DUK NISAN JIFA 18

Advertisement

                                18

Cike da kasaita kamar za’a ciro maganar daga bakinsa ya ce” Yaya baki saka hijab ba zaki fita BILLKISU? ” Ja ta yi ta tsaya tana jin wani haushi haushin kin amsa gaisuwarta da bai yi ba, Akwatin hannunta ta duka ta zuge hakan ya saka shi rage girman idannuwansa yana binta da kallo


Ciro hijab ta yi fari kal mai tsayi ta saka a jikinta ta rufe akwatin 

Tana kokarin kinkima ta ji ya kuma fadin” Wa kika tambaya zaki tafi gidan Aba? “


Gabanta ne yanzu ya fadi hakan ya sa ta juyo da dan sauri tana kallonsa


Idannuwanta ta yiwa rauraurau da kyar ta budi bakinta da yaren filatanci wanda ta tabata Mama da tati kawai suka iya yaren nata a wajen sai shi ta ce”  Miyecci Dada kanko on hokkiyam lawol hamma am (Na fadawa mama, itace ta bani dama Yayana ) “

Advertisements


Bakinsa ya dan tabe yana kallonta tsai cikin ido ya ce”  Yaushe Mama ta fara baki damar zuwa wajen da zaki kwana? “


Sai kuma ya rage amon muryarsa sosai da yaren hausa ya ce” Yaya kike so na iya rintsa idona bayan kina nesa da ni? “


Gaba daya wata irin kunya ce ta gama kama mama hakan ya saka ta mike ta shiga gyare gyaren zanin jikinta fit ta shige cikin kicin


Tati kuwa harta da bakinta daidai yake da budewar da ta yiwa idannuwanta tana kallon ikon Allah cike da mamakinsa


Aisha kam har ga Allah sai da gabanta ya yanke ya fadi , wanda bata san ko na meye ba


Mahaifiyarta kuwa ta kara kura masa ido tana kallonsa itama da mamakin furucinsa, me yake son nunawa? Ko dai da Aisha ta ce ba zai taba sonta ba Bilkisu yake so din yake son tabatar masu? 

Advertisements


Bilkisu kam gaba daya sai ta rasa a yannayin da take ciki, a sama take ko a kasa take, a wani irin yannayi take jin kanta? Gaba daya lakar jikinta sai ta zare, ta nemi kuzari ta rasa sai na kyafta ido da bin fuskarsa da kallo, ………..inama zai gane cewar yana ilatata? Inama zai gane tatausan lafazi ko nuni da an damu da mutun a yanzu idan yana yi mata yana sakata a hakin ha’ula’in rayuwa? Inama zai zabureta, ya hankadeta, ya turata zuwa wajen da zata ji ta tsani ganninsa ko jin labarinsa? Inama zai kasance mai adalci a yar marainiyar zuciyarta da ta rayu da begensa?


Da yaren filatanci wannan karron ya ce”Mijabi do dum jarrabore on do bo dum salan to de donma de dillai mihosi banni dau hoddirore am on hamma am  (ki kula da kanki, ki kula da ibadarki, ki kare mutuncin kanki, Allah ya tsare Bilkisuna….) “Sai da ta hadiye yawu mai kauri tana dubansa a hankali ta dago hannunta ta duba agogon hannun nata, muryarta a sanyaye cikin ta kara lumshe idannuwanta ta ce” Na yarda da cewa jarabawace wannan kuma zata kauce, idanma tana nan bata kauce ba na dauki hakan a matsayin kadarata Yayana  “


Gabansa na faduwa ya mike tsaye daga zaunen da yake, a hankali ya ringa nufota, su kuwa kamar wa’inda aka dasa su ukun nan ba wanda ya matsa daga wajen da yake, hasalima Tati kadai ke fahimtar abinda suke fada da yaren filatanci, su biyun kuwa kowace da abinda take son ganni a bayane


Sai da ya zo daf da ita ya kura mata ido a sanyaye cikin yaren filatancin ya ce”  don jarrabore fere je jodanima der berde na ko don ko ayidi yeccugo am do dama berdema laram hado miko am yeccam minbo mihaban ko be moi hader duniyaru do gam miyi,a mihokkimamo (Akoy wata jarabawa da ta tsaye maki a rai ne? Ko akoy abinda kike son sanar mani dake damun zuciyarki?, kaleni nan kanwata ki fade shi ni kuwa zan yi kokowa da ko wanene a duniya dan gannin na baki shi!)”


