DUK NISAN JIFA 19

Advertisement

                19

Shara ta yi ta mamaki, domin baki daya balbalin gidan nan sai da ta share shi tas tas sannan ta nufi wajen kwanonin da ta ga a ajiye duda basu da yawa haka ta wanke su tas sannan ta koma dakin ta dauko kayan wankanta da hijab dinta ta nufi bayi


Bayin tsakar gida ne da su har kwaya uku, na wankan ta shiga mai dauke da pampon sama da na kasa 

Bata yi wankan ba sai da ta wanke shi tas tas, ta fito ta shiga sauran bayin suma du ta wanke domin a kowani bayi akoy clean da hypo da tsintsiya da buta ta wanke bayi, sai da ta gama tas  sannan ta yi wankanta ta fito


Tana fitowa sukai ido hudu da matar gidan sanye da hijab a jikinta da alamu ta fito ne dan fara aikace aikacen cikin gidanta


Har kasa ta duka ta gaisheta cike da ladabi da biyaya hakan ya saka matar yin sokoko tana kallonta kafin ta amsa mata sai kuma ta bita da kallo har ta shige dakin Mami

Advertisements


Ajiyar zuciya ta sauke ta koma dakinta har gari ya hantse sai ta fito ta dora girki dama ta fito ne ta tsaftace gidan sai ta ga yarinyar da ta kasa cire kishin mahaifiyarta da tsoron kar a je wata mai baudadan hali ce rana tsaka za’a ce zata wani zo ta zauna da su ta share gidan ta tsaftace kwanoni harda bayi


A kasan zuciyarta ta ayanna ‘Ba dai zan sakar maki fuska ba domin ba’a yabon dan kuturu sai ya shekara goma da yatsa, ban san me ya kawo ki gidana ba, kar a je mamanki ta turo ki ki kulan wata fitina ina zamana lafia da mijina, ta rabu da shi shekara da shekaru ta kasa aure kar a je yanzun ta waiwayo min abina ne dan ta hadasa min rashin kwonciyar hankali kamar yanda shekarun da ya aureta na kasa samun kansa har sai da ya rabu da ita!’


Wankan da Bilkisu ta yi sai ta samu jin dadin yannayin, hakan ya sa tana kwonciya sai baci ya dauketa 


Ba ita ta farka ba sai kusan sha daya, a rikice ta mike tana salati tana kallon agogon dakin mami 


Da sauri ta shuri brosh dinta ta fito tsakar gida


Mami na zaune tana daka a turmi sannan tana yiwa mamansu hira sunna yar daria ta dago da kanta ta ce” Hala har bacin ya isheki haka? Ko zafi ya tashe ki ne? Mama sam bata yi baci ba tsakiyar dare ban san ko me ya hanna mata rintsawa ba”

Advertisements


Mamanta ta ce” Eyah ” daga haka ta yi shiru bata kuma tofa wani abin ba


Ita dai sai da ta wanke bakinta da fuskarta sosai sannan ta mayar da shi ta cenza audugarta ta kule wada ta cire din a leda baka da ta zuba a jakarta dan irin haka sannan ta fito ta nufi bayi mai dauke da masai


Tana shiga ta saka cikin masai din sannan ta rufe  ta kunna pampo ta kara tsaftace jikinta sannan ta fito


Tana fitowa ta ga maman Mami tsaye kikam, ido cikin ido ta ce” Meye kika shiga da shi a leda ? “


Bilkisu ta dan tsura mata ido sai kuma ta sada kanta muryarta a sanyaye ta ce” Auduga ce na saka a masai Mama “


” LAFIA kuke tsaye haka a bakin bayi? ” muryar mahaifinta ya karade wajen yana karasa shigowa da kafafuwansa


Matarsa ce ta dan daburce sai kuma ta ce” Ba komai baban Mami “


Murmushi ya yi yana kallonsu, Bilkisu ta duka ta gaishe shi


Irin yanda yake amsa mata cike da kulawa sai take jin wani irin yannayi na daban a zuciyarta a kansa, kauna ce irin ta mahaifi tsaftataciya mai kima, kauna ce tataciya mai daraja ke ahiga zuciyarta ko tace ke yin tsiro a cikin zuciyarta


“Ta karya ne?” Ya tambayi Mami dake tsayen itama jikinta du a mace sakamakon abinda mamarta ta yi na rashin yarda da nunawa da take kamar Bilkisun ta zo ne ta yi mata wani abin dan ta bata zamanta da mijinta ko ta saka ya maida mamanta dakinta ta dan girgiza kai ta ce” Yanzu ai ta farka Aba “


