MATAN HAFIZ 14

Advertisement

4.

“Barka da yammaci baba” abinda Hafiz ya furtawa Mlm usman knn yayinda shi kuma ya amsa cikin fara’ar sa.

sam baba usman bai tuntubi jin farkon batu ba daga bakin Hafiz dan haka cigaba da cewa yai

“shi al’amarin rayuwar duniya da kuke ganinsa baqaramin Abu bane musamman in zama ya had’aka da mutum  kuma ace zaman nan na har abada ne to dole fa yau da gobe asamu wasu kura kurai daga juna wnn ya 6atawa wa wnn da Sani ko akasin hkn, dan HK har kullum zakuji anacewa ma’aurata ayita haquri a zamn aure dan samun dace ranar gobe qiyama,

 to zakaga wasu na cewa musammn ma sudin sabon aure ne zakaji suna fadin ‘to haqurin mi zasuyi da juna bacin Suna qaunar juna to bazasu gane abinda ake mgn ba sai yau da gobe ta gifta,

dan haka a rayuwa no condition is permanent,

 dadi bai daurewa haka wahala bata daurewa a rayuwur duniya” 


d’an tsagaitawa yai snn yadubi zainsb ya jefeta da tanbayar data sake hautsina mata yen ciki, shiru zainab tai tareda sunkwi da kanta, tsawa mahaifinta ya daka mata tareda maimaita mgnr da fadin “zainab nace ko zaki iya qara maimaitamun mgnr da kikai man anan gameda Hafiz?”!

Advertisements


cikin rawar jiki zainab ta dago bakinta na rawa tace 


“kayi haquri Baba wlh nama alqwarin bazaka sake jin ance ga abinda naiba”


” oh kenn dama mgnta ta zama gskiy danace qarya kike a maganganunki kan sakin da Hafiz yy miki ko?” 


matse qwalla tay takasa mgn kuma.


 gyad’a kai yai gamida juyowa gun Hafiz yace 


“kayi haquri d’ana dn Allah ka fad’amin gskian lamarin abinda ya faru kaida zainsb” 

Advertisements


batareda bata lkc ba Hafiz ya kwashe dud iriyar wutar da zainab ta jima tana rurawa a gidnsa gamida had’as@ da matars sa kan tana masa sace sace zuwa  raina  yn uwansa datai har kawo fadan dasu kai da qanwarsa da hukuncin daya zartar kansa Kn yaji zafin maganganun da taiwa hajiyarsa shikuma.


sam kasa mgn Mlm usman yai sai zuwa can yaja numfashi kamin yaita bawa Hafiz haquri gamida wanke zainab da fad’a  harda markuka 2 tasha da zazzafan ranqwashi aka, taita kuka abin ya hade mata 2, baban yayi rantsuwa muddin takuma hasala Hafiz ya saketa saidai tanemi dangin mahaifiyarta suci gaba da riqonts a bazawara wlh badai shi ba, sosai kuma yasa tabawa Hafiz haquri qafafu bibbiyu,

babu ynda za’ayi hafiz ya iya ja inja da lattijon arzikin nn aminin babnsa kuma,

dole tasa  ya haqura yace babu komi ya maidata,

baban kuma yaroqi Hafiz akan daganan yatabvatr yakai zainsb tabawa hjyr sa haquri, haka Hafiz ya tashi ya fice zuwa motarsa zuciyarsa Bb dadi dn gskia babu ynda ya iya ne da har abada da ya gama zmn aure da zainab sai kuma inaa Allah bai nufa ba, 


zee kuwa jiki na rawa ta kwaso akwatin kayanta ta fito tabude motan yafigeta da gudu  ya wuce sukahau hanya

batareda ya ko kalle taba.


Ita ko sai satar kallonsa tk ammsn kwarjininsa ya danne mgnr datake kokarin masa. Kofar gidsnsu (main house)

ya tsaida motan yaqi mgn kuma shi bai fita ba, ganin tana niyyar 6ata masa lkc yasa shi juyowa gamida watsa mata mugun kallo a hassale yace 


“koko saina sake maimaita mk abinds mahaifin nk yace kixo gidan kiyi dayake kwalwan kifi gareki ko?” 


da sauri ta gane nufinsa 


“Kayi haquri Dan Allah” 

ta furta gamida ficewa daga motar. 


ya bita da dogon tsoki  gamida dauke Kansa gefe yana fadin 

“mad woman kawai.


tayi rashin sa’a babu kowa gidan sai ‘yan aiki dan HK ta dawo ta sheda masa hjyn basu nan bayn ta shiga motar, baice nata qala ba yaja motar suka wuce gida aranta quta kawai takeyi dud zatay maganinsu shida uwar tasa sudai shigo hannun ta saisun zama soory wlh. 


