GOBE NA 20

Advertisement

 GOBE NA…*

By Khadeeja Candy 

2️⃣0️⃣

DEDICATED THIS PAGE TO Mai Dambu, Allah kara miki lafiya Gwanata❤ son so Fisabilillahi💞😍

                  ***        ***      ***

Kamin mu isa gidan har wani jiri nake jin yana dibana, zuciyata kam kamar ta fashe ga wani uban zafi da kirjina ke yi, kaina sai sarawa yake. 

   Ko parking din kirki be yi ba na bude motar na fita na shiga cikin gidan cikin tashin hankali kamar yadda su ma na tararda su cikin tashin hankali, gaba daya ban tarardar yan mata gidan mu ba da

samarin biyun duk sun fita neman Namra Baba na tsakar gida rike da sandar damuwa kara a fuskarsa. A bakin balcony na zauna na dafe kaina. Inna na min bayanin yadda abun ya faru da guraren da aka je nemanta bata can. Mahaifinta ne ya fado min a rai.

“Ko Aminu ya dauke ta ba a sani ba?”

Na fada ina kallon Mama, a yayinda Abdulhamid ya shigo yana gaisawa da su. 

Advertisements

“Mi zai saka Aminu ya dauke ta, mutumen da tun da ya bata baya be sake dawo ko tambayar lafiyarsu ba”

Cewar Inna sai Mama ta karba mata. 

“Nima dai shi na gani, kuma a ina ma zai ganta?”

“Ko tana gidan Abdallah?”

Na fada ciki ina hawaye. 

“A a bata can tun dazun da shi ake ta nemanta, shi ma yace kar a fada miki saboda kar hankalinki ya tashi, yanzu yanzu ma suka fita da Samira har…. ”

Baba ne ya tari numfashin Inna da ke maganar yana fadin. 

“Ku ba Allah cigiya In-Sha-Allah za a ganta, idan ba dan sake irin na Hafiza ba taya zaka fita da yaro ka ce ya same ka titi bayan yaron be san gurin ba”

Komawa nai na zauna a gurin na fara rare musu kuka, idan ba kukan ba ban san abunda zan yi a yanzu ba.

“Bari naje na duba makarantarsu…”

Cewar Abdulhamid yana kokarin juyawa sai Inna tai karaf tace. 

“Ai har can Abdallah ya tafi….”

Advertisements

Baba ya sake saurin tarar numfashinta. 

“A a be je can ba, islamiyarsu dai yaje, zaka iya zuwa can ka duba”

Sai da Abdulhamid ya fice sannan Baba ya hau yi ma Inna fada wai ta cika tsoma baki a maganar da babu ruwanta. Ni kam sam ban ga illar maganarta ba kamar yadda ita ma kanta da Mama ba su ga haka ba, wata kila kuma akwai abunda Baba ya hango. 

“Mama zan je gidansu Aminu na duba ko tana can”

“To da Abdulhamid din be wuce ba ai sai ya karaki”

“A a shi yaje can din ni zan duba gidansu Aminu”

Na bawa Mama amsar ina mikewa tsaye.

“Mi zai kaita can ma”

“Nema ne ai Mama”

Ban tsaya na jira su kara kashe min jiki ba na zari jakata na fito cikin gidan kamar wata mahaukaciya. Kamin mai napep din na kai ni gidan su iyayen Aminu har na matsu abunka da wanda je cikin tashin hankali. A bakin gate ya tsaya ni kuma na shiga cikin gidan da sallama. Kana gani na kasan hankalina ba a kwance yake, ba Hajiyar Aminu ba ko kanensa sun yi mamakin ganina a cikin gidan, ban musu magana ba kamar yadda suma suka saki ido suna kallona kamar wata bakuwarsu. Har cikin falon na shiga na gaishe ta ita ta amsa min da dan mamaki sannan na tambaya ko Namra tana nan. 

“Namra da kuka kekashe kasa ke da yan’uwanki kuka ce ba za ku bayar ba, bayan kun gama ikirarin an bata ta mi za mu dauko ta tai mana? Ai mun yafe miki ita ki dafa ki ci ko ki saida babu abunda za mu da ita”

Mikewa nai tsaye cikin bacin rai na ce. 