Da mamakinsa take kallon fuskarsa, yaya aka yi ya yi tunanin dan ya girmeta a haife yana mai sakata a hanya har yake tunanin yana iya sakata a cikin hali na mugun matsuwar da zata budi baki ta kale shi shi ta furta masa kalmar dake da matukar girma da nauyi a bakinta? Ko ya manta ita, itace fa bafilatanar domin mahaifinta filo ne? Ko ya manta cewar shi ke iya furta rashin lafiarta tsabar yanda take fama da nauyin baki? Lalle ya dauki lamarinta da wasa.

….


Murmushi ta yi masa ta langwabe kanta, yan lebunnanta ta hade ta kuma bude a sanyaye ta ce” Bana tunanin haka, ban yi furucina dan wata manufa ba,  sababin halayan yayana nake yiwa inkaya da jarabawa, kuma na san zasu kauce, zan je na kwana biyu na dawo ko dan na ciro anko in sha Allah “


Tsatsareta da manyan idannuwansa ya yi, hakan ya sa ta ringa dan wasa da yan yatsunta tana kallonsa


Bata taba tunanin abinda zai fada kennan ba, bata kawowa ranta cewa HISHAM zai iya wannan tataciyar maganar ba, sai ji ta yi ya furta “NA RUNGUME KI? ” 


Dan zabura ta yi ta matsa baya kadan tana kallonsa hakan ya saka shi sakin dan murmushi ya juya wajen Tati dake binsu kuri da kallo ya dan girgiza kai yana hangen yanda Mama ke son fitowa aman ya gagara dan sai ta leko kanta idan ta ha sunna nan sai ta koma da sauri


Dan daga muryarsa ya yi ya ce” TATI, yarinyar nan yar kauye ce, koda yake filatancin ne ko meye wama ya sani, aman in ba filatancin ba ni ai Yayanki ne dan kawai na ce zan rungumeta kin ga wata zabura da ta yi kuwa? “


Yanzun kam Tatin ce ta juya takim takim ta gudu da kafafuwanta, kusan a tare suka aikata hakan ita da Bilkisun domin kuwa a da tana gannin jakarta da nauyi ba zata iya dauka ba sai gata ta kinkimi jakar ta yi wata kwana ta fice a fallon


Sai da ya sauke ajiyar zuciya ya dantse lebensa na kasa har ta bacewa ganninsa sannan ya juyo ya kuma kallon Aisha da mamansa


Kallon tsaf, kallo irin na gaku zaune, ku ne kuka shigo min rayuwa a yannayin da kuka ga dama kuke son yi min wasa da rayuwa ko? 

Sai kuma ya juya ya fice yana daidaita agogon hannunsa cikin takunsa na kasaitacen namijin da ya san kansa ya kuma gane cewar yana birge mai kallonsa


Jikinta a mace ta karasa gaban mahaifiyarta ta duka kusa da kaffafuwanta tana kallonta, kukanta da take rikewa ya kasa rikuwa hakan ya sakata yin magana cikin muryar kuka tana son rage sautin muryarta da karfi da yaji ta ce” Cikin wannan yannayi da suke ciki ake son raba su? Tsakanin wannan soyayar biyu ake son saka ni? Idan ya wulakanta maku ni shin kuna da damar nuna kun ji ciwo kuwa? Idan na fuskanci rayuwar rashin y’anci a tare da shi ba zan taba gannin laifinsa ba mama, ya furta , ya bayana, ya nuna ga wada yake  so  mama, me yasa kuke son saka ni a tsakaninsu? “


Mamanta ta dora hannunta a gefen kuncinta a sanyaye ta ce” Ba zaki gane ba Aisha, ina son tabatar maki cewa ko wani mahaifi burinsa yaronsa ya samu wajen da zai huta, wajen da hankalinsa zai kwonta, Aishatu a tunaninki soyayar da suke danewa suka kasa furtawa junnansu har soyaya ce? Ke a ce a cikin soyaya tsamo tsamo muka tarar da su irin wace basa iya second daya basu ga junna ba kina tunanin bayan auren itace zata ci gaba da wakana a tsakaninsu? A gabanki aka tambayeta shin da wani abu tsakaninsu? Ta bada amsar *aa*,  shima a gabanki aka yi masa tambayar shin wani abu ke tsakaninsu?  Ya nuna aa kanwarsa ce! Mahaifiyarsa sai da ta kara tambayar marikiyarsa itama ta nuna AA ba hakan bane, idan mamansa ta masa zabin abokiyar rayuwa mu sai mu kiya? Babu fa wanda ya zalince su, ba wanda ya shiga hakkin soyayarsu, idanma tunaninki ke nuna maki an zalince su zan fada maki cewar su fara tuhumar kansu kafin su tuhumi wani! “


