DUDUWA 26

Advertisement

 _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:


            _*🧞‍♂️NA DUDU🧞‍♂️*_

          _(cigaban Duduwa)_


~26~


Sai kusan azahar inna ta bar gidan mai gari, ganin duduwa ta ɗan ware har hira take tana baiwa inna labarin mafarkin da tayi a ɗan kwanciyar da tai bacci ya kwashe ta,a ranar kulu ce tayi girki ta tsaftace gidan ta kuma tsula wankan sikari tasha janbaki da gazal ga ture kaga tsiya kamar ƴar budurwa shi kansa mai gari daya dubeta wani murmushi jin daɗi ya saki haɗe da cewa”””


Advertisements

“ko kefa kululuwa ta,dube ki kamar ƴar tsana har na tuno randa kika kawo mun ragadada a dandali na sharɓi abuna kusan irin wannan kwaliyar kika gabzo min har tuntuɓe kika sanayi,cike da kunya kulu tayi rau rau da ido ta ce”


har kabani kunya ranka shi daɗe,ka manta amaryar taka ne a ɗaki.


wane ni na manta amarya ta guda,dangin ƙamshi tana kwance cikin raina ina zan manta ɗawisu wajan ado ko dai amarsu tabaki sirin kwaliyar tane eyi kululuwa,haɗe rai kulu tayi ta dubi mai gari daya zuba mata ido tace”


Sai ka tambayo ta muji ko ita tayi muni ma gaba ɗaya ni jiya wai ba kwana na bane ka gudu ɗakinta ka kwanta ashe ma bata gidan.


ba dole na gudu ba wannan kwaliyar dakikayi gaba ɗaya firgita ni take ga wani lanƙwasa da coge ƙafa da kika koya kamar sabuwar kamu,kuka kulu ta saki tana yi tana faɗin””


eh dole kace mun mahaukaciya saboda kayi sabon aure daga tambayar haƙƙina sai ka zageni,tunda ka tsane ni baka sona ai sai ka sayar dani kowa ya huta ko kuma ka jefani bula..


Advertisements

innalilllahi kulu yaushe nace na dena beginki.


baga shi yanzu ka kirani da shatara ba saboda wat…………kulu ta ƙame sakamakon hango duduwa da tayi,ta fito daga ɗakin ta ta nufo inda suke,da zuwan ta ta ce””


“Yaya kulu sannun mu da warhaka,lafiya dainko.


amsawa kulu tayi da””Yauwa gashi ki tambaye shi yasan lafiya ko ba lafiya ba, ta sake dashe baki tana kuka,cike da damuwa duduwa ta dubi mai gari da yayi saranda a tsaye kamar wani soja ta ce masa.


“”Sahibi lafiya yaya kulu take kuka haka,ko dai wani abu kayi mata mara daɗi,ai hannu kulu ta ɗora aka ta kuma runtuma ihu tana””


“Daga wannan sai wanchan innalillahi wai Sahibi,kulu ta kuma ƙara sautin kukan ta,tayi ɗakin ta zungwi zungwi tana mai maita SAHIBI,SAHIBI,a bakin ta,ɗakin ta shiga birkicewa tana wargatsa kayan ai tunda mai gari ya kirata da shatara gwamma tun yanzu ya fara gani,tana watsi da kaya tana ihu ita kaɗai a ɗaki.


Mai gari ya kasa cewa komai duduwa tabi kulu ɗaki da sauri tana.


   “Kiyi haƙuri yaya kulu ki dena kukan nan sam banjin daɗi ina ganki a haka ko ni ce na ɓata miki rai ban sani ba,cikin sauri kulu tace””


wallahi ke ce silar duk abinda yake faruwa.


ni kuma yaya kulu dan Allah me nayi miki.


Kulum sai kinyi wanka kin goge ƙafa sannan kiyi kwalliya ki kashe ɗauri har da sanya turare.


to ai ba laifi bane yaya kulu dan na gyara jikina.


na rantse da Allah laifi ne tunda mai gari yana fifita ki akaina har wani leƙoki yake yana neman yin tuntuɓe dan kawai kinyi kwaliyar dana kasa,dana kwaikwayi irin naki na ƙara da basirar da Allah yabani daya shigo ya gani da gudu ya arce yaga mahaukaciya yanzu ma na ɓata lokaci na tsala abata wai ni zai duba yace mun ƴar tsana duk saboda yariga yaga taki kwaliyar,kulu ta durƙusa ƙasa,””ki yiwa Allah ki dena yi masa kwaliyar nan ki dana kiran sa da Sahibi ko nima ya dube ni ya yaba,mai gari dake bakin ƙofar ɗakin kulu ya faɗo cikin ɗakin yana”””


“bazata dena ba tunda masifar kishi ke da munki yanzu nan na gama yabonki amma ki juya akalar yabon da wata muguwar manufa,tir da baƙin ƙishi irin naki kulu yanzu Amarya duduwas ta soma tsula mun zafafan kwaliya gaba ma har ai lobiyu zata dinga ce mun ba sahibi ba ƙarewa sai ki haɗiya baƙar zuciyarki ki mutu.


Kwanciya kulu tayi a ƙasa tana ihu wai ta shiga uku mai gari yace da duduwa ai lobiyu ita yakira ta da ƴar tsana da ƙyar duduwa ta shawo kanta bayan mai gari ya fita waje akan zata dena kwaliyar da kiransa da sahibi kulu ta goge hawaye da majina ta ce.


