MATAN HAFIZ 7

Advertisement

7.

     “Ke kad’ai ce mace a gidannan ne? Ko a kanki aka fara kishiya?

Ita Heemah bata da raine da tayi hakuri ta danne abinda take ji sai ke zaki d’agawa mutane hankali.

Da ba a yi ke za a kawo ki?

Ko kin manta kema zuwa kikayi kika samu wata?”


Cikin hasala ta d’aga mishi hanu.

“Ni ba wata ba ce, ni Zainab ce kaga kamar yadda suna suka bambanta haka ma halayya.

Ni ba irin lusaran matannan bane da basu san muhimmancin mazajensu ba.

Advertisements

Ina son mijina kuma ina qaunarshi dole in nuna kishina kan abinda nakeso.

Ko ka tab’a ganin anyi kishi kan abinda ba a so?”


Abinka da shaid’an da a ko da yaushe bibiyar al’umma yakeyi yaga tab’arb’arewarsu.

Take zcyr Hafiz ta fara ayyana mishi cewar yanzu Raheema ta daina sonshi shi yasa bata kishinsa.

Wani irin b’acin raine ya ziyarceshi ba shiri ya daka mata wata uwar tsawar da saida ta razana yana cewa.


“Get out of my room idiot.”

Gaba dayansu haushinsu yakeji.


Da gudu zainab ta bar dakin dan ba karamin tsorata tayi ba.

Dakinta ta shige ta fada kan gado tana rabza kukan bakin ciki.

Advertisements


Ko ta kansu bai bi ba washe gari ya fara shirin tafiya.

Su ma d’in babu wacce tu kulashi a cikin su.

Abinci ma a ranar a gidan su yaje yaci ya kuma samu ya zauna da yaran shi sosai suke rage mishi b’acin ran da yakeji.


Sallamar tafiyar ma dukansu sama sama yayi musu ya ajiye musu kud’i yayi gaba.*****


Fatima kam bata yarda mahaifiyarta ko cikin ‘yan uwanta sun gane cewar tana da wata matsala ba.

Saboda kawarta ta zo sunyi shawara kuma ta kawo mata mafita da take gani shi zai ficce ta .***


Duk da ango bayanan shirye shiryen biki akeyi ba kama hanun yaro daga gidansu ango da amarya.


Su kam Matan Hafiz basu san wainar da ake toyawa ba saboda basu sake ji daga gareshi ba.

Bai cika kiransu kamar da ba idan baya gida.

Saidai su su kirashi.


Wani lokacin kuma zainab ce take dagewa tayi ta wayar karya tana zuba shagwab’a idan taga Raheema kusa da ita.


Tun abin na damun Raheemah har ta fahimci iya shege ne kawai ranar tayi mata mai kankat.


Suna zaune ta dauki waya ta fara zuba kalaman soyayya a zuwan a na fada mata ne tana mayar da martani.


Kallonta Raheema tayi lokacin da ta katse tana murmusawa tace.

“Wannan shi ake kira isar da ba a isa ba.

Ni fa idan ban manta ba kin sha cewar kinfi karfin ayi miki kishiya, ni dinma kinfi karfin zama dani.

Sai kuma gashi nima na gagareki har kuma shirin karo miki wata akeyi.”


Kokarin kore kunyarta da hauka ta fara inda ta tuntsire da dariya tare da fad’in.

“Dadin abindai dukanmu biyu zaa yi wa kishiyar.”


“A yanzu dai zan iya cewa kishiya taki ce tunda nidai an riga da anyi min, kuma an dai karya alkadarinki , cika baki ya riga da ya kare sai kuma a ci gaba da karyar soyayyar waya da miji.”

Raheemah na gama fad’in haka ta wuce zuciyarta k’al ko ba komai ta d’an rage rad’ad’in da takeji a zuciyarta.


Tun daga ranar zainab tayi sanyi qlau a gidan.*****Tunda aka fara hidimar bikin ake zuba idon ganin ango amma har akaci aka sud’e babu alamunshi.


Biki kam ya kayatar dan dangin ango sunyi rawar gani sun nuna bajinta.

Uwar gidaye kuma sunyi iyakar kokarinsu dukansu biyu ba a samu wani tangard’a ta b’angarensu ba kasancewar suna tare da ‘yan uwansu masu basu shawarwari nagari.

Wa’azi da nasiha kuma sun sha su kamar ba gobe.


An watse biki lafiya inda aka bar amarya da uwargidayenta saidai babu ango.


Kamar yadda uwargidayen suke kokarin rike girmansu haka ita ma amaryar take nata kokarin wajen ganin ta basu girmarsu.