Tsayar da maganar ta yi gannin mama ta fito dauke da abinci a hannunta ta kawo masu tana murmushi ta ajiye tana duban yannayin Aisha ta ce” Lafia take kuka? “


Mamanta ta ce” Kin san bata iya sabo ba hajia, wai Bilkisu ta tafi “


Mama ta ce” Ayyah, ai zata dawo nan ba da jimawa ba, abinda bikin ba da jimawa za’a yi ba, dolema ta dawo a yi bikin nan da ita ki daina kuka kin ji Y’ata?”Aisha ta sada kanta tana sauke ajiyar zuciya , sai da Mama ta tafi sannan Aisha ta dagi tana duban mamanta ta ce” Sai nake jin tsoron mahaifiyarsa, sai nake gannin matar da bata yiwa wada ta rike mata yaro da gaskiya  adalci ba,  anya idan ta gama samun abinda take nema ba zata juyo da gabarta a kaina ba? Ko tace zata juya min da ragamar nawa gidan ba? ,  Mama sai nake gannin matar nan kamar irin matan nan ce masu zama da mutun idan yana da shi, idan ba wata alfarma zaka iya yi mata ta rayuwa ba sai nake gannin kamar ba zata iya zama da kai ba Mama sai nake jin tsoro da tsoron shiga hakki na kama zuciyata “


Mamanta ta yi mata murmushi ta ce” Sai kike gannin kamar ita din kaska rabu mai jinni jika ce?”


Da sauri Aisha ta sada kanta tana tsoron kar mamanta ta rufeta da mugun fada


Mamanta ta ce” Haka ne, bari ki ji wani abu, sannin cewar da na yi mulki zamani ne, a yanzu ana iya cirw mahaifinki daga saman kujerarsa a dora wani mai yiwuwa ya samu wajen da ya fi wanda aka cire shi, mai yiwuwa kuma a kara yin kasa da shi sha’ani na siyasa ya saka ni zagewa na hau na zauna kan maganar aurenki da PROFESSOR HISHAM, ita, ita ke rike da ATTAJIRI, ita ke rike da dama a hannunta, ba’a yiwa likita kutse ko a yaki ba’a yakar likitoci da yan jarida, Bale nata, watau mai gidan likitoci, Hisham din yanzu ya fara girma a haka, yanzu ya fara gidan Aisha, kar ki ga laifina dan na nemawa y’ata wajen da zata huta, ko a musulunci ba laifi na aikata ba, idan kuwa tunaninki zata samu abinda take so ta dawo ta wulakanta min y’a ai nima ba mahaukaciya bace da zan zauna na zaune, kin kuwa san ita ke mararin zama kawata ni kuwa ni ke tunkahon a san ina tare da uwar wannan wata sha kallon? Kar ki damu da shariyarsa, da yannayinsa, na san me yake nufi kuma ina sane da take takensa, ba komai zai yi ya gama ne! “


Ita kam Aisha bata da ta cewa sai mikewa da ta yi ya nufi dakin da take kwana ta kwonta tana mai kashe wayarta baki daya dan bata son damuwa, so take ta fuskanci magangannun mahaifiyarta da kuma irin yanda mamanta ke nuna mata ba laifi bane dan ta auri Hisham, irin yanda take nuna mata ba kanta farau ba, irin yanda take lwadaita mata rayuwa da wannan bawan Allahn da maganar fatar baki bata taba hadasu da junna ba


Sai da ya budi bakinsa da dan karfi ya ce” BILKISU mun karaso fa ” sannan ta yi firgigit daga lumshe idan da ta yi ta bude tana zuba idannuwan nata a bangaren da kofar gidan mahaifinta yake


Mahaifinta ne tsaye cikin shiga ta doguwar rigar jalabiya kansa dauke da hula saman lalausan gashinsa yana kallon bangaren motar yana murmushi


A hankali ta ringa jin sanyi a cikim zuciyarta tana kallon fuskarsa daga nesa


Cikin nutsuwa ta bude ta fita a motar zuwa lokacin Kader ya fita ya ciro mata jakarta ya nufi wajen Abanta


Da fara’arsa ya fadada yana fadin” Oyoyo Mai gado, ki ce zaki kwanar min wannan karron? “


Kanta ta sada ta nemi zubewa kasa dan gaishe shi tana murmushin itama, sai dai bai bata damar hakan ba ya rikota ya dagota yana kallonta ya ce” Tashi tashi Mai gado “


Muryarta a sanyaye ta shiga gaishe shi , su ba sakewa sosai domin bata taba zuwa da niyar kwana a gidansa ba


