DUDUWA 20

Advertisement

 ~20~

“Bata tsaya a ko ina ba sai a ƙofar gida,duk wanda yazo giftawa sai ya dubi gwaggo da har yanzu hannun ta na baya tana sosar inda aka shauɗa mata bulalar,Basiru yazo zai gilma kenan ɗan gidan Asabe makotan su kulu ya hango gwaggo na matse kwallah da sosa baya ya gaida ita taƙi amsa masa,saɓanin da da ta hangoshi daga nesa zakaji gwaggo ta fara”ɗan jikalle da wasa da dariya har ya wuce suna wasan jika da kaka,Basiru ya sheƙa gida a guje yaje ya sanar da Asabe halin da yaga gwaggo a ciki,Asabe ko takalimi babu tayo ƙofar gidan da sauri ta nufi gwaggo dake tsaye tana sosa baya,nufota tayi cikin sauri haɗe da furta”


“Gwaggo lafiya kuwa?


“Asabe ina fa lafiya shiga gidan ki gano.


Me yake faruwa a cikin gidan gwaggo ina Hauwa kulu take,to subhanallahi ba dai ita ke ihun nan haka ba bari nagani,da gudu Asabe tayi cikin gidan tana sallati,da shigar ta gidan tayi ɗakin da ihun kulu ke fitowa kai tsaye ko ƙarasa shiga asabe batayi ba aka kwasha ƙafafuwan ta aka yarɓar a tsakar ɗakin ga uban bulaliyar da aka shiga jibgar Asabe da ita,ta ƙafa ta ka har jikin ta ba’a bari ba Allah yabata ikon tashi a guje Asabe ta kwashi kafafuwan ta tafito tana a sosa da wani irin kukan zuci me wahalar fassaruwa,mutanan da suka cika ƙofar gidan sukayo kan asabe suna tambayar lafiya Asabe, cikin su har da ɗan ta basiru,Asabe ko tata bata iya fadi ba tayi hanyar gidan ta tana tafe tana a sosa,data sosa ƙafar sai tayi sauri ta dawo kanta tana wani irin kukan zuci da babu kwallah a idon tsabar masifar zafin da bulalar take dashi.


Advertisements

        Ma’u ce ta dubi sauran maƙotan da suka taru agun tace.


“bari muma mu leƙa muganewa idon mu abinda ake yi a gidan wata ƙila kulu ce tafara haukacewa daga anyi mata kishiya”ai kuwa Ma’u leƙo mana muga me take shukawa tunda gwaggo taƙi sanar damu banda soshe soshe babu abinda take yi ,ɗaya daga cikin matan ta furta,kai Ma’u ta tura cikin gidan tashiga saɗaf saɗaf yanda baza’aji takun taba ma bare a raɗe ta,acewar zuciyar ta har ta iso ƙofar ɗakin da kulun take,a hankali ta ɗan leƙo da kan nata ciki ta hango kulu ta haɗa jini da majina tayi baje baje a ƙasa tana rasga uban ihu,Allah cikin ikon sa sai ji Ma’u tayi an daki ƙeyar ta tabaya an hankaɗo ta cikin ɗakin aka sake kutufar hancin ta,ta gaba,a take ma’u ta zube a ƙasa tana lalubo inda hancin nata ya faɗi.

A haka ma’u tayo ƙundun bala tayi iyo cikin laluban ƙofa tayi ƙofar gida da rarrafe tana tafe tana””


“””hancina Uwale,ku bani hancina na maida.


da gudu sukayo kan Ma’u suka ɗagota,uwaila ta kama hannun ma’un data rufe hancin da ɗaya hannun nata da ƙyar ta kwaɓe daga kan hancin ma’u


 ƙafafuwa me naci ban baku kowa ya ibi na kare yana”


Jama’a Hanacin Ma’u………….

