YAU DA GOBE 7&8

Advertisement

 ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

  ๐ŸŒนYAU DA GOBE๐ŸŒน

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

Story & writing by mmn fareesa

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C7p4CLXSUZl7bJQb6ERPgF

 ๐Ÿ…ฟ๏ธ7&8

Wannan shafin na y’an team d’in Sumayya ne๐Ÿ˜Š๐Ÿƒโ€โ™€๏ธ

….Zaman kurame sukayi acikin motar bbu Mai mgn”yyinda Sadiq kesan yyi Mata mgn yarasa abin cewa”harga Allah yanason sumayya sbd ya yaba da hankalinta da nutsuwarta da kamun kanta”Kuma atsarinsa haka yakeso matar aurensa takasance… matsalar sa yanzun UMMA!yasan bazata tab’a yarda”gashi Yana k’ok’arin yakice sumayya aransa Amma sai sake shiga ransa takeyi….ahhhh washhh! Sumayya tafad’a tana dafe cikinta”da sauri yadawo hayyacinsa yadubeta fuska cike da tausayi yace sannu kinji?”munkusa isowa asibitin”da munje

zaidubaki…gyada Masa Kai kawai tayi batare datace komai ba…

Sunayin parking yafito tana biye dashi suka shige cikin asibitin”yana Kara waya akunnansa yana Kiran Dr safana!

Advertisements

      Tana jin suna mgn awaya”amma batasan dawa yakeyiba” har suka iso office d’in sa”suka tsaya bakin k’ofa wata ta fito tukum Sadiq ya shiga Yana cewa sumayya tabiyosa…tunda ta d’ora hannunta kan  k’ofar gabanta yake wani irin fad’uwa…tayi addua tashiga…da sallamah!wani mugun shock taji had’e da daburcewa “sbd arba da fuskar Dr safana datayi kansa aduk’e Yana rubutu a wani file..dakewa tayi ta Ida shiga”Sadiq yace sannu sumayya zoki zauna kinji?”da sauri dr safana ya d’ago kansa jin ance sumayya”dama shi besan wacce zai dubaba”kawaidai Sadiq yace ga patient Abba yace yadubata”had’a ido sukayi shida Sumayyar”atake yahad’a girar sama data k’asa yyi kicin kicin da fuska”kafin yadubi Sadiq dake latsaya waya yace you can go!ok Sadiq yafad’a Yana kallon sumayya dake kallonsa itama”yyi murmushi yace I’m waiting for you”bejira cewartaba yafice…Dr safana yaja gajeran tsaki had’e da cigaba da abinda yakeyi”yyinda sumayya kezaune kan kujerar duba patient”tana jiran daga iya gudun ruwansa….kusan 5 minit”mararta tayi wani irin murd’a wa”k’ara tasaki tana runtse ido”yyinda Dr safana ya yatsina fuska irin ko ajikinsa d’in nan… sumayya kuwa tayi danasanin zuwa asibitin yafi ak’irga”Kuma datasan wajen wannan me girman kan ne zaa kawota datace Tasha magani “sbd bazata iya musu da Abba ba…tunani takeyi azuciyar ta to meyake nufi da irin wannan kalar wulak’ancin”tabbas besan irin darajar da Allah yyiwa d’an Adam ba! Shiyasa yake wulak’anta d’an Adam…saidai Tasha alwashin kozasu tabbata ahaka bazata Masa mgn ba”sbd ai shine likita,shine zai tambayeta meke damunta har tafad’a Masa…

Dr Nasir ne ya murd’a k’ofar yashigo da wani kati ahannunsa yyi sallama!kallon sumayya yyi wacce ke rintse da ido tana yamutsa fuska alamar tana jin jiki”ahankali yace sannu bewar Allah! bud’e ido tayi ta kallesa tana gyada Masa Kai kawai… yyinda Dr safana yyi tamkar bbushi a office d’in”sbd shi azatonsa sumayya batada kunya y’ar rainin wayoce “tashigo office nasa yadubata ai zata gaishesa ko bbu komai… safana ka Gama duba patient d’in takane?”muryar Dr Nasir takace Masa tunani…banza yyi dashi bece komai ba ,fuskarnan ahad’e tamkar besan miye dariya ba”murmushi kawai Dr Nasir yyi sbd yasan halin abokinsa in and out!

