SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 13

Advertisement

 *BOOK ONE*(1)

6angaren amarya gimbiya bilkisu kuwa yau jinta take tamkar ta mutu sbd baqin cikin daya cunkushe mata zuciya, amarya jiddo ko don dole ta binne takaici da baqin cikinta a can qasan ranta ta soma sanya hannu cikin hidimar biki sbd tana gudun kar mai martaba yyi zaton tana yunqurin bijire masa ne, uwar qamshi hjy kulu d’an malikin zazzau ita ta baje kolin taskar qamshinta akan gimbiya, duk ta inda ta wuce saidai aji tashin qamshi, gyara kuwa mai sunan gyara jikinta ya amshe shi abunku da diyar gata kuma auren gata, safiyar ranar wani d’anye leshi ta sanya wanda ya had’iye dubban nairori, leshin kalar silver ne da ratsin ash, hannunta kuwa yasha awarwaraye da zoben gold, hkm sarqar dake wuyanta, bisa al’adar masarautar adamawa sai ranar daurin auren suke kawo lefe don hk ranar suka taho da lefensu a private jet, akwati ne dai dai har guda talatin da biya, set daban daban kowanne shaqe yake da kaya na mgn, na taqaice muku bayani al’qalamina har faduwa yyi sbd galala da nayi da baki ina kallon wannan ruwan dukiya da aka 6arnatar, wasu hamshaqan mata ne su shidda wadanda dukkaninsu isassun mata da sukayi matashi da daloli a gidan mazajensu sune suka kawo lefen, aikuwa sun samu tarar girma da

karimci, tukuicin kujerun makka fulani ta ba kowacce daga cikinsu inda hajjo amarya kuma ta musu kyautar motoci, k’arfe goma daidai babban limamin masallacin juma’an dake gidan sarki ya d’aura auren yariman adamawa da gimbiyar zazzau kan sadaki naira miliyan d’aya lakadan, 6angaren yarima kuwa ranar yyi kyau iyakar kyau sai walwali yake da d’aukar idanun jama’a, sanye yake da wata VIP gexna dark blue sai hularsa zanna bukar itama da ratsin dark blue a jikinta, hannunsa sanye da diamond watch nashi sai kuma MR cover shoe d’insa black, OMG, he looks terribly handsome like take away, saidai fuskar nan tamke take tamau kamar dai kullum, sai shegen izzah da qasaita tamkar wani dawisu, lkcin da liman ya sanar da d’aurin aurensa, kaffara abokansa sukayi tamkar sun had’a baki tuni suka soma tsokanarsa suna masa shaqiyanci, yarima haydar wanda shine babban aminin ango ya kalli sauran friends nasu wanda cikinsu har da turawa yace” yau dai gimbiya tayi nasarar d’amqe wannan k’wallon shegen” gbdy suka bushe da dariya ban da uban izzah daya sake had’e rai, lkcin dubban jama’ar da suka shaida wannan daurin aure suka soma qoqarin fita,  cikin hanzari sarkin takalmi ya gyara masa takalminsa ya tsaya daidai yadda ze sanya kafarsa yasa sannan suka fito, a yadda tsarin masarautar adamawa yake masu kawo lefe suna zasu tafi da amarya bayan d’aurin aure, aikuwa tuni aka qara gyara amarya aka sanya mata wata alkyabba mai mutuqar kyan gaske kalar ruwan goro, mai martaba ya bata bayi goma sha biyu cikinsu har da babbar baiwarta wato yar buzuwa amma saida fulani kilishi ta nemi alfarma wurin dangin ango akan su bari sai zuwa yamma su wuce sbd ta gayyaci tsohuwar kid’i mai aliko ta nishad’intar dasu da kid’inta na k’warya,6angaren ango kuwa ana daura aure bayan duk sun fito ana shirin shiga motoci a wuce fadar sarkin zazzau ya janye jikinsa a sace sarkin garmai ne daukeshi a mota yakaishi airport yabi jirgi sai birinin yola, su kuwa sai nemanshi suke sama ko qasa babu shi babu alamarshi, gashi zasu tafi kai gaisuwar surukai dole saida ango, yarima haydar hnklinsa ya tashi sosai son besan abunda ze sanar da lamid’o da suke jiran isowarsu a fadan mai martana sarkin zazzau ba, gashi waziri sai kiransu yake akan su hanzarta isowa ana jiransu don ya kira wayoyin yarima duk a kashe, ba shiri suka shige motocinsu suka nufi fada, lkcin da waziri ya gansu ya taso da sauri yana tmbyrsu inah yarima suka sanar dashi ai yarima baya jin dadi ne zazza6i ya rufeshi shiyasa ya wuce hotel ya kwanta ya huta, jikin  waziri a sanyae ya wuce ya sanar da lamid’o abunda ke faruwa, ran

