DUK NISAN JIFA 20

Advertisement

                            20

Mugun nauyin zuciyarta ta ringa jin yana sakinta, saima ta ji kwata kwata tana iya cire wani wai HISHAM a cikin zuciyarta,sai ta ringa jin damuwar bata kai wajen da zata shiga tunanin kaka naka yi ba, a hankali ta ringa jin ko a yanzu zata iya zuwa a dama din da ita, ba dan komai ba sai dan nasihar yar uwarta ta ratsata, tabas naci a kan abu bashi da kyau, tabas tunda Allah ya kawo haka a tare da su to fa lalle su din ba alkhairin junna bane a matsayin ma’aurata, a hankali ta kara cusa kanta a kirjin yar uwarta tana jin kunya na lulubeta, muryarta a sanyaye ta ce” Mami kin san wani abu? “


Mami ta girgiza kanta tana sauraronta


Bilkisu ta ce” Na hakura Mami, na hakura kuma in sha Allahu zamu koma tare da ke a yi bikin Hamanmu tare, Mami har anko zamu ciro na gayaci kawayena mu sha bikinmu ko?”


Mami cike da tausayawa da kuma mugun kaunar kanwar tata ta ce” Kwarai, harma mu yi ranar saka kayan filani, mu yi bukukuwanmu sosai kanwata “


Advertisements

Ajiyar zuciya ta ringa saukewa hakan ya saka Mami mikewa da ita a jikinta suka koma saman shinfida daya yau suka kwonta


Basa kallon junna , hakan ya sa Bilkisu juyowa ta fuskanci Mami ta ce” To idan aka saka kusa da aurenki fa ango Umaruru zai barki kuwa?”


Ido Mami ta zarro ta dungure kan Bilkisu ta juya da sauri a bayane tana karra zarro ido ta ce” Ja’ira “


Bilkisu ta ringa daria a hankali ta shiga yi mata waka kamar haka” Mami amaryar Umar, yayata yar fara mai farin aniya, gata kamilaliyar yar kwalisa, zata tare da umaruru dan albarka “


Mami ta ringa rintse ido a bayane ta ce” Balki? “


Bilkisu ta amsata tana daria 


Advertisements

Mami ta ce” ko ki min shiru ko na dane ki a dakin nan na jibge ki “


Wata dariar Bilkisu ke yi hankali kwonce tana kara rike yar uwarta, a haka har sukai baci


Da asuba suka tashi suka yi sallar asuba, sai suka dora azkhar, hakan ya kara sanyaya zuciyar Bilkisu sosai ta ringa jin ranta sakayau


Karfe bakwai na yi suka fito suka shiga share gidan, sunna gamawa suka hau wanke wanken kwanoni hankali kwonce sunna hira da daria


Bilkisu ta kuma gyara zama ta ce” Matar Umar “


Mami ta dafe kirjinta ta ce” Ke wannan y’a sai kin saka gudawa ta kama ni, a tsakiyar gida kike kama sunnan wancen mutumen? Idan Maman gidannan ta fito ta kama mu ai har tace hirarsa muke”


Bilkisu ta dauki roba tana wankewa ta dan yatsina bakinta ta ce” Kunyarku ta yi yawa Mami, Meye a ciki dan na ce Umaruru? “


Ai kau Mami ta ciko kwani da ruwa ta ce” Bara ki ga na yi maganin bakin nan naki


Da gudu Bilkisu ta mike ta aniya tatare hijab dinta tana kyalkyata daria tana neman wajen buya daidai mahaifinsu ya shigi gidan daga masalaci yana jan carbi da gudu ta yi bayansa da yaren filatancin da sam ta manta cewa basu san  cewar bata iya ba ta ce”   Baba am yukkinam dada am sobnan am daga viyugomo bagado(Abana boye ni Mami zata jikani daga ce mata amarya ) “


Daria yake yana kallonsu cike da kauna, daidai lokacin kuma maman Mami ta fito itama daga dakinta tana kallonsu dan hayaniyarsu ta fitar da ita


Abansu ya kamo hannayensu baki daya ya karasa wajen tabarma ya zauna, da yake sanyin safiya ne da innuwa ga iskar shukar mangwaro na kadawa


Da yannayin farin ciki ya dan dago habar Bilkisu ya ce”  Nana am dama awawi fulfulde mi anda noi wadi amedai hollugo am awawi(Nanata, dama kin iya filatanci ban sani ba? Yaya aka yi baki taba nuna min kin iya ba?)”


