GOBE NA 32

Advertisement

 *GOBE NA…*


By Khadeeja Candy 3️⃣2️⃣


Barka da Sallah Allah ya maimaita mana 🙏❤


Hannu na kai na rufe bakina, wannan karon ba kuka ido da baki kawai nake ba har da zuciya da kwakwalwa da jikina amsa amo yake. Kuka nake ta ko’ina irin kukan da ban taba yi ba, irin kukan da ban taba sani yana tare da ni ba karkawar nake kamar wacce ta shekara a cikin kankara hakorana na hadewa da juna suna wata kara, wani kalar hayaki nake ji a cikin kaina. 

Advertisements


“Ashe har yanzun kukan be kare ba Halimatu”


Mama ce tai maganar sai na dago na kalleta tsaye take jikin kofar dakin da nake ita ma kuka take kamar ni. Kai na gyada mata kamar wani abun arziki sai kuma na ji ana fisgata kafafuwana suka kasa daukata, wani farin haske ya baibaiye idona tashin hankali da nake ji a yanzu bana jin cewar ko daya daga cikin yayana ne ya mutu zan samu kaina a yadda na samu kaina a yanzu. 


“Ki ce Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”


Mama ce take fada min abunda zan fada, ba dan ina ganin fuskarta ba, ba fuskarta kadai ba komai bana iya gani a yanzu sai dai ina jin hannunta a jikina tana rike da ni. Unkuri nai da zimmar na bude bakin na furta abunda ta umarce ni sai bakin yai min nauyi kamar ban taba magana da shi ba. Daga lokacin ban sake sanin inda nake ba sama nake kasa nake duniya nake ko a lahira ban sake sani ba, sai duniyar ta duburce min hankalin ya tafi numfashin ma yai min dogon zango….AHMAD POV. 

Advertisements


Tun bayan da aka kai Baby Namra a gidanta na gaskiya be sake zama a aje ba, duk wanda ya kira wayarsa ko ya zo gidan da sunan masa gaisuwa ba zai dauka ba ba kuma zai fito ba. Wani abu yake ji a tare da shi shi ba tsoro ba ba kuma fargaba ba, baya son ayi masa gaisuwar mutuwar yarsa, har yanzu kuma ya kasa saka komai a bakinsa bayan ruwa, ya kuma kasa jin komai a game da mutuwarta. Ita kanta Hajiya a yanzu tafi shiga tashin hankalin da gwarzo yake ciki fiye da jimamin mutuwar Baby Namra, ta fi kowa sanin danta yana da hakuri da juriya, sai dai wannan karon ta kasa banbance hakurin ne ko kuma damuwa? Ta san yadda yake son mahaifiyar yarsa balle kuma ita yartasa.


Yana tsaye gaban madubin dakinsa Hajiya tai sallama ta shigo jiki a sanyeye damuwa da bakinciki karara a fuskar uwa mai damuwa da ciwon danta. A bakin gadonsa ta zauna tana kallonsa har ta bude baki tai magana sai ya tari numfashinta.


“Hajiya Allah kadai yasan irin ihun da Baby tai kamin ta mutu, ita kadai ta san irin ciwon da ta ji”


Idonta ya cika da hawaye tana masa kallon tausayi. 


“Ka fara jin zafin mutuwarta kenan”


Juyowa yai ya kalleta.


“Har yanzu dai, kawai na rasa dalilin da zai saka a kashe min ƴa ne”


Kallonsa Hajiya take da uwar ramarsa da rashin kuzari da yake fama da shi. 


“Na kasa yarda cewar matar nan zata iya tura yarka a rijiya ta mutu bayan kai ka ceto ta ta yar, kullum mahaifinta da yan gidansu sai sun zo gaisuwa a gidan nan, babu yadda mahaifinta bw yi ba akan ya ganka amman saboda kace baka bukatar ayi maka gaisuwa na hana, ita kanta matar da kake zargi sun fada min cewar tana asibiti bata san inda kanta yake ba sanadin wannan abun”


Dan murmushi yai kadan na takaici. 


“Hakan yana nuna da ganganta ta aikata, saboda ta ji nace zan daureta ne  shiyasa ta shirya ciwon karya”


Zuwa yai ya zauna kasa kusa da Hajiya ya dora kansa a saman cinyarta sai wasu hawaye masu zafi suka soma sauko masa. 