    Dubar sumayya yyi yace yadu bakine?”ta girgiza Kai kawai”kafin Dr Nasir yace wani abu Sadiq ya shigo sbd jin shiru bata fitoba… sumayya Yaya,angama dubakine?? Yafada Yana kallonta..mik’ewa tsaye sumayya tayi had’e da cewa muje wata asibitin  adubani Yaya !Sadiq yasaci kallon Dr safana yaga Yana latsa laptop hankalinsa kwance ko ajikinsa”Dr Nasir yace Sadiq kuje kawai… Sadiq bece komai ba”amma yaji bbu dad’i sbd ai Abba yaturosu “Kuma bazaiji dad’i ba inbe dubata ba! Amma me sumayya tamasa da zafi haka??dafe ciki sumayya tayi had’e da cewa dan ALLAH muje inda akasan darajan d’an adam ba inda ake wulak’antashi! dad’in abun nima banina nazo nace adubaniba balle amun wulakanci” hasalima bansan nan asibitin zamuzoba da wlh bazanzoba”shikuma Wanda yace adubanin dan ya isa da mutum ne”yace yaduba”Amma tunda be isa ba bbu…you are very stupid!Dr safana yafad’a Yana huci sbd ganin k’aramar yarinya nagaya Masa mgn agaban Sadiq da Nasir Basu tsawatar mataba”cikin kakkasaur murya yace ke k’azama y’ar k’auye kin Isa kishigo da k’azamin jikinki a office d’ina kigayan mgn yafad’a Yana mikewa tsaye cikin b’acin Rai….Dr Nasir yace calm abokina! sumayya muje Dan ALLAH kayi hakuri Yaya”cewar Sadiq Yana kallon Dr safana”doguwar tsuka sumayya taja had’e da cewa saime danbe hakuraba”nayi mamaki wlh daka d’auki wannan a kurkin office harkake hura hanci dashi”y’ar k’auye dakace bbu komai aikowa k’auye ne tushensa da inyi wayewar wulak’anta jama’a” gara nazauna a y’ar k’auye na….wani mugun juyi Dr safana yyi yadira gaban sumayya yana huci…da sauri Dr Nasir da Sadiq suka rirrik’esa….



Dr Nasir yace calm down abokina meyayi zafi haka?”zaka tsaya kana fad’a in fad’a da mace!kurabu dani dallah malamai”cewar Dr safana Afusace…Sadiq yace sumayya maza kifita nace banasan rashin kunya”yafad’a fuska a’daure”sumayya kuwa dama atsorace take ganin yadda lokaci guda Dr safana yazama zakin fama…lollx..inhar basu rik’esaba Allah kawai yasan me zaiyi mata”tafice sum sum tana tura Baki….ajiyar zuciya Sadiq yyi yace Dan ALLAH Yaya Aliyu kayi hakuri kunsami mis understanding ne”amma sumayya nada hankali da…shout up your mouth!cewar Dr safana Yana k’wace jikinsa  dg gurunsu”yaja tsaki had’e da cewa Ina hankalin yake?” tanamun rashin kunya acikinku bbu Wanda zai tsawatar Mata”to dama bana buk’atar hakan “kufice mun dg office… murmushi kawai Dr Nasir yyi sbd yasan bak’ar zuciyar safana! Fitarsu shiyafi alkhairi”Amma gefen zuciyar sa yaji sumayya tayi mugun burgesa dabataji tsoron safana ba”yasan halin miskilancin sa,k’ila wani wulakancin yamata itakuma bata d’auka.sbd yasaba yima y’an Mata wulakanci. musammun masu cewa suna sonshi..Sadiq ma bece komai ba yajuya suka fice tare d dr Nasir…



   Suna fita Dr Nasir yakalli sadiq yace kayi hakuri da halin d’an uwanka Kuma aminina”inya sauka dg dokin zuciyar zai hakura… Allah yakyauta kawai Sadiq ya fad’a”Dr Nasir yace ameen” but inbbu damuwa ka kirata muje office nawa saina dubata”kasan Abba bazaiji dad’i ba”in yasan abinda yafaru pls karka sanar Masa… okay kwai Sadiq yafad’a “yyinda Dr nasir ya wuce office  kan kujerun bin layin ganin likita ya Sami sumayya azaune fuskarta a’daure sbd shikanshi Sadiq din yabata haushi…sorry my sumy !kinji? Yafad’a cikin wata murya dabata sanshi da itaba”da sauri tadago Kai suka had’a ido yyi murmushi had’e da cewa koba tawa bace? Janye idanunta tayi had’e da tashi tsaye tace pls Yaya muje wlh inajin jiki”kinajin jiki kikayi rashin kunya”sumayya naga k’arfin halinki nayiwa Yaya Aliyu rashin kunya”karki sake kina jina ?”koni bazan iya Masa rashin kunya ba”in Abba yaji ai bazaiji dad’i ba ko?”turo Baki tayi had’e da cewa to amma Yaya kasan shi meyamun ne?”hmmm yanzun komai ya wuce ,muje Yaya Nasir abokinsa yadubaki…kayi hakuri bazan koma Gurin abokinsa ba sbd shi ai  abokin nashi zai dubani”

