MATAN HAFIZ 16

Advertisement

16.

Kwance tashi Babu wuya a wajen Allah, sai gashi Ahmed ya cika shekara goma a duniya Yana aji d’aya a college, makaranta ce ta ‘ya’yan masu kudi makudan kudade malam Ismail ya biya kasancewar makantar kwana ce, acan ake Basu komai week-end kadai yake zuwa gida yayi shima wani lokacin baya zuwa, Ahmed Yana da kokari sosai saboda kullum na daya yake zuwa a ajinsu shi yasa malamai da dama suke kaunarshi. 

Tun daga kan Ahmed Allah Bai Kara Basu haihuwa ba, shi ya sa suke bashi Kulawa na musamman Kuma hakan Bai Hana su sawatar mishi idan yayi laifi.

Shekarar na juyowa malam Ismail ya baiyama iyalenshi gaba daya aikin haji harda surukansa da limamin unguwarsu, Kai ya sha addu’o’i wajen mutanen nan sosai ya nuna musu cewa Babu komai Komai mukaddari ne daga rabbil izati. Ahmed yana Kara girma a ko da yaushe kyawanshi yana Kara bayana kasancewa iyayenshi fulani ne gaba da baya, sai ya kasance shi ba fari ba koma ba Baki ba. 


Bayan shekara ashirin da shida abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda kammala karatun Ahmed na sacondry har ya fara University idan ya zabi fannin likita, mahaifansa malam Ismail ya Kara manyanta kokari yake ya sama mishi gurbin karatu a garin Madina saboda ya cigaba da karatunshi a can, Alhamdulillah kafin sati daya ya gama hada komai washe gari zai bar kasar. Misalin karfe goma na dare zaune yake a gaban iyayenshi inda suke mishi nasihohi na yauw da kullum irin ya rike mutuncinshi da darajar da Allah ya mishi Babu ruwanshi da kulla abokan banza, yayi karatun da ya kaishi kawai malam Ismail Yana gama jawabinshi cikin hikima ya goge hawayenshi ya kalli matarshi da tun da zu take kuka ya ce “Haba Hajiya lami ya zaki saka yaro a gaba ki dinga kuka? Salon ki karya mishi da zuciya yace ya fasa tafiyar, bana so ki daina addu’a zaki mishi Allah ya dawo mana da shi lafiya ya bashi nasara a kan abinda ya kaishi”.


Da kyar ta mishi addu’o’i tana son Ahmed Kamar ranta da tana da iko da ta Hana wannan tafiyar Amma Babu yadda za ta iya an fita iko. Bayan sun gama ya mike ya wuce dakinshi hawaye na zubo mishi shima tabbas zai yi kewar iyayenshi ba kadan ba da Haka har barci yayi awan gaba da shi. 


Advertisements

Washe gari misalin karfe takwas suna filin jirgi da wani takardu da ya kamata ya cika yayi saida jirgin nasu ya tashi suna dawo gida tare da kewar tilon Dan nasu.


Haka dai rayuwa ya dinga tafiya shekaru nata wuce wa har gashi yanzu Ahmed ya cika shegara shida a Madina sauran shekara biyu ya gama ya zama Dan gari kullum suna waya da mahaifansa karatun nashi ma yana tafiya dai-dai tun shigowarshi makarantar ya haru da wata yarinya ana ce mata ana ce mata Amina tana yawan zuwa ajinsu saboda yayi mata Karin haske a kan karatunta na banki tun Yana dari dari da ita har ya saki jikinsa, watarana idan bata zo bama sai ya shiga damuwa.  


 Wacece Amina? Amina Diya ce wajen Alhaji Anwar da Hajiya Khadija su biyu kawai iyayensu suka Haifa ita da kanwarta Kaltum, a kwai ta da saurin shiga rai gata da kyau  kun dai san larabawa Allah yayi musu ruwan kyau batada tsayi gajera ce Amma ba can ba tanada manyan idanuwa Masha Allah shekararta ashirin da hudu a lokacin, iyayenta suna zaune a garin Madina  sosai suke sonta Amina yarinya ce mai rawarar Kai idan har tana son Abu duk rintsi sai ta sami abin gata bata da hakuri ko kadan wannan shi ne kadan daga cikin tahirin Amina mahaifiyar Hafiz wannan kenan.

Wasa Wasa soyayya mai karfi ya shiga tsakanin Ahmed da Amina su kansu Basu San yadda aka Yi kawai tsintar kansu suka yi da tsananin kaunar juna. Ahmed Bai fada ma iyayenshi ba ita Kuma Amina tsoron fadi take saboda su larabawa basa auren wani jinshi Amma ta kudurta ma kanta duk tashin hankalin da za’a ba zata iya rabuwa da Ahmed saboda ko wanne bugun zuciyarta sonshi karuwa yake a ranta, kullum idan Ahmed ya ce zai zo gidansu sai ta nuna mishi iyayenta sunyi tafiya wannan abin yana damunshi sosai yauw dai ya sakama ranshi sai idan sun fita aji zai jirata ta fada mishi idan har da wata matsala ne ta sanar dashi.karfe biyar na yama bayan sun fito daga ajin karatu zaune suke a karkashin wani bishiyar mangoro wajen Babu hayaniya sosai ajiyar zuciya ya sauke ya ce,


“Amina wai me yasa Baki so na zo gidanku? Idan har kinsan baki Sona ki fada mini na kama gabana, ni ba yaro bane da zaki dinga wasa da hankali na. Ki fito fili ki fada mini abinda yake ranki yafi wannan boye boyen da kike mini ya ida maganarshi tare da hade rai.”


