MATAN HAFIZ 11

Advertisement

11.

 Hafiz Yana fitowa daga wanka yaja dogon tsaki saboda har yanzu Fateema tana nan inda ya barta, kananan Kaya ya saka ya dauki filo ya bar mata dakin ya nufi falo, a yadda yake jin zuciyarshi yana tafarfasa zai iya lakada mata Dukan tsiya.


Daurewa Fateema ta yi ta Mike a hankali ta shiga toilette domin ta yi wankan sarki hawaye na ta zubo mata sai tsine ma Hafiz take a zuciyarta duk ranar da ya shigo hannunta zai gane baida wayo, zama ta yi a cikin baho ta tara ruwan zafi a ciki ta zauna ruwan Yana ratsa ilahirin jikinta sai da ta canza ruwa kusan so uku ta fito ta zura doguwar Riga tabi lafiyar gado tare da rufe ilahirin jikinta da lalausar bargonsu.


Wajen su Mufeeda kuma ta na cigaba da samun lafiya saboda mahaifinta  Yana bata kulawa na musamman shi da kanshi yake dubata. Yayi mata fada sosai a kan kada ya kara jin ta kara zuwa gidan Hafiz idan har ba zuwan arziki za ta yi ba, ta na kuka ta ce


“Yanzu Abba Haka zamu zuba musu ido muna gani su kashe mana dan uwanmu da bakin cikin su?”


Advertisements

Dr Ahmed yayi murmushi irin na su na manya ya ce,


“Ni na rasa wa kika biyo wajen tsiwa, koda yake na san wa kika biyo yana magana yana kallon matarshi ta kasan ido ita bata ma san Yana yi ba abin duniya ya bi ya isheta, Na dai fada muku kada wacce ta kara zuwa gidanshi da sunan tashin hankali tunda jikin naki da dama zan rubuta muku takarda sallama ki Kira Abdul ya zo ya tafi dake Allah ya tsare gaba ya na gama maganar shi ya bar dakin bai tsaya jin ta bakinsu ba”.


Ashe tun bayan wannan rigimar da ya faru Zainab ta bar gidan babu Wanda ya tsani saboda fargaban abinda zai je ya dawo, ita Heema bata ma sani ba sai hidimar yaranta take saboda zaman Hajiya a asibitin yaran nata suka dawo hannunta, kullum direbansu yake kaisu makaranta ya dawo da su hakan yayi mata dadi sosai saboda tana kaunar yaranta, Yauw take sa ran dawowar mijinta Hafiz ba ita ce za ta karbi girki ba saboda da za su tafi a dakinta yake, har karfe sha daya na safe bata ga Zainab ta fito domin shirya mishi abinci, abun ya daure mata Kai sosai. To wai ita Zainab ita take zuwa ne tun da farar safiya? Saboda ta rage zama falon tun bayan fadan da suka yi da Mufeeda Kai ita ta jima bata ji motsinta ba, mikewa ta yi ta nufi bangarenta ta kwankwasa kofar taji shiru ta shiga Kiran Sunanta nan ma shiru, sai kawai ta basar saboda sanin halin ita Zainab d’in da tayi da ranin hankali watakila tana jinta ta yi mata banza, Kitchen ta wuce ta fara aiki tana yi tana wutawa har ta shirya masu dabun kuskus da zogale sai dabun nama Kadan da lemun zobo da abarba da kunun gyada gidan ya gauraye da kamshin abincin da ta dafa karfe Biyu ta gama komai ta jera su a dining tebl, ta gaji Sosai direct dakinta ta wuce domin ta yi wanka ko taji dama dama, ta na cikin saka Kaya Sulatana ta shigo dakin tana cewa


“Mami kinga Sultan ko marina yayi ban masa komai ba tana goge  hawaye”.


Yi shiru kinji zan rama miki, ta rike hanunta suka fito tunda Sultan ya ji motsin su ya boye bayan kujera, yaro kayi ka gama ka fito naci kaniyarka bakada aiki sai jibgar mini yarinya,


 “Watakila laifi ta yi masa Mman yara”

  

Advertisements

Da sauri ta kali kofar shigowa Hafiz ta gani Yana sakar mata murmushi da gudu Sultana ta ruga wajensu tana dariya daukarta yayi ya Ida shigowa falon mai gadi ya ajiye jakukunan su ya juya ya fita, Takaici ne ya rufe Fateema ta wuce bangarenta ko gaisuwar da Heema take mata bata amsa ba. A hankali Heema ta isa wajen Hafiz cikin muna ta rungume ta da sauri ya janyeta Yana dariya saboda ta manta da cikin jikinta hannunta ya rike suna shirin shiga dakinsu Sultan ya rungume Abban sa Yana ihu da dariya juyawa Hafiz yayi ya tsuguna ya kama kunnensa ya ce,


“My boy ka daina rashin ji kaji Sultana kanwarka ce ka daina cin zalinta ko laifi tayi maka ka sanar da Aminka kada ka daketa”


