DUK NISAN JIFA 17

Advertisement

                               17

Tana dawowa ta tarar da Tati na tsaye kan Bilkisu , tana ta lalabata kan ta yi hakuri ta tashi ta ci abinci aman fir ta ce bata jin yunwa Aisha dake zaune gefe tana kallonta ta lumshe idannuwanta tana jin ba dadi a kasan zuciyarta, ita ta kasa gane kan su biyun nan, wai a kan me ba zasu iya bijire wannan lamari ba bayan sunna da damar yin hakan? 


Mama ta girgiza kanta ta ce” to in ba zaki ci ba ki tashi ki ba mutane waje kafin na tsintsinkawa fuskarki mari mai gado, ka ga marar kunyar kawai shine har kike wani lalamata kamar yarinyar goye?! “


Tati ta kaleta ta ce” Haba aunty, yarinyar ba lafia maimakun a lalabata sai a ringa kirta mata fada me ya yi zafi, ni dai ta tashi ta sha magani ko zafin jikin ya barta? “


Bakuwar Tati ta ce” A yi hakuri maman Y’ata, wannan fada haka ? Ni sai na dauke y’ata mu yi gaba su Elhaji sa isko mu”


Advertisements

Yar daria Mama ta yi ta cire  hijab dinta ta ajiye saman kujera ta ce” Ai sai ku yi, bara na yi sallar la’asar ni “


Du da ido suka rakata kafin Bilkisu ta mayar da idannuwanta a hankali ta lumshe, bata san da wani ido zata buda ta kalli Tati na, bata san ta yaya zata fahimci kaunar da take nuna tanai mata ba, a yanzun burinta ta yi nesa da wannan mumunan mafarkin, yau kwana biyu kawai du ta rasa tunanin me zata yi, cin abinci na gagararta , walwala ta kaurace mata, da gaske suke maganar auren yayanta da gaske ake magana ta kankama domin har baba na Kanya ya zo da kansa sakamakon kiran da mama ta yi masa (Mahaifin tsohon mijin Mama), sai ta ji kamar zazabi zai rufeta , sai ta ji kamar ta yi ta rusa kuka…..lalle ta lazumci adu’a dan samun saukin yannayin aman cikin ikon Allah sai ta ji ita dai bata jin saukin nan


Ta dauki dan lokaci sannan ta tashi daga wajen ta nufi dakin mahaifiyarta, hakan ya saka Tati rakata da kallo sai kuma ta sada kanta, Aisha kam ta zubawa tati ido tana karantarta, haka kawai take ji a zuciyarta wannan mata anya zata yiwa d’an adam alfarma? Ta kasa fuskantar y’ayanta d’an wa zata fuskanta?


Bilkisu na shiga ta nemi waje ta tsugunna gaban Mama da ta gama sallah tana jan carbi


A hankali Mama ta kura mata ido ta kasa ce mata komai


Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya ta ce” Mama, ina son na je gidan Abana na yi sati daya dan Allah “


Advertisements

Mama lumshe idannuwanta tana jin wani irin abu mai ciwo a ranta, wai Bilkisun da bata iya motsawa nan da nan yau itace ke son zuwa har ta yi kwanaki gidan mahaifinta, yarinyar da mahaifin nata shi yake so ta zo masu ta yi masu koda kwana daya ne sai ta kiya ta nuna aa mamanta ba zata iya baci ba idan bata nan yau gashi da kanta zata tafiarta

A sanyaye mama ta ce” Yaushe ? “


Bilkisu ta kara sada kanta ta ce” ko yauma Mamana “


Mama ta yi dan murmushi ta ce” Zaki iya har sati guda? “


Gyada kai Bilkisu ta ringa yi hakan ya saka Mama cewa” to tashi ki je ki ci abinci, ki sha magani sai ki kimtsa kayanki idan rana ta kara yin sanyi sai na saka Kader ya kai ki “


Kanta ta kuma gyadawa a hankali ta ce” Na gode Mamana “


Har ta kusa fita Mama ta yi kiran sunnanta hakan ya sa ta dawo ta kara dukawa a kusa da Mama


Mama ta ce” Zaki guje ni ne? Zaki kaura wajensa da zama ne tun kafin aure ya raba mu? “


Bilkisu ta ji zuciyarta ta karye, a hankali ta matsa sosai jikin Mama ta dora kanta a gefen kafadar mama ta sanyaya muryarta ta ce” So nake na bi umarnin mace mai daraja a cikin mata, so nake na taya mutun mai daraja a rayuwata samun aljannah, shi yasa zan yi nesa da nan na dan lokaci, Mamana ko aure ba zai rabani da uwata ba sai dai mutuwa in sha Allah”


