MATAN HAFIZ 17

Advertisement

17.

Iyayen Raheema sunyi rawar a zo a gani, saboda sun Kawata gidan Raheema kujeru ma seti biyu aka saka mata a falon kasancewa yana da girma sosai dakuma shida ne sai katon falonsu bayan yan kawo amarya duk sun watse sai yaba tsarin gidan suke.              Bayan Hafiz ya sallami abokanshi ya shigo

gida sakiyar gadon ya hangota  sai kuka take, da sauri ya karaso wajenta ya rungumeta yana lallashinta ya mikar da ita tsaye suka shiga toilets domin yin Alwala dan gabatar da nafila. Wannan daren dai Hafiz ba zai taba mantawa da ita saboda sun raya daren  Heema tasha Albarka ba adadi. Wani irin kulawa Hafiz ya dinga bama Heema burinsa ya faranta mata dudda dai bashi garesa a kokcn ba Amman yana qoqari, sunga rayuwa suma ,sosai hema tai haquri da yanayin samun mujinta in an samu ayi in ba’a samuba kuma a haqura,  kullum suna manne da juna , komai tare suke yi. 

Inko zaya fita qwadago harda  kukanta da kyar yake lallashin ta ya tafi ta zauna bisa daya daga cikin kujerun falonta ta yi tagumi da taga kadaici zai dameta sai ta kunna daga tayi sa’a kuwa an turo littafin da take mugun so nan fa ta fara karanta wani lokacin tayi murmushi ko tayi dariya ita kadai har karfe biyu tayi bata sani, da sauri ta kashe datar ta shiga toilets domin yin Alwala. Haka dai Rayuwrsu ta cigaba da tafiya tun Hafiz yana yi mata fada a kan ta rage karance karancen littattafan da take har ya zuba mata idanu yaga iya gudun ruwanta suna cikin wannan halin ta fara laulayi sosai take shan wahala musamman cikin dare kwana take taba amai sai da cikinta ya shiga wata shida ta samu kanta. Daga nan ta cigaba da sana’arta wato karatun falon nata ma sai tayi sati bata gyara shi ba , dakin barcinsu kuwa sai dai Hafiz ya gyara da kanshi ita bata da aiki sai tayi wanka taci ado ta zauna falo so uku abincinta yana konewa har fushi Hafiz yayi da ita duka da ta gyara Amma a banza a haka dai wata ranar juma’a Allah ya sauketa lafiya ta samu bby boye kyakyyawa dashi ranar suna yaron yaci sunan Sultan, saboda Hafiz ya nuna bai amince taje shan kunu gida sai mahaifiyarta ta aiko mata wata dattijuwa ta cigaba da bata kullawa na musamman, gidan ya gyaru sosai saboda matar kullum cikin aiki take bata gajiya ko kadan har Hafiz yaji aranshi dama ta zauna tare dasu ne. Heema tana yin arba’in Inna Rumana ta tafi kafin sati ungulu ta koma gidanta na tsamiya wato kazancin Heema ya dawo wataranar asabar sabar  Takaici Hafiz ya mike yana gyara falon sai sallamar Mahaifiyarsa yaji abakin falon tashigo, subahanallah ni Amina me zan gani? Wato Hafiz sabar iskanci Yar aikinta ka zama? Yana shirin yin magana ta daga mishi hannu, yi mini shiri ko naci mutuncinka yanzun nan marar hankali tsoko kawai, ta juyo tana balla ma Heema harara ko gausuwar da take mata ma bata amsa ba tace, “Raheema ce wace irin mata ce marar tunani da sanin ya kamata? Kina zaune mijinki yana aiki tsabar lalaci da rashin sanin ciwon Kai to tun wuri ki gyara tun lokaci bai kure miki ba tana gama fadar haka ta wuce ta tafi tana ta fada”. 


abubuwa dayawa dai sunata faruwa a lkcn harda na farinciki, domi kuwa arziqin mahaifin Hafiz yadawo sakamon abokansa nan guda 2 Alhj sabe da Alhj muttaqa sun dawo masa da dukiyarsa hrda riba ba adai(Ashe dasukaje qasan waje wani baban business sukai da kudin kuma sun fidda layukan da za’a samesu sbd ayanda sukaji lbrn business din bakaramin kudi ake qara samuba shiyasa sukabace 6@t basu ba labarinsu don niyyrasu su dawoma da mutumin kirkin abokin nasu doctor Ahmed surprise dan dukiyarsa tafi tasu yawa aciki ba kadan ba kuma gashi kuwa. Familyn Alhj Muhammad farinciki da gidiyan Allah babu tsagaitawa kuwa da sukai a lkcn. 

