DUK NISAN JIFA 6

Advertisement

                         6


Cike da mamaki SG ya k’ara k’ureta da kallo, Zeinab dai ta kasance mace mai biya’ya sosai da sosai a wajen aikinta, ita fa a dunia wannan nema nata shine rayuwarta, a kan maganar aiki du abinda aka ce ta yi zata iya aikatawa a sauk’ak’e ba tare da tunanin komai ba,

A kan aikinta tana shirye da duk’ama koma waye.


Sannan a wajen aikin ta kasance irin mutanen nan da ake kira kaska rab’u mai jini, idan ba wani abin zaka anfaneta da shi ba sam Zeinab bata yi maka fadanci.

A zaman nan da aka yi baki d’aya ita ce mai k’aramin muk’ami a cikinsu, hakan ya sa kanta sade cike da biyaya take sauraronsu sai a yanzun da ta hango maganar nan, maganar da ta bata mamaki, wace ta zo mata a yanzu yanzun, kar ku yi mamakin cewar Zeinab bata san irin matsayin da yaronta na cikinta ya taka a dunia ba, tabbas ya taka matsayin da har yanzun bata gama fahimta ba…sai dai bata yi k’asa da gwiwa ba jin sunan da cikaken kwatancen yanayin ya sakata dira da furta kalmar nan wato *D’ANA NE* ba ko kunya da tsoro!.


         *TUSHEN LABARIN*

Advertisements


Haifafun wani d’an k’auye ne mai sunna Kanya dake jihar damagaram, filani ne su su biyu rak yan mata da iyayensu suka haifa. Basu yi ta’lar nono ba, sai dai sukan yi yar sana’arsu ta yan mata su siyar.


Asma’u sai Zeinab su kad’ai Allah ya baiwa iyayensu, Asma’u takan yi yar alewa ta kai bakin makarantar islamiya ta ajiye ta shige makaranta, ana tashi ta dawo wajen tsohuwa ta amshi alewarta ta siyar da abinta sannan ta dawo gida.


Zeinab kam yarinya ce mai zafin nema, takan zaga cikin k’auyen da sana’ar maka da dan wakenta da dakaken yaji tana siyarwa lungu lungu, sam bata zuwa makarantar islamiya sai ta boko kad’ai da take zuwa ta zauna ita ma dan ta ji cewar shugaban k’asar da ake haskowa a TV d’in gidan yar mai gari karatun boko ya yi ya zama wani abu.


Mahaifinsu yana iya k’oknarinsa dan fita hakk’insu , basu da yunwa bare k’ishin ruwa, daidai gwargwado sutura ta yayan talaka mai zuciya suna da shi, a hakan ASMA’U take godewa Allah tana rayuwarta a sauk’ak’e domin kuwa takan kalli wa’inda ta fi ne a koda yaushe ta k’ara godewa sarkin sarauta ba wai wa’inda suka fita ba.


Ita kuwa Zeinab a kullum idan ta tashi burinta ta kamo wata da ta fita ko ta halin yaya, hakan ya sa tana girma tana k’ara sanin yan k’auyukan dake mak’ota da nasu, harma ta san cewa baban garin Damagaram ya fi kusanci da k’auyansu fiye da kowani k’auye, tafiar a k’afama zaka iya yi ka shiga ka dawo lafia domin ba wani hatsari bakin baban titi ne mai d’auke da sojawa da manyan kostan.


Sannu a hankali take yin k’awaye, kala daban daban masu halaya daban daban, dan ta ga burinku d’aya, abin zai d’ore ne, idan ta ga kai burinka ba wani bane sai ta yakice abinta.

Advertisements


Tun Asma’u na da shekaru goma sha biyar  ta samu mai son ta, malaminsu ne na islamiya ya fito da zuciya d’aya yana son ta.


Mahaifinta bai tsaya ja ko neman fiye da haka ba ya amince ya bada damar ya fito domin a lokacin tuni ta fara jini.


