MY UNCLE 11

Advertisement

 Page 11

Aliyu yawani irin shagala da kallon hannayenta harta tura mishi abincin agabanshi baimasan anyiba saida takira sunanshi sannan yayi firgigit yana Sosa keya tareda kara shan omo yatsare gida , Aunty tayi wani irin murmushi irin nasu namanya Wanda ita kadaice tasan manufar yinsa 


Abincinshi yafaraci yana lumshe ido domin bakaramin dadi yayi mishiba hakama Pepe chicken din yaci sosai zobokam saida yaji ba’inda zaikara shiga sannan yasaurara mishi domin bakaramin dadi yayi mishiba 


Iman kam sai tsakurar abincin takeyi domin dama ita bama’abociyar cin abinci maiyawa bace bare ma yau datake jinta wani iri 


Salma kam tazage tana ta cin abunta ba abunda yadameta 


Advertisements

Salma ce tadan juyo tazo kusa dakunnen iman yanda bawanda zaiji tace da’alam abincinnan yayiwa mijinnan naki dadi domin naga sai wani lumshe ido yake


Iman tazabga mata harara tareda cewa Allah ya’isana muguwa ita dinma ahankali tafada yanda bawanda zaijita 


Yana kammalawa ya haura sama zuwa dakinshi 


Wanka yafarayi sannan yakwanta domin yanaso yadan huta aikuwa hakan bata samuba domin kiran salim ne yashigo wayarshi dan tsaki yaja sannan yadaga 


Ango ango kasha kamshi salim yafada ciki da tsokana 


OK dama kakirani ne domin kabatamin raiko Aliyu yafada 


Advertisements

A a bashibane nakira kane dama nace maka tunyanzu har amaryar tafara boye mana kai kashigo gari amma koka nememu kodayake banga laifin kaba irin wannan jarabar taka ai dole kasharemu tunda ansamu new world irin wadda ba’ataba jiba to bari kaji dan Allah kabimana kanwa asannu dan nasan halinka karkace zaka nuna mata halin sojoji yafada yana kyalkyalewa dadariya 


Dif Aliyu yakashe wayar domin salim yanason tadomishi da tsohon mikinshi daya jima baitashiba 


Tabangaren salim kam murmushi yayi domin koba komai yafadi abunda yakeso yafada 


Aliyu kam kwata kwata salim yarikita mishi lissafi sai juyi yakeyi yarasa abunda kemishi dadi Sai misalin 1:45pm yadauro alwala yanufi masallaci sanda yafito falon ma bakowa dan haka kai tsaye masallaci yanufa 


Yana fitowa daga masallaci yanufi yanufi gidansu family house


************

Su iman kam shirye shiryen bikin kawarsu suke ta islamiyya domin su ukku ne suke matukar shiri a ajin har sunkoma kamar yan uwa iman,salma,da kuma suhaila to ita suhaila dince zatayi aure dan tadan girme su iman da shekara biyu dan ita tayi candy kuma aka idar gidansu kana gama secondary akemaka aure 


To shirye shiryen bikin nata suke 


Ran Wednesday za’awanke Amarya 


Su iman kam sune agaba

Manya manyan kawayen amarya 


**********

Kwana yagagare Aliyu ciyon nashi yamatukar tashi yau sai juyi yake yana dafe Mara 


Saikusan asuba yasamu yadan kwanta amma yasha matukar wahala 


Wanda yayanke shawarar dolene yayi aure domin idan har abun yaci gaba datafiya ahaka to gaskiya shima yasan zai iya rasa ranshi 


********

Yau laraba yau za’ afara event din suhaila su iman har anshirya sai rawar kai akeyi sanye suke cikin wata pink gown tayi matukar amsar jikinsu musamman iman tayi kyau matuka tayafa gyale saikace yanmata   suna fitowa sukaci karo da Aliyu kallonsu yayi sama dakasa yakara maida kallonshi kan iman haka kawai yaji ranshi yabaci kan wannan shigar tasu


Suna gaisheshi amma ko ansawa baiyiba saima tambayar dayajeho musu 


Ina zakuje  da wannan shigar


Uncle bikin kawarmu akeyi suhaila ta islamiyya shine zamuje iman tabashi amsa harara yazabgamata 


Ina wasa dakune maza kuwuce gida ba’inda zakuje  wakuka tambaya dazaku fita

 

Uncle dan Allah kayi hakuri wlh idan bamujeba bazataji dadiba iman tafada kamar zatayi kuka 


Ke raini yafara shiga tsakaninmu ko ina fada kina fada to ance bazakijeba  salma wuce kije kekuma idan naga kafarki waje wlh sainayi mugun saba miki


Jiki narawa salma tafita itakam tunda ambata dama iman kam kuka tasaki tasheka tashiga falo aunty tatarar a falo dagudu tayi gunta tana kuka 


Ke lfy iman meyafaru iman aunty uncle ne wai bazanje bikin suhailaba aunty dan Allah kibashi hakuri yabarni inje tafada tana kara fashewa da kuka 


Dai2 lokacin da Aliyu yashigo falon 


Aunty takira sunanshi Aliyu dan Allah kabarta taje meyasa zaka hanamata xuwa 


Aunty kibarta kawai ba’inda zataje kuma kitashi maza kihadamin coppy yanzunnan inajiranki yafada yana haurawa sama 


Da harara IMA tarakashi tanafadin lallaima mutuminnan yarainani to wlh bazankaimishiba saidai yakasheni wannan wani irin abune adakeka ahana maka kuka 


πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MY UNCLE 20

Advertisement  Ψ§Ω„Ψ­Ω…Ψ―Ω„Ω„Ω‡   Ψ§Ω„Ψ­Ω…Ψ―Ψ§Ω„Ω„Ω‡  Ψ§Ω„Ψ­Ω…Ψ―Ψ§Ω„Ω„Ω‡ abokanai,dakuma masoya ina godiya sosai da addu o inku nagode sosai Allah yasaka da…