Mama ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce” Allah ya yi maki albarka, ya baki miji na gari “


Bata amsa a bayane ba sai a cen kasan zuciyarta hakan ya saka mama furta mata furuci kamar haka” Yin nesa da abinda ke saka maka damuwa ba laifi bane Bilkisu, tashi ki tafi, ki dauki adadin kwanakin da kike so har ki ji sanyi sanyi a kasan zuciyarki, aman ina mai tunatar da ke Matar mahaifinki mamanki ce, tsakaninki da ita kar na ji kar na gani maganar raini ko wulakanci, ki yi mata biyaya , ki yi aikin gidanku da dukan karfinki, ki zauna lafia da kowa ki yiwa yayunki biyaya hakan zai sa kowa ya kaunaceki idan kin tafi tafia a yi kewarki, kar ki yarda ki je bakunta waje kina zaune ana aiki a gama a baki ki ci hakan na sakawa ki gunduri mutanen gidan koda kuwa gidan mahaidinki ne”


Bilkisu ta ringa gyada kanta alamun amsawa sannan mama ta ce” Tashi ki tafi, Allah ya yi maki albarka”


Tashi ta fice a dakin, hakan ya saka mama daga hannunta ta shiga kora adu’o’i zuwa ga mahalincinta, shi take kaiwa kukanta, shi take fadawa damuwarta, shi take fadawa ya shiga lamarin iyalinta


Sai da ta sha madara mai sanyi sannan ta hadiyi maganin zazabin dake taso mata 


Tana cikin hada kayanta Aisha ta shigo dakin ta jingina da jikin garun dakin

Aisha yarinya ce mai matukar sanyin hali, tana da wayewa da kuma hakuri, uwa uba ita din ba mai naci a kan komai bace, du abinda ta ga ya zama na jayaya ko na naci takan saki, Aisha bata son a duniyarta ta kwonta da sannin ta cutawa wani, hakan ya saka take bin iyayenta da kallon abinda suke zumudin hadawa, su ko bari basa yi kakanta ya warke sumul? Dan sun san idan ta shaida masa ga irin auren da suke shirin hadawa ba zai lamunce masu hakan ba, shi yasa mahaifinta yake ta rawar jiki shine harda cewa ba sai an kai sadakinta da kayan aurenta garin Niamey ba tunda ga shi a nan ga mahaifiyarta kawai a bada komai a nan gidan su mijin da za’a aura mata, a haka bata gannin an siyan mata mutunci, gani take kamar abin hannunsa ke saka su rawar jikin nan, hakan ya sakata cikin zulumi 


Da bakinta ta shaidawa mahaifinta cewa bata cikin maganar hadin nan, domin akoy wace ta fita son sa kuma shi din kansa ita yake so, sai cewa ya yi ita bata son sa? A gaskiya karya ne ta budi baki ta ce wai  bata son Docter Hisham, aman kuma bata son rigima, bata so ta rayu da namiji tamkar ba mace ba, ta yi rayuwar nan irin ta dole, rayuwar nan bata da ma’ana domin rayuwa ce marar yanci


A cikin akwatinta take saka kayanta a nitse, tana jejera su har ta saka kala goma, manyan suturu na mutunci da hijabai da su pant da bra da clean sai turare da mai da sabulu


Rufeta ta yi ruf sannan ta mike ta nufi bayi


Ta dauki lokaci mai tsayin gaske a ciki, domin sai da ta ci kuka harda na mamaki sannan ta kimtsa kanta ta fito


Sasaukan shiri ta yi, sai turare da ta wanke jikinta da shi


Agogo ta saka a hannunta sannan ta daure gashinta a tsakiya ta yafa dan mayafi a saman kanta bata daura dan kwalin lesh din ba 


Ido hudu suka kuma yi da Aisha a hankali ta taka gabanta ta tsaya tana kara binta da kallo

Murmushi ta sakar mata, murya ciki ciki ta ce” ALLAH YA SADA MU DA ALKHAIRI AISHATU” 


AISHA ta kara wara idannuwanta da mamaki a kan yarinyar, what? Shine abinda take fada a kasan zuciyarta


Juyawa ta yi ta duka ta dauki katuwar jakar hakan ya saka Aisha shan gabanta da sauri ta ce” Meye wannan? Me kike nufi da wannan? Kin kuwa ji cewar ni ake shirin aurawa muradin zuciyarki? Ina zaki je? Ba zaki tsaya ki nuna masu cewar kin fi kowa cencenta kasancewa mai dakinsa? “


