GOBE NA 25

Advertisement

 *GOBE NA…*

2️⃣5️⃣

“Abun nan fa ya wuce iya abunda kike tunani, Wallahi mutanen nan ba za du yi karya ba, kuma ga zahiri kina gani, abubuwa sai kara kwabewa suke”

Aminu ne yake wannan maganar yana shafa kansa cikin tsananin damuwa, hannunsa na dama rike da takardar transfer. 


“Iko sai Allah, ni wani abun yana bani mamaki Wallahi, taya za ka biye maganar bokaye? Tun farkon fari ma mi ya kai ka gurin ya saka tsinbo? Da har za su fada maka karya da gaskiya ka yarda”


“Hajiya ai dubiya yanzu babu wanda yake zaune, ba maza ba mata ba kowa kuma yadda lamurran nan suka fara lalacewa ai dole na saka a bincika min, ba ni kadai ba ko Alfa da ya kai ni sai da abun ya daure mata kai”


Advertisements

“Allah kadai ya san gaskiyar wannan lamarin wata kila ma gurin malaminta ka fada, ko kuma shi alfan yana goyon bayanta ne, shiyasa suka hada kai ai maka haka”


“Babu wani zancen goyon baya Hajiya fa a zahiri kike ganin komai sai lalacewa yake”


“Kai fa baka iya tashin hankali ba, kai yanzu dan Allah Aminu har ka kawo maganar dawowa da Halimatu a gidanka? Mace da bata kaunar uwarka bata son yan’uwanka? Ka duba ja ga har kazafi tai wa Sadi fa? Wallahi har a bada ba zan taba son Halimatu ba”


“Hajiya abunda ba ki sani ba, ko wane dan’adam yana da good side of him kuma bad side, Wallahi Hajiya ba dan ina son dawowo da Halimatu ba, acire zancen arziki, Hajiya Halimatu ta fi Murja hakurin zama da ni, Halima ko bata son abu bata nuna, sannan ko fada nai mata ko na ci zarafinta sai dai tai kuka ta ba ni hakuri, and tana kokarin ganin ta gujewa bachin raina, zan iya tafiya inda nake so nai iya adadin kwanakin da nake so na dawo bata ce min komai, amman ban isa nai ma Murja haka ba Wallahi Hajiya, idan na dawo tara na dare Wallahi sai Murja ta yi min fada, amman a lokacin da Halima take nan zai iya kai wa 1 na dare a waje kuma ba zata ce min komai ba, Murja ta bi ta saka min ido akan komai nawa, ba ni d sukunin daukar waya na latsa a cikin gidana idonta na kai”


Hajiya ta saki baki. 


“Ban gane idan kai dare tai maka fada ba? Uwarka ce ita? Ita ta aje ka ko kai ka aje ta da zata maka fada? Ita ba mata ba ce da ba zaka mata magana ba”


Advertisements

“Hajiya ba za ki gane ba ne, idan ranta ya bace, jikina har rawa yake Wallahi”


“To acan gurin malaman da kaje ba su fada maka komai akanta ba?”


“Me za su fada min? Ni yanzu ba ta nata nake ba, ta Halimatu na ke domin sun fada min matukar ban mayar da ita ba, ba zan taba ganin komai daidai ba, kuma ga alama nan kina ganin bayan rage min mukami da akai yanzu an min transfer zuwa enugu, duka duka yaushe ne rabuwar mu? Idan aka kara dadewa kila ma bara zan koma, tun da sun ce ita ke da kashin arzikin duk abunda na samu saboda ina tare da ita ne, ni da farko ma na dauka ko sammu ne kai mi shiyasa ma har na biye ta Alfa ya kai ni gurin ashe ba asiri ba ne rabuwar da mu kai ce, Hajiya ki duba fa ki ga abun hawa ma neman gagara ta yake, motata na mata gyara uku abunda ban taba ba, yanzu na siye sabuwa ita ma engine dinta ya tsaya, sabuwar mota fa Hajiya Motar miliyan biyar ace engine dinta ya tsaya”


“Wai kana nufin ba da motar ka zo ba?”


“Wallahi Alfa ne ya sauke ni bakin gate, tun jiya motar ta tsaya tana can gurin ma su gyara”


“To abun nan fa d daure kai ni na fi zargin sammu gaskiya, asiri ne akai maka, ko ita ai zata iya maka asirin na ka lalace tun da ta ga ka sake ta, ko kuma abokan aiki ko makota”


“Hajiya Malami hudu msgana daya suke, babu wanda yace asiri ne, ni dai ki taimaka min ta dawo dan Allah”


“To ai ban ga ta inda zan iya taimaka maka ba, matar nan fa ma aure tai gidan wani take”


Dafe kansa yai.


