SHARUZZAMAN 1 PAGE 1

Advertisement

 *BOOK (1)*

      _SHARUZZAMAN_🌟

BINTU S££R_✍🏻

   Tsiririyar hanya ce tamkar gada da akayi da manyan katakwaye da rodina, qasan gadan wani qaton rami ne, ramin a bushe yake k’amas sai busassun ciyayi irin wanda suka saba fitowa a k’asar sahara, yawancin masu shiga k’asashen africa ta haramtacciyar siga ta wannan hanya suke ratsewa su shiga k’asa,  suma motarsu na bisa wannan hanya tana tafiya, motar cike take da bak’in haure, yawancinsu buzaye ne daga mabambamtan garuru daga cikin janhuriyyar nijar, wani babban abun tausayi shine har da yara da tsoffi a wannan tafiya mai cike da hadari, zafi ake sosai domin ana zagba rana mai zafin gaske kundai san yacce zafin rana yake a k’asashen sahara,

yawancin k’ishin ruwa itace ke dawainiyya dasu musamman yaran da cikin wannan tfy, ruwan da sukayi guziri yyi k’asa sosai sai chanchanen shi suke gashi ko rabin tfyr ma basuyi ba, tfy suke kawai cikin ikon Allah sai fama da gumi suke,   cikin hk har Allah ya basu damar haye wannan gada, nan kuma suka soma tfy bisa tur6aya na rairayin sahara,motar sai girgiza take da layi kamar zata kife ga tsananin zafin rana, babban tashin hankalin shine yadda yara da masu raunin cikinsu suka soma sumewa sbd k’ishin ruwa da tsananin zafi da kuma wahalar wannan tfy mai cike da rud’ani, wata dattijuwa na hanga sanye da wata babbar riga irin ta buzaye, matar fara ce sol mai kyau da ita duk kuwa da tsufan daya soma kawo mata farmaki tare take da surukarta wato matar d’anta saidai ita tsatson fulanin nijar ce ba buzuwa bace sai yara y’an mata biyu dake tare dasu, d’ayar bazata wuce shekaru sha uku ba alamun sun nuna itace babba, sai kuma d’ayar wacce take da shekaru sha d’aya dukkanin kama da kakarsu sukayi, suna da hasken fata da tsawon gashi mai santsi, suna da asirtaccen kyawu mai mutuk’ar d’aukar hnkli tamkar d’iyan aljanu gashi basu da yawan zance tamkar basa mgn, abun dana lura dashi a game dasu shine daga su har uwar tasu suna masifar shakkar kakar nan tasu, tfy dai motar ta cigaba dayi bisa rairaiyin sahara har rana ta soma shirin fad’uwa, dare ya soma ketowa daidai lkcin kuma motar tasu ta k’ame a wuri guda ta dena tfy, mutane suka soma salati da sallalami domin suna tsakiyar rairayin sahara ne babu motsin komai bare su sanya ran samu wani agaji, drivern motar yyi iyakar qoqarinsa amma motar tak’i tashi abunka da k’arfen nasara bashi da tabbas, yara da mata suka soma kuka hk suka kwana suka yini, ganin hk yasa fasijojin motar sukayi k’ungiya suka soma tfy a k’afa bisa wannan sahara a tunaninsu ko a gaba zasu samu wani agaji, tfy suke da k’afafunsu a cikin rairayin sahara amma cikin hukuncin Allah babu motar data biyo ta wannan hanya tun suna sanya rai har suka soma sarewa, dare yyi suka yada zango a wani wuri  gari na wayewa suka d’ora tfy, lkcin da rana ta fara kunno kai ne zance yasha bambam, mutane suka soma zubewa sbd zafi da k’ishin ruwa don gbdy ruwan guzirinsu ya k’are, tun suna tsayawa idan wani ya fad’i har ya zamto duk wanda ya kasa haka suke tsallekeshi su wuce saidai idan yana da yan’uwa su tsaya tare dashi, yara kuma idan sun kasa iyayensu su daukesu, tsananin wahalar tfy da k’ishin ruwa ne ya soma kisa a wannan tawaga, rana na takewa wahala da k’ishin ruwa na k’aruwa, daidai lkcin mahaifiyar wad’annan buzayen y’an mata ta zube, yaran nata sukayi kanta suna kuka suka rirrik’e, ba abunda take fad’a sai ruwa, ruwa, hk suka soma neman ruwa su bawa mahaifiyarsu amma basu samu ba, sauran tawagar kuwa gaba sukayi abinsu batare da sun tsaya tare dasu ba, kowa a wannan lkci k’okarin tsira yake da rayuwarsa domin kuwa cikin sahara suke babu gilmawar kowa, izzah wato kakarsu kenan ta kallezu kenan ta kallesu d’aya bayan d’aya tace”kun ga ku kyaleta kawai ku taho mu tafi karsu mana nisa da mu mace gbdy a nan tsuntsaye su cinye gawarmu gwara wasu daga cikinmu su tsira” kallonta