Sai a lokacin ta tuna cewar ashe fa filatanci ta yi, hakan ya sakata kama yan yatsunta tana wasa da su da kalmar hausa ta ce”  Aba , baka taba yi min ba shi yasa ban yi ba “


Mami ta yi yar daria ta kamo hannunta tana kallonta cikin yaren filatancin itama ta ce” Balki am dada ma ekkitima fulfulde ashe kai minani beldum wlh minumi awawata (Balkina Mamanki ta koya maki filatanci ashe? Kai na ji dadi walahi na zata baki iya ba) “


Bilkisu ta ringa murmushi tana kallon hannun mahaifinta dake cikin nata, shima har wani murmushi yake daban ya kalli Mami da hausa ya ce” Mamina, kin ga idan Autana ta yi irin zurfin cikin mamanta to fa ko yanzun ina mai tabatar maki bata san yaren zai fito ba, sai dai Autana bata sani ba yare ai shi karfi ne da shi a harshen mai shi, ko yaya ka so dane shi sai wasu kalaman na fitar da kansu “


Ya kuma kamo habar Bilkisu wannan karron da dan turancin dake bakinsa dan matars tsaye take kikam so take ta ji abinda zasu shiga daki ta kama mita , du irin kyautatawar Bilkisu ita jira take ta ga da mugun nufin da ta zo mata gida, wai ita kar a rabar mata miji, bata san ko wancen karron da ya biye mata dan yana da kwakwaran dalilinsa, dalilinsa kuwa ba komai bane sai irin yanda kwata kwata Mama ta ki ta dawo gurbin da yake da iyalinsa, abinda ya ringa yi masa ciwo idan tana nuna ba zai iya rike mata yaronta ba, bayan shi din mutun ne mai matukar son y’aya, dan ko a yanzu abinda ake fada a kauye wai Baban mami bashi da kunya, baya alkunya ta d’an fari watau yayan su Mami bare a kan Mami, shi fa da zai tara y’aya ashirin walahi yana so, kuma kowane zai so abinsa da zuciya daya ya tarbiyantar da kayansa, ita kuwa Mama a lokacin bata hada komai da yaronta, tsoronta kar ta tare da d’anta a gidan namiji mai mace har da y’ayansa a zo ana samun matsala, kai ita a lokacin bama zata iya da matsalolin an yi an yin nan bane, shi yasa ko da ya ringa janyewa ta yi zamanta a inda take dan kuwa ta sakawa ranta cewar zamansu ne ya kare, Aba ya ce” Haka take itama ko? Bata son fadin abinda yake ranta ko? Ko yanzu ta girma ta daina zurfin ciki da kunshe magana a bakinta? Ki fada mata kunshe magana a baki na saka mutun warin baki walahi”


Daria suka saka Mami da Bilkisu hakan ya saka shi shima yin dariar yana girgiza kansa mai dauke da yar furfura yana kallon yaran nasa


Hade fuska ta yi tana binsu da kallo, sam bata san me ya ce ba kuma gashi sunna daria, saima ta dauka kawai gulmarta aka yi ko wani abin ya fadawa Bilkisun, wannan ai munafurci ne ehe! Juyawa ta yi ta koma dakinta tana kara kumburo fuskarta, su kam cikin yannayi na farin ciki suke sam basu kula da halin da take ciki na fushi ba, daga nan sai kawai Abansu ya shiga basu labari irin na kauyensu, da kasuwa, abubuwan al’ajabi da na daria, a ranar dai sai ita matar tasa ta kuma fitowa ta karasa wanke wankenta tana mamakin rashin kunya irin na mijin nata, yanzu baya tsoron wani ya salamo ya tardo shi zaune dare dare a tsakar gida ya saka y’ayansa na cikinsa a gaba yana basu labari sunna hira sunna ta daria? Wannan abin kunyar da me ya yi kama? Da baban Mami da Mami, da Bilkisun dukansu basu da kunya!
Salamarta ta biyar kennan tana karawa, shirun da ya tabata a wajen maimakun ta juya ta koma sai kawai ta dana kanta cikin tankamemen fallon


Bata san lokacin da ta saki baki tana kallon fallon ba


A hankali ta gama juyinta hannunta rike da baban farantin dake shake da abubuwan abinci da na sha da Tati ta sakata kawo masa dan ya karya, domin rabonsu da su ganshi tun shekaran jiya, yakan zo aman sai dai mamansa kadai ke ganninsa dan sai sun kwonta ita tana zaune ba zata iya kwonciya ba sai ta ga shigowarsa


Turus ta yi gabanta ya yanke ya wani irin faduwa sakamakon cin karro da ta yi da shi kwonce saman doguwar kujera


Jikinsa ba riga, sai dogon bakin wando da wani baban hoto a saman cikinsa a ajiye


Motsin da ya ji tun shigkwarta ya saka shi yin tsai dan jin maganar wanda ya shigo masa haka kai tsaye duda ya ji muryar ba ta mamansa bace aman bai motsa ba


Cikin inda inda ta shiga fadin” iiiiiina kwana, ga ga abinci aka ce na kawo maka “


Shirun dai da ya kuma biyowa baya ya sakata dukawa jikinta na dan rawa rawa ta ajiye sannan ta juya tana so fa yi ta bar dakin


“ZO NAN” ya fada cen kasan makoshinsa, sai dai da yake ba hayaniya a dakin kunnayenta sai suka jiyo mata furucinsa


A hankali ta juyo, wannan karron sai da ta ji fitsari zai kufce mata, ba dan komai ba sai dan ganninsa ya mike zaune , 

