GOBE NA 21

Advertisement

 2️⃣1️⃣

Yayi parking daidai da lokacin da yake sauke wayarsa daga kunne. A natse ya bude motar ya fita ya nufi kofar shiga falon. Da sallama ya shiga falon kamar yadda ya saba, Suwaiba ta amsa masa murya kasa kasa ba tare da ta kalle inda yake ba sai aikin latsa waya take. Kusa da ita ya zauna yana sauke gajiya idonsa na kan matarsa. 


“Kawo min ruwa”


Ya fada bayan ya kai hannu ya fisge wayar daga hannunta, facebook take kan wani page na Real Life Diaries, sannen shafi ne da yake wallafa matsalolin mata da mazan ma aurata domin samun mafita ta addu’a ko shawara ko taimako idan ta kama. 

  Sama sama ya duba labarin page din wani gurin yai dariya wani abun kuma yai tsaki musamman idan ya leka comment section. 


“Gashi”

Advertisements


Ta mika masa ruwan fuakarta ba yabo ba fallasa bayan ta bata yan mintuna kamin ta kawo masa. 


“Ni na manta when last na leka page din nan, wani lokacin post din mutane bata min rai yake wallahi”


“Wani lokacin kuma ana samun mafita ai, shiyasa ake yin posting din”


Ta fada tana kokarin zama kusa da shi wato a inda ta tashi dazun. Kallonta yai kamin ya kai ruwan a bakinsa ya shaye gaba daya sannan ya aje kofin ya kai hannunsa ya janyota ta kwanto jikinsa.


“Ya akai Subee? Fada min matsalar ki”


“Babu komai”

Advertisements


Ya fada still fuskarta na nuna akwai damuwa. 


“Ba mu saba boyewa juna damuwa ba, fada min matsalarki”


“Ba komai”


Ta sake maimaitawa. Wayarta ya mika mata yana fadin. 


“Ba ki tambaya ko anga Namra ba?”


“Ai na san an ganta, da ba a ganta ba da ba zaka dawo gidan nan ba”


Kallonta yai for few seconds sai kuma yai murmushi as usual. 


“Shine abunda ya bata miki rai?”


“Tun safe ka fita gidanan baka dawo ba sai yanzu, ko rantsuwa nai ba zan yi kaffara ba wata kila ko aiki baka je ba, ka tashi hankalinka gurin neman yarinyar nan wanda na san ko Inteesar ta bata ba zaka tashi hankalinka kamar haka ba”


Wannan karon raba jikinsa yai da nata ya juyo da kyau ya kalleta yana karantar yanayinta. 


“Yar yar’uwata ce ta bata fa, ita ma din kamar yata ce”


“Ta ma fi yarka ai, gatan da kake musu baka ma yayanka wannan gatan, makarantar da ka saka su Inteesar 60,000 ake biya duk bayan wata uku amman Namra makarantar da aka saka su dubu 130,000 ake biya duk term”


“And…?”


“And ba su da wanda zai dauki dawainiyarsu ne sai kai Abdallah? Why kai why?”


“Amman ai kin san mahaifinsu ya rabu da Halimatu ko? Kuma yaran nan a yanzu abun tausayi ne suna bukatar tallafi a rayuwarsu, kuma Halimatu yar’uwata ce kin fi kowa sanin haka”


“Dan ya rabu da ita sai dawainiyarsu ta dawo kanka? Miyasa Abdulhamid b dauki dawainiyarsu ba? Be fika kusanci da mahaifiyarsu ba?”


“Abdulhamid babu ruwansa da yara kin sani, ba sai an fada miki ba”


“Amman ita kadai ce mai yaya a familynku? Miyasa ba kai wa wasu ba sai ita? Komai daga ita sai familynta? Lokacin da Hafiza ta zo nan ta fada maka Namra ta bata kuka fita tare ko magana ba ka min ba”


“What are you try say?”