suka tsaya yi cike da tsantsar mamakin furucinta, khadi itace qarama,  tace”kyallu ki tafi kawai ke amma mukan bamu tfy batare da  innaro ba” wata uwar tsawa ta daka musu ta finciko khadi ta hank’ada k’eyarta tare da damk’e hannunta sannan ta kalli rumana wacce take itace babba kuma alamu sun nuna kamar ita d’in kurma ce bata mgn shiyasa bata furta komai ba saidai tana rik’e da  mahaifiyar tasu k’am a jikinta, hannu kyallu tasa zata fincikota daga jikin mahaifiyarta ta tirje tayi gefe tana hawaye tana girgiza kai alamar bata tfy, harararta kyallu tayi tace” shegiyar yarinya sai ki zauna ki mutu ke da ita ai” jan hannu khadi tayi da k’arfin tsiya tana kuka sukayi gaba da sauri, khadi sai waiwayowa take tana kallon uwarta da yar’uwa tana kuka amma bata iya kwacewa daga rik’on da kyallu ta mata hk har suka 6acewa hange, rumana tana rumgume da mahaifiyarsu a jikinta tana kuka, zuciyarta cike da rauni musamman data ga kamar idanun innaro ya fara k’akkafewa, fashewa tayi da kuka mai sauti sosai tana girgizata,kamar ance ta d’aga idanu ta hango tahowar wani bawan Allah nesa sosai daga inda suke, sanye yake da k’aton farin rawani irinna buzaye hannunsa rik’e da sanda, k’ugunsa mak’ale da gorar ruwa, cike da al’ajabi take kallonsa har ya k’araso dab dasu, batare daya furta komai ba yasa hannu ya ciro gorar ruwan dake mak’ale a k’ugunsa ya mik’a mata, hannunta na masifar rawa ta kar6a gorar ruwa ta bud’e ta soma tuttulawa mahaifiyarta ruwan a baki sai lkcin ta fahimci suma innaro tayi saurin watsa mata ruwa tayi sannan ta shafa mata a fuska cikin izinin Allah sai gashi tayi ajiyar zuciya, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke cike da hamdala ta d’ago dakanta da niyyar yiwa wannan bawan Allah alamar gdy kasancewa ita d’in kurma ce bata mgn saidai ta nuna alama abun da take nufi da hannu ko da idanu, bisa ga tsantsar al’ajabi da tarin mamaki shine tana dago dakanta taga wayam babu wannan mutumi ba alamarsa, waiwaye ta somayi amma bata ga kowa ba, tana duba gefenta taga ya ajiye mata gurasa, har takai hannu zata d’auki gurasa saita janye cike da tsoro, abunda ta tabbatarwa kanta shine wannan mutumi ba mutum bane aljan ne, tsoro ne ya k’ara shigarta sosai tuni ta soma addu’oi, kowacce addu’a ta shigo bakina karatawa take, dubawa tayi gabas da yamma,kudu da arewa babu kowa babu komai sai shimfid’add’en rairayin sahara, suna nan wurin rana ta soma shirin fad’uwa sai gurasan nan tayi shahada ta d’auka ta bawa mahaifiyarta taci itama taci suka sha ruwa, hkn yasa innaro ta soma dawowa da kuzarinta,  duhu yana soma shiga suka mik’e suka soma tfy sbd sun fi ji dad’i tfyr dare, tfy suke sannu a hnkli kawai ba zato ba tsammani suka hango hasken wata k’atotuwar mota cike da kayan smuggling, sauri suka somayi su sauka bisa siririyar hanya da motar take suka ga tamkar 6ata lkci ne sai kawai suka kwanta suka mirgina suka gangare bisa hanya don daman a can sama da wannan hanya suke, tunkan motar ta k’araso suke d’aga hannu har ta k’araso wurin da suke, drivern yaja ya tsaya don tun daga nesa ya hangosu, innaro har da tsugunawa tana rok’on kan ya taimakawa rayuwarsu ya d’aukesu juyawa yyi kamar bazai d’aukesu ba sai kawai kuma ya juyo yace”bani da wurin sanyaku saidai a cikin kaya” cikin sauri innaro tace”ko a ina ne ma ka samu”  haskasu ya kuma yi da wata tsungureriyar tourchlight d’insa shida yaron motar sannan suka bud’e musu wurin kaya suka shiga suka takure shi kuma ya yaja motar suka soma tfy, Allah abun gdy cikin kwana biyu suka haye bodar dake tsakanin nijar da nigeria suka soma shigowa nigeria suka ratse suka shige birnin zazzau, a wannan gari na zazzau suka sauke innaro da rumana, basu san kowa ba a nigeria sun rasa ina zasu soma tunkara cikin fad’in garin zazzau, ranar a rumfar kasuwa suka kwana, washegari, suka shiga gari suka fara da bara…….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like