“Kai Hajiya, ko wane da idan yana cikin matsala gurin uwarsa yake zuwa ta sama masa mafita, amman ke sai kokarin kin yarda kike da ni”


“Ba yarda ne ban yi da kai ba, nawa binciken zan yi akai”


“To ki kara bincika mu ji idan za a samu results daya, ni yanzu yarana nake son na fara dawowa da su hannuna, na san ina dauko yaran nan hankali zai dawo kaina dan bata hada su da kowa ba”


“Tana son su za tai aure ta bar su?”


Cewar Hajiya tana tabe baki. 


“Wannan ai na dabam ne, idan naja yaran a jikina na nuna musu su janyo uwarsu ai dole hankalinta ya dawo nan, Wallahi shegen son ya’ya ne da ita Allah kadai ya san yadda akai ma tai aure ta bar su”


“Kudi ta bi, shi wanda ta auran ba ance dan uwanta ba ne kuma mahaifinsu ya bar musu dukiya, ai kudi babu abunda basa sakawa, ni ganin na ke komai kai ba zata bar wacan mijin ta dawo maka ba”


“Zata dawo ai kin dan yadda take so na, kuma daman first love shine so ai, kuma ni na san Halima na so sosai Wallahi, zata dawo da gudu ma”


“Uhm… ”


Mikewa yai tsaye. 


“Motarki na nan Hajiya?”


“Wallahi na aiki Musa direba da ita Mafara sako zai karbo min, ka kira Sadi ya kawo maka motarsa daya mana ai mota biyu ne da shi”


Ba musu ya koma ya zauna ya ciro wayarsa ya kira kanensa Sadi. Ringing biyu zuwa na uku ya daga. 


“Sadi kana ina?”


“Gani kusa da gidan Hajiya”


“To ina gidan karaso ka sauke ni gida”


“Okay”


Bayan na sauke wayar, Hajiya ta cigaba da yi masa maganar so take ta karkarto hankalinsa da barin zancen maido Halimatu domin ita a ganinta ba mafita ba ce, zuciyarta ta fi natsuwa da sammu akai masa ko dai Halimatun tai masa ko kuma wani dabam, ba a wuce minti ashirin ba Sadi ya shigo gidan cikin sabuwar shadda light yellow da hula kubu sai kamshin turare yake. S tsaye ya gaisa da Hajiya domin shi ma a hanya yake akwai inda yake son zuwa. 


“Gida zaka sauke shi”


“Ina motarka ne?”


Sadi ya tambaya yana barin kallon Hajiya wacce tai masa maganar. 


“Wallahi ta samu matsala wai engine dinta ta buga”


Aminu ya fada cike da damuwa a fuskarsa. 


“What, motar da ka siyo satin nan ko dai wacan tsohuwar”


“Tsohuwar ai siyar da ita nai, wannan dai sabuwar”


“Garin ya?”


“To ni ina ma zan iya cewa ga dalili, abubuwan ne dai sai hamdala”


“Allah ya kyauta, tashi muje”


Sai da Aminu da Hajiya suka amsa da Amin sannan ya mike tsaye suka fice tare. Har gida Sadi ya kawo Aminu, bayan ya bude motar ya fita Sadi ma ya bude ya fito wai bari ya gaisa da Madam. Aminu na shiga cikin falon Murja da taso da sauri ta rumgume shi tana masa oyoyo sai shagwaba take zubawa kamar wata karamar yarinya.


“Ina tare da shi fa Hajiya” 


“Dan kana tare da shi sai ya hanani nunawa mijina soyayya?”


Murmushi Sadi yai ya dauke idonsa ya nufi kitchen. 


“Bari na sha ruwa”


Kitchen din ya shiga da kansa ya dauko cup ya bude freezer ya dauko robar ruwa ya bude ya soma bulbulawa. Kamar daga sama ya ji am rumgume shi ba shiri ya dire ruwan da yake sha ya juyo da sauri yana kallon kofar kitchen din. 


“Kai dan Allah sarkin tsiro, ya shiga dakinsa”


“Amman ai zai iya saukowa yanzu kuma ya shigo nan”


Ya fada da rada hankalinsa a tashe yana kallon kofar kitchen din dan ya san the worst thing da zai aikata shine ya bar dan’uwansa ya san alakar da ke tsakaninsu.


“Ka daina zuwa kwana biyu, i miss you”


Ta fada tana dora hannunta a saman lips dinsa sai lumshe ido take da fake eyelashes dinta. 