BILKISU da zuciyarta ta kyekyashe da wani koke koke ta kaleta tar cikin ido ta ce” Mun taba yi da ke cewar ni din nan shine muradin zuciyata? Me ya ke ba zaki dubi iyayenki ki nuna masu cewar bakya so a shafa maki lafia ba? Me ya  sa ba zaki daina hashashe a kan lamarina?, Abinda ya hanna ki kallon idannuwan iyayenki ki bijire masu nima shi yake dawainiya da ni! AISHA ni bafilatana ce ciki da bai na ga damar na saka ki shakun sunnana bale wai har ke ki san abinda yake cikin zuciyata, zan tafi wajen mahaifina ne domin yana garin nan ba wai dan wani abin ba!”Aisha ta saka hannunta ta riko damtsen hannun Bilkisu ta juyo da ita sosai ta ce” Ama baki san ciwon kanki ba ko? Wasa zaki yi da damar ki a kan wani dalili? Har zaki tafi ki bara mana gidan sai kace dole? “


Wajen hannun ta bi da kallo ta kuma kallon fuskar Aisha da wata irin daure fuska hakan ya sa ta cika mata hannunta


Hannunta ta kama ta nufi wajen kujera da ita ta zaunar da ita, hannayenta ta dora a saman hannayen kujerar tana kallonta ta ce” Ki kular min da shi domin shi din ba burina bane, Aisha DOCTER HISHAM *RAYUWATA* ne, ba tafia ce zan yi na bara  maki gida dan na kasa, zan kara gaba ne dan fadan nan idan na ja sunnana marar nasara, furucin mahaifiyata na cikin lamarin, da ba dan haka ba Aisha na iya daura zani na iya saka gefto a kasan sket haka kuma na iya tuka tuwo!, zan je ne na samu nutsuwar zuciyata ne na dawo na buga kalangun auren ubana, ke miji aka baki, D’ansu suka baki, ni kuwa ubana ne, Aminina ne, HISHAM RAYUWATA NE!  ba zan iya daga kai daga umarnin wace ta sakoni duniya ba, domin haihuwata aka yi”


Tana gama fada ta mike ta ja akwatin dan ba zata iya daukanta ba ta fito falo 

Aisha kuwa tamkar mutun mutumi haka magangannun Bilkisu sukai mata kuwa kafin ta tashi a hankali ta bi bayanta


Gabanta bai taba tsintsinkewa ya fadi irin na yau ba


Sanye yake cikin bakin yadi mai sasaukan kwaliya, irin zaman da ya yi kafarsa daya ya dan tankwasata saman kujerar hakan ya sa ake iya gannin tafin kafar dayar kuwa a ajiye a saman cafet

Gefe da gefensa su Mama ne da Bakuwa, sai Tati zaune


Akwatin hannunta yake kallo hakama du wanda ke fallon ya bi akwatin da kallo


Bakuwar ce ta fara fadin” Aa, ya da kaya haka ina zuwa y’ata?” 


Murmushi Bilkisu ta kakaro kafin ta yi magana Mama ta ce” Zata je ne ta yiwa Mahaifinta kwana biyu Hajia kin san a nan yake”


Mama ya tsurawa ido da dan mamakin abinda ta fada, yaushe Bilkisun ta fara zuwa har ta kwana a gidansu? Sai dai bai ce komai ba ya mayar da dubansa kanta, wanda hakan ke sakata jin tamkar zata fadi


Tati ta mika mata hannu ta ce” Zo “


Ajiye katuwar akwatin ta yi ta karasa gaban Tati tana shirin rage tsayinta 


Tati ta kamota tana kallonta, muryarta a matukar sanyaye ta ce ” Baki da lafia fa, maganar auren yayanki kuma ake fa, ba zai dauki lokaci ba, bakya nan waye zai yi bukukuwan? “


Idannuwanta dake lumshe ta bude a hankali tana kallon Tati


Muryarsa kasa kasa ya ce” Ba gaki ba Tati, ko ba komai ai ke ce kirjin bikin domin ke kika haifa? “


Du dubansa aka yi hakan ya saka shi yin murmushi ya kalli Mama a hankali ya ce” Ai zata yi komai ko *rayuwata tunda kin bata dama*? “


Sai kuma ya kai dubansa wajen su Tati, 

Kunyar furucinsa ya saka Tati sai sasada kai take, ita ta haifa? Dama bakinsa na iya fadin ba dadi haka?