“Dawaniyar ta maka yawa Abdallah, kai mata kai wa iyayenta kai wai yayanta kai wa yan’uwanta why?”


“Pls just stop…..”


Ya fada yana daga mata hannu fuskarsa na nuna tsananin bacin ransa. 


“Dukan abunda zan yi ma wani a familyna ki kawarda idonki, babu nairar ki a ciki, kuma familyna ne ba naki ba so babu ruwanki da abunda ya shafi family na, dukiyata ce yan’uwana ne”


Yana kaiwa nan ya mike tsaye ya nufi hanyar dakinsa cikin bacin rai. A take ranta ya kara baci, iyakar abunda zuciyarta take raya Abdallah yana son daya daga cikin kannenta Especially Hafiza ganin kamar jininsu ya fi haduwa a cikin kanenta, daman can tana raya ma zuciyarta haka sai dai bata dauki abun da gaske ba kamar yau ganin yadda hankalin mijinta ya tashi akan bata Namra.

 

Yana shiga dakin ya cire kayan jikinsa ya daura tawul, yana kokarin shiga wanka wayarsa tai ringing, dawowa yai ya dauki wayar Doc Auwal ne rubuce a wayarsa.


“Hello Doc Auwal”


“Doc Abdallah ya kake?”


“Lafiya kalau”


“baka shigo ba yau gashi Abdulhamid ya ce na baka sakonsa”


“Sakon me?”


“Ban san na minene ba daga kano dai jiya Doc Faruk ya kawo min yace na baka kai kuma ka bada Abdulhamid”


“Ba zan shigo yau ba sai gobe, wallahi wata yata ta bata ba mu ganta ba sai yanzu”


“Okay bari na biya na kai masa kawai”


“Okay”


Wulga wayar yai a saman bed dinsa yama fadin. 


“Abdulhamid kana ta wahalar da kanka, tun asirinka na rufe har kowa ya ji sirrinka, after you already know za ka samu lafiya ne kawai only if na haifi da namiji….”


Bathroom ya shiga ya sakarwa kansa ruwa, har yai wankan ya fito ransa a bace yake da maganar da matarsa tai masa. HALIMATU POV. 


sai da hankali ya kwanta sannan na kira Abdulhamid na fada masa cewar an ga Namra tana tare da ni ma, godiya yai ma Allah ta cikin wayar nake ina jiyo shaukin muryarsa kamin mu yi sallama. 

A lokacin ne Husna take min zancen wai ta kira Abdulhamid tace yaje gidan radio saboda an yi sanarwa wata yarinyar kamar yadda suka ji daga bakin jama’a.


“Ayya ma zai je ai ba wani son motsa jiki yake ba ni har mamaki nake idan yai nasa yayan ko ya zai yi”


Kallonta nai ina murmushi yayinda na ke gyarawa Namra zama a cinyata. 


“Kin san kowa da rayuwarsa, na fi kyautata zaton Abdulhamid yana kishin rika yaran wasu ne, kuma kin ga daman can Abdulhamid babu ruwansa da yara”


“Ai ba yara kadai ba har manya ba wani so yake ba, shiyasa be taba burgeni ba ni Wallahi da ma Abdallah kika aura tun farko  ya…..”


Hafiza bata karasa ba Mama ta tari numfashinta, wanda hakan yai min daidai.


“Wannan wace irin magana ce Hafiza? Mace ta taba auren wanda ba mijinta ba? Kuma wanda mace take so ai shi zata aura, kar na sake jin irin wannan maganar a bakinki”


Bata sake cewa komai ba ta dauki wayarta da dan guntun gyalenta ta da saba yafawa ta fice daga falon na Mama zuwa dakin Inna wato dakin Mahaifiyarta. A gidan an wuni sai bayan sallah isha’i Abdulhamid ya zo daukata ya shiga cikin gida ya gaisa da su Mama sannan ya fito muka kama hanyar gida. 