“Murja alakar mu ta da ba kamar ta yanzu ba ce fa, saboda dan’uwana kike aure dole nai tsaka tsantsan”


“Auren dan’uwanka ya hana alakar mu cigaba ne? Tun farko ba kai kaja ba, da aka aurena zan auri yayanka ne, sai wani kwana kwana kake min jikina kawai kake so”


Saurin turarenta yai daga jikinss ya fito daga cikin kitchen din jin kamar motsin fitowar Aminu a falo, kai tsaye ya nufi kofa ya fice daga falon gaba daya. Dariya murja tai ta nufi dakin mijinta, da taimakonta yai wanka ya shirya cikin farin yadi marar nauyi sannan ta gabatar masa da abincin rana. Cin abincin suke yana ta sake2 yadda zai bullo mata, so yake ya fada mata cewar yana son ya dawo da yaransa a gidansa amman yana jin tsoronta, baya son bacin ranta idan ranta ya bace ji yake kamar zai mutu, ko motsi dai sai ya rasa natsuwarsa saboda tsoron abunda zai fito daga bakinta, haka Allah ya saka masa tsoronta kamar mutuwarsa, idan ranta ya bace har kuka yake mata gurin bata hakuri abunda be taba yi ma wata mace ba, ko Hajiyarsa baya tsoro yadda yake tsoron Murja. 


AHMAD POV. 


“Na dauko Baby Namra daga gidan Hajiya, ka dawo gida da wuri karka wuce 8”


Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya amsa mata ta okay. 


“Yayi Mommy’s Boy”


Rahim ya fada yana dariya.


“Ba fa abun dariya ba ne seriously bana jindadin abunda kake min”


“Okay sorry but abun nan yana ba ni dariya”


“Ba abun dariya ba ne, abun nan gaba yake kara yi ba baya ba, na rasa yadda zan bullowa lamarin nan, yanzu fa ta kai har wayata Hajiya ta ke karba ta duba, irin ita bata yarda da ni ba,kullum ganin take kamar yan mata wayo za su min”


Rahim ya kara matsowa kusa da shi ya da fashi.


“Magani kawai kai aure Gwarzo, matukar ba aure kai ba zai Hajiya ba zata daina ganinki a yaro ba”


“Auren ba mafita ba ne, yaure uku nai kamin na auri Halima amman ko wace ta kasa zama da ni sai Halima ita ma kuma saboda ta yi hakuri ne, bayan rasuwarta mace biyu na aura Hajiya bata barin na zauna da mata, tun da idan bata ga dama ba sai ta hana ni cin abincin mace ta ce bata yarda da shi ba, kuma ko yarinyar na nemo idan bata gamsu da ita ba ba zata bar ni na aureta ba”


“Wata mace zaka aura ba yarinya ba, mace mai hakuri da sanin ya kamata, kuma kamin ka aureta ka fara gabatar mata da Hajiya ka fada mata komai na ka karka boye mata, kai idan ta kama ma kai auren a boye kai yi dan samawa kanka mafita, dan Hajiya har yanzu bata daina ganinka a yaro ba, bata yarda ka girma ba”


“Wallahi abunda take min ko Baby Namra albarka, dan yau idan Baby Namra ta ga dama zata iya zuwa wani guri a cikin familymu tace can zata kwana kuma Hajiya ta barta amman ni ban isa ba, abun da Hajiya take min har dauren min kai yake wani lokacin har daure min kai yake”


“Ka samu wata ka aura, irin macen nan da ta saba shan wahalar gidan aure, ka aureta kuma ka fada mata komai karka bi soyayya ka auri yarinya ta zo tai ma Hajiyarka hauka ko ta kasa hakuri da kai, iirin dai mace mai yaya biyu uku aha”


“Kai ba zan iya auren macen da wani ya aura ba, you know ina da kishi sosai, ba zan iya zama macen da wani ya aura ba balle ma wacce tai aure har fiye da daya”


“To ai kaji matsalar ka fi son ka auro yan matan nan na zamani kansu na hayaki dole su ce ba za su zauna da Hajiya ba, ba wai dan kana sonta zata aureta ba, kai ko auren kwangila ne kai kawai da zarar ka samu yancinka gurin Hajiya sai ka rabu da ita ta auro wacce kake so, ya kamata ka amsa sunanka na Gwarzo fa, na san baka daukar rainin kowa a kamfani, idan ka bawa mutum umarni jikinsa har rawa yake ya cika maka aikinka, to ko a gida ya kamata kana motsawa”


“Da Halima na nan da yanzu na amsa, Ba zan taba son wata ba Rahim, ni mijin matacciya ne, na riga na auri Halima kuma na auru, duk mace da zan aura zan aureta ne kawai dan samun mafita amman ba dan kauna ba”


Yayi maganar cikin sanyayyiyar murya, yana sotsa lips din, zuciyarsa na sosuwa da kauna Halimatunsa Uwar Baby Namra. 