“Hajiya kina iya tuna lokacin da take cewa bata son ta mutu ita kadai? Idan zata mutu zata tafi tare da ni da ke?…” 


“Tana yawan fadar cewar bata son ta sha wahala idan zata mutu”


Hajiya ta karasa masa. 


“Ta yi mutuwa mafi kaskanci Hajiya, ta samu rauniya ka dama, Allah kadai yasan wahalar da tasha kamin ta mutu”


Ya fada yana shafewa da kuka, for the first time bayan mutuwarta yau ya ji wani abu marar misaltuwa yana ratsa zuciyarsa, kewar yarsa yake ji a yanzu ji yake kamar ya rumtse ido ya bude ya ganta a kusa da shi, wani irin bakinciki ne ya soma rufe shi ta koina.


“Hajiya ina ma ace ba da gaske ba ne, mahaifiyar yarinyar nan ta tafi yanzu kuma….. ”


Sai ya kasa karasawa saboda kukan da ya ci karfinsa. Daga shi har Hajiya aka rasa mai rarrashin wani. Kanwarsa ce Siyama ta zo bakin kofar dakin ta tsaya tana kallonsu itama kukan take kamar su. 


“Be kamata a kyale matar nan ba, ta raba mu da farincikinmu, ta dasa mana bakincikin da ba zai tana goguwa a zuciyarmu ba”


“Ba zan kyaleta ba, ba zan bar wannan abun ba Siyama”


Ya furta cikin mueyar kuka still kansa na kan cinyar hajiya kamar wani karamin yaro, ita kuma ta dora hannunta a saman kan nasa tana ta rarrashinsa. 


“Ka dake ka daure ka shiga jama’a kuma ka amsa kiran wayarka, duk wanda akaiwa mutuwa yana jin babu dadi amman a haka yake daurewa, yau ake sadakan uku ya kamata ka fito cikin mutane ka zauna irin wannan kebancewar da kake kana kara bayyana rashin tawakalinka ga Allah ne, ya kamata mu yi imani da kaddara dukanmu”


Kuka yake ba dan kadan ba, kuka yake ba na wasa ba, kukan da be tana irinsa ba, kukan da be taba saka ran yinsa ba. Kukan da tun da Namra ta mutu be ji irinsa na kusanta shi ba, ko mutuwar matarsa be yi kuka haka kamar na Namra ba, tun Hajiya na taya shi kukan har ta share hawayenta ta koma bashi hakuri tana karfafa masa. 

Daga karshe dukan maganganun Hajiya sun shiga jikinsa ya ji karfin hali da karfin zuciyar da yake jin zai iya fita ayi addu’a ukun yarsa da shi. Haka kuwa akai ya fita ya shiga mutane ana ta masa gaisuwa yana amsawa cikin karfin hali, sai dai a duk lokacin da akai masa gaisuwar sai yaji wani abu ya tsaya masa a zuciyarsa daker yake iya hada yawun bakinaa ya hade abun, tun yana iya hadewa da yawun har ta kai sai ya kurba ruwa yake jin abun ya wuce masa, wasa wasa ya fara jin numshinsa na yin kasa har sai da ya koma ambaton mahallincinsa. Babu wanda be tausaya masa ba, duba da irin shakuwar da ke tsakaninsa kuma sanin cewar ba shi da mata a yanzu, gashi mahaifiyar yarinyar itama ta rasu, ga wata uwar ramar da yai cikin kwana biyu kawai ya koma kamar wanda ya shekara kwance yana ciwo. 

   Bayan sallah la’asar akai addu’a sai mutane suka fara watsewa, wasu kan so su sake masa gaisuwa sannan su wuce musamman wadanda ba su samu ganinsa ba sai a yau. A cikin mutanen har da mahaifin Halimatu wanda tun da akai mutuwar kullum da shi ake karbar gaisuwar. Da hannunsa ya turo wheelchair dinsa ya karasa kusa da Ahmad ya mika masa hannu Ahmad ya mika masa nasa hannun yana amsa gaisuwar da yake masa.