kankance mi arziki yadawo mazauninsa, a kuma shekarar ne Hafiz yasamu aikin soja kuma a babban muqami,snn gefe guda ga kasuwancin da sukeyi da mahaifinsa da sauran yayunsa da suma a lkcn sunbar aikin teaching sun zama manya manyan ma’ikatan gwamnati.


gida hadadde gari guda haifiz ya gina Wanda babu ne kawai babu a cikinsa sultan da mamansa gata suke ta sha gun oga Hafiz dan a yanzun kam basuda matsalr komi na matsin rayuwa sai jin dadi, 

wata safiyar juma’a heema ta tashi da ciwon Kai zazzabi mai zafi gaske tana zuwa asibiti likitoci suka tabbatar mata da cewa tanada shigar ciki har tsayin wata biyu tayi mamaki sosai da bata gane cewa tanada shigar sa ba.

Advertisements

nan ta kama kumbure kumbure har ta isa gida ta fada ma Hafiz yayi murna sosai saboda Hafiz yana son yara yayi mata kashedi cewa kada ta kuskura ta salwantar mishi da yaro idan ba haka ba zai saba mata badan ranta ya so ba. 


Haka dai ta cigaba da kulawa da yaronta Sultan yana da wata takwas ya cire kanshi nono haka dai abubuwa suka dinga da wakana wata ranar Alhamis Heema ta tashi da nakuda wannan karon bata wani sha wahala sosai ta haifo bbyn ta mace mai kama da Mahaifinsa ranar suna aka rada ma yarinyar Sultana. Tun bayan haihuwar sultana abubuwan suka Kara rincabe mata har watarana Mahaifiyar Hafiz ta zo gidan tana shigowa falon ta koma da baya da sauri saboda wani irin wari da kazani da suka yi mata sallama falon ya baci kaca kaca. Wayarta ta ciro ta Kira Hafiz tace mishi duk abinda yake ya zo gida tana jiranshi ba’a dauki lokaci mai tsayi sai gashi baima gyara parking motarshi da Kyau ya zo wajen Mahaifinsa yana tambayar ta lafiya?” Magana ta fara yi cikin takaici da bakinci “Hafiz ni wacece a wajenka?” Cike da manakin tambayar ya ce “Mahaifiyarta!” Ta ce “To idan har ka daukeni a matsayin Mahaifiya ina so ka Kara aure nan da sati biyu sati biyu kawai na baka ba shawara nake baka ba umarni ne ta sa Kai ta tafi”. Ko motsin kirki Hafiz ya kasa yi yana mamakin wannan lamarin, da kyar ya daga kafarshi ya shiga falon ai da sauri ya toshe hancinshi saboda wani irin kazani da falon yake, Sultana da Sultan duk sun bata falon ita ko Heema sai shating take tana murmushi bata ma San ya shigo ba, da sauri ya fisge wayar a hannunta yayi gifa da ita, tana Shirin magana ya balla mata wani uban mari kafin ta dawo hankalinta ya Kara mata wani ta dafe kuncinta tana kuka sosai ta ce”Hafiz ni ka mara?” A zazzafe ya ce “An mareki din nace an mariki ko za ki rama ne? Sakacinki da rashin hankalinki ya janyo mini auren da Ban shirya ba, Ni na kasa gane ce wace irin mata ce? Kalli falon ki yadda ya koma sai ka rantse yayi wata uku ba’a gyara ba, dubi yadda yaran nan suka maida mini falo ko ina jurwayin futsarin su, tana Shirin magana ya daka mata tsama duk ilahirin jikinshi rawa yake idanunshi sunyi jajawur, wallahi kinji na rantse zan nada miki dukan tsiya idan kin bude mini bakin naki, me zaki fada mini? Yayi kofa ya juya ya nufi waje” da karfin tsiya ta daga murya yadda zaiji ta tace “Yo kayi auren mana Dan Allah ka auro mata goma idan ka isa marar mutunci kawai azzalumi Kuma ban yafe maka ba Marin da kamini ta fashe da wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro” yana jinta yayi banza da ita saboda yana komawa wajenta zai halakata a yadda yake jin zuciyarshi tana kuna shi yasa ya kyaleta ya shiga motarshi ya koma wajen aiki tare da damuwa mai tarin yawa, shi ba wani yan mata yake kulawa ba ballai a Kai ga maganar aure. Saida Heema tayi kukanta mai isarta ta mike ta gyara falon sab ta kunna turaren wuta ta yi ma yaranta wanka, ta shirya su suka zauna a falo tana Basu Madara da biredi wayarta ta dauka taga duk ya tarwatse ta Kara fashewa da wani uban kukan tana yi ma Hafiz Allah ya isa. Hafiz yana zaune a falonshi sai Mahaifinsa ya kirashi a waya yace mishi idan ya tashi daga aiki ya je ya karbo mishi sako wajen abokinshi, haka ko akayi karfe shida ya wuce gidan ya amso sakon a nan ya hadu da Zainab Babu laifi ta hadu yaji ta kwanta mishi a rai ba’a dauki lokaci mai tsayi aka daura musu aure Zainab ta tare a gidanta. Tunda Zainab ta shigo gidan Heema ta canza kadan tana kokartawa wajen gyara falonta ba kamar da ba Amma babu abinda ya canza gameda karance karancenta littafinta kullum nemanta Zainab take ita kuma bata kulata sai hidimar yaranta take, shi ne watarana bayan ta daki yaran da gudu Zainab ta Kira Mahaifiyar Hafiz ta sanar da ita saboda dama ta tsani ganin yaran a gidan hajiya Amina tana zuwa ta tafi da yaran wannan abin ya ma Zainab dadi sosai. Kullum maganar Hafiz yashe zai samu kwanciyar hankali a gidanshi. Wannan kenan.


