DUK NISAN JIFA 15

Advertisement

                       15

Da sauri ya mik’e tsaye, kai kawon da ya ringa yi ya fi a kirga sannan ya dawo ya tsaya gaban Mama yana kallonta ya ce” Ba zan iya hak’ura da Biliisu ba mamana, na rayu ne da k’aunarta, ina matsanancin kishinta, na yi shiru ne dan kar na fallasa wannan abu a k’ananun shekarunta, na yi shiru ne dan ina so sai na kai wajen da zan iya biyan dukan buk’atocinta, sarauniyata ce ta ni kad’ai, jin cewar wani ya furta mata kalmar so na saka min zazab’i, mamana ai maganar shayarwa ta kasu ta rabu, malamai sun yi sab’anin hujoji, wasun sun nuna haramtar hakan wasun sun nuna halastar shi, mamana ko da kin shayar da ni din tunda shayarwar ne ai Bilkisuna tawa ce.”


Mama ta kamo hannunsa tana kallonsa ta ce” ka nutsu Hisham, idan akai irin wannan sabanin barinsa ya fi zama alkahiri.”


“Mama ba zan iya ba” ua fada  wannan karon muryarsa na cracking.


Hannunta ta kai wajen fuskarsa a hankali ta dan mari fuskar tasa ta ce” Kai bana son rashin kunya, yaya ina nuna maka abu kana ce min ba zaka iya ba? Ba zaka iya me ba? A kan mace zaka yiwa mahaifiyarka gardama ko ka ki bin umarninta? A kan mace zaka saka kanka a halaka? To bari ka ji wani abu, idan ka yarda ka dauki bangaren malaman da suka halasta maka Bilkisu ka ce aurenta zaka yi aura maka ita zamu yi, aman ka sani tun a nan gidan duniya sai kun dawo kun tsani junna kai da Bilkisu domin kuwa Allah zai rikita zaman namu ta hanyar sakawa mahaifiyarka take umarninta da ka yi, uwa wasa ce? Umarnin uwa wasa ne? Uwa fa Allah cewa ya yi idan kana cikin sallah mahaifiyarka ta tsananta kiranka ka katse ka amsa mata! Kai kuwa ka san girman darajar matar da Allah ya saka aljanarka a karkashin kafafuwanta? Kai zaka yi gigin daga kanka a kan umarninta? Wasu iyayen zaune suke a anguwar da bata dace ba, sunna aikata masha’arsu aman idan Allah ya albarkace su da y’aya masu albarka haka zasu ringa bin su sunna masu biyaya sunna masu wa’azi, da yawa sun mayar da rayuwar y’ayan nasu tamkar ukuba tsabar muzguna masu da suke aman haka suke yi masu biyaya sunna like da su! Da yawa ana haihuwar tasu kaisu aka yi aka siyar, daga baya suka nemo iyayen nasu suka runguma, kai ita da aure ta same ka, da yawa a haka aka same su kuma idan Allah ya yi masu kimtsi ne sunna nan tare da iyayen nasu! Meye laifinta, dan ta kawo min kai? Na wulakantaka ne? Ko ka yi dana sannin kasancewa a tare da ni ne? Tsayin rayuwar da muka yi da kai ka taba jin an ce da ita karuwa? Ta kama mutuncin kanta, nema da karrin ilimi kuma ba haramun bane, HISHAM ka yiwa mahaifiyarka biyaya ga dukan umarninta idan ba haka ba zaka hadasa min kuka ba dare ba rana HISHAM.” 


Advertisements

Hannunta ya kuma rikowa yana kallonta, a hankali ya kai hannun nata wajen fuskarsa ya dora ya rage muryarsa sosai da sosai ya ce” Mamana, da ace kin san girman juyani da abinda nake ji a zuciyata games da kanwata da kin tari koma waye kin yi fada da shi kan kar ya kuskura ya shiga wannan lamari, ina zaune a Niger ne dominta dan bana son na gusa wani ya shigar min wajena, mamana dan Allah kar ki min haka.”


Mama ta kara rike fuskarsa a tafin hannunta tana kallonsa ta ce” ina iya fada da kowa a kan yarona, sai dai bani da karfin gannin yarona kai kansa ga halaka, a irin wannan lokacin kuma zan iya fada da yarona, domin bijirewa mahaifiya yarona na iya kona kansa, abinda ya yi dominsa bai ji dadinsa ba haka kuma ya je lahira ya tashi a babu!”


Sakin hannunta ya yi a hankali ya ringa ja da baya yana kallonta.


Dago hannun nata ta yi muryarta sanyaye ta ce” HISHAM”


da sauri ya juya ya kama kofar ya bud’e.


Tsaye take sunna kallon junna ido cikin ido, gabanta bai idasa faduwa ba sai da ta ganshi a irin wannan yannayi, baki daya jaruminta ne tsaye dukan halita ta kakarfan jarumin da ransa ke bace hankalinsa ke tashe sun bayana a tatare da shi.


Advertisements

Hawayen da take zubarwa ya saka shi k’ura mata ido yana kallonta.


A hankali ta dan rike gefen sket dinta sai kuma ta saki tana kallonsa.


Bata taba zato ko tsamani ba, bata yi aune ba, bata kawowa ranta ba sai jinta ta yi a cikin kirjinsa.


Wata irin wawuyar runguma ce ya bata wace ta sakata sakin kara domin ji ta yi zai karyata zai rabata biyu.


Baki daya jikinta ne ya dauki bari ta fashe da matsanancin kuka tana jin yanda jikinsa ya dauki zafi da kuma irin yanda k’irjinsa ke bugawa.