“Ke kika fi kowa abun yi da ita saboda jininki ce, kuma tambaya kawai na zo saboda idan tana nan na tafi da ita saboda kula da tarbiyar”

Mikewa tai tsaye ta nuna ni da yatsa. 

“Ke Halima ki shiga hankalinki karki ce za ki so har cikin gidan nan ki min rashin kunya, ki bar ganin an kyale ki Wallahi kika min iskanci sai an karbe yaran nan daga hannunki”

“Da kuwa kin bude abunda yake rufe, da kin tona asirin danki dan sai duniya ta ji abunda ya aikatawa yar dan’uwansa”

Na bata amsa a fusace sannan na juya na fice na barta tana ta surutanta, inda na bar mai Napep din a nan na same shi. 

“Kai ni igala quarters”

Na fada bayan an shiga Napep din, yana tafiya ina nuna masa inda za abi har ya sauke ni a kofar gidan Aminu, bayan Hajiya ban san ko tana gidan ba neman be ba a cire tsammani wata kila ma ya ganta a wani gurin ko kuma ita ta fadi can a kai ta ba tare da mun sani ba. 

  Mai gadin yai na’am da ganina yana ta washe min hakora da tambayar yaushe gamo.

“Dan Allah Malam Garba tambaya nake ko kaga Namra a gidan nan?”

“Namra dai ta wajenki?”

“Ita, ta bata tun jiya”

“Subhanallahi Wallahi ban ganta ba, amman ki tambayi Alhaji ai yana ciki, Hajiyar ma tana ciki”

Fadar Hajiya ma tana nan ciki ya tabbatar da cewar Aminu yayi sabon aure kenan. 

“Aa bana bukata na gode”

“Allah ya tsananta rabo”

“Amin”

Na amsa ina hawaye, ina shiga cikin napep din kuka ya kwace min.

“Hajiya Lafiya?”

“Yata ta bata tun jiya kuma ba a ganta ba… ”

“Subhanallahi a ina?”

“A gurin biki taje ita da kanwata”

“Aiko na ji ana cigiyar wata yarinya a fm dazun, amman ban sani ba ko ita ce”

Da sauri na kalleshi. 

“Yaushe? A ina? Ya sunanta?”

“Wallahi ban rike sunanta ba amman dai dazun ina sauraren fm a napep na ji ana cigiyarta”

Ya karasa yana kunna fm din. 

“Dan Allah ka taimaka ka kai ni can mu binka kasan inda fm din take?”

“Eh na sani Allah yasa ita ce”

Kamar nai tsuntsuwa na tashi na isa fm din haka naji, abun ka da guri mai nisa daga igala quarters zuwa Damba sai tafiyar ta zame min kamar ta wani gari, muna isa na fita na shiga ciki na fara tambayar mutane hankalina a tashe, sai wani ya shiga ciki ya duba takardun cigiyar ya rubuto mana number wayar da aka bada sannan ya fada min sunanta. Ina jin ya ambaci Namra wani dadi marar misaltuwa ya lullube ni.

“Sai kinje Samaru ki tambaya gidan Alhaji Muhamad Gwarzo”

“Na gode”

Tun kan ya gama magana na juya da sauri na fito na shiga napep din na fada masa unguwar da zai kai ni, a hanyar mu ta tafiya kiran Aminu ya shigo wayata, na gane ne numbersa ne saboda na haddace ba dan number tana da suna ba. Har na yi kamar ba zan dauka ba sai kuma wata zuciyar ta hana ni na danna picking na kara a kunne na. 

“An ga Namra?”

“Ashe kana iya damuwa da ganinta ai na dauka ka manta da kana da yaya”

“Halima bari kiji na fada miki wallahi duk yata ta bata ko wani abun ya sameta sai na wulakanta ki, sai na sa kin yi nadamar haihuwarki da akai a duniyar nan Wallahi Wallahi dan haka ki nemo min yata tun wuri”

Be jira abunda zance ba ya katse kiran, wani uban haushi ne ya cika ni har na ji ina ma dai ace ban dauki wayar ba. 

  Da tambaya muka gane gidan, domin number da aka bamu mun yi ta kira ba a dauka ba, daga baya ma sai aka kashe wayar. Wani irin katon gidane mai katon gate irin na manyan mutanen nan da suka ci arziki har sukai kashinsa, kai idam ma baka sani ba za kai zaton gidan fillar kai ne saboda girmansa da tsaruwarsa, ko ina na gidan an kawatashi da fulawoyi da kuma irin dagayen itacen nan masu haska gida. 