 lamid’o yyi mugun 6aci don yasan qarya ne lfyrsa lau kin zuwa kawai yyi sbd be ga daman ba, daurin auren ma saida yyi da gaske ya sako shi gaba suka taho shine yanzu ya sulale yyi tfyrsa ya barshi da jin kunya,  mai martaba sarkin zazzau kuwa nuna masa yyi ya babu komai tunda dai sun gana a wurin daurin aure, a cikin gida kuwa mata na nan suna sha’aninsu, mai aliko nishad’intar dasu da kid’inta na k’warya, marok’a kuwa sai kirari suke tamkar muryarsu zata k’are, kud’i kuwa kyautarsu ake ana kuma watsasu tamkar ba’a sonsu, hjy zainaba matar gwamnan kaduna kuwa tayi 6arin daloli ranar hk tayi ta yiwa amarya manni, ranar naga tarin manyan mata tamkar gasa suke wurin watsa kud’i kawai zuge bakin jaka suke suna fito da dumun kudi suna watsi dashi tamkar babu gobe,hmm, lalle kam biki na ya’yan girma dole mutan girma suyi sha’aninsu,abu nasu maganin a kwa6esu,malam talaka kuwa iyakar nashi kawai kallo, a farfajiyar gidan sarauta aka sanya kid’in kwaryan mata suka chashe, maroqa kuwa ranar sun samu abun arziki, bayan an gama shan budurin da yammaci dangin ango suka soma shirin tfy da amaryarsu, kuka kam gimbiya tasha shi tamkar idanunta zasu rufe, Allah ya dasa mata tsanar wannan aure cikin ranta daidai da second guda bata ta6a son auren nan ba, dakyar aka iya rabata da jikin mahaifiyarta tana rusa kuka itama amarya jiddo na kuka duk cikinsu an rasa mai k’arfin halin rarrashi, a private jet aka d’auki amarya tana tirje tirje hk dai dole ta tafi d’akin aure……
_*Masarautar adamawa*_……


Duk da kasancewar garin ya fara duhu amma hkn be hana na gano muku tsantsar kyawu da k’ayatuwar wannan gidan sarauta ba, fitilu ne ta ko’ina suna haske ciki da wajen masarautar yadda ko allura ce ta fad’i qasa za’a ganota haske tamkar rana, bushe bushen algaita ne kawai ke tashi, gbdy fillaci ne kawai ke tashi, saririn gidan sarauta shimfid’e yake da dogon jan carpet ga dangin ango nan sun yi sahu sahu suna jiran isowar amarya, aikuwa qarar wata algaita da suka ji ne ya tabbatar musu da cewa y’an kawo amarya sun qaraso, hk tawagar amarya suka shigo, kakar ango yagwalgwal dake gefe guda sanye da