tay sa’a babu kowa falon dan HK da sauri ta haye saman side dinta gamida sauke ajiyar zuciya dan daman tsoronta samu sauran matan nasa sugnta da akwati sufahimci wani Abu,shima dakinsa yawuce dan qagare yake yajisa yasakarwa kansa shower dan rage zafin da zuciyarsa ke masa, 


dudda abincin da fateema amarya ta shirya masa ta killacesa a dakinta bisa carpet tanata tsumayin dawowarsa saidai sanda ya shigo bata saniba  tanacen sun qule a cikin bedroom da qawar ta mufeeda cikin d’aki wanda ko minti 5 cikakke batayi da zuwa ba, 


Mufeedan tace “to nidai na fada miki ki tashi tsaye wlh inda kinji ance baison haihuwa to kikiyaye zuwa nn gaba inkin kamasa da hannunki saikiyata sambado yara wlh kicike gidan dasu dam ynda zasu gaji arziqin ubansu ynda yake da kudin nan haka ga aiki yanayi ga kasuwanci motors motors kala kala guy din fa yayi  kud’i kota Ina baida Case dasu kudi ay sune rayuwar dama, shawarace nake baki qawata wlh ynda kike babbar likitan nan kinsan kuma magunun da zakiyi amfani dashi kina sha, kada ki kuskura ki dauki ciki ynx kizama bora uwa waccen heeman kmr yadda kikaji zainab din tace”


 dariya suka kwashe dashi suka taba snn mufeeda tace “shiyasa nk sonki Qawata akwai iya bada Shawara mai kyau, yanda kikace HK za’ayi, ynx kmr nawa kike ganin za’a kaiwa malamin nn yaimana aiki kan Hafiz din ya zamana baida tunanin kowa da soyayr kowace mace a ransa a duniyar  nn hatta wann addababbiyar mahaifiyar tasa face ni??”


mufeeda tace “Kada ki damu saidai kin jini bari na wuce komi knn kyaji wayata” fateema tace to shiknn nima hutun dana dauka na amarci ya qare jibi zan koma aiki” 


mufeeda tace

” to ay koba komi kinsha amarci doctor temo dubi yadda kike ta qyalli fa, dariya suka kumayi tare tawuce itakuma tahau duba kayan dazata saka Dan bata jima da fitowa wnka ba, nan akabi aka cancada kwalliya a fuska, balaifi doctor fateema itama masha Allah tanada kyaunta, wata farar atamfa tasa dinkin buba doguwar riga, snn takashe d’auri tajawo wayarta danufin kallon lkcn dawowar Hafiz din.

” to miya tsaidasa yau?” Tanbayar dataiwa kanta knn tana dogon nazari, 


‘daammmm!!!!


wata zuciyarta ta buga bayan cewa Mata datai kodai yana can tareda wata ne? Dasauri ta miqe tana zagaye dakin tana fadin Kay INA bai yuyuwa, dasauri ta nufi window din dakin taleqa motor park, to gadai motoci nan iri2 ciki hadda ta sojoji Amman tarasa tantance da wacce ya fita bare tai tunanin koya dawon bata sani ba.Heema CE baje cikin dakinta komi ya hargitse a cikinsa can undie can bra can pant can kayan daud’a komai dai barkace , Amman Sam takasa kimtsawa Dn rabon dakin yaga gyra tun zuwan yan gidansu, tsoki tai matsalr Hafiz yaqi ajiyemusu mai share sharen dakuna iyaka saidai mai share falo dasauran wuraren gidan. dancewa yai daki Sirrin maishi ne kowata gyara nata, samutai tamiqe daqyar tadan  tsince kayan daudan takaisu cikin matching ta tsubesu, Amman batun sharar dakinma ko zomata arai baiba Dan tun fitar Hafiz tadawo daki ta kwanta tanata dannar wayar ta ibada sai ynx da caji yaqare ta haqura ta ajeta ta sata a cajin.

rabon ta da wanka yau 2 days knn gashi sai faman kartar kay takeyi Wanda yajima a kwance shima bakitso ba kula, samutai ta sharce kan ta qullesa dudda ba gashi gareta ba tabarsa ya kakkabe Amman yana iya yin parking harda dan saura,

 d’an martabar cikin jikinta ne yasa gashin yafara dawowa sakamon da dayabi ya kakkabe SBD qazanta ko parking baiyi.