“Sannu Malam dan Allah yata na ke nema kuma ance tana nan”

Na fadawa mai gadin bayan nai kwankwasa kofar gidan ya bude min na shiga ciki. 

“Ina aka ce miki?”

“Ce min akai gidan Alhaji Muhammad Gwarzo”

“Eh nan ne shiga ciki”

Kai tsaye na doshi cikin gidan, a maimakon na shiga part din farko sai na nufi dayan part din da shi nake hango kofarsa tsabanin babban part din da na kasa ganin kofar shigarsa, wata kila kuma ta karamin ake shiga. 

  Kofar falon na hango a bude tun ka na karasa, na yi iya yadda shari’a tace wato yin sallama da na ji ba amsa min ba na kunna kai cikin katon falon mai cike da sanyin ac da daddadan kamshi sai dai ban fasa sallamar duk kuwa da ban ga kowa ba.

Ina kokarin juyawa na fita wani mutun ya fito daga wani bangare na falon yana rike da plate da ke dauke da soyayyen kwai sai kofin tea. Wani shegen short ne a jikinsa kirjinsa kuma a tsirara dan babu riga a jikinsa. Da gila ya tambayi abunda ya kawo ni falon.

“Yata ta bata aka ce tana nan gidan Alhaji Muhammad Gwarzo… ”

Wani kallo na watsa min daga sama zuwa kasa sannan ya zauna ya aje plate din hannunsa a saman center table din dake kusa da shi yana cigaba da kallo, zuwa can kuma ya dauke kai ba tare da ya ce da ni komai ba. 

“Yata nake nema na fada maka”

Banza yai min kamar ba zai amsani ba, sannan ya ce. 

“Idan kin ganta ai sai ki dauka”

“Idan bata nan ka fada min bata nan ba sai ka wulakanta ni ba domin ba bara na zo yi ba”

Na fada a fusace, ina tuna inda na taba ganinsa. Uffan be ce min ba ya dauki tea gabansa yana sha tare da maida hankalinsa gurin katuwar plasma dake manne a wallpaper falon. Juyowa nai a hasale na fito daga falon marasa na murdawa, kamin na isa dayan part din sai da na rike cikina kusan sau uku. Ina isa na zauna a gurin na runtse ido ina sauraren radadin da take min. Daker na iya tsada hankalina har na lura da kofar falon, cike da karfin hali na unkura na mike tsaye na isa bakin kofar ina kokarin kai hannu na nai knocked aka bude kofar daga can ciki. Fuskar Mutumen dazun din nan ne da ke wacan part din da na baro, sai dai wannan karon akwai jallabiya a jikinsa, mamaki ya kama ni shi din ko kuwa su ma twins ne kamar Abdallah da Abdulhamid? Ko kuma wata hanyar ya biyo ta can ciki ya isa wannan part din? Sai da nai kamar ba zan masa magana ba, sai kuma wata zuciyar ta hana ni abunka da nama. 

“Dan Allah yata nake nema aka ce min tana nan”

Be ce min komai ba ya fito daga falon ya sauko stairs din ya nufi gurin wata mota dake fake kusa da inda nake zaune.

“Tana nan ciki”

Ya fada bayan ya bude motar. Unkurawa nai na tashi na nufi kofar falon na shiga ina takawa a hankali saboda abu nake jin kamar zai zubo min. Na yi mamakin karamci da sakin fuskar da na tarar a fuskar Hajiyar gidan ina yin sallama ta amsa min tana min sannu da zuwa kamar ta san ni, Namra na ganina ta taso da sauri ta nufo inda nake tana dariya. 

“Momy”

Rumgumeta nai na lumshe ido. 

AHMAD POV. 

Da gangan yake son ya shiga motarsa ya yi tafiyarsa saboda kar ma mahaifiyar yarinyar ta ga fuskar yi masa godiya ko yi masa wata maganar. Ji yake kamar ya fada mata bakar magana son ransa aka my wufintar da yar da tai amman ba shi da damar wannan tun da shi ba uban yar ba ne kuma ba shi da alaka da ita. Ko ba komai dai ya san hankalinta ya tashi tun da ga shi har tana zubar jini. 

