DUDUWA 25

Advertisement

 _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:


            _*🧞‍♂️NA DUDU🧞‍♂️*_

          _(cigaban Duduwa)_


~25~

 


Ta ƙwaɓe kayan jikinta ta ɗora kan ƙyauren banɗakin ta soma saɓa sabulu da soso dan yin wanka,daga tsakar gida tajiyo yaro ya shigo yana na faɗin.

Advertisements


“wai ana sallama da dije,charaf Dije ta amsa.


“kace ina zuwa wanka nakeyi,wai ma waya aiko ka.


bai gayan sunan sa ba,yaron yabawa Dije amsa a taƙaice,saɓa jikinta ta soma yi ta sake cewa””


jeka tambayo mun wa ne ne shi.


yaron ya juya ya fita bai jima ba ya sake dawo ya ce.


wai inji Balarabe.

Advertisements


to ka ce masa gani nan zuwa kaji,yaro ya amsa da”To,ya koma ya shaidawa me kiran Dije,,da sauri sauri Dije ta gurguraɗa ta watsa ruwan ta fito tayi ɗaki Adda na binta da kallo har ta lamɓata mai ta shafa hoda da janbaki ta yafa mayafi zata fita kenan Adda ta ce da ita””


“Kiji tsoran Allah Dije da auran ki yanzu zaki fita ƙofar gida wajan wani ƙato ba mijinki ba ko kin manta mijinki bai sauwaƙe miki ba igiyarsa uku na kanki tana yawo amma da anyi sallama jikin ki har rawa yake dan ki fita waje.


to wai Adda ni nace karya bani takarda ta,nifa bazan koma gidan saba duk abinda za’ayi wallahi sai dai ayi fita kuma dolle na fita tunda ba bani sabulun wanka da na wanki akeyi ba.


zo ki dake ni ba rashin kunya ba,tunda bakida mutunci ba dama agaya miki gaskiya sai kin maidawa mutum magana sabulu kuma dakike cewa ba a baki ba,anki abayar ɗin idan kinyi zuciya yau ki koma ɗakin ki tunda ba riƙeki mukayi ba ƴar banta uba kin girma baki san kin girma.


yasin babu inda zan koma kwayi ku bari kuma fita saina fita a hanani idan an isa,fuuuu Dije tayi soro tana sababi.


Kuka Addah ta fashe dashi tana salati,”yau na shiga uku Dije zata jazamin masifa da auranki wallahi gun mai gari zan kai ƙararki tunda kunnan ƙashi gareki,Addah ta matse ƴar ƙwallarta tayi ɗaka.


Tun daga ƙofar gida dije ta hango ƙyakyawan saurayi fari tas dashi ya zura hannayensa biyu a aljihunan rigarsa wandon jikinsa har ƙasa dan ya rufe takalmin daya sako har wani iyayi Dije ake akayi masa iso zuwa cikin zauran ya shigo daga ɗan nesa da dije suka gaisa tsabar kwarjininsa kasa haɗa ido dije tayi dashi a daddafe ta amsa gaisuwar tasa ya ce.


“Dije ko?


eh ni ce nan ya hanya?


lafiya ƙalau ya nasameku.


ƙalau ƙalau wallahi kace ba anan kake ba ma.


eh tafiya ta da nisa dan nahiyarmu akwai tafiya ba kowa ke iya zuwa ba.


Allah sarki ko ya sunan malamin.


da sauri haka.


ummm na ƙagu naji ne kasan ina da ƙarrama baƙo musamman irinku wa ƴanda suke zowa daga nesa nesa.


gaskiya kuwa ki ɗago ki dubeni sai na shaida miki.


Dije na jin haka ta ɗan ɗago kanta kaɗan idonta ya sauka kan kofaton sa da sauri ta dubi fuskar da halitar sa gaba ɗaya ta sauya,haƙoransa zaƙo zaƙo da ƙwala ƙwalan idanu ko hanci babu sai kunnuwansa da suka kusa rufe fuskarsa tsabar girma da faɗi dije ta arta a guje zata shige gida taji ta maƙale a wajan ko motsin kirki batayi daga inda yake ya ziro dogayen hannunsa masu farata zaƙa zaƙa ya chafki wuyan dije da tafara wani irin nishi tana kakarin amai ya murɗe kunnuwan da ɗaya hannun ya wage bakinsa zai cinyeta sai kuma ya fasa,cikin kakkausar murya ya ce.


“gidan uban wa zaki gudu?


 


fitsari ne yafara zirarowa daga zanin dije ta dinga karkaɗa kai kamar tsohuwar ƙadangaruwa hawaye na dilalowa da yawun bakinta tsafar tashin hankalin datake ciki,sake matsata yayi ya zaro ƙwala ƙwalan idanunsa ya ce”


“”Zaki koma ɗakin auranki ko zawarci zaki ci dan ubanki.


dan koma na rantse da Allah yanzu ma kace natafi da gudu zan tafi.


Kin taki sa’a ki shiga ciki ki durƙusa ki bawa Addah haƙuri ki nemi gafara akan rashin kunyar da kikai mata,idan ta haƙura ki wuce ɗakin ki ko daƙiƙa karki ƙara,


to to to naji billahillazi zan bata.


kamar ƙiftawar ido da buɗewa Dije taji tan saketa mutumin kuma ya ɓace a sittin ta dafe sayyadarta sai gaban Adda ta kwanta male male aƙas ta damƙi ƙafar Addah tana tayafe mata ta tuba zata koma gidan ta.


cike da mamaki Adda ta ce”


Sakar mun ƙafa salon rashin kunyar taki haka ya koma,wato ki tiɓar dani ki karyan kwankwaso kiji daɗi Dije ki sakar min ƙafa na ce,Addah ta fusgi ƙafarta Dije ta kuma sufa ta kamo tana kuka wiwi kamar ubanta ya mutu,sai da Addah taga kukan da gaske Dije takeyi ta ce “na yafe miki Allah ya yafemu gaba ɗaya,Addah na faɗin haka dije ta sakar mata ƙafa tayi ɗaki da gudu ta kwashi buhun kayanta tace da Adda.


“”Na wuce ɗakina Addah.


da wuri haka dije ki bari su shema’u su raka ki.


suyi zaman su na yafe da kaina zan koma saduwar alkhairi Addah,dije tayi zaure da gudu tabar Addah da sakakken baki tana tafa hannuwa da dariya🤣🤣.


*****


Ko da gari ya waye inna da kanta ta rako Duduwa gidan mai gari suna sallama kulu na ɗaka ta fito tayi turus ta amsa haɗe dayi musu barka da zuwa,ɗaki suka nufa gaba ɗaya inna take shaidawa kulu rashin lafiyar na duduwa ko daran jiya amanta bakwai basu sami bacci ba,anan kulu ta gano ashe Duduwa ma bata kwana a gidan ba ta ɗauki hakkin mai gari amma meyasa yaƙi kwana a ɗakin ta,tambayar da babu amsa tayi duduwa sannu ta tashi ta kawowa inna ruwa tana kuma yiwa duduwa sannu.


*kuyi haƙuri da wannan yarona ne bai jin daɗi😥*


_*By*_

_*Maman Dr*_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUDUWA 22

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 23

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 2

Advertisement 🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_            _2_ Bakin rijiyar Duduwa ta nufa cikin rashin sa’a Bata iske…

DUDUWA 26

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…