Cikin tashin hankali ta fara magana “Kayi hakuri Allah ba haka bane ta shiga fada mishi irin kallubalen da yake gabansu da yadda take iya kokarinta wajen ganin ta magance abin.”


Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, “Amina Ni dai kawai ki bani dama in zo gidan insha Allah Babu abinda zai faru sai alheri”. Da kyar ta amine akan next week ya zo. Haka dai abubuwan suka dinga wakana shima Ahmed iyayenshi sunki amince mishi ya auri Amina, a cewarsu me zai yi da larabawa su da ba’a musu kishiya ga hausawa Nan iri iri yace sai bare. Malam Saida ya je wajen megari tukunna mahaifansa ya amince ita ma Amina iyayenta sun amince saboda sakasu tayi agaba da kuka Bata cin komai.

Advertisements


Bayan shekara uku abubuwa dayawa sun faru ciki kuwa harda kammala karatun Ahmed da Kuma auren da yayi har Allah ya azurtashi da samun maza 2 haisam da nura sai Aisha,

  suna zaune a garin kano kasancewa a can aka turashi aiki. 

Aisha  tana yin shekara biyu aka haifi Hafiz tun Daga shi haihuwa ta tsaya musu cikin ikon Allah Hafiz Yana yin shekara shida aka Kuma samu Mufeeda bayan wasu shekaru aka samu Nabeela autar Mama kenan, yaran sun taso cikin tsananin kulawar mahaifansu su yaya nura sunyi aure da matayensu, itama Anty Aisha ta gama makarantar ta na jarida Daga Nan aka Yi mata aure tareda wani Dan kasuwa inda ya nuna shi Bai amince tayi aiki ba babu yadda ta iya dole ta hakura badan ta so ba, yaransu uku Imrane, Mubarak, Sudays. Ita ma Mufeeda ta gama school ta auri wani Dr Muhsin yarinyarta daya Aymana, ita Nabeela karatunta take Babu ruwanta da samari saura shekara uku ta gama Burinta ta zama Dr ta gaji mahaifinta. Hafiz ma ya gama karatunsa,

saidai a shekarar ne kuma karayar arziqi ta samu mahaifinsa doctor Ahmed sakamakon kudi daya zuba maqudai a harkar wani kasuwanci nasa da abokansa aka nemi abokan da kudin aka rasa shiyasa rayuwa take d’an gaya musu a lkc,

danma sauqinta yaya haisam da Yaya nura suna temakawa gidan nasu sosai dud in sun samu albashi ,(dashike teaching sukeyi)  


Hafiz tun Yana yaro yake sha’awar aikin sojoji da ya fada ma iyayenshi Basu hanashi ba addu’a suka masa Allah ya tsare shi yasa kuma burinsa ya cika, to dayake yanayin qasan tamu inba kanada wani tsayayye ba ko cin hanci a wasu wuraran to ba lalle aiki yazo ma da sauqi ba, shiyasa yahada da yan Neman nakan sa shima a lokacin bai zauna haka ba buga nan buga nan.

 hafiz haddaden saurayi dan kimanin shekaru talatin da biyu matashi mai jini ajiki Yan mata sai kawo tallan kansu suke Yana watsar da su saboda shi mutum ne mai son natsatsiyar mace Kamila mai addini da tsabta, dan alokacin bai kula kowa face heema dantun yana karatu ta tsaya jiransa batareda ta kula kowa ba dan sunyi alqawarin aure, farkon haduwansu yafara ne wataran tunda arziqin babansa yafito gidan nasu a mota daya daga motocin gidansu

wabda tuki yake a hankali Yana sauren karatun shek Sudays Yana bin karatun har ya wuce sai ya dawo baya ya tsaya kusa da ita, tana ganinshi ta kauda kanta ta cigaba da tafiyarta da sauri da sauri yunwa take ji saboda saukowarsu Daga islamiya kenan, ta sani naci wallahi dibeshi sai wani binta yake Kamar ya santa watakila irin mutanen nan ne masu bata diyan mutane mtsss taja tsaki ta shige cikin gidan su da gudu. 

Raheemat kenan Diyar Alhaji jafar da Farida ita ce ta biyu a wajen mahaifanta ta Kamala karatunta na Family economy tana zaman jiran aiki, tana da kyau dai-dai misali Bata fiye son hayaniya gata da son karatun novel shi yasa basa shiri da mahaifiyata saboda ita ta zauna tana karatun ko motsi Bata yi a shekara kiranta Bata ji, Momy ta tayi bugun har ta hakura yayarta da kanwarta kuwa haushinta suke ji. Wannan kenan


Ajiyar zuciya Hafiz ya sauke ya lumshe idanunsa saboda yarinyar ta tafi da ruhinsa juyawa yayi ya ahiga motarshi ya tafi da nufin gobe zai dawo koda za ta wulakantashi ne shi dai kawai ta saurareshi ko hankalinshi zai kwanta.


Agurguje, haka dai Hafiz ya dinga tsintirin zuwa gidan su Raheema tun tana fitowa da kyar har ya shawo kanta. Soyayya sosai suke ma junan su tamkar su hadiye juna, to ana cikin hkn kuma sai wnn ibtila’e ya fadawa arziqin babnsa, 


to a iyayensu suka shiga maganar ba’a dauki wani lokaci mai mai tsayi ba aka daura musu aure abinsu cikin rufin asiri da temakon ‘yan uwa na Hafiz din…


*By 4 writers fasaha*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like