MIN QALB 10

Advertisement

 _*MIN QALB 11*_

_mamuhgee_


Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins hudu golden and red sbd girmansa ga kalar dasuka qara qawata palon,

Shine palon da dukkanin familyn ZABEERA ke meeting acikinsa qarshen kowane wata to wannan watan ma hakan ce tafaru dukkanin daukacin zabeeras dake jahar suna cikin palon kusan su sama da arbain kowanne yasamu guri ya zauna ana tsimayin fitowar me kankat wato Modibbo Wanda fitowarsa tayi daidai da tsit da gurin ya dauka sai gaisuwa kawai dake tashi Yana amsawa ta hanyar ‘daga Kai batareda ya bude baki ba.


Zama yayi Yana bin kowa da kallon jinjinawa na riqe wannan al’adar dasukayi har idanuwansa suka sauka akan MD ZABEERA wanda ke zaune can bayani iyayensu dukkanin hankalinsa gabaki daya Yana Kan waya dayake karanta email din saqo daya shigosa,


Kallon zamansa Modibbo yayi har zuwa fuskarsa dake daukeda wani irin kwarjini da haiba ya jinjina Kai Yana cewa’

Advertisements


Tabbas Babu wani zabi daya wuce akan mulkin zabeera ayau taron naka ne.


ZARAH kuwa duk da ta shige cikin ‘yan uwa da qawayenta ‘yan uwanta Amma hankalinta na kansa akai akai take satar kallon gefen dayake sbd ganin yauma dai kamar ko yaushe arayuwarsa ya kebe ne daban duk da yanzu duk Wanda yashigo cikin qanne da tsaransa ma harma da wainda suka girmesa zuwa sukeyi suna gaidashi Wanda Shima yawanci daga Kai ne kawai bai cika bude bakinba Yana amsawa musamman sbd rashin sabo da Yan uwan duk wasu da dama baisansuba.


Khalil ne abokin zamansa akowane meeting tun quruciya Amma yau Khalil din baishigo da wuri ba Abinda baitabayiba ranar meeting wato latti.


Khalil kuwa yanacan ne hanyar gidansu amatu data Hana rayuwarsa da zuciyarsa sukuni,

Tsawon kwanakin Nan bayan haduwarsu da ita bincike yayi me kyau akanta sbd shigo da ita a rayuwarsa Dan sauya musu ingantacciyar rayuwa dakuma tunaninta daya kasa fita ransa da kansa,

Tabbas yasan babban laifine a zabeera neman aure a waje wanda bama ataba yiba asai yanzu dazai Fara shigo da tsarin karya dokar manya sbd bayajin zai iya hkr da maganar amatun a shirye yake daya tallefi yarinyarda zuciyarsa ta riqe a gani na farko Koda hakan na nufin barin zabeera ne barema yasan zai shawo kansu da taimakon MD.


Babban rashin sa’ar dayaci shine bayan isarsa kawu yayi Masa bayanin aiki tasamu ta tafi training Amma dai yabasa numbernta Dana usi din duk da shi Usin Rakata kawai yayi dawowa zaiyi.

Advertisements


Koda ya karba lambar agogo ya duba yaga yayi lattin meeting ga umme Bata gansa ba sai kiransa takeyi 

sai bai tsaya Kiran numbrn ba yayi saving tareda dawowa zabeera cikin sauri sbd yasan zuwa yanzu anfara meeting din.


Yana qoqarin shiga gate din zabeera yaga motar ‘yan jarida na tsayawa ta gate suna qoqarin gyara cameras dinsu ya Dan tsaya Yana kallonsu cikin mamakin meya kawosu musamman ma da zabeera basa muamala da duk Abinda zai hadasu da ‘yan jarida sbd tsira da mutuncinsu da sunans ahalin,

Ganin yayi latti sauri yakeyi yasa bai tsayaba yashigowarsa,

Yanayin parking harabar gidan Kiran nuratu nashigowa wayarsa ya saki siririn tasaki Yana dafe kansa dake Masa ciwo sbd rashin bacci kwana biyun yayi rejecting kiran ko Ina bai tsayaba Kai tsaye ya nufi palonsu na meeting dasuke Kira da zabeera hall.


Yana shiga yaga har anyi nisa yayi saurin yin gefenda ya hango md zaune Ya lumshe fararen idanuwansa ya kwantarda kansa ta baya jikin kujerar dayake Yana sauraron Abinda ake fada cikin nutsuwa.


Qoqarin miqewa alhaji qarami yakeyi zaiyi mgn suka Fara jiyo hayaniya me ‘dan qarfi tana tashi daga wajen qofa,

Sharewa sukayi alhaji qaramin yafara bayani Amma sai gaba hayaniyar keyi

Alhaji qarami ya kalli yakub babban ‘dan alhaji qaramin yace”


Yakub dubo meke faruwa ne.


