DUDUWA 28

Advertisement

            _*🧞‍♂️NA DUDU🧞‍♂️*_

          _(cigaban Duduwa)_

*Thanks thanks thanks sosai ƴan uwa rabin jiki,aradun Allah naji daɗin comments ɗinku jiya da yau ba ɗan kaɗan ba, lalai kun nuna min kuna yin Aunty duduwa margayiya😓,ɗari bisa ɗari,nima ina yinku har cikin ƙallemun zuciyat💗,wannan page ɗin sadaukarwa ce a gareku masoya ina muku fatan alkhairi da wanzuwar farin ciki me ɗorewa a rayuwa,acigaba da sambaɗa comments a ko yaushe one love ni daku😘*~28~

         Bayan inna ta koma gida ne ta iske balaraba jikar Abu maƙotan su ta haihu amma ƴar ba rai ta koma duk aka shiga yiwa junna gaisuwa anan ne Abu ke tuntuɓar Inna ko za a baiwa balaraba *NA DUDU* ta shayar dashi a cewar Abu jiya yini guda nonan na balaraba na zubar da ruwan nono saboda cikar da yayi ko riga kasa sawa tayi,inna tayi shiru chan dai ta numfasa ta ce sai ta nemi shawarar mai gari tukunna tunda shi ne mahaifin yaro ba ita ba,abinda ya yanke to haka za’ayi Abu ta amsa da “to ai shikenan na san ma mai garin bazai musa ba tunda balaraba ba aure gare ta ba yanzu,inna ta ce dai zata je da kanta ma anjima ba sai ta jira mai garin yazo ba ta tambaye shi,dan kusan kullum yana kan hanyar zuwa duba *NA DUDU.*Advertisements

     bayan inna ta niƙi gari taje ta sanar da mai gari,mai gari ya buɗe baki ya ce.


“Sam ban amin ce da hakan ba inna,ban san halin ita balaraba ba yarona zai sha nono daga gareta ayi duk abinda ya dace ko dukiya ta zata ƙare zan bayar in dai akan Na Dudu ya samu kulawa ta musammman to wallahi zanyi inna amma banda wannan zance,inna tayi murmushi ta ce.“yo nima dai haka na hango bazan yi saurin katse abu bane kar taga ni ce bana so,amma tunda kace haka ai shikenan faɗuwa tazo dai dai da zama sannan naji an ce a burni ana sayar  da wata madara ta jarirai da akan basu ko ita zamu jarraba mu gani ranka shi daɗi.Alhamdulillah,tun da har an samu madara ai gwamma asayo madarar a bashi zan kira Ƙasimu dake chan burni naji yanda abin yake in yaso duk dare ya sayo ya kawo abashi tun yau isha.


 Allah sarki Na Dudu sam baya da damuwa ko kukan jariran nan da sukan ɗanyi shi bai cika yi ba,idan kaji kukansa to yunwa ce kuma da zaran na bashi dabino da wannan zam zam ɗin daka kawo take zakaji yayi ɗif sai barci kamar yasan gyatumar sa bata nan,da ƴar ƙwalla inna ta ƙare batun tana mai miƙewa tsaye mai gari ma ya share hawayen daya sako kan kuncin sa ya miƙe tsayen yana.


Advertisements

       bari na kira kulu ku gaisa naga bata leƙo ba ko bataji zuwan naki ba ne ina ga.da ka barta ma nima a kan hanya nake wata rana ma gaisa ina zo ko ita taje.to shikenan inna an gode Allah ƙara girma da nisan kwana.


haba sai ka ce ba ɗaya ba,ai na dudu ya riga da ya haɗa mu har abada yallaɓai fatanmu Allah ya raya shi cikin imani.“Amin amin inna nace kayan abincin sun ƙare?.


lalalala ai ko rabi basu kai ba kasan ni kaɗai ke ci dan ma wani lokacin ina baima maƙota sadaka Allah ya saka ya ƙara arziƙi me amfani yasa Na dudu yayi maka yallabai.amin dai inna dan Allah kafin su kai ga ƙarewa asanar dani da wuri insha Allahu zan kawo wasu sai kuma ƴan buƙatu dan Allah inna ki riƙa sanar dani nima jika ne a wajanki yallaɓan nan ki dena kirana dashi.