Advertisements


     

*yo ni kai na dana hango hancin ma’u,wato na ɗauka da gaske babu hancin,gaba ɗaya an shafe babin sa a mazaunin sa ya shige loko ko ƙofofin hancin sai kayi da gaske zaka lalubo su,wannan kutufo ko dame akayi shi aradu😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂fan’s waya san hannun daya naushi ma’u hekarunsa nawa a duniya😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂*


“kusan gaba ɗaya matan wajan guduwa sukayi daga ma’u dake ihu sai gwaggo dake susa sai mazajen matan da sukajiyo ihu da guje gujen mata a wajan suka zo wajan da sauri suna tambayar ba’asi nan yara da ragowar mata dasuke da dakakkiyar zuciya suka shiga faɗa musu abinda ya faru har da ƙara gishiri akai gaba ɗaya hankalin kowa ya dawo kan gwaggo,Zaliha ce ta dubi gwaggo ta ce”””.


“wai gwaggo meye a cikin gidan naki yau yake rikita mutane haka kiga hancin ma’u yanda ya bashe kamar kwalta………………”wayyoo gwaggo wayyo kai na,ku kai ni gidan mai gari dan Allah ku miƙani kar su kashe ni da duka,innalillahi ta ina gidan mai garin yake.


kulu ce ɗauke da jakar bakko ɗin ta aka idon nan ya kaɗa yayi jajir fuskar duk shatin bulala tayi inda gwaggo ke tsaye,gwaggo na ganin kul tayo gunta tayi cikin mutane tana””


Ku ɓoye ni,kar ku bari ta gano ni.


cike da mamaki jama’a suka fara tambayar.


Kulu ina za’akai ki.


gidan mai gari zaku kai ni,na rantse bazan kuma fitowa ba har na mutu ku taimake ni ku kai ni dan Allah,”ku rakata mana tunda tace akai ta nima ba iya zama zanyi da ita ba ɗan haru dan girman Allah ka sakata akan hanya tayi tafiyar ta salin alin bakin kowa aleko jikin mu ya huta.


     “Haba gwaggo ba a cikin hankalin ta take ba kiga yanda takeyi kamar mara lafiya ki ce akai ta shi me ya hana mai garin zuwa yin bikon ta.


Ni dai ku miƙani wallahi na yafe masa bikon duniya da lahira zan koma haka,na shiga uku ɗan haru ka miƙani nace.


ku miƙata dan girman Allah ɗan haru kar kayi gardama gashi har jaka aka bata.


gwaggo ki barmu da mai garin nan babu inda kulu zata kom…………ɗan haru bai ƙarasa faɗin abinda yake son faɗi ba aka zuba masa tashi bulalar datasa ya ɗauki hanya ɗoɗar babu waiwaye,daga chan sukaji ana.


      “Ya ku bil adam,ku ɗumguma ku raka kuluwa gidan ta na aure duk wanda ya tirje hmmmmmmm,akayi shiru nan da nan jikin kowa ya soma makyarkya ta,kowa ka duba idon sa a firgice maza da mata suka saka kulu a gaba suna baya tana gaba suka rako ta har gidan mai gari babu buɗa bare waka magana ta fatar baki ma babu wanda ya iya tankawa daga rakiya kowa suri takalman sa ya fece daga nan su gwaggo akayi gidan ƙanwarta ladi dan gidan gaba ɗaya tsoransa takeji yanzu.

   Ba ƙaramun mamaki mai gari ya shaba ganin kulu duƙunƙune a saman gado da sauri mai gari ya ƙaraso yana dashe haƙori ya ce”””


“”Aa kaga uwar gida ran gida saukar yaushe,ya kai hannu zai ɗan bigeta da wasa,kulu tasaki wata ƙara kasan cewar duk jikin ta a raunane yake …………… 


_*By*_

_*Maman Dr*_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUDUWA 9

Advertisement  _*🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_           _9_ Ko kawar fitowa daga cikin motar jama’a suka fara yi,tsabar…

DUDUWA 2

Advertisement 🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_            _2_ Bakin rijiyar Duduwa ta nufa cikin rashin sa’a Bata iske…

DUDUWA 28

Advertisement             _*🧞‍♂️NA DUDU🧞‍♂️*_           _(cigaban Duduwa)_ *Thanks thanks…

DUDUWA 25

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 24

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…