Ba’a wani dauki dogon lokaci ba aka yi auren Asma’u, aka kaita gidan sirikanta wanda mijinta ya tada mata d’aki ya rufe mata aka yi mata jeranta a sauk’ak’e 


Cikin aminci suka shinfid’a rayuwar aurensu, iyayen mijinta sun kasance masu kawar da kai da cire ido a harkar zamantakewarsu, ko yar rigima suka yi irin na zaman yau da gobe sukan  tsawatar ne ba tare da sun nuna wariyar shi dansu bane ko wani lamarin, hakan ya sa take jin dad’in gidan aurenta fiye da tunanin mutun, ta yi k’iba ta k’ara hasken fatarta dan kuwa mijinta mai zuciya ne, idan ya fita nema idan aka dace baya tab’a shigowa hannu goma, yakan zo da leda ne, ita kuwa takan fitar ta raba ta kaiwa iyayensa a tsaftatacen kwano sannan ta dawo ta kula da mijinta. Yakan yi mata d’inki ne daga ya samu dama ba sai sallah sallah ko wani gagarumin biki ba, hakan ya sa take da atampopi masu dan kud’i kala daban daban da hijabai masu yawa a cikin akwatinta.


Iyayenta na k’ok’arinsu a kansu, basa gajiyawa haka kuma sukan yi masu nasiha, sukan yiwa yarsu nasiha kan a duniya idan ta saka hak’uri, ta sada kanta, ta yiwa kowa biyaya ita zata tashi da ribar zamantakewar rayuwa.


A haka sukai ta rayuwa da wannan bawan Allah sai dai ko batan wata bata taba yi ba, sam ba haihuwa sama ko kasa ba alamunta, tun ba’a damu ba har aka fara dan neme nemen haihuwar ta sanadiyar wannan suka shirya dan shiga baban birnin Damagaram dan su ga likita.


A wannan lokacin Zeinab ta kai shekaru goma sha takwas a duniya, gandamemiyar budurwa ce a k’auye dan kuwa sa’anninta du an masu aure d’aid’aiku ne basu samu auren ba irinta wa’inda fitowa ke gagararsu domin kuwa yaran k’auyen kad’ai sun ishe su, ita kuwa ba wannan ne a gabanta ba, hasalima karatunta na boko gaba ta ci da shi sannan takan kawo sana’arta bakin titi ta siyar ta koma gari, ba wai masoya ne ta rasa ba a cikin Kanya, ko d’aya, ta fi k’arfinsu ne ta fad’a ta k’ara.


Ita ce yar rakiyar, sun je Birni sun je sun sha fama da k’yar su ga likita wato docter Zalika.


Ta basu dukan abubuwan yi sun yi iya yin su sai dai a dukan bincikenta mijin Asma’un ne baya haihuwa dan haka ta shaida masu abinda ta gani a takardunsu.


Sun shiga tashin hankali mai tsanani iya su biyun, inda Zeinab ta ringa bin manyan motocin dake shige da fice da kallo tana k’ara gyara tsayuwarta da yar jakarta jajajir d’auke da madubinta a ciki da yan cenjinta.


Hannayen matarsa ya rik’e yana kallonta yana jin wani iri a k’asan zuciyarsa, a hankali ya furta” Asma’u, nin e bana haihuwa, ba zan iya tauye ki ba asma’una.”


Gannin yana neman wuce gona da iri da sauri ta tare shi da cewar “Hakan na nufin ba zamu samu haihuwa a duniya ba mijina, dan Allah wannan maganar ta tsaya iya mu, bana so ko da wasa a ji a gida dan bana son yan zigi ko yan shiga sharo ba shanu su shiga lamarin iyalina.”


Kallonta kawai yake, aman bai wani gamsu ba, a haka suka dawo gida, sai dai suna zuwa suka tarar da tashin hankali.


A wannan yar fitar tasu mahaifinsu ya je gyaran bakin rijiyar gidan mai gari rijiyar ta rufta da shi ya fada ta kansa hakan ya sa ko da aka ciro shi babu, rai ya yi halinsa.


Sosai sukai kukan rashin sa, sosai suka bi shi da adu’a, a nan mai gari ya yi iya yinsa, ya basu gona da kudin noma, ya basu taimako da dama ciki kuwa harda kara biyan karatun Zeinab.


Mahaifiyarsu a dole ta fito daga daka ta ringa kula da lamarin gonar nan, domin a yanzun wannan gona a cikinta ne zasu iya ci su sha, su tifata ba tare da sun yi bara ba.