“Ni ne kakan abokiyar yarka Namra…”


Baba na rufe baki Ahmad ya tsaya cak yana kallonsa kamin yai saurin janye hannunsa. 


“Me ka zo yi nan?”


Baba yai shiru kamar mai tunanin ta inda zai fara. 


“Ka fada min cewar yarka bata da laifi? Ko kuma ka bani hakuri akan abunda tai? Ko kuma saboda ka yi min gaisuwa sai na ce na yafe mata…?”


“Da dai ka saurareni d’a na”


Baba ya fada cikin sanyayyiyar murya, a take Ahmad ya daga masa hannu yana mai jin baya ma bukatar saurarensa.


“Bana son jin komai daga bakinka, ka fadawa yarka ta jira kiran kotu, domin ba zan kyale wannan maganar ba, yarka kake kokarin karewa ni ma kuma kadin yata zan bi”


“Haba dai d’ana arzikin ba hauka ba ne ka saurareni mana”


“Ni ba danka ba ne da danka ne ni da yarka bata kashe min ya ba….”


Yana kawai nan ya juya a fucewa ya bar harabar gidan. Part dinsa ya shiga ya ya dauki wayarsa dake ringing sai ta ya fara amsa kiran amsu masa gaisuwa sannan ya samu damar kiran lauyansa. 
***   ***    ***


Cikin tsananin damuwa Baba ya tura kekenasa ya fita daga gidan, daman haka yake idan zai tafiya mai nisa saboda baya iya taka kafa sai ya hau kekensa a maimaikon yai tafiyar da sanda, baya damuwa yace dole sai yaje da yayansa sun turashi ko su rika shi, ganin duk yayan nasa mata ne sa maza biyu da basu gama tasowa ba. Da kansa ya tari Napep bayan ta tsaya ya mike tsaye ya taka kafar a hankali ya shiga bayan ya fada masa inda zai kai shi, mai nepep din da kansa ya fito ya kama keken Baba ya nade ta ya saka ta a ciki sannan ya koma mazauninsa ya kunna napep din.

  Har suka isa gida Baba be daina tunanin maganar da Gwarzo ya fada masa ba, idan har da gaske yace zai daure Halimatu to dukansu suna cikin matsala domin za a kara mata wata damuwar ne bayan wacce take fama da ita a yanzu, ga kuma mahaifiyarta wacce ta koma sai an kwantar idan zata tashi ma sai an rikata saboda ciwonta na hawan jinin da ya saka ta a gaba. Cikin rashin kuzari ya isa gida sai da mai napep din ya fito masa da kekensa sannan ya ciro 200 naira ya mika masa bayan ya shi canja ya kwalawa dansa karami kiran. 


“Abbah….”


Sai gashi ya fito da gudu. 


“Shiga da wannan kujerar koma ciki ka dauko min sandata”


A nan ma da gudun ya shiga ya da keken ya dauko sandar ya kawowa mahaifinsa sannan suka shiga cikin gidan tare, a kishingide ya samu Mama saman tabarma Aisha na mata fita kofin fura a gefenta an saka kankara a ciki domin ita kada take iya sha a yanzu sai kuma maganin da aka rubuto mata asibiti. Daga inda take ta daga kanta ta kalli Baba tana ganin yanayinsa ta san ba zai bada labari mai dadi ba, sai ta maida kanta ya rufe ido. 


“Sannu… ”


Baba ya fada sai ta daga masa kai a hankali, tana cizon baki tare da sauke ajiyar zuciya a hankali. Baba ya dubi Aisha 


“Aisha kin dawo?”


“Eh Anty Hafiza da Husna da Inna suna can”


“Ya jikin Halimatu?”


“Wallahi Baba har yanzu bata magana, bata san wanda yazo kanta ba, ko motsi bata yi idan ba su likitocin suka juya ta ba sai dai tai ta kallon mutane ko kuma tai ta bachi”


“Al-hamdulillah Allah mun gode maka, a nan din ma ba wani sauki, ina ganin mutanen ba za su bar maganar nan ba, ya tabbatar min da bakinsa cewar sai ya kaita kotu”


“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”


Mama ta fada a hankali sannan ta bude idonta. 


“Ka yi magana da shi?”