 ya kara duban tati  da kyau ya ce” Mama? “


Shiru wajen ya dauka 

A hankali ya kuma cewa ” MAMA? “


MAMA ta hadiyi yawu a makogwaronta cike da mamakin sabon Hisham din dake zaune dangalgal yana aniyar yayaba magana cikin ruwan sanyi ba da hayaniya ba, tun da ya zo ya zauna daidai da gaisuwar da ya yiwa mahaifiyar Aisha sai da ta ji kamar ba Hisham dinta ba domin cewa ya yi yaya dai sarakuwar? Ido cikin ido kuma yake fadin magana ya aiko da murmushi kamar wanda ya shanyo masu giyarsu ta kansu, sai take ji dama bata tirsasa masa zuwan ba a irin wannan lokacin

Jiki a mace, murya a sanyaye yannayin motsinta a hankali ta ce” Na’am? “


Dubanta ya kara yi ya sada kansa, sosai ya rage muryarsa ya ce” Ke mamana sunnanki, ita kuwa *Mama* dan cewa ta yi na ringa kiranta da Mama”


Mama ta ringa jifansa da kakausan kallo dan ya kama kansa ya daina wannan abin aman sai sun yi ido hudu sai ya sakar mata murmushi hakan ya matukar kayar mata da gaba, ya tayar mata da hankali , kallonsa kawai take ta kasa wani kwakwaran motsi, wannan tsaurin idon da tsayayar ba yaronta bane, wannan kafe mutun din da ido bata san danta da shi ba , so take ta dan mike ta ja hannunsa ta yi dakin cen da shi ta tuna masa cewar ita ce fa? Aman kuma tana gudun kar a ga zakewarta da yawa a kan lamarinsa bayan zainab ta gama shekar cewa ita ta haifi abinta


Rasa abin cewa ya saka tati mikewa ta nufi ciki dan daukowa Bilkisu sako, Bakuwar gidan kuwa sam bata gane abinda yake faruwa ba dan ita a ganninta normal dan ya kira mahaifiyarsa da sunna Mama


Da ido Aisha ke kallonsa, tamkar zata dauke shi da idannuwanta haka kuma sai ta juya dubanta wajen Bilkisu


Sai da ta duka har kasa ta gaishe shi, aman abin mamaki kallo irin kallon da ake kira na kasa kasa a bayane ne yake jifanta da shi, wanda du wanda ke wajen in dai zai kale shi to fa dole ya ga irin kallon nan ya zarce misali kuma mirsisi ya ki amsa gaisuwar tata har ta kai wani dan lokaci a tsugunen nan 


A hankali ta dan dago da dubanta daidai lokacin da Tati ta dawo dauke da leda a hannunta tana jira Bilkisu ta mike ta bata


Bai amsa mata ba, sai ido hudu da suka yi

Kakausan kallon da ya watsa mata ya sakata kara sada dubanta sannan ta mike tsaye da dan sauri tana wani soshe soshen gaban goshinta


A hankali ta raba gefen Mama ta dan rungumeta a jikinta muryarta a shagwabe ta ce” i’ll miss u mum”


Mama da turancinta ba wani nesa ya yi ba sai dan abinda ba za’a rasa ba ta sakar mata murmushi tana dan dadaba bayanta, muryarta ciki ciki ta ce” ki kula da kanki, ki kare mutuncin kanki, zan kirayi maman naku in sha Allah “


Bilkisu ta gyada kanta sannan ta juya a hankali ta koma wajen jakarta


Tati dake tsaye du baki daya yannayin ba dadi yake mata ba, tana ta tunani kala daban daban a cikin zuciyarta, shin zata dawo ta ce da shi basu sha nono daya ba? A me zai kaleta? Yaya alkawarin da ta yiwa mahaifin Aisha? 

Yaya zata yi da kunyar abin kunya a ma’aikatarta? Ba zata iya jure wannan ba, dole ta yi hakuri da yannayin nan ta tabata na dan lokaci ne, idan Bilkisun ta matsa dinma zata fi sakewa a kan maganar auren nan


Hannu biyu Bilkisu ta saka ta amshi ledar hannunta , fuskarta dauke da dan murmushi ta ce” Na gode Tati, Allah ya kara arziki “


Bata iya bata amsa ba sai lumshe idannuwanta da ta yi


Shi kam ya mayar d ita TV, take takenta kawai yake kallo, to waima da izinin wa zata wani je gidansu?


Har sai da ta kai wajen kofar fita daga falon ya sauke kafarsa daya dake tankwashe cike da kasaita da isa ya budi bakinsa ya ce”                       ðŸ’ƒðŸ»

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like