DUDUWA 22

Advertisement

 _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:


            _*🧞‍♂️NA DUDU🧞‍♂️*_

          _(cigaban Duduwa)_


~22~


      Bayan Duduwa ta hattama yanaka albasar ta iya yanda take da buƙata ta sake miƙewa da saurin ta,ta nufi windon su mai gari suke ta ce””


Advertisements

  “To kulu a kimtsa da kyau a shirya gani nan tafe mai gari ka riƙo min ita da kyau dan ban son kasala yanzu zan hura wutar ta kama mu babbake ƴar banzar kowa ya huta, duduwa ta juyo daga windon ta dawo wajan murhun na ta,cikin abinda bai wuce daƙiƙu ba Duduwanka ta hura itacen nan da nan wuta ta kama ganga-ganga ta ɗauki kaskon suya ta ɗorashi akan wutar,kubar dake saƙale a wuyanta ta zaro tayi bakin ƙofar da jin duduwa ta fara ƙoƙarin buɗe ɗakin kulu ta diro daga kan gadon  ta shige chan cikin ƙasan gadon duduwa ta faɗo ɗakin tana”””


“Miƙo min ita mai gari…. 


turus tayi ganin babu kulu a inda ta hangota ɗazu ta dawo da duban ta ga mai gari dayayi saranda yana jiran ɗanyan hukuncin da duduwa zata aika fuska a haɗe duduwa tace da mai gari.


Ranka shi daɗe ina ajiyar dana baka?


gata nan ta shige saman gado,mai gari yabawa duduwa amsa saman gadon duduwa ta kuma hangawa taga wayam babu kowa a kai,ta sake duban mai gari a karo na biyu ta ce””


Au kace kawai ka ɓoye ta dan kar na gasata,to tunda haka ne bari kai ayi maka wal……….,ki dubi Allah karki faɗi wallahi tana ƙasan gadon nan a ruɗe nake ne gaba ɗaya ki gafarce ni duduwa ta.


Advertisements

kar ka kuma ce mun taka,ka sunkuya ka jawo min ita na faɗa maka ka dena firgita naka hukuncin na tafe saurin meye kake yi haka ne mai gari.


durƙusawa mai gari yayi ya jefa hannunsa zai damƙi ƙafar kulu tayi charaf ta wawuri hannunsa ta gantsara masa cizon daya sashi sakin ashar babu shiri ya mike tsaye yana yarfa hannuwa, duduwa tace ya matsa chan gefe ya bata waje ashe shi rago ne,mai gari ya matsa daga chan bakin ƙofa yana hango hanyar da zaibi ya fece,charaf duduwa ta ɗage gadon ta damƙo kulu da sai ihu da kiraye kirayen sunan jama’a take ta juyo zata yiwa mai gari magana.


wayam bubu mai gari babu dalilinsa sai silifas ɗinsa kaɗai a ƙofar ɗakin,dariya duduwa tayi ta saki kulu tana.


“idan kika gudu na rantse da Allah sai nayi miki abinda yafi babbaka,ki nutsu ki kwantar da hankalin ki ba soyaki zanyi ba,ba kuma gasaki zanyiba nasiha zanyi miki ki zauna anan wajan ki jini.


a fargice kulu ta zube ƙasa sai jan majina take hawayen fuskar ta na kuma bulbula ta zubawa duduwa ido kawai tana jiran abinda zata faɗi,duduwa tayi gyaran murya tace.


Na faɗa miki ki dena yi mini kuka anan kina ɓata muni rai tunda ban kashe uwaki da ubanki ba kiyi mun shiru karki fusata ni,gum kulu tayi har da riƙe bakinta,ta sharɓane hawayen da majinar a jikin rigarta tayi zuru da ita tana duban duduwa da ita ma duduwan take kallon ta tana””


     “Allah na gani da zumar zaman lafiya nazo gidan nan ba da nufin baƙantawa kowa rai ba amma kina son chanja ni da nufin dana shigo gidan nan dashi,idan har nazo da sharri bazan sa adawo dake ba kuma duk inda kike sai na biki nayi miki abinda naga dama ke meyasa kikai min sharri akan abinda banyi ba yaushe naje har gidanku kulu na jibgeki da kai na,na dai san nasaka an jibgeki danki dawo gidanki ka zauna da mijinki shine sakamakon yi mini sharri,kulu kin san ba ƙarfina zaki fiba duk kitimurmurar dakika faɗawa mai gari ina zaune kusa daku ina jinku amma sam ku baku ganiba wai danya soki ni ya ƙi ni,to ki rufawa kanki asiri ki zauna dani lafiya nima lafiya lau zan zauna dake idan kuma kika cigaba da sharri hmmmmm na lahira sai ya fiki jin daɗi kin sani sarai kuma kin san sauran dama Tunkiyata ce ta kasa inna tasa aka yanka mun ta aiko dashi na gyara shi yasa kikaga ina haɗa wuta badan na babbake kiba, ki fito mu soya kafin mai gari ya dawo kin jini,mai gari ya faɗo ɗakin kai tsaye yana.


“”Amma ko kulu kin ɗuma asara ashe duk zuƙi ta malle kika shinfiɗa muni don tsabar son zuciyarki tir da baƙar zuciya irin taki da nasan hakane aradu da da kaina zan babbake ki,ke ma bari kiga barin irinku a gari ai babbar matsala ce,mai gari yayi kan kulu data fashe da matsanancin kuka tana.


billahil lazi naji kuma bazan ƙara ɓata mata ba indai zamu zauna lafiya don Allah kuyi haƙuri ku gafarce ni na tuba na dena daga rana me kama da ta yau……………….


_*By*_

_*Maman Dr*_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUDUWA 27

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 2

Advertisement 🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_            _2_ Bakin rijiyar Duduwa ta nufa cikin rashin sa’a Bata iske…

DUDUWA 1

Advertisement 🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_            _1_ ‘Aaa ruwa ruwa na malale……… Ai ruwan bana yaci samari,Amma…