 Samu tai tayo wanka Sama Sama koda ta fito tsane jikinta tai batareda tashafa maiba bare turaren dahar ynz batason qamshinsa, tazura rigar ta doguwa a sharp ta yadin material ja ta fice falo dan yunwa ta isheta. 


bataga komi ba a dining tsoki tai tarasa gane cikin zainab da fateema wakeda girkin bai ba,

sabida tsabar wulaqanci abar mutum da yunwa. 


Kitchen ta wuce tahado madara da snack ta tsaya ta ci ta koshi snn ta fito falo, ta zauna. 


ko minti 5 batayiba da fitowa saiga zainab ta fito anci wanka na wani tamfatsetsen less Riga da siket sai qamshi take bulawawa abinta, 

tafiya tk cikin takun isa tana waya da qawarta tana fadin 


“to shiknn saina jiki goben kishigo pls ramla akwai mgn OK by saina ganki”. 


katse kiran tai ta zauna kujerar dake facing herma ta dubeta ta tave baki tana cigaba da taunar cwingum yanata qara Qas Qas, takaici taji ganin cikin heema sai barazanar shirin fitowa duniya yake, aranta cewa tai 


“hmnn basai kin haifi d’an cikin naki da ranshi ba, target dina na farko kan cikin jikinki zai fara heema dan bazai yiyu inaji ina gani kicika gidan hafiz da ya’ya ba niko babu amo babu labari, kamin najuya kan waccen dayar shashar matar tasa(tana nufin fateema, Niko nace hmnn zee fatimar da kikasani bata ynz ba Amman dai bari muga ko matan Hafiz din zasuyi nasara kan mijin nasu a junansu) 

“Hey sannu hjy hema mai ciki yakikaji da qwarin jikin?” 


abinda zainab tace knn wa hema a raine da kllon wulaqanci.  Kallonta hema tai dudda tafahimci da salon mgnr zee Amman saita share gamida furta 


“lfy” 

daga haka taja bakinta ta tsuke tamaida hankalinta ga TV tana kallon wani Indian film mai suna 

Asaka Tara(poris) munaqisan dake cikinsa a baqaramin mamaki takeyiba kodayake ba abun mamaki bane HK rayuwar take a koina.

Fateema ta fito daga daki ganin matan Hafiz zaune yasata mamakin toku yadawo ne?

zama tayi a wata one theater tana binsu da wani kallon raini tana tabe baki,

 wayarta ta fiddo tana buga game tanata sheqa dariya.

zee ta qufula damn taji haushin fateema datazo ko miqo gaisuwa baitawa kowace ba kmr ynda ta saba saima wani kallon banza dataga kmr tana musu, kodai idonta bainuna mata daidaiba?, danhaka fuska daure ta dakawa fateema tsawa da fadin 

“dalla malama daina mana dariyar hauka anan wnn ai wawanci ne tsabar kin rainamu kinzo kinsamu manyanki a waje ko sallma babu bare gaisuwa wnn yanuna ba’a samo  tarbiyya ba a gida ga alamdai gidan ku ba manya k….. tun kamin zee ta qarasa Fatima ta miqe afusace itama dantaji ciwon mgnr datai mata, tamayar mata da cewa ” ke saurara kece dai gidanku ba manya dan kowa kikaga tana zagin iyayen wasu to uwarsa da ubansa ya raina su, sanna ynz daidai Nike da kowace ‘yar iska wlh a gidan nan ynz ba da bace kowace tacemun kulle zan cemata cas koda dinma da kukaga inamuku lubbu lubbu  dannaga kamin luddenkune kuma nafahimta anyi walqiya ta haska mun Ku dan haka kowacce ta riqe kanta imba hakaba kuwa mukwashi yan kallo yanda kike taqama da kanki haka nike taqama da  nawa dan kinsan ko qashi zamu hada baki isa ki d’ibi komi a jikina ba bare su o’e kilishi ba abin sai kwadayin ayi cikin a haihu ba’asan ynda za’a kula da miji ba a faranta masa tayi mgnr tana jifan raheema da harara tana riqe da qugu. 


ko kallonta raheema bataiba amman abun yamata ciwo wato dudda suna abinsu bata samasu baki ba amman hakan baisa ta tsira ba knn saida aka gaya mata ba dadi? zee kuwa tsabar mamakin fateema yasata surrender tasaki baki kawai tana kallon ta, daqyar ta had’a yawu ta dubi heema tace 


“heema yaushe fateema ta koma tambadadiyar watsattsiyar yarinya ban sani ba wacce ta kwashe kayanta daga gaban manzo?”


kamin heema tace wani Abu sukaji  mgnr Oga Hafiz kamar daga Sama yana fad’in……

*By 4 writers fasaha*😍

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like