A haka Zeinab ta shiga karatunta hankali kwonce, zata je makarantarta ta dawo sanan zata yi abin sana’arta ta kai bakin titi ba dan komai ba sai irin samarin da take gani masu da shi a hannu…a haka har ta samu wani baban soja ya fito neman aurenta.


An kai ruwa an kai mari a kan maganar auren nan, dan kuwa mutun biyu kawai suka zo neman auren da mak’udan kud’i, mai gari ya so k’warai aiwatar da bincike sai dai kash, Zeinab bata bashi damar hakan ba ta nuna masa a yi kawai.


Mahaifiyarta bata yi kuka ba sai da ta ga d’aukan amarya mijin kawai ya zo a wata galeliyar mota ya d’auketa suka tafi, a lokacin ta yi kuka kamar ranta zai fita , sai dai a dole ta yi hak’uri ta ci gaba da rayuwarta da d’ayar dake gabanta

Mafarin rabuwarsu da Zeinab.


Zeinab ta yi rayuwa da mijinta ne wata irin rayuwa, ya kasance mai sakar mata kud’i, ya kaita waje ya kilaceta ya sakata a makaranta aman bata san kowa nasa ba. A sati sau biyu kawai yake ziyartarta, wannan ba shine damuwarta ba domin kuwa ko da TV din kadai da ya bata ya barta ya gama yi mata komai na rayuwa, gashi har mai aiki ce da ita yar yarinya dake yi mata aikace aikacen cikin gida, ga kudi ga yawo a mota ga karatu, sai kawai ta shafe maganar kauye a cikin ranta take fuskantar birni da koyon rayuwar cikin birni.


Kasancewar bata takurawa MUHAMMAD KARIBULLAH kan dole sai ta san ahalinsa sai ya kasance mai kyautata mata fiye da tunanin mutun, ya mallaka mata gida har biyu domin daga baya ya d’auketa daga k’aramin gidan nan ya mayar da ita wanda ya fi shi, sannan ya mallaka mata takardunsu.


Ba ita ta je Kanya ba sai bayan shekaru hudu cir ta taka kauyen shima dan mahaifiyarta.


Ta tarar da inna cikin rashin lafia, Asma’u na jinyarta, ta raina gidansu domin ko zama kasa yi ta yi dan kuwa gidan du ya duke a haka ta sa a fitar mata da inna , sai dai sam inna ta ki hakan ta nuna a barta a gurbin da mijinta ya barta ba zata iya fita ba.


Yanayin Inna ya saka dole ta je gidan mai gari ta kwana domin ba zata iya kwanan gidansu ba gaskiya.


A haka mijinta ya saka aka kawo likita ya duba Inna, aka ringa bata magani anna kara kulawa da lafiarta, sai dai cikinta ne ke kumbura haka kawai.


K’arshe dai wannan ciwon sai da ya kai Inna k’abari. Asma’u ta yi kukan da bata tab’a yi ba a rayuwarta, ta rik’e hannun k’anwarta da hannu bibiyu tana kuka ta ce” Zeinab yanzun idan kika tafi sai yaushe? Bani da kowa sai ke sai mijina Zeinab, kar ki tafi ki barni na rok’e ki”


Ita kanta wayar gari ba uwa ba uba ya saka zuciyarta tsintsinkewa, sai dai bata tunanin a yanzu wani abu zai saka ta dawo k’auyen nan da zama, hakan ya sa ta rarrashi Asma’u ta hanyar fadin” Asma’u inada wani ne bayan ke? Da mijinki zai amince da kun zo birni na baku gidana kun zauna, Asma’u aure ya kai ni birni, dole na koma, aman na yi maki alk’awarin wannan karon ba zan ringa jimawa har haka ban zo inda kike ba, ki siyar da gidan nan, ki gyara rayuwarki sannan ki saka mijinki ya ci gaba da nome gonar cen hakan zai sa ku ji sanyin rayuwa.”


K’arshe ta bata kud’ad’e da suturu ta tafiarta ta barta da kewa sosai dan kuwa Asma’u kam akwai son mutane da son d’an uwa dan bata da yanda zata yi ne.Haka rayuwa ta ci gaba da tafia, a shekararsu ta bakwai da aure Zeinab ta samu ciki.