    Had’e Rai yyi had’e da cewa zakizo muje kokuwa sainakiran abban tunda niban isa dakeba!mamaki sosai Sadiq yabawa sumayya”awane dalili zaiyi iko da ita?”wani hawaye taji sbd tuna rashin ubah yaja Mata agolanci gidansu…batace komaiba tabi bayan sa suka nufi office d’in Dr Nasir..



Advertisements

Sadda suka shiga bbu kowa”nan Sadiq yatsaya yace ta shiga”nan Dr Nasir yyimata tambaya gameda abinda ke damunta?”cikin jin kunya da nauyi tamasa bayani…yarubuta Mata magunguna”cikin tsokana Dr Nasir yace abokiyar fad’an abokina “shekararki nawa”badan tasoba tace 20 sbd hakanan taji tanajin nauyin Masa rashin kunya…godiya tamasa ta fice”yyi murmushi harga Allah sai yaga safana sunyi mgun dacewa da sumayya…tsaki yaja daya tunada rukky…



***************


Yaya Aliyu kuwa mamaki yakeyi akan tsaurin idon wannan tsakuwar yarinyar”saidai yasha alwashin duk lokacin data sake shiga gonarsa wlh zaiyi maganinta”yajima cikin b’acin Rai dg baya yahuce byn yyi sallar azahar sukayi meeting”kafin yaja motarsa batare da yyi sallama da Dr nasirba”nasarawa yyiwa tsinke !wato gdn hajjah kakarsa wacce tahaifi mahaifin sa”sbd yau kwanansa5 da dawowa bejeba ,yasan halin mitar tsohuwar shiyasa zai daure yaje yau kawai..

    A bakin get yabar motarsa”yashiga cikin babban parlourn gdn…zaune hajjah take da glass a idonta da abun yanke farce tana yan kewa tana Kuma sauraren redio d’inta”

Ahaka Dr safana yyi sallama cikin k’asaitacciyar  muryar sa”Baki washe hajjah ta amsa tana cewa gadanga k’usar yak’i “likita bokan turai!ka koma nayi fushi.. murmushin dabaiyi niyaba yasubuce Masa yazauna kusada ita”yadafa ta yana cewa my Mata!ture hannunsa tayi had’e da cewa “kadaiyi matar “dama jiranka nikeyi inshi Usman d’in bazaiyi maka mgn ba “to dole kayi aure dg Kai har saddiqun..kungirma gand’an gand’an daku bbu aure…lumshe ido yyi yanata kallonta azuciyar sa,yace dakinsan yadda namatsu da nayi aure dabaki ce hakaba…yanxun ita rakkiyar tagama karatun ko kuwa??” Murmushi yyi yace haba granny Rukayya fa kokice rukky”…ohon makadai koma minene nidai yadda na iya fad’a Zan fad’a… hannunta yakama yace kiyi hakuri very soon kishiyarki zatazo…fisge hannunta tafisge had’e da cewa”inbazakayi mgn da yarena ba kabari”komai inzaka fad’a saiyi da harshen nasara… tab’e Baki yyi sbd dama yasan tabbas saitace hakan. dakuma yyi aure shiyasa kafin yajeUK besan zuwa gdn..tashi tsaye yyi yace tunda bakya murna da ganina sai mita Zaki tasani gaba kinamun sai anjima”haba kaikuwa me gd na “yanzun Ina tsarabata? yatsina fuska yyi yace banyi dakeba ta my rukky ce duka tsarabata… harararsa tayi had’e da cewa to ko ruwan gdn bazaka shaba! murmushi yyi yataka gaban fridge dake parlourn yafito da robar swan water yace Kinga alamar na isa nasha  ko?”kaidai kasani “yanzun kaje gdn antynku?”(zainab) yace eh naje jiya nasameta cikin wani yanayi”ayanzun haka inasan Abba yyi mgn da mijinta bbu dole inbazai iyaba yasawake Mata aurenshi ai haihuwa ALLAH kebayarwa ,bakuma Dan bayasanta ba kebe bata ba!hmmmm kaidai bari wlh ai gara kadauki mataki”abun Yana b’atan rai”robar ruwan ya ajiye had’e da fito d kud’i y’an 1000 ya ajiye gabanta Yana cewa Mai idon cin nera.murmushi tayi had’e da cewa sunan y’arka ta fari Fatima”dole asaka Mata sunana.. nagode Allah yatsareku yajikan mahaifinku da rahama…cikin wani yanayi yace ameen had’e da Mata sallama yafice…