Abansu ya ce” To maza ku zo ku dauki abincin cen na dakina ku ci, bana son wasa da yinwa “


Mami ce ta fi kazar kazar, ita Bilkisu matsala ta rashin saurin sabo da mutane na damunta hakan ya sa sai dai ta bi Mamin da kallo har ta dauke wata kyakuawar kula shake da lafiyayan abinci ta ajiye masu saman tabarma kasan shukar mangwaron da ya yi diya sosai ga sanyi


Ruwan sanyi ta dauko masu da cokali sannan ta yiwa Bilkisu Bisimillah cike da kulawa


Zasu fara cin abincin kennan saurayin Mami ya yi salama


Da sauri Mami ta kafe Bilkisu da kallo a hankali ta ce” Na shiga uku me ya zo yi daidai lokacin da zan ci abinci? “


Bilkisu ta saki murmushin da ya fito mata tun daga cikin zuciyarta , domin irin yanda ta tsatsare Bilkisun da manyan idannuwanta sai abin ya mugun kasheta da daria, kunya, asalin kunya irin ta filani ce Mami ke nunawa a dukan motsinta, shi da kansa sai ya zauna ya maida gabansa gabas yana gaishe da su Mama


Abinda ya kara birgeta ya kasheta ya bata daria irin yanda maman ta tikice sai wani murza goshi take ta rasa inda zata tsoma ranta, ba irin sirikan zamani ba dake shagalinsu gaban sirikan nasu ba abinda ya dame su wai wayewa


Aba ne ya fito ya dan toge ya ce” Yauwa ka kawo? “


Kansa sade ya gyada kansa ya mika masa sako a leda sanann ya mike da sauri ya fice


Sai da ya fita, Aba ya bar wajen , sannan ta sauke ajiyar zuciya harma ta iya yin numfashi mai dadi


Waigawa Bilkisu ta yi ta ga Maman bata nan, hakan ya sakata yin daria a bayane ta ce” Ina Mama? “


Mami ta ce ” Uhum, ai bata san zai shigo yanzun ba, da bai tardota ba, yanzu wannan gannin nata da ya yi da ranar nan gata ga shi ai ba zamu kuma ganninta ba sai gobe”Cike da Mamaki Bilkisu ta ce” Aman meye anfanin hakan? Ina ce aurenku bai fi saura wata ba?”


Mami ta zarro ido ta ce” Ke Balki, mamanki ba bafilatana bace ina? Yanzu mutumen da aka saka mana rana saura yan kwanaki sai kawai mahaifiyata ta yi ido hudu da shi? Ai ko ni nan ana cewa wai bani da kunya ina sauraronsa idan ya zo min zance bayan basu san ba ni ba abinda muke cewa junna da wannan mutumen”


Bilkisu na rike dariyarta ta ce” Sunnansa UMARU ai”


Kanta ta dafe ta ce” ke kam idan aka saka maki rana ban san yaya zan yi da bakinki ba, birni ta lalata ki, yanzun sunnan wannan mutumen kike kamawa haka? Uhum”


Bilkisu kam a yau sai take jin kanta a wata duniya ta daban, a hankali ta ce” Sai nake gannun kunyar nan ta yi yawa, kin ce aurenki ya kusa ban ga an shiga yi maki shirye shiryen nan da ake yiwa amare ba, ban ga ana baki abubuwan sha ba, ban ga kema kina nemawa kanki wasu abubuwan ba bayan yanzun zaki ga yan mata da kansu suke nema gyara ne”


Mami ta gyada kanta ta ce ” Haka ne, gyara ne, aman kin ga mu wancen tulun da kika gani dauke yake da maganin zafi, irin mai cire datin nan mai kashe sanyin nan, iya shi ake mana, ba’a yi mana wani gyare gyaren fata, idan mun je dakinmu sai mu yi abinmu a dakanmu, Bilkisu mu idan budurwa ta tsiri irin haka ai ta janyowa kanta da iyayenta abin magana, sai kace ba budurwa ba? , kuma maganar kunya ai Bilkisu kunya ado ce ga y’a mace, bari ki ji ko a zuciyarki bakya jin kunyar nan arota ki yafawa kanki, ba’a so mace ta zamana ita bata nuna halaya irin na jin kunya a gaban namiji, ko mijinta ne ko abokanan zama ne na yau da kulun, kunyar nan baban makami ne da muke takama da shi a duniyarmu”