   Ba mu yi wata fira a motar ba saboda ciwon marar da ya kasa sakina, pad ma sau hudu ina canjawa, shi kuma na lura kamar baya cikin walwala. A haka muka kwana ko wanne da abunda take sakawa a zuciyarsa, nawa tunanin dabam shi ma nashi dabam duk kuwa da kasancewar ban san damuwarsa ba. 

  A rungume da juna muka kwana kamar yadda muka saba, sai dai na riga shi tashi saboda na gyara kaina, sannan na shiga dora mana abun karyawa cikin kankane lokacin na gama komai saboda ina son zuwa asibiti.

  Sai da nai wanka na shirya sannan na shiga na tashe shi ya fito muka soma karyawan. 


“Ban maka magana tun jiya ba, ina son naje asibiti marata tana min ciwo tun jiya na yi zaton ko zan ji sauki kamin yau amman ban ji alamun haka ba”


Na masa maganar a yayinda muke cikin karyawa. Dagowa yai ya kalleni sai kuma ya kai fork dinsa ya dauki dankali ya ci. 


“Kina Menstruation ne?”


“Yes”


Mikewa yai tsaye kamar ya nufi dakinsa ya dauko wayarsa kamin ya karaso kusa da ni ya kira Abdallah. 


“Kana asibiti ko gida?”


Ban san mi yace masa ba na ji dai ya sake cewa. 


“Okay ga mu nan zuwa, Halima ce bata jindadi zan kawo ta yanzu”


A take na ji gabana ya yanke ya fadi, gashi bana son ya zargi wani abun balle na ce masa bana son Abdallah ya duba ni. 


“Bari nai wanka sai n kai ki gidan Abdallah ya dubaki”


Kai kawai na iya gyada masa ya juya ya koma ciki, har yai wankan ya shirya ya fito ban samawa kaina mafita akan abunda zan yi ko na ce da zai hana zuwan gurin dan’uwansa ba. 

A dole tasa na saka hijab dina na na dauki jakata da wayata na fice ina gaba yana baya har muka fito daga falon, a gaban motarsa naje na tsaya ina jiran ya karaso ya cire key din na bude sai ji nai an rumgumeni ta bayana. 


“I love you so much”


A hankali ya fada min haka sannan ya sake ni ya danna keys din hannunsa motar ta fita daga lock. Front seat na zauna shi kuma ya shiga driver seat a usual, sai dai har muka isa gidan Abdallah be kalli inda nake ba be ce min uffan ba kuma ban ga wata walwala a fuskarsa ba, hakan yasa na fi kyautata zaton wata kila rashin lafiyarsa ce ya saka a rai ta hana ni sukuni a take tausayinsa ya rufe har idanuwa suka soma cika da kwalla. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na bude motar na fita, wannan karon shi ne a gaba ni ina baya. Mun dan jima tsaye a gurin kofar kamin Suwaiba ta bude mana. Na yi kokarin kirkirar far’a na yaɓa a fuskata duk kuwa da irin halin da nake ciki, sai dai yau na same ta akasin yadda na saba samunta ko kuma na ce nake ganinta, domin tun da na auri Abdulhamid ban taba zuwa gidan da sunan kawo mata wuni ba sai yau shi ma kuma wannan da daliline. 


Cikin falon muka shiga na zauna a saman cushion Abdulhamid kuma ya zauna kusa da ni yana ta kallona kamar ba shi ba. Bayan kamar minti biyar Abdallah ya fito a daya daga cikin bedroom din da suke falon. Shi ma dai fuskarsa babu walwala kamar ta matarsa, sai da ya mikawa Abdulhamid hannu suka gaisa sannan ya zauna ba tare da ya kalli inda nake zaune ba. 


“Ina kwana?”


Na mika masa gaisuwa ina ta kallon zoben hannunsa, zoben da ba kasa samun natsuwa da shi har yanzu. 


“Ina kwana”


Sai ya dawo min da gaisuwar still be kalleni ba sai Abdulhamid yake tambaya abunda yake damuna. 