Wannan ciki ya ringa kawo yan cenje cenje a zamantakewarta da mijinta, dan kuwa sai wani lamari na kusanci da bayyanar yan sirrika suka ringa bayyana a tsakaninsu.


Ya fara fad’a mata sirrikansa na irin dukiyar da ya mallaka, asalin shi d’in wanene, irin matsayin da ya taka a duniya da dai sauransu.


A ranar da ta haihu ta samu d’a namiji a ranar ya rungume yaron cike da damuwa da wani irin farin ciki ya kalleta yace “Kamar yanda na fad’a maki ni sunana Muhammad K’aribullah Zeinab, ni balarabe ne gaba da baya, kasancewar haka ya saka a danginmu muke da wata banzar al’adar auren jinsinmu, bama aure sai balarabiya yar uwarmu, ina da aure kusan shekaru goma sha takwas kennan a nan cikin damagaram matata da mahaifiyata suke, a lokacin da na ganki na jewa mahaifiyata da maganarki, sai dai tashin farko ta nuna karma na fara kar na jaza mata abin fad’e a cikin dangi, matata bata tab’a haihuwa ba, kuma na k’ara auren wata balarabar ya gagara dan kuwa na rasa me ya sa mahaifiyata sam ta k’i na k’ara auren wai yaro ne ni, kin ga na aureki ne a b’oye Zeinab, gashi a yau ni ne rik’e da gudan jinina, Allah ya raya min *HISHAM*.”


Bata wani mugun damu ba, haka kuma bata yi wani uban taro ba, iya k’awayenta yan gayu da ta yi ta gayyata suka rak’ashe. Sai bayan wata biyu ta je ta kaiwa Asma’u Hisham, a wannan rana ta ga wani irin lamari wai shi son y’aya, dan kuwa Asma’u har fad’i take zata bita su dawo birni ta raini Hisham, dan Allah Hisham zai kirata da mama?.


Irin abubuwan nan suka bata daria, ita kanta da zata samu ta biyotan ta zo ta k’arata da wahalar jariri da ta so hakan, dan kuwa a gaskiya bata son takura duk da yan rainonsa hakan baya wani d’ad’ata da k’asa.


Hisham na da wata bakwai tafia ta taso wa mahaifinsa zuwa daji


Kafin ya tafi ya yiwa mahaifiyar Hisham alk’awarin yana dawowa zai d’auketa ya kaiwa mahaifiyarsa da abinda Allah ya azurtasu da shi.


Da wannan suka rabu da mak’udan kud’i da wasu gidajen biyu da motar da ya bar mata ko da buk’atar wani abin zai taso baya nan, sai dai bai tantance mata su waye iyayen nasa ba, a ina suke da sauransu, ko a larmรฉ ba’a san da zamanta ba bale yaronta a haka ya tafi wannan dajin da bai dawo ba, wanna dajin da bata ga gawarsa ba sai a TV take ganin suturarsa da aka gabatar. Wato yak’i ya ritsa da mijinta, wanda bata ga iyayensa ba sai a TV aka hasko fuskar mahaifinsa ta mahaifiyarsa da wata a kusanta d’auke da nik’af.


Bata tab’a dana sanin auren nan nata ba sai a wannan rana, gata zaune a d’aki ita daya ba mai rarrashi ba wanda zai yarda cewar mijinta ne ya rasu sai wahalar rayuwa ta ci kuka har kamar za ta haukace.


A hankali abubuwa suka ringa rincab’e mata, ta rasa madafa, ta rasa shin idan ta fita dan neman dangin mijinta su wa zata ce? Iya sunansa ne kawai ta sani, idan ta je TV ana iya ganin dan ta samu kud’i ne zata yi masa sharri, idan ta je ma’aikatarsa zata iya jazawa kanta matsaloli ne da ba zata iya fitar da kanta ba.


Dan dole ta zauna a d’aki karatunta na neman lalacewa, komai nata na neman tsayawa cak a irin wannan lokacin da ta saba da kud’i da rayuwar kud’i.