Advertisements

 wata baqar laffaya ita tafi da sauri ta riqo hannun amarya suka fara tfy a hnkli bisa wannan dogon jan carpet d’in, y’an kawo amarya kam sai gud”a suke hk har aka wuce da ita 6angaren baturiya wacce take mahaifiya ga yarima, 6angaren nata yana da zurfi da fad’i hk dai suke tfy suna wuce furanni masu ban sha’awa har suka qarasa babban falon baturiya, tana ganin shigowarsu ta taso da sauri ta taresu da fara’a da murmushi, tana musu lale marhabin cikin harshen fillanci, qasak’e kawai nayi ita qare ma wannan mace kallo, kunsan abunda ya bani mamaki shine gbdy kamanninta irinna na turawa ne amma da yaren fullanci take mgn hkm shigar dake jikinta jan laffaya ne, falon nata sai tashin qamshin turaren wuta yake, qafarta da hannunta d’auke yake da zannen jan lalle, sunkuyawa gimbiya tayi gabanta kanta a sunkuye, murmushi tayi tasa hannu ta yaye mayafin daya rufe fuskar amarya tuni fuskar gimbiya bilkisu ta bayyana sha6e sha6e da hawaye, gbdy suka soma kiran masha’Allah,masha’Allah, wata bunk’asashshiya mace dake gefen baturiya wacce da ganinta akwai tarin izzah itace fulani habiba uwar soro yayar yarima ce ita yake bi daga ita sai shi,daukan hndkhchp tayi ta  miqawa yagwalgwa ta amsa ta soma gogewa amarya hawayen daya 6ata fuskarta, dayake dukkanin maganganunsu da harshen fillanci suke dayawa daga yan rakiyar amarya ba jinsu suke ba, ita kanta amaryan ba fillancin take ji ba, bayan uwar ango ta sanyawa amarya albarka ne suka baro sashinta suka nufi 6angaren lamid’on

 adamawa shima ya sanya mata nashi albarkan daga nan suka  nufi 6angaren fulani innoh wacce take uwargida, makirar mace kenan mai fuska biyu, sosai ta tare da fara’arta da wasa da dariya wanda a lkcin sai ayi zaton tafi kowa kirki sbd dariyar baki irin nata, daga fulanin innoh da yagwalgwal da fulani habiba da fulani shatu da fulani uwani suka rankaya suka yiwa amarya rakiya zuwa 6angarenta har cikin d’akinta suka kaita, d’akin daya ji kayan alatu don an narkar da naira a furnitures da sauran kayan d”akin,  yagwalgwal ta kalli uwar biyu dake tare da gimbiya tace” a sake shirya amarya adda shatu zata shigo don ta mata rakiya zuwa turakar mijinta” gimbiya bilkisu na jin hk gabanta ya yanke ya fad’i don tayi rantsuwa wlh bata ta6a baiwa wani budurcinta sai masoyinta wanda a rayuwa take da muradin aure, sallama suka mata suka fice ya rage daga ita sai uwar biyu da fulani kilishi ta turota ta kula da gyaran jikin gimbiya, aikuwa babu sanya tana jin hk ta shige toile ta dafa ruwan dumi a boiler din dake bathroom din ta cika ruwan da sinadaran qamshi sannan ta fito ta sanar da gimbiya kan ta shiga ta sa

ke wanka, babu musu ta tayata cire alkyabbar dake jikinta ta daura towel ta shiga wanka, uwar biyu ta sanar da ita ta fara tsarki da ruwan tukun, babu jima ta fito daga wankan tuni d’akin ya kuma gaurayewa da wani asirtaccen qamshi mai mutuqar sanya nishad’i, tana fitowa taga uwar biyu na jiran fitowarta, tana fito ta sanya mata turaren tsugono dana turare ya turarata sosai sannan ta fito mata da wasu shegun sleeping dress, silk ne masu kwanciya a jiki su fallasar da dukkanin baiwar ma’adanar dake jikin mace musamman ma tudun qirji, wando iya guiwa yake sai rigar dake iya cinya, gbdy kayan farare ne qal, kallon sama da qasa gimbiya ta yiwa kayan tace” kina nufin wadannan abun zan saka a jikina” cikin sauri uwar biyu tace” ranki ya dade wadannan din sune yafi chanchanta kisa a irin wannan dare da ake kira da farin dare” daka mata tsawa tayi tace” kin ga tafi na sallameki zan qarasa shiryawa dakaina” zata kuma mgn ta kuma magana ta sake daka mata tsawa ba shiri tayi hanyar fita, har takai kofa tace”idan kin fita ki turomin yar buzuwa” tace” toh ranki ya dade” tana fita ta taje ta tarar da rumana har ta soma bacci a dakin da aka saukesu sbd gajiya, tashinta tayi ta bude idanu da sauri, alama ta mata wai gimbiya na son ganinta, har kofar dakin gimbiya uwar biyu ta kawota sannan ita ta koma, sallama tayi ta nemi izinin shiga sannan ta shiga, tana shiga gimbiya bilkisu ta dauki wadannan matsiyatan kayan baccin da uwar biyu ta fito mata dashi ta sanya ta miqawa rumana ta mata alama data shiga bathroom ta sanya, cike da mamaki da shakku rumana ta amshi kayan tayi hanyar bathroom, tana shiga ta warware kayan tana qare musu kallo, gabanta yyi mugun bugawa data ga irin kayan, har yanzu ta kasa fahimtar meye dalilin dayasa gimbiya zata bata wadannan shegun kayan tace wai ta saka, shirun da gimbiya taji ne rumana bata fito daga bathroom din ba yasa ta tura kofar bathroom din ta taddata sanye da kayan amma ta kasa fitowa, wani shu’umin murmushi tayi tasa hannu ta riqo hannunta ta fito da ita, nad’a mata

