji kunya amma yayi fuska dan kar Nadiya ta gane yana yin da ya shiga, kallonta yayi tare da matsawa wajan ta yace. 
“Samin turare ku fito mu wuce.” 
“Innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un” 
Ya fad’a cikin zuciyar sa kafin ya nemi waje ya zauna a kusa da ita ya janyo ta zuwa jikin sa. 
“Menene kike kuka baby?” 
_”Ban sani ba! rainin hankali, wai ita yake tambaya bayan ya riga ya sani.”_ 
Ta fad’a a cikin ranta, ji tayi ya tura ta kan gadon ya kuma danneta yana sanya bakin sa cikin kirjin ta, turesa ta dinga yi amma fur yak’i d’aga ta sai ma juyo da ita da yayi yana lashe mata hawayen fuskar tata tare da shafar gashin kanta hakan ne yasa zuciyar Balqees fara yin sanyi sai da yaga ta dena hawayen sannan ya mik’e tare da shiga bathroom ya d’akko towel tare da tsugunnawa a gaban ta yace. 
“Oya hau ke kuma na goyaki sai mu fita parlor itama ta ganki.” 
Dariya tayi tana cono mai baki tak’i hawan ya juyo yana kallon ta ya kashe mata ido tare da cewa. 
“Kin yafe kenan?!” 
Share shi tayi tare da gyara fuskarta tana yafa maya fi tace. 
“Ni ka tashi mu tafi bana so…” 
Sannan ya rankwafa dai-dai saitin fuskarta ya tura mata baki alamar tayi kissing d’in shi aikuwa tayi mai sannan suka juya suka fita, a parlor suka tarar da Nadiya sai kawai suka jera suka bar parlorn zuwa parking space, mota suka shiga suka bar gida…..safe trip

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like