Get din kofar aka bude aka fito

Wata budurwa ce ta fito cikin shiga ta dogon hijab


Wata irin fara’a ce a bayane a fuskarta ta nufo su da sauri tana fadin” Lalle marhababuki kanwata “


Itama murmushin ta sakar mata tana kama hannunta kamar yanda ta miko mata ta ce” *MAMI* na same ku lafia? “


Mami ta janyota jikinta ta ce” Ke meye kike wani dari dari, zo mu je ciki mana”


Har sun juya zasu shige ciki mahaifinta ya kirayi mami hakan ya sa suka dakata ta juyo tana kallonsa ta ce” Na’am Aba? “


Da yaren filatanci ya ce” Dan Allah bana so ko da wasa mamanku ta nunawa Bilkisu wani abin, kin ga Bilkisu y”ata ce ta cikina, ku biyu kawai na malaka kuma ina son abina”


Kanta ta gyada ta ce” In sha  Allahu Aba, ai na gyara mata dakina ta yada zata walala da ranta, in sha Allahu ba abinda zai faru”


Bilkisu dake kallon kasa baki daya tana jin su, basu san cewa ta iya filatanci ba hakan ya saka mahaifinta yin yaren a kusa da ita, dan basu taba yin filatanci da shi ba

A kasan zuciyarta sai take jin wani dardar na tsoron shiga cikin gidan, shin matar gidan bata maraba da ita ne ko me? To me ta yi mata ita kuwa da ko ta zo gidansu bata taba yin zaman sama da awa daya ba bale ta ce ta  mata wani laifi? 


Sukuku ta bi bayan Mami har suka shige cikin gidan


Kofar dakin mahaifiyar su Mami din suka tsaya suka ringa salama sama sama


Da kyar aka amsa masu, cikin sanyin Murya Bilkisu ta ce” Mama nice Bilkisu ina yini “


Maman nasu ta dan yi jimm kafin ta amsa a dakile ba tare da ta kuma tambayarta gida ko mamanta ba ta ci gaba da ninkin kayanta 


Janta Mami ta yi suka nufi dakin mamin


Abinci ta gabatar mata da su ruwan sha , baki daya a ciki  farin cikin ganninta zaune yau itama tare da yar uwarta mace jinni guda, tun dazun da mahaifinta ya shaida mata maman Bilkisun ta yi kira cewar gatanan zuwa zata kwana biyu ta kasa zaune ta kasa tsaye  sai da ta tabatar ta gyara mata waje ta mata girki sannan ta kimtsa tana gadin zuwanta


Bilkisu ta kalli hannunta dake cikin na mami ta saki murmushi a hankali ta ce” Lah, jibi tsagun hannayenmu sun kusa zuwa iri daya bayan bama kama Mami”


Mami ta fadada fara’ar fuskarta ta ce” Bilkisu, ima farin cikin kasancewarki a tare da ni, dan Allah ki yi zamanki a nan mana, kin ga Aba burinsa kennan ya hade mu a waje daya duda an kusan yi mani aure aman ina mai gabatar maki ko an min zan ringa zuwa kulun ina ganninki kanwata “


Bilkisu ta ringa jin wata irin kauna irin ta dan uwantaka na ratsa dukan gabai na jikinta, 


A nan suka shiririce sunna ta labari, har mutumen da zai auri yayarta ya zo, watau UMARU 

Ba wani zance sukai ba, Mami sai lalabewa take hakan ya ringa saka Bilkisu kilkilar daria har tana rike cikinta 


Bai wani jima ba ya tafi, Bilkisu dama tana cikin hakin wanki, wanka kawai ta yi ta nemi waje ta ajiye hakarkarinta dan samun baci duda bata tunanin in har zata iya rintsawa


Haka kuwa ta kasance, domin kwana ta yi tana juyi sam bacin ya kasa zuwar mata, ga cenjin yannayi, ga rashin sabo, ga damuwa, zata iya cewa Alhamdulilah bata ga baci ba

Da sanyin safia ta farka ta fita tsakiyar gidansu

Tsintsiya ta dauko ta shiga share balbalin gidan mahaifinta mai girman gaske cike da kuzari domin ta dauri aniyar aikata nasihar mahaifiyarta ko dan ta samu zaman lafia da matar mahaifinta

. …………. *Walahi Jama’ar gidan DUK NISAN JIFA baki na yi , shi yasa kuka ji ni shiru ba labari, aman ina biye da comment din ku sau da kafa, na gode Allah ya saka da mafificin alkhairi, ina ji da ku fiye da tunaninku, Allah ya baku ikon ci gaba da bani zafafan comment*                           Barkanmu da juma’a

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like