  Tun kamin ya karasa gate aka bude masa gate din, ganin wani tsaye da mota a bakin gate din gidan yasa ya tsaya ya sauke gilashin motar yana kallon Abdulhamid da na shi gilashin yake sauke. 

“Malam lafiya?”

“Wata yarinya muke nema aka ce tana nan gidan mun kira number da aka ba da a sanarwa muka jita a kashe shiyasa na zo”

“Kai ne mahaifinta?”

“No ni ne dai nake auren mahaifiyarta”

Abdulhamid ya amsa kai tsaye, sai Ahmad ya kalleshi da kyau sannan ya dauke kai. 

“To ka tsaya nan za a fito maka da matarka”

Ya karasa yana kallon wayarsa. Number sis dinsa ya lalubo ya aika mata kira, in few seconds tai picking.

“Sis ki fadawa matarta mijinta yana jiranta a waje”

“Okay Ammn bro bleeding ta ke, ya dan jira ta shiga bandaki”

“Ki fada mata na ce”

Yana fadar haka ya kashe wayar ya karawa motarsa wuta ya hau titi, Abdulhamid na zaune cikin wata mai kama da Ahmad din ta budo karamar kofar gate din ta leko shi daga can cikin motar da yake zaune tace. 

“Kai ne mijinta?”

Abdulhamid ya gyada mata kai. 

“To ka dan jira ta fito tana bleeding amman ta dan shiga toilet ne”

“Ta ji ciwo ne?”

“No i think ta samu miscarriage ne… ”

Ta fada tana dan zare. 

“Miscarriage…?”

Ya maimaita. 

“Yes ban dai tabbatar ba, amman kasan idan am samu tashin hankali yana iya causing wannan matsalar, amman ba lallai ne ya zube duka ba, amman dai shawara ka kaita asibiti yanzu dan tabbatarwa”

Tun da ta fara yake kallon yadda take ta zuba masa zance har ta gama, daman daga ganinta irin yan matan nan ne masu surutun fadi baa tambaye ka ba.

“Okay”

Ya amsa mata zuciyarsa cike da mamaki, kai ta gyada masa sannan ta juya ta koma ciki, kamin ta isa falon wayar da ke hannunta tai ringing alamar kira. Soul mate ne rubuce a saman screen din, murmushi ne ya bayyana a fuskarta jikinta har rawa yake ta kara wayar a kunnenta sannan ta nufi wani bangare na gida cike da shauki tana amsa wayar. 

HALIMATU POV. 

Ban lura da jini dake zubo min ba har sai da na zauna a saman manyan cushion din dake falo, shi ma saboda Hajiyar ta yi magana ne. 

“Subhanallahi kin ji ciwo ne?”

A lokacin da na duba sai na lura da jinin ya bata duk sawun kafata yake jini ya bata gurin. A iya sanina dai ban ji ciwo ba ban fadi ba balle na ce na ji ciwo ne, jini ba ta kafa yake min zuba ba ta cikina ne duk da kuwa da bana da tabbacin hakan domin ban ji zubowar komai ba sai jin alamar zubowar da na ji dazun ashe har ya zubo ban sani ba. 

“A a ban ji ciwo ba”

Na amsa mata gabana na faduwa wani sabon tashin hankali na kusantata. 

“Allah ya tsare idan ba miscarriage kika samu ba”

Hajiyar na rufe baki wata budurwar da ke zaune a dinning ta ta amsa da. 

“Shi ne ma, kin san tashin hankali yana saka haka ko da ciki ya yi kwari ba re kuma ace yana sabo kuma…. ”

Bata karasa Hajiyar ta daka mata tsawa. 

“Haba idan kin fara zubawa ba ki san ki tsaya ba? Shiyasa kike samu matsala da Yayanki kina da yawan magana”

Da hannu tai zip up din bakinta.

“Taso muje ciki ki gyara jikinki”

Naga karamci sosai a gurin matar nan babu kyama ta shiga da ni har cikin dakinta ta kai ni bandakin ta bani duk wani abu da nake bukata tun daga pad da pant da doguwar rigar da zan canja. Kamar kazar da kwai ya fashewa haka na fito daga bandaki jikina babu kwari na dawo falon a maimakon na zauna sai na yi tsaye kamar an dasa ni wasu sabbin hawayen na cika min ido. 