BILKISU ta ringa gyada kanta tana kallonta, tabas ko da wa ka zauna zaka karu da sanni da dabi’u irin nasa, zaka anfana da ilimi na yau da gobe, tana da kunya mai girman gaske fa, aman a yau ta ga ahalinta da suka dameta suka shanye a kunya


Mami ta janye hannunta daga saman cokalin ta dibo abincin ta nufo wajen bakin Bilkisun hakan ya sakata dan zarro ido ta girgiza kanta


Mami ta yi murmushi ta ce” Baki isa ba, ina sane da tunda muka fara baki ci da yawa ba bayan Mama ta iya girki sosai, ci ko na dane ki na maki dura bari gannin kin dan fi ni gwabi “


Daria ce ta kama Bilkisu, kwarai ta fita gwabin sosai ma kuwa, Mami na fama da rashin lafia irin cutar kashi, mai karfin nan, cutar tata ke karar da ita lokaci zuwa lokaci, wani sa’in idan ta tashi har sai an cire rai da ita sai kuma Allah ya tashi kafadunta, tun tana jaririya mahaifiyarta ke fama da dawainiya da rashin lafiyarta, idan aka ce sanyi ya matso ko lokacin damana, kai wani lokacin ko zamanin zafi ciwon yakan tashi , sai ta kare kaf ta dawo sai kashi sannan ta samu lafia kuma sai ta dan farfado ta dan maro


Sai da suka gama cin abincin sannan suka nufi madafar, a cen suka gama dafa abincin da Mamansu ta fara suka zuzuba suka kilacewa kowa nasa


Sai bayan sallar la’asar yayansu ya dawo, nan Mami ta sakata daukan litafi suka je kasan innuwar nan bayan ya gama cin abinci suka shiga karatun alkur’ani mai girma


Irin yanda Bilkisu ke karatu ya saka shi jinta har cikin ransa, da farin ciki dankam a kasan zuciyarsa yake tambayarta a wace makaranta ta yi karatu ne? 

Nan take shaida masa a makarantar Malan Hafizu (Allah ya jikan ka malamina, dan Allah ku mu yiwa Malan hafizu kulhuwalahu kafa uku uku Allah ya jadada rahama a kabarinsa da kuluhin musulmi, Allah ya sa kwonciya hutawa ce, domin kuwa shi din malami ne kuma uba a wajenmu Allah ya saka da alkhairi ) “


Tabas ya san mutumen, malamin akoy hakuri da jajircewa hakan ya saka su yin karatu mai tsayi yau domin tilawa suka yi ta bakara har sai da suka kai karshenta……………….


A gidan mahaifinta yau kwananta hudu, sau biyu sunna waya da mamanta ta wayar Abanta domin a gidan yayansu da Aba kadai ke anfani da waya, Mami bata da ita, hakama maman mami


A zamanta a cikin gidan nan ta shaku da yan uwanta har take jin tsayin lokacin da ta dauka ba tare da su ba ta yi asarar rashinsu a cikin rayuwarta


Sosai suke fahimtar junna da Mami, takan kiya mata wasu al’adun nasu na filani da ita bata sansu ba domin mahaifinta da mahaifin mami asalin filanin jeji ne masu al’adu da dama haka kuma sunna rike da al’adunsu kai da fata


Takan sha daria idan Umaru ya zo zance, Umaru dan kasuwa ne yana harkar waya da yadika, yana da kokari sosai domin irin yanda yake iya yinsa dan gannin amaryar tasa na cikin walwala sai Hamdallah


Umaru d’a ne a wajen kanwar maman su Mami, bata taba gannin matar ba, aman shi Umaru yana da kirki daidai gwargwado


Irin yanda Mami ke sakata a tsakiyarsu idan ana zancen abin ke sakata tikar daria da nishadi, wani sa’in idan labe laben ya isheta sai ta shamaceta ta gudu daki, hakan ke saka Mami fit itama ta tsero dakin tana zarar ido ta dira mata su yi ta kokowa tamkar kawayen junna ba yaya da kanwa ba sunna kyalkyata daria


Yayansu kuwa yakan zaunawa ko wani yamaci su yi karatun islamiya, sosai suke karatu ya dora masu wajen dake.dan cije masu har sai sun shanye sannan su yi hadisai da sauran litatafai 