Kud’ad’en hannunta duk ta kashe sai mota sai gidaje, gata ko acc bata da shi dan kuwa a hannu yake zuba mata ita kuwa ta kashe.


A hankali ta fara neman zaucewa da jigilar yaron da aka sabawa shan madara, madarar gwongwani ana bud’ewa bata rufe kwana biyu

Yaro jajajir da shi b’ulb’ul da shi sai k’ara k’iba yake yana yawonsa ko ina.


A ranar da ta wayi gari ba isashen cenji a jakarta sai kawai ta had’a dukkan abin had’awarsa ta shiga motarta dan kuwa ta sallami yan aikinta ta nufi k’auye.


Ta kuma zuwa ta zubawa yayarta dukan damuwarta sun yi kuka kamar me, sannan ta rik’e hannayenta tace “Aunty Asma’u ga Hisham, ba zan iya rayuwar karatu ba mai tallafa min ba ga kuma yaro, aunty Asma’u ki saka Hisham a makaranta, ki kula da lamarinsa, zan siyar da sauran gidajen da ubansa ya bari na je garin niamey na k’ara karatu na samu aiki, sai ku shiga d’ayan gidan ku zauna, aunty asma’u yaron nan naki ne dunia da k’iyama, Hisham ba *D’ANA BANE*, zai kira ki da Mama, ko da wasa kar ya kira ni da Mama, ga wayar nan zan bar maku ita ku yi anfani da ita, duk lokacin da na samu dama zan ringa kiranku, haka kuma sai dai na tabbata zaku wahala domin a yanzun bani da kud’in da zan ringa turo maku, idan na samu wani auren mai tafe da cenji zaku ji ni, idan zan dogara da kaina ne sai dai na k’ara baku hak’uri.”


Sosai Asma’u ta so ta rik’e yar uwarta, ba irin abin da bata nuna mata ba kan ta zauna a gari ta gama idarta, ta kilace kanta ta samu mijinta, ta yi aurenta Allah shi keda komai.


Sai dai kash, hakan ya gagara, dan k’arara ta nuna mata wannan rayuwar ba tata bace, k’arshe dai tare suka juya ta nuna mata gida ta bata takardunsa , basu bar garin ba sai da suka k’ulla alak’a da mak’otan gidan ta bar masu amanar saka kunne a motsin gidan domin akwai kayayaki na anfani , kayan abincin ciki kawai ta fitar ta bayar sadaka, sun amshi number juna da matar gidan sannan suka yiwa juna sallama.


Asma’u ta yi kuka tana kallon yar uwarta ta tada mota ta tafiarta ta barta tsaye da yaron da bai san kowa ba sai mamansa aman rana tsaka ta cire shi a nono , ta cire shi a jikinta ta tafi nema kamar wani namiji ko waiwaye babu.


Abinka da k’auye sosai aka so sakota gaba dan wannan yaro, sarakuwarta ta so ta d’auki ziga cewar yaron shege ne aka kawo aka yarda masu, sosai ta fara nuna halayan da ba nata ba cewar dan d’anta yana zaune da ita a haka juya ba haihuwa shine za’a jajab’o masa wani jan d’a kamar d’an mai jan kunne a kawo masa ya ciyar. Sai da ya ga abin ba na k’arewa bane ya fayyace masu cewa shine baya haihuwar ba ita ba.


Tun daga lokacin sai ta samu sauk’i a wajen uwar mijinta, aman mutan gari sun kasa yarda cewaHisham ba shege bane, an d’ora cewa shege ne uwarsa ta kawo ta yardawa yayarta ta koma yawon ta zubar d’inta.


Haka tafia ta ci gaba da mik’a, a haka ajalin mai gidan Asma’u ya riske shi a hanyarsa ta dawowa daga maradi. Har sai da Asma’u ta yi jinyar wannan rashi, ta dawo zurum da ita, abu d’aya ke sakata sakin ajiyar zuciya idan Hisham ya rik’e hannunta ya kireta da ” *MAMANA.”*


               Alhamdulilah

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

DUK NISAN JIFA 54

Advertisement  ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ           *DUK NISAN JIFA*            _(K’asa zai dawo)_…

DUK NISAN JIFA 47

Advertisement   ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ           *DUK NISAN JIFA*            _(K’asa zai…