“yanzu naji batu idan ma zakiyi to nima ki yi mun irin takin duk sai ya taru yana dubanmu.


bama zanyi ba ai magana ta ƙare zaman lafiya yafi ɗan sarki yaya kulu,hirarsu suka shiga yi harda dariya amma achan ƙasan zuciyar kulu akwai ƙulli.


*******


Tun da dije ta koma gidan liman ta kwaɓe kaya ta fara ƙoƙarin mulla masa tuwo me ɗan karan daɗi,ba ƙaramun tsoro da firgici ta shiga ba aranta ta ƙudiri niyar ita da gidan liman me rabasu fa sai dai mutuwa bazata ƙara kwatanta abinda tayi ba.

   Liman na masallaci Ya’u ya garzayo a guje ya shaida masa dawowar mahaifiyarsu,cike da farin ciki da ɗokin ganin dije liman ya miƙe har da manta hulars a cikin masallaci ya’u ya koma dan ɗauko masa shi kuma ya yo gida kai tsaye yana murna.


     tun daga zaure liman yasan an samu chanji a gidan fas fas ko ina gwanin ban sha’awa saɓanin da da ko ina ka duba shara ce da ƙasa tiri tiri a gidan dan ba iya komai a gidan liman yake ba sai dai Adamu ko Ya’u idan sun gaji da ƙurar su ɗauki tsintsiya su share,sallama liman yayi ya faɗo tsakar gidan fuskar sa ɗauke da murmushi da gudu dije ta fito daga ɗaki ta amsa sallamar sai murmushi itama take aikawa liman tayiwa liman sannu da zuwa haɗe da shinfiɗa tabarma a gefe ya zauna yana kallon dije.


Shiru kowa yayi chan dai liman ya ce”


Dijangala ta liman yau ke ce a gidan na mu.


Wallahi malam gamu mun dawo sai dai ayafi junna da abinda ya faru,ta sunkuyar da kanta ƙasa,gyaran murya liman yaja ya kuma gyara zamansa yadda zai kali dije sosai ya ce””


“Abinda ya faru ya riga ya wuce Allah kai mana maganin wanda yake agaba,a dinga haƙuri da rayuwa mu kamu bamu san haka zata kasance damu ba,kowa na iya kasancewa a yanayin da muka samu kanmu a lokacin zaka gane me sonka dan Allah da akasin haka.


dije ta karɓi zanchan.


“Haka ne kam malam nayi rashin tunani a baya amma kayi haƙuri bazan sake yi ba ina Allah ya yarda.


To Allah ya amin ce sai dai kuma akwai matsala ɗaya,


wace iri yar matsala ce malam,dije ta dubi liman shima ya dube ta ya ce””


to gaskiya ganin na biki ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba kin ƙi dawowa yasa daga baya nayi shawara da na ƙara aure kawai na huta zaman kaɗai ce,dije ta zaro ido ta dafe ƙirji haɗe da cewa””


Aure kuma malam?


ƙwarai kuwa aure zan ƙara dije har na kai kuɗin zance nan da maku biyu za’a ɗaura aurena insha Allahu,kuma wani ikon Allah ma da budurwa yarinya shagaɓ ƴar shekara goma sha uku dije kinga inda haƙuri ya kai ni.


kasa cewa komai dije tayi sai mutsitsika ido take tana ƙara maimaita ƴar shekara goma za’akawo mun ni dije ko Ya’u dayake ƙarami ya girme mata nesa ba kusa ba bare kuma Adamu,jiki ba ƙwari dije ta miƙe ta kawowa liman tuwo da miya har da ruwa a kwanon sha,ya gyara zama ya kwashi abinci har wani lumshe ido yake dan daɗi ita ko dije ta haɗa kai da gwiwa sai tunanin auran liman take wa yarinya ƙarama wai zata zama kishiyar ta.


…………………………………………………


Kwanci tashi ga mai rai ,cikin duduwa ya soma girma a hankali yana bunƙasa har kulu ta farga hankalin ta ya tashi a ranar ko ƙwayar loma ɗaya bata kai bakin salati ba sai kuka a ɗaka,kar ku so kuga kulawar da mai gari yake bawa duduwa gaba ɗaya ya murza kwalli a idon shi,shi da kansa yakewa duduwa girki da wanki kai har gyaran ɗaki da gida wai karta wahalar masa da ɗan shalele ko ƴar shalele,kulu kuwa kulum da baƙin ciki take kwana ta tashi ta tufka wanchan ƙulin ta kwanche wanchan duk akan cikin na duduwa ga ɗan banzan tsoro ta kasa aikata komai sai kuri,akan baƙin cikin ne ma tace ita dole sai duduwa ta fito tayi aikin gida tunda itama mata ce a gidan,mai gari yace sam duduwa bazatayi ko changal ba abin cikinta ya gaji in kulu bazatayi ba to shi saiya tuɓe ya kwashi girki da aikin meye a ciki,kulu tasaka kuka Allah katafar mai gari ba zaiyi ba ita zata dingayi da dai yasaka hannu shi yayi ita bai mata ba to gwamma ita tayi da kanta,a haka take girkin tana kuk dan baƙin ciki,tasha aunawa zata zubawa duduwa abu a abinci taci cikin ya zube data tuno wace duduwa sai kuma ta saka kuka ta zubar…….


_*By*_

_*Maman Dr*_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUDUWA 9

Advertisement  _*🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_           _9_ Ko kawar fitowa daga cikin motar jama’a suka fara yi,tsabar…

DUDUWA 28

Advertisement             _*🧞‍♂️NA DUDU🧞‍♂️*_           _(cigaban Duduwa)_ *Thanks thanks…