Irin kirar dake jikinsa ce ta sakata jin matsanancin tsoronsa, wai dama har haka yake ba riga? Lalle tana gannin damatsunnansa a cikin riga tana kiyasta irin mai tatauran damtsen nan ne, aman bata zaci abin ya kai haka ba

Gaba daya ya cike wajen, ya gaje wajen, ya kasance babu wani abu da take gannin ya yi saura a cikin dakin


Kafafuwanta na rawa ta nemi tsugunnawa, lokaci daya kuma ta ainahin gannin hoton dake hannunsa


Lokaci daya tausayin kanta da tsoro suka kara kama zuciyarta, mijin da zata aura ne, wanda ya kawo kudin aurenta million biyu da dari biyar, ya bada kudin sadakinta dari biyar kwonce rungume da hoton wace take ainahin abincin ruhinsa, mijinta ne wanda a yanzun ya kara yi mata sukar mashi a kahon zuciyarta zaune a gabanta a matsayin wanda bai fi saura sati biyu a daura aurensu ba aman kuma magana bata taba hada su da junna ba sai yanzun da ya furta mata kalmarsa ta farko tsakaninsu watau “ZO NAN” , wai anya ya san sunnanta ma kuwa? Anya ya san kamaninta ma kuwa? 


Da yan yatsunsa ya yi mata nuni kan ta dauke abincin hakan ya sakata kai dubanta saman fuskarsa


Irin yanda fuskarsa ke hade  bata san lokacin da ta duka ta dauki farantin ta juya da mugun sauri ta bara masa dakin ba


A hankali ya lumshe idannuwansa yana cije lebensa na kasa,


‘Billy am ni? Ni kika gujewa ko? Bakya tuna ni, kin yi tafiarki kin yi watsi da ni, na tabata an fada maki na yi kira shine kika share ni, Billy ga wayarki dan Allah ko zan ringa samunki, hala fushi kike min? Hala kin tsane ni? Ko har kin manta da labarina a duniya?’ Yake fada a cen kasan zuciyarsa yana kara gyara zamansa


Kamar yanda ya san idan ya masa salama ba amsawa zai yi ba dan sabon kalar wulakancin da ya kankaro kennan sai ka ringa rafka salama muryarka sama sama shi kuwa yana jin ka sai ya amsa kasa kasa ta yanda ba zaka taba jinsa ba kuma ya yafka maka fuska baka da damar yin korafi


Yana shigowa sukai ido hudu


Bai cire takalminsa ba dan so yake ya kaishi wajen da zasu yi ta yada zai saurare shi a cikin hayacinsa


Takim takim takim ya tataka masa cafet ya karasa wajen kujera ya zauna


Shi kuwa tun da ya shigo da takalmin yake bin takun kafafuwan nasa da kallo har sai da ya zauna sannan ya maida dubansa kan fuskarsa cike da mamakin iskanci iri  na Kader


Kader ya dora kafa daya kan daya yana dan karkadawa yana kallonsa ya ce” Hi “


‘Kut’ shine abinda Hisham ke fada a kasan zuciyarsa


Kader ya kara gyara zamansa ya ce” Kai ina rigarka kake zaune haka wani tikeke da kai salon ka tsorata y’ayan mutane, walahi dai Hisham ka rage daga karfe ba yi bane, yanzu dan Allah a haka ba sai ka raba y’ar mutane biyu ba? Kai ko kunya baka ji ta yanda kake hawan nan kamar fulawa? Kai an dai ji kunya walahi, an fadi ba nauyi, to dan ka fini karfi sai aka yi kaka? Dan iskanci a haka ne aka ce wai ni na baka tsaro? Suma sun raina ni, in ba iskanci irin na manyanmu ba ai sai ku kalli yannayin mutun, a kashe sai ya kasheni aman ku ce ni ni kadiri nine zan bashi tsaro? “


Hisham ya gama sauraronsa ya tabe baki, a hankali ya saka hannunsa dan juyar da hoton Bilkisu, domin hoton rigar dake jikinta jar riga ce da bata da girma sosai, rigar iyakacinta da kadan ta dara gwuiwarta hakan ya sa ake dan gannin kasan gwabrinta kadan, rigar nan yana sonta sosai, dan ba zai manta shagon da ya siyeta ba, haka kawai ta birge shi ranar da ya saka ta sakata kuwa hotunan da ya mata sun fi a kirga


Sarai Kader ya ga abinda yake rufewar aman sai ya share ya ciro ambulope din da ya shigo da ita ya mika masa yana kara tsatsare shi da ido, watau du abinda ya san baya so ne yake yi masa dan kawai su raba hali


Bai bude ba sai cewa ya yi” Menene a ciki Kader? “


Kader ya kara kallonsa da dan mamakinsa, sai kuma ya dan tabe bakinsa ya buda ya ciro katin gayatar da ya je aka buga, bugawa irin ta kwaliya mai shegen kyau ya miko masa ya gyara zama ya ce”

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like