DUDUWA 19

Advertisement

  ~19~

             Ki ciɓus suka yi da me unguwa zai shiga masallacin, tsabar firgici da rashin nutsuwa mai gari gaba ɗaya bai kula

da me unguwa ba ya wuce zai giftashi ta baya,me unguwa ya damƙo rigar sa da gaban ya koma baya,bayan kuma ya dawo gaban rigar ya ce da shi”


“Ran ka shi daɗe lafiya  ka fito a irin wannan yanayin.


ummm da ummm,mai gari ya shiga yi yana ƙara duba fuskar me unguwa da kyau,har wani murza idon yake yana daɗa zara idon waje amma bai shaida ko waye a gabansa ba kamar wani zararre me unguwa ya janyo shi suka dawo gidan sa ta bayan masallacin suka shiga ɗakin sa da mai gari yana ta dube duben hanya shi kaɗai,

waje ya kaishi ya zaunar ya miƙe shi zai koma masallacin dan yasamu jam’i,da gudu mai gari ya zabura zai fito daga dakin me unguwa ya riƙunƙume shi gam yana tofa masa Addu’a dashi ma mai garin yake tofawa me unguwar yawu yana wani irin abu kamar sha tara har ya koma ya zauna a hankali yana mai da numfarfashin sa yana kuma duban me unguwa.

       Yafi minti shida a zaune ba umm ba umm umm daga gyangyaɗi ya kwasheshi sai kaga yayi firgigit ya farka yana ta tofe tofe hankalin me unguwa ya tashi ya kasa cewa komai sallar asubahin ma sai a gidan sa yayi yasaka mai gari shima yi a ɗakin kasan cewar duk turbaya ne bayan ɗakin sukayi sallah suka zauna gyangyaɗi yafara ɗaukar mai gari har bacci me nauyi yayi awon gaba dashi a wajan me unguwa ya miƙe ya nufo cikin gida yana kwarawa Rabbi kira.

Advertisements


Amsawa Rabi tayi da sauri tazo ta risina a gaban me unguwa ta ce”


“Gani me gida na shiga madafa ne zan ɗora ruwan koko,naji kana ta kirana,ko wani abun kake da buƙata a kayo maka.


“Eh,ina tare da baƙo ne kiyi maza ki haɗa karin kumallo da wuri ki bawa ɗaya daga cikin yaran nan ya siyo mana ƙosai da suga na metan,dan Allah abashi ƙosan da zafi kar ayi min irin ta ran nan.


to insha Allah zan gaya musu,idan an kawo a haɗo maka da kokon?Eha dukka ki basu su kawo mun ina ɗakina.


Advertisements

to,Rabi ta furta ta miƙe daga tsugunan datayi ta koma cikin madafa,shi kuma me unguwa ya dawo ɗakin sa yana tunanin abinda yake damun mai gari,ko dayake ba abin mamaki bane dan wacce ya aura ɗin ta daban ce a cikin mata yaji an fichar da atishawa daga inda mai gari yake bacci,da sauri me unguwa ya juya yana.


“Wala,Ya’uduhu hifzzuhuma,wahuwal Aliyyul Aziim.


Yayi sakatau yana kallon mai gari daya nufo in da yake,koda isowar mai gari sai cewa yayi.


“Aa me unguwa me ya kawo ni gidan ka da safe,ina ita amaryar tawa take?


yallaɓai ga guri ka zauna labarin na da tsayi ka bari cikin mu yagama ɗauka sai kaji yanda abin yake.


Aa sanar dani da wuri ina Duduwa take ba dai wani abu ne yafaru ba me unguwa.


babu abinda ya faru sai alkhairi,duduwarka na chan gida lafiya ƙalau,ka zauna dan Allah kayi karin kumallo sai kaji daddaɗin labarin,mai gari ya samu waje ya zauna yana murmusawa har ɗaya daga cikin yaran me unguwa yayi sallama daga bakin ƙofa me unguwa yaje ya amso kayan ya dawo dan kar ma asan waye a ɗakin ya ajiye a gaban mai gari ya ce.Bisimillah,ranka shi daɗe ga koko da ƙosai da zafin su.