๐Ÿ๐Ÿ๐Ÿ๐Ÿ๐Ÿ


Bangaren Sadiq da Sumayya kuwa”suba barin asibitin sukaje wata chemist babba yasiyo duka magungunan tukum suka nufo gd “a irin zaman su na d’azun bbu Mai mgn”tun kafin yagama parking hjy jamilah ta bayyana agaban motar tana huci sbd safeenah tasanar Mata taga fitarsu… sumayya kuwa aranta tace Allah yakyauta!ta bud’e ta fito”hjy jamilah namata mugun kallon tsana tace ke agola dg gdn uwarwa kuke yanzun dakuka fita da safe??”Dan ALLAH umma kibarta”asibiti Abba yace nakaita Bata lfy….cewar Sadiq murya amarairaice..oh gaka Kai driver d’in ta ko?”sumayya kanta aduk’e”Sadiq yace ga magungunan ki”ahankali tadago Kai takarb’a”hjy jamilah taja tsaki had’e da cewa yadda uwarta ta shanye ubanka kaima shanyeka zasuyi?”to bazai yuyuba wlh “tun Muna girma da arziki ka fita hanyar matsiyatan muta nan nan ” rintse ido yyi cikin rashin jin dad’in kalamun umma yacewa sumayya wuce kishiga cikin gd…da sauri sumayya tabar    Gurin…Sadiq yazare key din motarsa ,yanabawa umma hakuri”aransa Yana kudurta hukuncin dazaiwa su jidda da safeenah sbd yasan cikinsu wani yasanar Mata..



Zarah ce zaune kan 2 seeter tana tunani”yau kwana3 kenan musty na gaba da ita baya tankamata inta mishi mgn Yana shareta”yau ko a skul be kulataba”sannan tanaso taji dalilinsa nayin gabar da ita dakuma meyasa yakejin zafi in wani yamata mgn ko ta kula wani namiji??”tashi tayi Kai tsaye ta nufi saahensu shida Yaya Aliyu tasan dama da marece duk suna gd”a parlour tasami musty”Yana ganinta yahad’e Rai..itama saitasha mur”zaunawa tayi gefensa yadubi jikinsa danata taga voil ne milk ajinsu”shine yad’inka masu shi iri d’aya”datasan shi zai saka dabata saka doguwar riga d’in ba…broth inaso kabani hankalinka zamuyi mgn! Batare daya kalletaba yace Ina saurarenki!meyasa kake gaba Dani kimanin kwana3??”sannan meyasa kakejin haushi Inna kula wani namiji kokuma masu cewa suna Sona?”ido cikin ido yace cikinsu wacce Zan amsa”?tabe Baki tayi had’e da cewa duka..

Murmushi yyi ahankali yace sbd ni ALMUSTAPHA inason FATIMA ZARAH!Sona aure”bansan tu  sanda nafara sonkiba”Dan ALLAH baby kisoni ko rabun son danike mikine.. yafad’a Yana dafe saitin zuciyar sa…


Sai Monday insha Allah sbd week end Ina tare da ogah๐Ÿ˜œ



Share pls


By mmn fareesa ๐Ÿ–Š๏ธ

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

YAU DA GOBE 45&46

Advertisement  ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ   ๐ŸŒนYAU DA GOBE ๐ŸŒน ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ Story & writing by mmn farees ๐Ÿ…ฟ๏ธ45&46 …..Ummi tana murmushin…

KWARATA 24

Advertisement ๐Ÿ…ฟ —— 24          Muna fita gidan biki Baba ฦ™arami ya ษ—auki wayarshi ya…

YAU DA GOBE 21&22

Advertisement  ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ   ๐ŸŒนYAU DA GOBE ๐ŸŒน ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ Story & writing by mmn farees ๐Ÿ…ฟ๏ธ21&22 *Kamu day* ….da…

YAU DA GOBE 33&34

Advertisement  ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ   ๐ŸŒนYAU DA GOBE ๐ŸŒน ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ Wannan shafin nakine halak malak my k’awar Amana.. mmn nurul…