DUDUWA 27

Advertisement

 _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:


            _*🧞‍♂️NA DUDU🧞‍♂️*_

          _(cigaban Duduwa)_


~27~

  

“Duk abinda mai gari ya siyo,to biyu zai shigo dashi cikin gidan ɗaya na duduwa ɗaya na kulu amma duk da haka ba gwaninta akayiwa kulu ba kullum akan ƙorafi anyi mata kaza ba amata kaza ba duba da yanayin duduwa data lura magana ma me tsayi wahala take mata bare ta tanka ta sai dai ta dubeta da ido ta bari.

    Cikin na duduwa ya girma yayi tirtsitsi,zama da ƙyar tashi da dabara wani lokacin har kuka take sakawa mai gari ya zauna yayi ta bata haƙuri yana faɗin,”ibada ce insha Allahu duduwa zaki haihu lafiya ki goyi abinda aka samu,sai duduwa ta sharɓe hawayen ta ce”amin ranka shi daɗe daga wannan bazan kuma ƙarawa ba ina Addu’ar Allah ya baima yaya kulu ita ma ta haifi nata.

Advertisements


mai gari ya murmusa ya ce,”Amin amin duduwa ashe dai duk abinda nake tunani akan ki ba haka bane abaya ke ɗan Alkhairi ce a gareni Allah ya barwa kansa sani,Allah yayi miki Albarka kinji yasa ki gama da duniya lafiya.


“Mu kuma da aka tsane mu aka zuba akwandon shara sai ayi yaya damu albarka ko ka saka ko karka sakan ranka shi daɗe zan samu tunda iyayena sun jima da faɗa mun,yo dan ni baka samin albarkar ba har wata abace sai me raguwa ko ƙaruwa zanyi eyyi,kulu ta ware hannayenta biyu haɗe da taɓe baki tana tsaye a bakin ƙofa,ɗan yatsa mai gari ya nuno ta dashi ransa a ɓace ya ce”””


keeeee”keeee kulu ki fita daga idanuna na rufe na rantse kika bari na fatoki daha hancina bazakiji ta, da daɗi ba ko kaɗan,duk ƙoƙarin da nakeyi akanku amma ke bakya gani sai surutun banza da wofi.


“Eh dole kace haka an jiƙa an baka ka shanye almatsutsai sun shaƙi wuyanka sun damƙe,to ni dai nan gani nan bari wa yasan abinda za’a haifa ko mutum ko kuma aljan………a fusace mai gari ya taso yayo kan kulu da tayi ɗakin ta da gudu yana””


“Ta Allah ba taki ba muguwa mai mugun nufi,Allah yasan halin jaki shiyasa bai yishi da ƙaho ba,mai gari yaja burki ya tsaya,kulu na daga ɗaki tana magana tana kuka ai an tsaneta saboda ita batayi cikin haihuwar ba to Allah zai bata ita ma taji yanda akeji,tausayin ta ya kama mai gari ya girgiza kai kawai yayi ƙofar gida.


koda kulu taga mai gari ya fice daga gidan share hawaye tayi ta fito,kan duduwa ta zo ta tsaya ta inda take shiga bata nan take fita ba mudi daya shigo ɗaukar abu yaji sababin da kulu keyiwa duduwa da sauri yaje ya sanar da mai gari,mai gari ya shigo zai auna ta gidansu da ƙyar da siɗin goshii duduwa ta bashi haƙuri har da kukanta,ganin kukan na duduwa yasa mai gari ya haƙura ya shiga zabgawa duduwa Addu’a yana samata albarka gaba ɗaya ran kulu ya dagule ta kumbura tayi sintim ƙarshe tasaka kuka😂

Advertisements


******


“Alhamdulillah,garin *Kanwa* yayi lafiya kasancewar yanzu kowa na nashi safgar idan ka dubi yanda duduwa ta sauya sai kaji tausayin ta ciki ba wasa ba,ana tsaka da shagalin bikin liman da amaryarsa ƴar charas duduwa ta yanke jiki a bayi ta faɗi da ciki nan da nan hankali ya tashi aka kira inna da mai gari da me unguwa aka ɗunguma a mota akayi asibiti cikin gaggawa inna sai kuka take tana Addu’a shi kansa mai garin ganin yanda jini ke bulbula daga jikin duduwa gaba ɗaya ya rikice hankalinsa ya tashi ya saka kuka me unguwa shi yake bawa inna da mai gari baki akan suyi haƙuri komai zai zo da sauƙi har suka ƙaraso asibitin dake cikin garin *Kanwa.*

       malaman asibitin da gudu suka kawo agaji aka zaro duduwa da taimakon su cikin nan yayi tsini da ƙayar aka fito da ita daga motar aka ɗora ta akan gado aka tura zuwa ɗakin haihuwa da shigarsu duduwa ta kama jijjiga tana firzar haƙori a wannan yanayin ta siluɓo ƙaton *ƊANTA* me kama da mai gari saka ita kuma ta cika,wayyo Allah mai gari da inna kwanciya ƙasa inna tayi tana kuka tana surutai mai gari sai matse ƙwalla yake yana wa duduwa Addu’a har aka yi cike ciken da za’ayi aka basu jariri da gawar duduwa sukayo gida kai tsaye.


      Nan da nan labari ya zagaya ko ina na rasuwar duduwa, aka cika ma’ƙil da mata da maza ba ƙaramin ƴan rakiya duduwa ta samuba haka aka kira mai gari da kulu suna kuka sukayi sallama da duduwa aka miƙata gidan ta na gaskiya jiriri kuma yaci sunan mai gari, *IBRAHIMU* inna ta laƙaba masa suna da *NA DUDU*.


An share kwana bakwai cir ana zaman makoki masu zuwa gaisuwa kam daga ɓangarori da dama har da burni da maƙotan garin kanwa,sadakar kuɗi abinci kuwa anyi babu adadi har aka cura kwana goma sha biyu,anan inna ta koka da neman alfarma wa mai gari ya barmata *NA DUDU* ko ta riƙa ganinsa kamar ƴar jikallanta margayiya duduwa mai gari ya amsa da to, yace amma idan yayi shekara biyu zai dawo gareshi inna ta amsa da Addu’a kuka ya biyo baya.


ba haka kulu taso ba,ta so abar jaririn a wajanta dan har mai gari tasamu tayi mai magana yace shi ba zai iya cewa inna komai ba akan jaririn idan aka bata tana da nono da zata bashi ,kulu tayi tsaki ta wucewarta ko sallama da inna bata bari sunyi ba tana ji suna kuka amma biris tayi dasu sai ma Addu’ar datake ta nanatawa azuciyar ta tana””


“Allah yasa shima ɗan yabi uwarsa inda ta tafi…….


*Su kulu anya da imani aran kuwa,kuji kamar ita a duniyar zata zauna.*


*Ina miƙa saƙon ta aziya ta ga ɗaukacin fans na duduwa gaba ɗaya sai haƙuri kar ku manta munyi rashi kuma mun samu *NA DUDU😥*,


_*By*_

_*Maman Dr*_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUDUWA 1

Advertisement 🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_            _1_ ‘Aaa ruwa ruwa na malale……… Ai ruwan bana yaci samari,Amma…

DUDUWA 22

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 26

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…