 laffaya tayi akan kayan ta janyo laffayar ta rufe mata fuska, takarda ta dauka tayi rubutu sannan ta miqa mata ta karanta, cike tashin hnkli ta kalli gimbiya tana kuka tayi qasa da sauri bisa kan guiwowinta tana ta daga hannunta alamar tana roqon gimbiya ta rufa mata asiri bata iya aikata wannan abu, daga hannu gimbiya bilkisu tay tsinketa da kyakykyawan mari tace” na rantse da Allah sai kin je” saurin sunkuyawa tayi ta dauki takarda ta rubuta mata abu kamar hk, idan har kkyi gangancin da asirinmu ya tonu kece da wahala a wannan masarautar don kar ki manta kedin qasqatacciyar baiwa ce a gareni shiyasa nk baki shawara ki aikata abunda na umarceki kawai batare da kuskure ba’ miqar da ita tsaye gimbiya bilkisu tana dariya qeta, hk ta mata ruwan turare sannan ta zaunar da ita a bakin gado ta ita kuma ta  sulale ta fice shan iska, wuraren goma adda shatu ta shigo d’akin sanye take da wata doguwar rigar bubu, siririya ce mai kyau da ita, wurin gadon ta nufo ta miqar da rumana tare da sake janyo mata laffayarta ta rufe mata fuska tace” madallah da diyar kirki yanzu zan miqa ki turakar mijinki” kama hannunta tayi suka fita batare data gane cewa an sauya amarya ba, rumana kuwa bata ta6a tsintar kanta a firgitaccen tashin hnkli ba irinnna yau, toh me kenan?me gimbiya bilkisu take nufi da ita?? tambayar da take ta yiwa kanta kenan har suka shiga tafkeken 6angaren yarima, falonsa yyi girman wani gidan kuma duk girman falon d’akin kwalli daya ne tal a cikinsa, kai tsaye dakin ta shigar da ita, komai na d’akin dark blue ne da fari, sannan dakin shima tafkeken gaske, bedshit din da aka lailaye katon royal bed din fari ne qal, ma’anar sanya farin zanin gado ranar daren farko shine suna son tantacewa shin mace ta kawo budurcinta gidan aure ko kuma ta 6arar, washegari yagwalgwal dakanta take shigowa ta duba idan taga jini toh hkn ya tabbata ta kawo budurcinta idan kuma babu toh da matsala, wannan karon ma dai hknne ya kasance, adda shatu na zaunar da rumana a bakin gado ta fice ba jimawa ta soma jin hayaniya ashe ango aka rako wurin amaryarsa, basu shigo bedroom ba daga falo suka dakata, ba jimawa kuma suka tafi, adda shatu ita ta kuma shigo da ango turaka sannan ta musu fatan alheri ta fice, jin motsin shigowar ango ne yasa jikin rumana ya soma karkarwa sbd fargaba da tsoro daya cika zuciyarta, shi kuwa ran nan nashi a had’e kamar kullum ya tsaya daga can nesa yana wurin kofa yana kallon 6angaren da take hannayesa a harde a k’irjinsa sai kuma ya saki wani shu’umin murmushi yana cije le6e cike da tarin mugunta fal ransa……………

Advertisements

*Littafi na Biyu na kudi ne*
Alkalamin Bintu ne……

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like