“Mararta ke ciwo”


“Tun yaushe?”


“Tun jiya, magani nake son ka rubuta mata”


“Ya kike jin abun?”


Wannan karon ya kalleni a yayinda yake tambayar tawa. 


“Ina dan jin tana min ciwo ne”


“Sosai ko kadan and tun yaushe?”


“Jiya”


Tashi yai ya shiga daki, be dade ba ya fito rike da takardar magani ya mikawa Abdulhamid. 


“Dan Allah daga yau idan matarka bata da lafiya ka kai ta asibiti direct ba sai sai nan ba, ko ba komai zata fi sakewa idan tana ganin mace yar’uwarta”


Ba Abdulhamid kadai ba, ni kaina da nake matar Abdulhamid na yi mamakin jin furuncinsa, wanda na tabbatar hakan be yi ma Abdulhamid min dadi ba ko kadan. Uffan be ce masa ba bayan kallonsa da yai ya karbi takardar tare da ce min na tashi mu tafi. Daga gidan Abdallah kai tsaye gidan Hajiya ya wuce da ni, ban so haka ba amman ban isa na nuna masa ba kasancewar mahaifiyarsa ce. Ita kanta ta lura da yanayinsa na rashin jindadi daman can yana fama da shi balle kuma yanzu da Abdallah ya kara masa da wata maganar. 

A gaban idona take tambayarsa abunda yake damunsa sai ya amsa mata da cewar babu komai, daga bisani ya kalleni ya ce. 


“Ki zauna a nan idan an dawo aiki zan biyo miki da maganin sai mu wuce gida, Hajiya ba ta jindadi shiyasa na kawo ta nan ta huta kamin na tashi aiki”


Ya karasa yana fadawa Hajiyar.


“Allah ya saukewa”


Ta fada tana dauke kai irin abun be dame ta ba. Shi kuma yai mana sallama ya tashi ya fice. Da kallo Hajiya ta bishi har ya fice sannan ta kalleni.


“Ke me ke damun mijinki?”


“Kwana biyu nan haka yake, kuma yanzu muka fito gidan Abdullahi ya kai ni ya dubani shine ya ce karya sake kawo ni to ban san ko shi ya bata masa rai ba”


“Husaini ne ya ce masa haka?”


A take ta daga wayarta a gurin ta jira Abdallah ta fada masa tana son ganinsa, abun ka da mai jiran kiran uwa a ko da yaushe, sai gashi ya zo cikin kankanen lokaci dama can babu tazara sosai tsakanin unguwarsu Hajiya da ta Abdallah. 

  Fuska a sake ya shigo kamar ba shi ne na tarar a can ya hade rai ba, ko dan wannan mahaifiyarsa ce oho. Bayan ya zauka Hajiya ta sallame ni ta hanyar cewa na tashi na ba su guri. 

Ba musu n tashi na fita daga falon sai an samu guri kusa da kofar falon na zauna ina ta sake sake a raina, ta wani bangare raina fes yake da zubar jinin da nake domin na san indai ciki na zube a yanzu, ta dayan bangaren kuma ina jin tausayin mijina. Ban san abunda Hajiya tace masa ba sai dai na ga ya fito ransa a bace har ya wuce ni sai kuma ya juya ya nuna ni da yatsa kamar ba Abdallah ba.


“Ina ta kokarin ganin na fita daga hanyarki, ya kamata ke gane ke matar dan’uwana na ce a yanzu, duk wani abu daya shafe ni ko kika san zai saka dan’uwana kusantar da ke a gareni ki yi kokarin kauce masa, idan ba haka ba ran mijinki zai yi ta baci fiye da yadda kike zato kuma za ki jawa mijinki shiga damuwa fiye da wacce yake ciki…”


Idanuwa ne suka fara yawo a fuskarsa.