Miqewa yayi ya fita Dan dubowar sukuma suka cigaba da meeting din.


Mintuna biyu da fitar yakub sai gashi yadawo da sauri yazo gefen babansa yayi qasa da murya yafada Masa abin dake faruwa da sauri ya kallesa Yana cewa'”


Mene?


Kowa najin haka yayi tsit suna jiran jin abindake faruwa.


Je kashigo dasu””alhaji qarami yace Yana qoqarin cigaba da bayanin dayakeyi.Sallama sukayi wadda tasa kowa juyawa hadda Shima dazaiyi maganar duk suka kalli qofar wadda ke seti tana kallon center inda Modibbo yake zaune Shima sbd ba’a taba barin wani shigowa ba idan suna taron yasashi dakowa ya kalli qofar.


Baba Jamila ce agaba amatu na bayanta fuskarta rufe da doguwar hijab dinda tasaka fuskarta da idanuwanta a kumbure sosai sunyi jajir tsabar aboniki dasuka Sha kamar wadda tayi wata biyu tana kuka.


Tsit sukayi kowa palon na aika musu da kallon mamaki da jiran bayani Amma sai qif qif baba Jamila keyi da idanuwanta tana sunkuyar da Kai.


Alhaji qarami ne ya kalleta tareda kallon amatun dake bayanta kafin ya kalli qafafunsu har zuwa zamansu ya gyara murya yace”


Malama Yaya dai??

Lafiya??

Daga Ina??


Saurin zubewa qasa tayi tareda sauke kanta qasa cikin rawar murya tanason fashewa da kuka tace”


Ranka ya Dade adalci nazo nemarwa ‘yata…,


Kowa kallonta yayi wasu Kam Kai tsaye kallon mahaukaciya suke Mata mamakinsuma yanda akayi tashigo zabeera harta iso Nan din.


Cikin mamaki alhaji qarami ya miqe ya qaraso gurinta ya tsaya Yana cewa'”


Malama adalci kike nema ai banan ake zuwaba,

Mu Nan Kinga Muna wani taro ne me mahimmanci kinyi batan hanyane kije security zasu nuna Miki qofar fita……


Girgiza Kai tayi wannan karon tana fashewa da kuka Mai shiga zuciya tana bubbuga kanta.


Yanxu Kam mamakinsu yafara cirewa sai fargaba

Kamar daga sama taji saukar muryar dattijo me ran qarfe,

Muryar data saka ‘yan hanjinta kadawa Dan tsoro da firgita da wani irin amo yace”


Idan da kanki a hayyacinki kikazo Nan kifadi Abinda yakawoki kokuma ki hadu da hukuncin kutse da datse mahimmin Abu acikin zabeera.


Jan hanci tayi tana shage hawayenta dasukaqi tsayawa murya na rawa tace”


Ranka ya dade ‘yatace gatanan cikine a jikinta……


Cikin tsawa me qarfi alhaji qarami ya e”


To Nan asibitine ko gidan aurenta dazaki……


Uban cikin Yana Nan”””ta katsesa cikin rawar murya tana sake bulbulo da ruwan hawaye.


Atake gurin yayi tsit kamar ruwa ya cinyesu musamman Modibbo daya gyara zama Yana kallon matar da kyau kafin ya dago ya kalli amatu dake tsaye har lokacin tana matso hawaye cikin hijab.


Kallon amatu yayi cikin wani irin amo yace”


Ke yarinya bude fuskarki kiyi bayaninda mahaifiyarki keson fada saidai duk Abinda zaki fada kifara tunanin a inda kike.


Qarar wayar Dr khalil ce ta katse maganar Modibbo wadda tasa kowa juyowa ya kallesa da sauri ya Danna wayar tareda miqewa ya fita da sauri Yana magana qasa qasa sbd daga asibitinsane ake Kiran wasu takardune da ake buqata emergency yace suzo su karba Nan gida.


Harabar gidan ya nufa gurin motarsa yana tareda budewa ya dauko takardun cikin Burnet din motar ya nufi bakin gate ya fita Dan miqawa Dr ashir.


Sama sama yayi Masa bayanin takardun sbd hankalinsa dake Kan ‘yan jaridar da har lokacin suna gurin take yaji yakasa samun nutsuwa da hakan,


Meke Shirin faruwane?

‘yan jarida a qofar zabeera,

Ga Kuma wasu baqi aciki suna maganar anyiwa ‘yarta ciki…..