“Baya son saurarena”


“Ka yi magana da mahaifiyarsa?”


“Shi mai karar be saurareni ba taya kike tunanin mahaifiyarsa zata saurare ni?”


“Ita ai uwa ce zata fi shi hankali da tunani”


“Bana tunanin ba da sanin mahaifiyarsa ko izininta yake wannan abun ba”


“Idan ka yi min izini ni zanje nai magana da ita”


“Ba za su saurareki ba”


“Ba zan iya ganewa ba har sai na yi magana da ita, idan bata saurareni ba sai mu kai kararsu a gurin Allah”


“Taya za ki iya zuwa ki yi magana da ita Mama ke da baki da lafiya ma”


Aisha ta tambaya. Sai Mama ta unkura ta tashin zaune. 


“Zan iya Aisha ciwon Halimatu ya fi ciwona damu na”


“Tashi ki taro napep mu tafi”


“Da dai za ki ji magana ta da kin zauna domin ba za su saurareki ba”


“Da dai ka bar ni na tafi hankalina zai fi kwanciya”


“To Allah ya sa’a a dace”


Shine abunda Baba ya fita da shi, sannan Aisha ta fita da kanta ta taro mai napep din ta dawo ita da Teema suka rika Mama suka saka ta a napep din. Kamin su isa har ta gaji saboda ciwon zuciya da ba jiki, ba a hana su shiga ba kusan gate din gidan ma a bude saboda masu zuwa gaisuwa da kuma wadanda ba su gama ficewa ba. Mama bata taba zuwa gidan ba sai yau saboda rashin lafiyar da ya same ta tun daga lokacin da aka kwantar da Halimatu asibiti, daga ita har Aisha da Teema daman Inna ce da su Hafiza suke jigilar zuwa gaisuwa kuma suje asibiti gurin Halimatu. Da taimakon mutane dake fitowa cikin gidan aka nuna musu kofar falon Hajiya har suka isa. Sun tararda falon a cike da mutane hakan yasa Mama ta fara gaisuwar ta kansu kamin ta kalli wacce take zaton matar gidance ta ce. 


“Ke ce Hajiya”


“Aa ni yayarta ce Hajiya tana cikin bari a kira miki ita”


Wata budurwa dake kusa da ita zaune aka aika ta kira Hajiya, sai gata ta sauko babu dadewa waya makkale a kunnenta har ta zauna, sai da ta gama wayar sannan Mama ta mika mata gaisuwa tare da ta’aziya. Hajiya ta amsa tana mata kallon rashin sani. 


“Hajiya zan iya kebancewa da ke? Magana nake son yi da ke”


Jimm Hajiya tai tana kallonta kamin ta mike tsaye ta nufi dakin baki da ke kasa. 


“To sai ki biyo ni”


Hajiya na gaba Mama na biye da ita tare da Aisha wacce ta rikota har suka shiga dakin. Madaidacin daki ne mai dauke da gado da katifar kasa sai kuma wardrobe da yan kayan kwaliya kadan. A saman gadon Hajiya ta zauna mama kuma ta zauna a kasa sannan ta kalli Aisha tace. 


“Je can waje ki jira ni”


“To Mama”


Amsa mata sannan ta juya ta fice sai ya rage daga Hajiya sai Mama ne kawai a dakin. 


“Na san baki san ni ba Hajiya baki taba ganina ba, ba kisan inda na fito ba”


“Haka ne ban gane ki ba gaskiya”


Hajiya ta fada tana aje wayarta a gafen gadon tare da tattara dukan hankali ta fuskanci Mama. 


“Ni mahaifiyar Halimatu wacce kuke zargin ta kashe muku jika….”


Shiru tai na dan wani lokaci tana shawaye kamin ta cigaba. 


“Alfarma na zo nema gurinki Hajiya, kuma ba dan yata ta aikata abunda kuke zarginta ba, Wallahi yata mutuniyar kirkice ba, ba dab tana nawa ba sai dan zan iya shaidar halinta ko da ba yata ba ce, sannan na san ke uwa ce za ki iya jin abunda wata uwar take ji idan aka lakawa yarta sheri alhalin tana da gaskiya, kuna da arzikin da za ku iya hadawa da ni da ubanta duka ku daure amman ba shi nake son ki duba ba, adalci nake son ki yi danki kuma ki yi wa yata”


“Wane irin adalci? Dazun Gwarzo ya fada min cewar mahaifinta ya zo yana rokonsa ke kuma kin zo yanzu idan har da gaske bata aikata ba miyasa kuke ta magiya? Anya mai gaskiya zai yi haka?”