murmushi inna ta kuma yi akaro na biyu ta dubi mai gari dayake a duƙe ta ce””Naji zan faɗa maka idan kayan abincin sun kawo ƙarewa buƙatu kuma duk ka biya su har yau kuɗin daka bani bai ƙareba,amma kiran ka da yallaɓai ko ranka shi daɗe bani iya denawa saboda girman da kake dashi a garin nan ai tun kan ka auri margayya haka nan nake kiran ka dashi to yanzu ma bani fasawa kayi haƙuri ranka shi daɗe,sosa ƙeya mai gari yayi haɗe da jijiga kai ya sake cewa””Nauyi nake ji inna gashi kin kuma maimaitawa.yo nifa na riga da nasaba bakina ya riƙe yallabai kamar shi ya raɗa maka ni na wuce mu jima da yawa ranka shi daɗe.to to Allah kiyaye hanya,inna ta fito daga zauren gidan mai gari shi kuma yayi cikin gida,da shigar sa cikin gidan kulu ta tari gaban sa riƙe da ƙugunta ɗaya sai jijiga take tana harare harare mai gari ya chake a wajan yana kalon ikon Allah har kulu taga mai gari bashi da damar tanka mata ta furta.“ita kuma wannan tsohuwar zawarci tazo ko ƙa…………a fusace mai gari ya tasowa kulu daya sata ja da baya da sauri yashiga yiwa kulu faɗa da ƙarfi yana”””“Ke dai mutuniyar banza ce da wofi daƙiƙiya mara hankali ko ƙasa kike ci zaki kira kakarki ko gyatumarki da me cin zawarci ashe haukan kishin naki har yanzu yana nan bai raguba sai ma ƙaruwa da yayi,to a hir na gaya miki hawainiyarki ta kiyayi ramata duk randa kika kuma muzanta baiwar Allah nan wallahi sai na ɓata miki na saɓa miki kulu.


wallahi si dai ka saɓa ɗin amma dole sai nayi magana ai ba gaskiya kake so ba,haka kawai ko mai naka ka tattara ka turawa matar nan ka mai da ita uwa saboda jikarta ta haifa maka ƴaƴa goma to mu zuba dani daku muga wanda zai kwashe ba dai akan ɗan tamilon jaririn nan kake gigiwa ba hmmmm.
ɗan nawa ne ɗan tamilo kulu?ƙwarai kuwa ɗantamilo na faɗa ɗantamilo ɗantamilo ka niƙani nafi gari yin laushi ƙarewa.bazan niƙa ki ba idan kura na maganin zawo tayiwa kanta mana muga naki ɗantamilon dan Allah in kina da zuciya maza fito min da naki na gani mara mutunci kawai.wayyo Allah na shiga uku ni kulu mai gari ni kayiwa gorin haihuwa wayyo Allah jama’ah.an yi miki shasha sha,mara ɗa’a me mugun nufi daga ci sai kashi,mai gari ya juyawarsa ya fita daga gidan,kuka sosai kulu ta kwarma harda majina da burgima a ƙasa wai mai gari yayi mata gorin haihuwa.….……………………
“Gwaggo Dije ina abinci na yake?“na haɗa danawa na cinye ke wai ban ce ki dena kirana da gwaggo ba ko ni na haifeki ne iyee.to gwaggo dije me kuma yayi zafi haka daga tambaya.na gwaggorawa gyatumarki mara mutunci ni zaki nunawa iya shege.tsalle yarinyar ta daka ta dire ta tafa hannu haɗe da murguɗa baki ta harari daje ta ce”wallahi tun da kika zageni a gidan nan sai na gasaki na dafaki kin dahu kinyi luguf gwaggo dije kuma bazan dena kiran ki da gwaggo ba na rantse.to kuwa zaki ci ɗan banzan duka tunda ni ba sa’ar gyatumarki bace.kika kuma zagina?


an zaga mara kunya mara ta ido,idan girki ne kin iya karɓawa ki shige ɗaka da malam ko tarin ƴar kusun ƙwa bakaji dan iya shege ne kuwa kina daga lambar farko zaki wani kirani da gwaggo da kin ɗaukeni uwa bazaki aure min miji ba,dije na rufe baki yarinyar ta ɓare baki ta kwanta a ƙasa male male tana””””””“”””Wayyo cikina,wayyo Allah gwaggo zata kasheni,mallam liman daya sako ƙafarsa cikin zaure jin ihu na tashi da gudu ya faɗo cikin gidan yana””
“Innalillahi,ƴar chakare meya sameki,waye ya buge ki,charaf ƴar chakare ta karɓe zanchan da.


    “”gwaggo ce, gata nan gwaggo zata kashe ni cikina wayyo Allah zan mutu liman.rikicewa liman yayi da sauri ya wafci ludayin zuba abinci dake hannun dije ya shiga rafkawa dije ta ko ina tana ihu da rantsuwa ba ita bace,malam liman na ƙara makawa dije ludayi yana Allah yasa tsakaninsa da ita zata naksta masa ƴar chakaransa har ɗaki liman ya raka dije da duka dije na ihun neman taimako………………


*Comments😉*


_*By*_

_*Maman Dr*_

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUDUWA 3

Advertisement _*🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_           _3_  Fadar cike take taf da mutane wasu a zaune wasu…

DUDUWA 1

Advertisement 🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_            _1_ ‘Aaa ruwa ruwa na malale……… Ai ruwan bana yaci samari,Amma…

DUDUWA 27

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…

DUDUWA 23

Advertisement  _*📚HAƊAKA📜WRITER’S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:             _*🧞‍♂️NA…