A hankali ya ringa sasauta rikon da ya yi mata a jikinsa, muryarsa a sanyaye ya ce” Ki ci gaba da rufe jikin ki du inda zaki je, ki ci gaba da kare mutuncin kanki Billyna, ki ci gaba da tsarewa kowani shara gida ki rike mutuncinki Billy, ki ringa cin abinci dan Allah, ki kula da shan magani idan baki da lafia, kin ga a cikin dakina babu wajen da zaki bude ba auduga idan kina da bukata ki je ki ciro adadin da kike so, Billy kar ki min bincike dan akoy abubuwan da nake jin kunyar ki gani kin ji? Billyna ban so kin ji komai a kan shirmen nan ba, idan kika yarda kika kuskure umarnin mamana du inda nake zan zo na sab’a maki ne, ko me ta ce ki yi , ki yi kar ki k’iya.”


A hankali ya lalubi hannunta bayan ya ciro kati na banki a aljihunsa ya saka mata a cikin hannunta ya ce” ko nawa kike so, ko a wani lokaci kike so, ki je ki saka ki ciri abinda kike so, cod din number wayarki ce, kar ki yarda ki tambayi wani namiji abin hannunsa kin ji Billyna?”


Da sauri ta dago tana kallon fuskarsa, irin yanda ta yi ja har abin tsoro, haka kuma idannuwansa sun yi jajajir sai irin yanda jijiyar gaban goshinsa ke  harbawa tana dik dik dik.


Da sauri ta kai hannunta wajen fuskarsa cikin muryar kuka ta ce” Me menene yaya? Ina zaka je? Kake min magana kamar zaka fita? Ina zaka tafi? Ka san a gari ana tsoron taba ni ne dan an san kana tare da ni yayana, ina zaka je?”


Da sauri ya cireta a jikinsa yana kallonta ya ce” Allah yana tare da ke, tsaro zai ninku a kanki domin ina tare da dukan motsinki, Billyna ko gawarki ba dai mutun ba sai dai Allah.”


Yana gama fada ya saketa a wajen nan ya yi gaba.


Da sauri ta dnaga k’afarta da niyar bin sa sai dai kiran sunnanta da Mama ta yi ne ya sakata juyowa da wani irin sauri.


Da gudu ta fad’a cikin dakin ta je ta fada jikin Mama ta fashe da kuka mai karfin gaske tana girgiza kai ta ce” Mama ina zai je? Mama hala tafia zai yi? Mama a kan me zaki ce da shi haka? Me ya sa zaki ce da shi haka? Mama me yasa zaku yi mana haka? Mama tati ce? Dama bata so na? Me muka yi mata?”


Mama ta riketa da kyau a jikinta da yannayin fada fada ta ce” Yaushema aka haife ki Bilkisu? Kuka ne kike kan namiji ko kukan rabuwa da yayanki? Ya ce maki zai je wani waje ne? Ba inda zai je yana nan tare da mu, maganar soyaya ce babu na soketa ko akoy abinda zaki yi ne? Karya kike nufin mun yi maku ko me? “


Da sauri ta ringa girgiza kanta tana kara kwontawa a jikin mama.


Mama ta lumshe idannuwanta hawaye masu zafi suka kuma zubo mata, bata taba sakawa zuciyarta cewa wai zainab zata iya aikata mata haka ba, bata san dalilinta na aikata haka ba, aman sai take gannin koma meye hujarta idan har ta sameta ta nuna mata cewar ta tsawatar a kan wannan take taken yaren ai daa ta tsawatar ba tare da ta saka su yin karya ba, yanzun meye hakan? Wannan abin yana mata ciwo a kasan zuciyarta, sai irin yanda ta fahimci irin ciwon da Hisham yake ji a kasan zuciyarsa, sai ga Bilkisun nan itama ashe abin na iya tabata haka? Irin magangannunsa da irin yanda ya nuna a gaban kowa ba zai iya boye kaunarta da abinda yake iya yi a kanta ba ta hanyar rungumeta a gaban mama ya tsaya mata a rai ya bata tausayi ya sakata tuhumar kanta, magangannunsa sun tsoratar da ita, aman bata tunanin in dai HISHAM dan hakal ne zai gujeta a kan wannan! Ba zata daina hawa kan decision dinta ba, ta hau ta zauna ba zata sauka ba kuma domin Hisham sonsa take tamkar dan da ta haifa ba zata barshi ya bijirewa mahaifiyarsa ba dan ba riba

A hankali ta ce” A islamiya, yaya aka fasarta maku girman uwa Bilkisu? Wanda ya bijirewa mahaifiyarsa yaya Allah zai hukunta shi? “

Bilkisu dake jin numfashi ya yi mata karanci a hankali ta ce” Mama, zai kasance a gaban hukunci mafi muni, domin wuta ce makomarsa, an ce mu yiwa iyayenmu biyaya da dukan karfinmu in dai ba a kan sabon Allah bane.”

Mama ta ce” zaki so ya sabawa tasa mahaifiyar da ta haife shi?”

Kanta take girgizawa a hankali bata ce komai ba

Mama ta kara riketa ta ce”…


ASALAMU ALAIKUM JAMA’A, DU WANDA KE KARANTA WANNAN LABARI NA TABATA NA TABA ZUCIYARSA A KAN WANNAN LAMARI, SAI DAI KU SANI SAKONA DAKE CIKI BA ZAI ISA GARE KU BA HAR SAI NA GABATAR DA LABARINA YANDA NA TSARA SHI, INA MAI BAKU HAKURIN KU YI HAKURI KU BI ZAKU JI DADINSA IN SHA ALLAH, 😁 taku ce yar mutan niger*

Mu je zuwa mutanena mor cmmnt mr pags in sha Allah

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like