Da matsala yafada Yana sallamar Dr ashir ya juya ciki da sauri Yana tunanin Dole da akwai inda matsala take,

Me zaisa wannan matar su gayyato ‘yan jarida??anshirya hakan ne Dan idan baa karbi cikin bane kokuma me??

Something is definitely fishy mezaisa tazo da masu jarida ita Bata damu da mutuncin ‘yarta bane idan Yan jaridar suka watsa to kodai tanada wani manufa be??? Oh no..” yafada da sauri tareda yin ciki da sauri haryana hadawa da gudu gudu…


Karo yayi da mutum Wanda yasashi yin baya zai Fadi USI yayi saurin rikosa Yana cewa'”


Dr.


Da sauri Dr khalil din ya dago Ya kalli Usin mamakinsa a bayyane Dan komai nasa ya nuna mamakin cikin sauri yace”


Usman?

Kaine anan?

Me kakeyi anan??


Kallonsa Usman yayi Yace”


Aiki amatu tasamu anan……


Saurin gintse bakinsa yayi sbd shaf ya manta Abinda ya kawosun.,


Ya shafo kansa Yana waskewa yace”


Dr kaima me kakeyi anan din???


Kafa Masa Ido Dr khalil yayi ba Wasa a fuskarsa yace”


Wane aiki ne amatu tasamu anan din??

Ina amatun take????


Shiru yayi Yana shafa Kai Yana qoqarin hado qarya Dr khalil ya katsesa da cewa”


Ina amatun?


Rasa yanda zaiyi yayi yace”


Tana ciki tashiga da wata Mata…..


Wattt???

Yafada da qarfi cikin firgici da tashin hankali yace”


Meke faruwa?

Me sukaje yi?

Infact meya kawoku Nan din nakeson ji””zuwa lokacin yafara hasala yace”


Kuma wlh karka kuskura kamin qarya.


Kame kame usi yafara Yana neman yanda zaiyi saidai gskia zai fadawa Dr khalil idan yaso qila shi zai taimakesa ya shawo Masa Kan amatun kar tayi Abinda zatayin

Kallonsa yayi tareda jansa gefe yace”


Dr Dan Allah kayi alqawarin zaka taimaki amatu bazakayi Abinda zai jefata hadariba Dan Allah kayi wannan alqawarin.


Cikin zaquwa Dr khalil din yace”


Koba Dan alqawarinka ba bazan taba Bari amatu tashiga hadariba zan tsaya Mata ako Inane just tell me.


Cikin fargaba Usin yafada Masa yanda amatun tayi da hajiya aisha saidai ya boye Masa da yardar amatun nuna masa yayi kamar tursasata hajiyar tayi sbd amatun ta daukar Mata kudi.


Tsit yayi kamar ruwa ya cinyesa 

Har wani duhu duhu idanuwansa ke gani sbd tsananin tsoro da firgicin zancen,

Ita umme ko tunanin hadarinda zata jefa ‘yar mutane batayi da kantama tunda komai jimawa dai wataran gaskia zata fito,

Idan ita amatu hankalinta bai Kai ba ita meyasa zatayi hakan??

Qarin tashin hankalinsa MAHMOUD za’ayiwa wannan mummunar 6ata sunan

Haqqinsa bazai bar umme ba hattasu yayanta sai haqqin MAHMOUD ya shafesu Dan haka bazai Bari tadau wannan alhakinba dazai ja Mata azaba gaban Allah hakama bazai Bari rayuwar ‘dan uwansa ta lalace ba hakama amatu rayuwarta nacikin mugun hadari…..


Da sauri ya kalli usi yace”


Usman Yi sauri kabar Nan katafi gida namaka alqawarin dawo da amatu Babu Abinda zai sameta maza katafi karka fadawa kawu komai..


Da gudu ya nufi ciki yayi hanyar palon Yana adduar Allah yasa amatun Bata bude fuskartaba Yana Isa ya fada palon da qarfi daidai lokacinda amatun tariga ta bayyana fuskarta akace ta fada cikin waye ajikinta,meye alaqarsu dame cikin?¿


Bude baki tayi hannuwanta da qafafunta na rawa zuciyarta na harbawa da qarfi zatayi magana tana kallon inda MAHMOUD ke zaune har lokacin idanuwansa lumshe Kuma duk yana jin abindake faruwa kawai dai ba huruminsa bane shiyasa ko hankali bai badaba,

 cikin wani irin sauri Dr khalil ya dako tsalle ya fado tsakiyar palon tareda cewa”


Allah ya taimaki Modibbo nine.


Wattttt????umme tafada da sauri tareda miqewa tsaye tareda haj Maryam

Nuratu ma da antynsa juwairiyya duk miqewa sukayi cikin tsananin firgici

Take palon yadauki hayaniya cikin rasa abin fada alhaji qarami yace kowa yatafi antashi meeting.