*Cigaban labarin*


Innalillahi wa’inna ilaihin raji’un shi ne Abinda Raheema take ta nanatawa sanda take shirin saukowa daga bene,(dan tun bayan futan Hafiz gidan bata sake safkowa ba kasan said ynz dataji zuciyarta tasamu sassauci daga 6acin ran su zainab dasuka cusa mata hour kusan 7 dasuka wuce  itada Fatima a hatsaniyarsu,)  ynx ma tunawa tai d’ayar wayarta na falon Inda ta tashi mafarin fitowarta knn santsi ya kwasheta saigata ta gangaro kif a kan karamin tayin cikinta, qara ta sake saki duk ta jike da gumi tana ta cizan yatsa, Hafiz ko dayashigo gidan a lkcn dasauri ya qaraso a rude ya riqota sai  sannu yake mata bata ma san Yana Yi ba saboda duk ta fice haiyacinta, wani irin murdawa cikinta yayi ta kurma wani uban ihu tayi Baya luuuu ta fada saman Hafiz idanunwanta suka rufe jikinta yayi sanyi.


 da karfi tsiya Hafiz ya shiga girgizata yana kiran sunanta mma Ina ko motsi Bata yi ba. dan girman Allah Heema kada ki mutu kibarni sune kalaman da yaketa nanata wa, ita dai Heema gata nan shimfide a tsaikiyar falon numfashin nata ya tsaya cak…

kankacemi saiga zainab da Fatima sun fito jin Qatar heema, waro idanuwa Hafiz yai qirjinsa ba bugawa sakamon jini dayaga yanabin qasan heema yana malalowa yayinda zuciyar zainab kmr ammata albishir dantasan tsinanen cikin ne yake ficewa daga gidan.


tsawa Hafiz ya dokawa fateema dacewa 

Advertisements

“Ina amfanin likitancin naki da baziki iya  mata wani taimakon gaggawa ba kike nufi komi?”!


 Kamin Fatima tayi wani yunquri haba tuni harya sunkuci heema batareda da damuwar jinin sake binsa ba yayi waje da ita hankali tashe yakejin bazaima iya jiran wata fateema  ba…


a hargitse ya iso hospital din mahaifinsa…

*By 4 writers fasaha*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like