“Baka da tausayi Abdallah ba ka da kirki, ba ka san damuwar kowa ba sai ta ka, kai baka tausayin dan’uwanka ma? Bayan halin da yake ciki na damuwa kake neman kara saka shi wani? Kamar ba uwa daya ta haife ku ba? Abun da ya kamata ace ka taya shi tausayin kansa da neman lafiyarsa amman sai neman kara jefa shi a damuwa kake?”


“Babu ruwana da matsalar mijinki, ba tausaya min ba, dan haka babu tausayi a tsakaninmu samun lafiyarsa ko zamansa haka har a bada be dame ni ba saboda shi ma be bar ni na samu farinciki na ba”


Kallon mamaki nai masa. 


“Ya kake kokarin aron wadansu dabi’u da halaye marar kyau ka yafawa kanka Abdallah, kana abu kamar ba kai ba? Dan’uwanka jininka? Wallahi Abdulhamid ba zai taba yi maka abunda zai hana ka samun farinciki ba, ba ka da kirki da halin kwarai shiyasa baka taba burge ni ba, kana da son kanka da yawa shiyasa ban tana jin son ka a zuciyata ba….!”


Fadada fuskarsa yai da murmushi kamar ba shi ba.


“Wani lokacin Wallahi mata ba ku da hankali”


Yana fadar hakan ya juya ya nufi gurin motarsa. 
AHMAD POV. 


Tura kofar falon yai ya shiga da sallama, Momy ta amsa masa tana rike da wayarta. 


“Dan halak, yanzu nake kokarin kiranka fa, tun da ka fita baka dawo ba”


“Ban dade da fita ba ai”


Ya fada yana kokarin zama. 


“Eh na sani, bana son kana yawon nan idan ba aiki ba ko wani uzurin”


“Haba Momy sai kace wani karamin yaro”


“Ba zaka gane ba ne ai, yan mata yanzu shegen wayo ne da su a take za su ci maka kudi su gudu, kuma na sna indai ka bar gidan nan ba iya kula kake da kanka ba”


“Yanzu ni kamata yan mata za su yi wa wayo?”


Ya nuna kansa. 


“Hmmm Baka san mace ba, har yanzu kai yaro ne, ka ci abinci?”


“Eh na ci abinci”


“Ka koshi?”


Murmushi yai yana ta mamakin yadda Momy take ta maida shi karamin yaro, sam ta ki yarda shi din namiji ne kamar kowa, sometimes har mamaki yake shi dai yasan ba girma ne be da shi ba balle ace tana ganinsa da karamin jiki, shiyasa wani lokacin ko yana bukatar baya nunawa saboda kar ta samu damar yi masa haka. Baby Namra ce ta fito daga bedroom dinta tana masa oyoyo. 


“Daddy sannu da zuwa”


Ya mika hannunsa ya rikota.


“Yauwa darling y scul?”


“Fine Daddy wannan Name sake din tawa ta tafi”


“Yeah Momy ta zo ta dauketa did you miss her”


“Yes Daddy”


“Ke da kika ce ba ki sonta?”


“Yanzu kuma na ji ina sonta, daddy za ka kai ni gidansu?”


“Ban san gidansu ba”


“Pls daddy”


“I’m serious”


Ya fada yana kara gyara mata zama a jikinsa, har cikin ransa yake jin son yarsa fiye da komai a rayuwarsa, musamman idan ya tuna cewar bata da mahaifiya a raye. 


“Idan kin je makaranta ki tambaye unguwarsu sai a kai ki”


Wannan karon Momy ce take maganar. 


“Wane class take Momy?”


“4 tace min kamar 4 kamar 3 na manta dai ki bincika”


Da sauri ta gyada kai tana murmushi.

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 43

Advertisement GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣3️⃣ ABDALLAH POV.  Advertisements He’s walking slowly tun daga inda ya aje…

GOBE NA 45

Advertisement *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣5️⃣ ABDALLAH POV.  Advertisements Zuciyarsa cike take da tunanin abunda Halima ta…