“Baiwar Allah ki zauna mana yau masu aikin na mu basa nan balle akwai miki ruwa”

“Aa na gode sosai Hajiya, gida zan tafi yan uwana suna can suna ta neman Namra, na gode sosai da karamci na ji dadi da yata ta fada hannun mace mai karamci da son mutane kamar ki Allah ya saka da alheri”

“Babu komai Gwarzo za ki m godiya ai, muna zaune ya zo da ita sai fada yake wai kun wofintar da ita, dan Allah a rika kula”

“In-Sha-Allah”

Bayan na amsa mata, ta dauki wayarta dake gefen cushion din ta kira number da na ke zaton ta wacan mutumen ce. 

“Za ta tafi da yarinyar nan”

Shine abunda na ji ta fada ban ji abunda ya fada mata ba, murmushi kawai na ga ta yi sannan ta aje wayar tana kallona. 

“A kula dan Allah ina zuwa”

Tsakanin shigarta dakinta da fitowarta be wuce minti biyar ba ta mikowa Namra dake rike da hannuna abu a leda sannan ta shafa kanta. 

“To bye bye jikata”

Murmushi Namra tai ta yi mata bye bye sannan nai mata godiya muka fito, har mu ka bar gidan ban saje ganin yarinyar nan mai shegen surutu kaar suda ba. Na yi mamakin ganin mai napep din a gafen gidan fake da napep dinsa, ni har na manta da shi lallai ba karamin hakurin yai ba na tsayawa jirana har na fito. Ya nuna min jindadin ganin yata kamar ya san ni har yake tsokar Namra wai ta tashu hankalin Mamanta. Ni dai na san na fada masa unguwar da zai kai ni wato family house dinmu sai dai tafiyar da isa cikin unguwar ban san an yi ba har sai da Namra ta girgiza ne, ashe hawaye na ke ban sani ba tashin hankalin da ke cikin kaina ya mantar da ni duniyata na dan kankanen lokaci, tsoro nake idan ba cikin ba ne kamar yadda Hajara tai min hasashe, sai dai taya bayan ban tana jin wata alama ta cikin ba? Hasalima ni sai na gama al’ada na ke saurin daukar ciki? Wata jarrabar ce ta sake hawa kaina? Ko kuma dai wani ciwon ne dabam ba ciki ba? No ciki ne! Ita ce amsar da nabawa kaina saboda azabar ciwon mararda neke ji ba irin wanda na saba ji ba ne,hakan ya tabbatar min da cewar cikin ne yake zubewa ko ma ya zube duk da ban tana yin bari ba ban san yadda abun yake ba. Muna fita daga Napep din yan gidan mu suka fito waje da sauri ganin Namra suka saka ihu, sai a lokacin na lura da motar Abdallah da ke fake kofar gidan. Jakata na bude na dauko dubu biyu na mikawa mai napep din ya amsa da murna yana min godiya, sannan na shiga cikin gidan kamar bana cikin hayyacina. 

“Al-hamdulillah”

Shine abunda Abdallah ya fada ganin an shigo da Namra, sai dai ko da wasa be kalli inda na ke ba. A lokacin ne na ji suna fadar su ma sun ji sanarwa a gidan radio kanen maza biyu ma sun nufi can tare da Hafiza. Ko minti biyar Abdallah be kara cikin gidan ba ya ce zai tafi Mama da Inna da Baba suna ta masa addu’ar Allah ya raya mana zuri’a ya saka masa da alheri. 

“Kuma Allah ya ba ni da namiji Mama ina son namiji sosai”

Ya fada yana saka hannayensa aljihu.

“To Allah ya baka namijin mai albarka, ko ya baka tagwaye maza irinku”

Cewar Inna tana dariya shi kuma ya amsa da amin shi da Baba da Mama. Daf da zai fice na yi juyo ina kallon bayansa zuciyarta na raya min abubuwa da dama, sai wani zafi take min kamar a dora tasa a saman garwasu a yanka zuciyata an saka ciki ana soyawa..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 4

Advertisement  *GOBE NA…* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy  4️⃣ “Sa’adatu kenan, kwana biyu ma kin daina dan lekowa,…

GOBE NA 43

Advertisement GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣3️⃣ ABDALLAH POV.  Advertisements He’s walking slowly tun daga inda ya aje…