“Halima ta yi min abunda wata macen bata taba min ba, ta haifa min Baby Namra, ta yi hakurin zama da Hajiya har na tsawon shekara biyu…”


Rahim ya soma lura da yanayin abokinsa, daman ya saba shiga a irin wannan yanayin a duk lokacin da aoa dauko maganar Halimatu, a kokarinsa na kawar da maganar ya dauko masa maganar kamfani. 


“Yauwa na manta ban fada maka ba, sun fa turo takardun nan ta mail din kamfani amman sai mun yi printing out….”


Mikewa Ahmad yai tsaye cikin damuwa. 


“Dan Allah ka daina maganar wani kamfani a yanzu, lemme go and rest…”


Fita yai daga gurin ya nufi motarsa, yana shiga ya dauki hanyar Exclusive City. 
HALIMATU POV. 


Na yi kuka iya wanda zan iya, na yi na gaji na rarrashi kaina domin ba ni da mai rarrashina a wannan lokacin. Daya daga cikin waitress din dake gurin ne ya zo yana tambaya idan ina bukatar wani abu? 


“Bana bukatar komai, akwai wanda na ke jira ne”


Juyawa yai ya koma gurin da yake tsaye, ya cigaba da danna wayarsa, binsa nai da kallo kamin na ji wata murya mai cike da bacin rai tana min magana. 


“Waya aje wannan matar a nan?”


Juyowa nai na kalleshi da kumburarrin idanuwana, mutunen nan ne daya taba ture ni a keke, kuma shi ne wanda na gani a lokacin da naje kai Namra School, kuma shi ne mutumen da ya tsinci Namra. Da saurin waiter din dazun ya zo yana tambayar ba’asi. 


“Taya za a bar wata ta zauna a seat din nan? Me ke damunku? Da alama kai bako ne, kuma laifin ba na ku ba ne laifin shugabanku ne, for more than ten years ina biyan kudin gurin nan saboda tsabar rainin hankali yau za ku bar wani ya zauna? Oh haka kuke idan bana nan daman you’re very stupid”


Sauran waitress din suka zo suns bashi hakuri, wanda ni ban ga dalilin hakan ba, ko da yake na ji ya ambaci sama da shekara goma yana biyan seat din da alama baya son kowa ya zauna ne. 


“Ke dalla malama tashi ki rasa kujerar da za ki zauna sai wannan”


Ko kadan maganarsa bata 6ata min rai ba, da alama macen da yake biyawa kudin kujerar tana da muhimmanci a gareshi, ba kamar ni ba. Mikewa nai tsaye na kalli kujerar sannan na kalleshi na ce. 


“Ka yi hakuri ban san cewa kujerar ta ka bace, ban san alakarka da mai seat din ba, mata, yar’uwa, uwa, ko ya ko kanwa, amman ka bata hakuri a madadina, domin ko wacece duniyarta kyakkyawa ce, kuma mai fadi ce shiyasa tai dace da mai kare martabar gurin zamanta ba ma ita din ba”


Hannu na kai na dauki jakata na yi gaba abuna ina jin zuciyata kamar zata fito, na taki sa’a ina kawowa bakin gate din gurin Motar Abdulhamid na kunno kai a harabar gurin, sai da ya faka motar yana kokarin fita na nufi gurin motar na bude na shiga. Ba tare da yace da ni komai ba yai ma motar key muka kama hanyar gida. __________________


Wai ni kadai na ke hango wani abu?🤔

Bari mu ga masu brain me kuke hangowa? 🤔

Tafdijam 😲 fatar dai kun shirya tafiyar domin yanzu aka fara….. 😊

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 20

Advertisement  GOBE NA…* By Khadeeja Candy  2️⃣0️⃣ DEDICATED THIS PAGE TO Mai Dambu, Allah kara miki lafiya Gwanata❤…

GOBE NA 48

Advertisement  *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣8️⃣ Tun daga yanayin tafiyata zaka fahimci ina cikin wani irin nishadi…

GOBE NA 45

Advertisement *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  4️⃣5️⃣ ABDALLAH POV.  Advertisements Zuciyarsa cike take da tunanin abunda Halima ta…