sannu me unguwa da ɗawai niya,nan da nan mai gari ya take kwanan shan da’aka zuba masa yaci ƙosan sosai yayi hamdallah,haka me unguwa ma yashanye nasa har da lakace jikin kwanan shan ya siɗe yayi farau farau da ragowar ya afashi shima ya shanye.


sai da kowa ya tsafe daga gumin daya tsatssafo masa kana me unguwa yace da mai gari yatashi su ƙarasa gidan nasa wajan duduwa,cikin hanzari mai gari ya miƙe suka ɗauki hanya da kowa ya gansu zai duƙa ya kwashi gaisuwa ya wuce suma su wuce har suka ƙarasa zauran gidan mai gari,me unguwa ya tsaya daga zauran shi kuma mai gari ya tura kansa ciki yana me yin sallama da siririyar murya.


*Ashe su mai gari an iya lanƙwasa murya😅*


     

      Duduwar ka najiyo sallamar abin ƙaunar ta ta, tayo waje da gudu tana.“Oyoyo oyoyo,ga masoyi mai gari ƙallemun cikin zuciya ta,ruwan randar dake sanya ni farin ciki sannu da dawowa,baki adashe mai gari ya amsa da.


“Yauwa duduwa ta,wai ni ya akayi nagani a chan gidan me unguwa,waye ya kai ni ban sani ba?


“ɗan dunƙule mana,ai shiya zo jiya tayamu farin ciki shine ya shige jikin ka..😳 Jikin wa?Naka mana masoyi sai yau da safe ya fuce daga jikin naka amma nace masa karya kuma taɓamin masoyi na har abada,ya amsa da to ba zai ƙaraba ka taho muci gurasa tun ɗazu inna ta,ta aiko mana dashi.Ni a ƙoshe nake,ke kici tunda baki karya kumallo ba wato dai jiya ni da kai na aka sharɓane a gidan nan Allah yasa banyi zandar ba kowa ya gani,maganar zuci ta fito waje.


babu wani zandar ɗin da kayi ai shiya saka me unguwa ya kai ka gidansa har kayi bacci a chan ni dai wallahi sai kaci gurasar inna.


shiru mai gari yayi yana tunanin taya zai ɓullowa da kulu tadawo cikin gidan sam bazai samu nutsuwa ba idan daga shi sai duduwa ne kar wata rana ayi abinda ba shikenan ba,karaf duduwa ta ce””Ka kwantar da hankalin ka anjima kaɗan kulun zata dawo da ƙafafunta amma sai kaci gurasar inna,ta turo baki tana ƙunƙunin soyayya,bayanda mai gari ya iya ya tsoma hannu ya ɗauki gurasa yana dannata da ƙyar kamar zata dawo har suka cinye ya baje a wajan yana bacci bai masan yanayi ba.

“””Kwance kulu ke a ɗaki,ita kaɗai abin duniya ya isheta,tunanin mijin ta,take na chan tare da wata daban,ba ita ba zuciyar ta a ƙuntace ran nan ko annuri babu,ita bata saki kuka ba,bata kuma yi dariya ba kawai sai ji tayi an wurgo mata ƙatuwar gana masgo a kanta da sauri ta miƙe zaune tashiga dube dube,duk babu komai a ɗakin sai gana masgon da taji an wurgota a kanta abin mamakin ma har da wata sharɓeɓiyar bulala da gani tasha man shanu sai sheƙi take tana wani irin walwali,kulu tayi kamar zata miƙe tsaye ta bar ɗakin sai kuma tasake komawa ta kwanta,ko kanta bai gama ƙarasawa kan fullon ba aka sharɓana mata bulalar ta ko ina ta miƙe da gudu zata fuce daga ɗakin ina sai jinta tayi ta daki bango ta dawo baya,ta sake yin hanyar ƙofar a fusace,aka kuma gwarata da bangon tasaka ihun daya taso gwaggo da sauri ta nufo ɗakin.


Gwaggo nasaka sayyadar ta cikin ɗakin ana shauɗeta da bulalar,har wani kutufo gwaggo takaiwa iska tayo waje da gudu tana ihu tana susar baya…………….……………………
_*By*_

_*Maman Dr*_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUDUWA 24

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 1

Advertisement 🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_            _1_ ‘Aaa ruwa ruwa na malale……… Ai ruwan bana yaci samari,Amma…

DUDUWA 22

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 25

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…