Mama ta daga kai ta kalli Hajiya hawaye na sauko mata. 


“Za ki iya ba ni kur’ane na rantse Hajiya? Wallahi ina zaune tare da ita a lokacin da jakarki ta fada rijiya, yara suka shigo da gudu suka fada mana cewar Namra ta fada rijiya, Wata kaddara ce take bibiyar Halimatu wacce ban san yadda zan kwatanta miki ita ba, ina tausayi Halimatu fiye da duka yayan da na haifa ni kadai na san halin da yata take ciki, bani da tabbacin rayuwa wata kila zan iya mutuwa yanzu ko anjima ko gobe amman ina son kamin na mutu na tabbatar yata ba zata je gidan yari da laifin da bata aikata ba”


“Idan har da gaske bata aikata ba to kotu zata bata gaskiya mu ta bamu rashin gaskiyar”


Kai Mama ta girgiza ta sake duban Hajiya tace. 


“Bari na baki wani labari Hajiya, kin taba haduwa da macen da akai mata fyade akai wa yarta kuma mijinta ya rabu da ita saboda tana kokarin kwatowa yarta hakkinta?”


A take fuskar Hajiya ta canja. 


“Wa aka yi wa haka?”


“Halimatu Hajiya….. ”


Babu abunda Mama ta rage daga labarin Halimatu sai da ta fayyacewa Hajiya komai tun daga aurenta da irin kalubalen da ta fuskanta har zuwa yau da wannan kaddarar ta mutuwar Namra ta fada mata, ba mama kadai ke kuka ba, wannan karon har da Hajiya da ake ba labarin sai da tai hawaye. 


“Amman kuma ita yarinyar kuka kasa kwato mata hakkinta?”


“Taya? Taya Hajiya? Taya za a kwato hakkin macen da mijinta ya karyatata ya gasgasta dan’uwansa akan yarsa? Mutun yarinyar kawai za a zubar a bata mata suna ita da mahaifiyarta”


Hajiya ta share hawayennta.


“Wannan ba hujja ba ce be kamata ku bar wannan maganar ba, kuka kokarin boyewa ne saboda gudun kunya, na tabbatar abunda kike kokarin boyewa na hana a bi wa yarinya hakkin kina kokarin daba wuka ne a ciwo, abun nan yana kasan zuciyarku ke da mahaifiyarta, miyasa za ku boye idan har za ayi wa mata da kananan yara fyade ana boyewa babu ranar da za a daina”


“Maganar ta dade da wucewa Hajiya, yanzu alfamar ki nake nema kar Halimatu ta sake shiga wani kunci”


“Zan yi mishi magana, za a samu mafita In-Sha-Allah”


“Na gode Allah ya kara sutura, Allah ya saka da alheri”


“Ita Halimatun tana can asibitin?”


“Tana can amman bata cikin hayyacinta”


“Gaskiya be kamata ku bar maganar nan ba, taya? Za a ketawa uwa haddi ayi ma ya kuma ku danne wannan bakincikin ku hade saboda gudun kunya?”


Mama ta unkura cike da karfin hali ta mike tsaye. 


“Na gode Hajiya na gode Allah yasa ki rike min wannan sirrin”


Cikin karfin hali ta fara takawa zuciyarta na mata mugun nauyi ta fice daga dakin.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

GOBE NA 9

Advertisement  *GOBE NA…* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy  9️⃣ “Wannan kaddararen aure yau Allah ya kawo karshensa, ni…

GOBE NA 4

Advertisement  *GOBE NA…* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy  4️⃣ “Sa’adatu kenan, kwana biyu ma kin daina dan lekowa,…

GOBE NA 20

Advertisement  GOBE NA…* By Khadeeja Candy  2️⃣0️⃣ DEDICATED THIS PAGE TO Mai Dambu, Allah kara miki lafiya Gwanata❤…