Daga ma mahaifinsa Kai yayi saboda shima abin yayi masa ciwo daga baya, daga Haka ya koma falo suka cigaba da  Wasan su shi da kanwarsa. Girgiza Hafiz yayi ya kashe ma Heema ido daya Yana jifanta da wani kallo, tunawa ta yi da cewa yauw ranar girgikin Zainab ce ta rada mishi a kunne nan da nan fuskarsa ta canza ya shiga dakinsu ya barta nan tsaye tare da binshi da kallo. Da sauri ta bishi ita ma ,Ta na shiga dakin ta hagoshi kwance  saman gado idanunshi a lumshe kamar mai barci, iskan bakinta ta busa masa a fuska yayi shiru ya kyaleta bakinta ta manna cikin nasa ta shiga tsosa a tana lumshe idanu kamar mai barci maida mata martani ya shigayi amma bai bude idanunshi ba kokarin janta yake ta tureshi tana dariya, shi ma dariyar yayi saboda ta tsokano shi da yawa, wanka zaka yi ko abinci zaka fara ci? Ya ce mata


“Ina ga wanka zan fara yi domin naji dad’in jikina duk kasala nake ji kuma kece sanadi, idan na kamaki hmmm zaki gane kurenki”


Dariya ta yi ta bar mishi dakin domin ya samu yayi wankan, ta iske an shirya yaranta sunyi kyaut sosai cikin kayan shan iska musamman Sultana wacce babu inda ta barota wajen kammanni, abinci ta zuba musu suna ci suna ci. 


A hakan Hafiz ya iskesu yaji dad’in hakan sosai dama ace farincikin nan ya dawamma a gidanshi har karshen rayuwarshi amma ina da kamar wuya. Mikewa ta yi ta ja mishi kujera ya zauna ta shiga zuba mai abincin,


 “Abban Sultan ko na Kira Fateema ne muci tare ? Ita Zainab fa ina ganin bata gidan kwana biyu na daina jin duriyarta, nayi tunanin ko rufe kofarta ta yi na buga naji shiru, dan Allah ka kirata muji inda ta tafi”


“Kin san Allah Heema idan kika kara kawo min maganar Zainab zan miki abinda baki taba tunani ba, ita kuma Fateema kyaleta da tana jin yunwa ai da ta fito ki zauna muci kin tsaya magangganu marar kan gado”.


Yana gama maganar ya janyo plant ya fara ci Yana santi saboda girkin ta mishi dadi sosai, tsuke bakinta Heema ta yi bata kara kawo mishi maganar ba. Ta zuba dabun naman Kadan ta fara ci, suna gamawa ta kwashe kayan zuwa Kitchen inda tace mai aikinta ta gyra Kitchen d’in kuma ta zuba abinci ta kaima Fateema a dakinta, tana saye ta dawo abinci na hannunta ta ce,

“Hajiya cewa tayi ba zata ci ba saboda bata san abinda kika saka mata ba a ciki”.


Ikon Allah shi ne abinda ta furta a cikin ranta, ta bar Kitchen d’in saboda bata so maganar ya yi tsayi a tsakaninsu, ta rasa gane me ya canza Fateema a lokaci daya a da ai tana bata girma amma yanzu sai wani kallon banza take mata da harara, Kai koma meye ita ta sani ni burna bai wuce Allah ya saukeni lafiya ya kuma kara mini sona a zuciyar Hafiz, falo ta zauna tana ta tunani a wannan halin Hafiz ya isketa ya ce,


“Heema Lafiya kike wannan tunanin Haka? Sai magana nake miki kin yi shiru” 


Kayi hakuri Abban Sultan addu’a nake Allah ya sa kafin ka koma na haihu, murmushi yayi ya lakaci hancinta ya ce,


“Hutun wata daya suka bani kafin hutuna ya kare Zaki haihu Insha Allah saboda kina cikin watanki na tara” suka cigaba da hirarsu na soyayya.


Fateema Yunwa take ji sosai shi yasa ta Mike ta hada shayi tana ta dauki wayarta tana Kiran kawarta da sanar da ita duk wukakcin da Hafiz yake mata, ta yi shiru tana sauraren hudubar kawar tata zuwa can ta cigaba da cewa gobe ta zo su wuce wajen bokan kawai saboda ita ta gaji da rainin hankalin Hafiz, da Haka suka yi sallama ta kashe wayarta abubuwa dayawa take ayanawa a ranta idan har burinta ya cika har ita uwar tashi da yan uwanshi ba za ta barsu ba. Saboda ko rantsuwa ta yi ba za tayi kaffara ba nan gaba za ta kara cewa Hafiz ya kara aure sabar rashin hakali irin na ta, ta rasa Wane irin kwakwalwa ne da mahaifiyar su Hafiz Macé bata da aiki sai umartar danta ya kara aure? Ai kafin tace Hafiz ya kara auren za ta yi maganin shegiya ta rufe mata baki.


Zainab tsugune take a gaban mahaifinta Yana mata fada sosai, sai kuka take tana jin zafi cikin ranta. Ita ma fa ta jimata amma sai fada ake mata a kan yar iska Mufeeda ta na kimtsa rashin mutuncin da za ta yi ma Mufeeda idan har ta koma gidanta, ta na cikin tunanin ta ji karar waya ta ruga dakinta murmushi ta yi da taga sunan Hafiz ta dauka tare da yin sallama bai amsa mata sallamar tata ba ya ce “Zainab na sake ki saki daya ta kurma wani uban ihu ta yi jifa da wayarta…



 *😍By 4writer’s Fasaha*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like