Yakan shigo da dan abin tabawa daidai da karfin nemansa, ya fi shigowa da fruits dangin su kankana da kankarar da suke wuni su kwana sha duda ana hanna Mami sha aman ina bata iyawa sai tace zafi kirjinta a barta ta sha, du tare taren nan ba zai hana mata mutuwa idan lokacinta ya yi ba


Yau daren kwananta na biyar kennan, tsakiyar dare tana zaune ta hade kanta da gwuiwarta tana zubar da hawaye ta ji an dafa kafadarta ta dama


Da sauri ta dago da dubanta ta sauke a saman fuskar Mami dake kallonta tamkar zata fashe da kuka


Muryarta na rawa rawa ta ce” Shin baki daukeni a matsayin yar uwarki bane ko tsoro kike kar na baza damuwarki? Me ke damun ki kanwata? Ke da wa? Mama ce ba lafia ko hamanki? Tun da kika zo bakya samun bacin dare sai dai ki yi sallah ki zauna ki kurawa waje daya ido, ban takura ki bane dan wani lokacin takurawa mutun fadin abinda bai yi niya ba bashi da dadi, aman abin gani nake kara damunki yake, shin meye matsalarki? “


Bilkisu ta tsareta da ido, sai kuma ta fashe da kuka a hankali ta dora kanta gefen hannunta, jikinta dake dauke da zafi zafi ta ce” Wai cewa suka yi mun sha nono daya? Shine kuma na damu da shi? Shima har ya furtawa mama yana so na, aman me yasa basu fada mana ba sai da muka kamu da kaunar junna? A irgena yau aka amshi sadakinsa da kayansa Mama ta ce za’a saka bikin kwana kusa sosai, shikenan na rasa shi? Inalilahi wa inna ilaihi raj’une”


A hankali take shafa gashin kanta tana sauraron yanda kirjinta ke dokawa, tabas ta gane da wa take magana, kuma ta gane inda yarenta ya nufa domin a sanninta dazu yayanta na fadin haman Bilkisu ya yi kira ya ce ya bashi ita yake shaida masa yana kasuwa shine ya ce to ya gaisheta , nan yake shaida masa ya fada mata wai za’a amshi kudin aurensa


To aman meye dalilin su mamansu na yi masu haka?, shi din me yasa ya yi kiran nan dazu? 


Aman koma meye zara kwatanta nata taimakon wa kanwarta, dan kuwa walahi har cikin ranta take jin damuwar Bilkisun na damunta


A hankali ta ce” Ake rasa raima Balki bale mutun na raye dan nisa ne da garun da ya maku iyaka? BALKI iyayenmu da suka kawo mu duniya sun fi kowa kaunarmu, ina mai tabatar maki ba zasu tashi su yi abun da ba dalili ba, ke kadarama baku sha nonon daya ba tunda suka nuna kun sha ku sai ku wani yi gardama ko me? Haba ai ko ba komai akoy biyaya, sannan akoy tawakali, akoy kuma kunya! Balki ke fa mace ce, kina shanye duka ki shanye bacin ran mutane da yawa, cikin nan naki mai iya kunshe abubuwa masu yawan gaske ne, ba’a yi ciki dan cin tuwo kawai ba, 

To Balki inace adu’o’i gare ki? Aman shine zaki ringa zama kina kallon waje daya kina hawaye? To ke Balki idan ba alkhairin junna bane ba ku fa? Ke kanwata aro jarumtar nan mu je a dama da mu, mu yi murmushi mu yi rawa ta arziki mu gode Allah, ina so kanwata ta sakawa zuciyarta cewa iyayenmu na adu’a a kanmu, in sha Allahu akasin alkhairinmu idan ya same mu to fa matakin da zai kaimu ga alkhairinmu ne, Balkina yaushema aka haife ki? Ke ba tsofuwa ba bale a ce ai kin kai wajen da ba zaki samu malamuncinki ba, idan kuwa an saka ku a cikin sarkakiya dan wata manufa ce kadara cewar Babu abinda ke faruwa ga bawa face wanda Allah ya hukunta sai ya faru da shi…….Allah zai rairaye, ya tankade ya baiwa kanwata kyakyawan zabi mai albarka, ina ji a jikina ba zaki tabe ba in sha Allah Balkina”


A hankali Bilkisu ta rike hannunta da kyau tana ta sauke ahiyar zuciya, muryarta ciki ciki tana jin nauyin zuciyarta na sakinta ta ce”


Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like