Hayaniya aka Fara saidai yanayin Modibbo yasa kowa yin tsit suka Fara sulalewa suna ficewa.


Kaf kowa ya fice Banda uwayensu maza da ‘yannansu maza sai iyaye mata hatta MAHMOUD na gurin bai fitaba lokacinda yaji muryar khalil amatsayin me cikin yasashi bude Ido ahankali ya sauke Kan amatu dake gefen Khalil din tana kallonsa cikeda mamakin daga Inda ya fado.


Kallonsa takeyi tanason Kiran sunansa Amma ganin yanayinsa ta tana hango tsananin 6acin Rai da takaicinda yake ciki,


Idan har da khalil da MAHMOUD yayan hajiya mama ne kamar yanda tafada mata to acikinsu duk Wanda tace shine me cikin ta cecesa daga hawa mulkinda zaa salwantar da rayuwarsa to kenan duk dayane koba komai zatafi farin cikin kubutarda Dr khalil sbd kurkinsa akansu.


Da hanzari umme ta qaraso gabansa ta kalli cikin idanuwansa cikin 6acin Rai tace”


Me kake fada?

Maza maza fice wannan ba Abinda ya shafeka bane…ba magana nake maka ba””ta fada cikin tsawa da firgici.


Gyaran murya Modibbo yayi akaron farko bayan shock din daya samu na daqiqu ya kalli khalil tareda kallon amatu dake kallon Khalil din cikin rashin Jin Dadi qunci da bacin ran datake hangowa cikin idonsa.


Khalilu ta Yaya kazama uban cikin jikin yarinyar na???


Hadiye wani yawu me mugun daci yayi sbd dai gskia bazata faduba Dan idan yafada gski umminsa da amatu duk suna cikin hadari Dan umminsa har zamanta cikin zabeera saiya ware.


Rintse ido yayi ya budesu suna kadawa jajir take jijiyoyin kansa suka firfito sbd qarya ba halinsa bane bare wannan qaryar datafi kowace muni.


Muna sauraronka Khalil kafin fushinmu ya sauka akanka kayi bayani”cewar alhaji qarami.Sauke Kai yayi daga kallonda Modibbo ya tsaresa dashi me girgiza jarumtarsa yace”


Mun jima muna qaunar juna tsawon shekaru uku 

Nasan bazaa Bari na aurotaba shine mukaje wani guri aka daura Mana aure…..tassssssss


Umme tasakar Masa wani gigitaccen Marinda Saida ya zube Kan gwiwoyinsa tareda sauke Kai.


Cakumo amatu tayi cikin tsananin 6acin Rai tace”


Modibbo ba gskia yake fadaba Khalil bazai taba aikata wannan qazamin aikinba wannan ita zata fada ubanda ya Mata ciki Amma badai Khalil ba….hannu ta daga zata kaiwa amatun Modibbo ya daka Mata tsawa da cewa”


Aishatu ki dawo hankalinki ciki ne ajikinta kada hannunki ya sauka jikinta..


Ke matso fili ki fada Mana Abinda yafada gskia ne kokuwa??


Fitowa tayi daga bayan Khalil din tana kallon idanuwan umme dake fitowa da ruwa tace”

Eh gskia ya fada.


A Ina kuka hadu??


A asibitinsa.


Shekara nawa yanxu da auren??


Rawar murya tafara tana neman dufewa tace”


Daya.


Aikuwa take kowa yaqarin tsit cikin tashin hankali.

##mamuh#
______________

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA’ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.


To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.


        Ina ma’abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.


Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.


Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana’arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.


Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.


______________________


#MIN QALB❤️

Mamuhgee


ZAFAFA BIAYAR


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


YANKAN BAYA

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Or 09032345899

Leave your vote

-2 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 40

Advertisement  ##Mamuh#*_MQ 40_*  Kasa daukarta bacci yayi Kuma ko juye juye takasa tadaiyi lamo cikin lullubin duvet tana…

MIN QALB 11

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…

MIN QALB 39

Advertisement   MQ 39_*     Direct wani kebantaccen guri suka nufa daga bayan joint din inda aka…

MIN QALB 18

Advertisement   *_MQ 18_* _Mg_       Koda anty zarah tace yazauna suyi breakfast tare baiso karya…

MIN QALB 50

Advertisement   #*_MQ 50_*     https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg Please subscribe to our YouTube channel 👆👆👆       Advertisements…

MIN QALB 12

Advertisement  *_MIN QALB 12_* _Mamuhgee Kasa riqe hawayenta umme tayi suka gangaro Kan fuskarta ta shafa cikin firgici…