Ko wace wayewar gari sai tazo ta gaishesu da dad’daya , hakama takan fito idan taji d’ayarsu a babban falo ko a kitchen a kokarinta nason karantar yadda rayuwar gidan ke tafiya.


**** Kamar yadda ta saba zuwa gaishesu kowace wayewar gari hakama yau ta fara da d’akin Raheema kamar yadda ta saba.


Daga can ta wuce d’akin zainab.

Zainab dake dakon isowarta tayi saurin kara wayarta a kunne kafin ta yi sallama ta fara cewa.


“K’awata ai ina fad’a miki babu wata maganar kishi tsakanina da matannan.

abinda kema kinsan ni d’in ta dabance.

Itama fa amaryar kwana biyu zaki ji ana maganar ciki gareta abinda kinsan maigidan kuma baya so.

Daga haihuwa kuma yaya kike tsammani zata zama?

Kinga zata koma tamkar ita uwargidan komai a sassake, itama cikin k’ank’anin lokaci a juya mata baya kamar dai waccar.”

Saida ta d’anyi shiru na d’an lokaci snn ta d’an dara tare da cewa.


“Balle kuma kinsan ita kam ba wani sonta yakeyi ba, mahaifiyarshi ce ta tilasta shi ya aureta.

Kinga ko lekowa yayi ne?

inda zaki tabbatar da bata da fada a gurinshi kenan ai.”

fashewa tayi da dariya snn ta kara da cewa.


“Zata shigo gaisuwa yanzu Baiwar Allah, ni har tausayi ma take bani.

Zamuyi magana anjima bye.”Komawa baya Fatima tayi tana jin kirjinta na bugawa.

Lallai fa gwara da ta shigo yanzu ta ji wannan babban sirri.

Ashe shi yasa zainab take shanawarta kullum kaji tana waya da miji tana baza kalamai.


Saida ta daidaita nitsuwarta kafin tayi sallama ta shiga.

Gaisawa sukayi a mutunce kamar yadda suka saba har tana cewa Fatima mai gidan ya ce a gaishesu.


****Saida akayi sati guda da biki sannan Hafiz ya samu zuwa.

Rashin nuna marmarin shi kan amaryar ya tabbatarwa da dukkansu cewar da gaske dai ba sonta ya ke ba.


Ya dai had’asu yayi musu nasiha.

Daga nan bai sake kula amaryar tashi.

Ko da ya je gidansu ma saida umma tayi ta ja mishi kunne kan amaryar tashi tare da jadadda mishi cewar lallai da ita zai koma.


Ranar farko Raheema ce dashi, ta tanadeshi yadda ya dace.

Sai washegari zainab itama an shana sai rawar kai takeyi da fi’ili.

A rana ta uku yayi niyyar tafiya tare da amarya.

Tun dare zainab ta fara mishi complain na ciwon kai, washegari ta kwanta riris zazzab’i takeji.

sai surutai takeyi ita tasan kewarshi zai kasheta.

Kuka takeyi rurus da nuna mishi irin kewarshi da zatayi.

Ita tayi hakanne ko zai tausaya mata ya fasa tafiya da amarya ya tafi da ita.


Abinda bata sani ba hakan da tayi ya sa mishi tunani ne kan Raheemah.

Ya riga ya tabbata Raheemah bata damu dashi ba tunda ko da ya shiga gurinta bayan ya dawo masallaci har fatan zaman lafiya tayi mishi da fatima.

Gashi ko nuna damuwarta kan tafiyar batayi ba.


D’akin Raheemar ya koma ya sameta zaune ta d’ora kafa d’aya kan d’aya , hanunta rike da waya.

Yana da tabbacin karatun nata na jaraba takeyi da sassafe.

Ita bata da wani damuwa sai karatu kawai.


Kwace wayar yayi yai jifa da ita yana huci.


“Daddyn sultan lafiya?”

ta fada a tsorace.


“Raheemah wai wani irin mutuwar zuciya gareki ne?”

ya tambaya da kakkausar murya.


“Me kuma nayi?”

ta tambaya hawaye na taruwa a idonta saboda kalmar mutuwar zuciyar ya mata zafi.


“Ke wace irin mace ce da bata san muhimmancin mijinta a gareta ba.

Duba fa yanzu tafiya zanyi, baki san ranar da zan dawo ba, baki da masaniyar zamu sake had’uwa ko kuma rabuwar kenan har abada ,amma baki damu da wannan ba,!

Damuwar ki kawai karanta labaran banza, kima dauki na amfanin cikinsu kinqi to ina amfanin karanta abinda  bazasu amfaneki ba duniya da lahira…???”!!!!

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like