SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 8

Advertisement

 *BOOK ONE* (1)

                   8️⃣

_*Dftn duk mun sha shagalin bikin sallah lfy, Allah ubangiji ya maimaita mn*_………

Lokacin da gimbiya bilkisu ta samu labarin dalilin ziyarar da lamid’on adamawa ya kawo masarautar zazzau yana da dangantaka da batun aurenta da yariman adamawa sai  gbdy hnklinta yyi mugun tashi domin ita a zahirin gsky bata k’aunar wannan aure duk kuwa da kasancewar bata taba sanin waye yariman adamawa a fuska ba kuma ba wani tsayayye ne da ita ba saidai tana da wanda takeso wanda a duniyarta sau d’aya ta ta6a tozali dashi a garin weston dake london lkcin da tawagar dalibai masu karantar history dake karatu a cambridge sukai ziyara ma’adanar tarihi dake tsohon garin weston dake birnin london, gimbiya bilkisu na daga cikin wadannan dalibai lkcin da suka gana da spokeman na wannan gida Dr.edward typical english man ne but mutumin da suke tare dashi a office din suna


 tattaunawa shine yyi masifar dauke mata hnkli, dogo ne sambal yana da dogon hanci tamkar biro gashi fari sol, eyes ball nashi blue shar tamkar baturen usul,  yana da wadataccen suma saidai kallo daya ta masa ta tabbatar da cikar isarsa don ko kallonsu beyi ba har ya miqe Dr.Edward yyi masa rakiya ya fice, lkcin ba ita kadai kawai tayi crushing nasa ba kusan dukkanin matan dake wannan tawaga yyi gaba da zuciyoyinsu, tunda daga wannan rana ta afka kogin soyayyar wannan mutumi da batasan waye ba sannan batasan ina zata sake haduwa dashi ba, wannan dalili yana daya daga dalilanta na korar dukkanin wanda yace yana sonta kullum tana cikin begen sake haduwa da muradin zuciyarta….
Advertisements

       Mahaifiyarta ma bata maraba da wannan aure sbd fulani kilishi jinin sarautar adamawa ce don hk take adawa da hadin sbd bata son hada jini da zuri’ar fulani don tace suna da baqin hali, wannan aure da mai martaba sarki yake son hadawa shine ya kuma kunna wutar qiyayya tsakanin yola da manbilah, mai martaba sarki  ya fahimci yadda amarya ke mutuqar adawa da wannan aure hk ne yasa yyiwa gimbiya bilksu umarni kan ta tattara komai nata ta koma 6angaren fulanin yola da zama don yana tunanin uwarta zata iya sanyata bijirewa umarninsa, ginbiya bilkisu na komawa yola tayi gamo da rumana wacce ta fahimci kurma ce hkn yasa ta za6i rumana ta kasance babbar baiwa mai mata hidima don tana ganin  tunda kurma ce  zata kare sirrinta, tun daga ranar rumana ta kasance babbar baiwa ga gimbiya bilkisu, ita take share mata daki ta goge ta gyara mata ko’ina hatta undies d’inta rumana ce ke wanke mata,  duk da hk ba wani yaba mata take ba saidai ma hantara da kyaraa da take mata kullum,  rumana irin mutanen nan ne masu binne damuwa cikin rai har sai ta musu illah, kun san dai kyan dirin rumana ga kuma kyawun fuska duk kuwa wahala da bauta sun rage annurin kyawun nata amma hkn be hana ta tsole idon wasu ba,  kyawun nata na daya da cikin abunda yasa gimbiya bilkisu ta tsaneta sosai don tana ganin kyau irin hk be chanchanta ga baiwa ba sai su diyan saraki, bata kiranta da rumana saidai tace mata yar buzuwa, cikin qanqanin lkci kowa ya koma kiranta da yar buzuwa, duk da qanqanta shekarunta bata da gandar aiki ko kadan, tunkan uwar dakin nata ta farka take gama tsaftace ko’ina sannan ta shirya mata kayanta tsaf a drawer don ita idan zata sanya kaya saita birkita komai na drawern ta watsosu waje,  rumana kuwa hk kullum take dawainiyyar gyaran drawern babu gjyw….
Komawar gimbiya bilkisu yola shine yasa yarima ayman ya rage shiga yola don yana tsoron kar gimbiya bilkisu ta fahimci manufarsa kan rumana don babu shakkar sai ta fadawa amarya wanda hkn kuma babban matsala ne musamman ga rumana, yau tana gama aikinta tayi wankanta ta sanya wata doguwar rigarta wacce take kalar sutturar bayin dake hidima ga yola,  gimbiya bilkisu ce suka fito fulani na riqe da hannunta suna mgn, kallonta tayi ta yatsine fuska sannan ta juya ta kalli fulani tace” ranki ya dade wannan baiwar ta fiye son qazanta irin nasu na  buzayen jeji” kallon 6angaren da take durqushe fulani tayi sannan ta nemi wuri ta zauna cike da izzah irinna uwargida sarautar mata, rumana tace” Allah ya gafarta yaja da ranki, barka da hantsi” kada kai kawai tayi sannan tace” gimbiya ta raina tsaftarki meye yasa hk rumana” saurin sunkuyar dakanta tayi qasa tayi shiru batare data ankara ba, gimbiya bilkisu ta sauke mata wani lafiyayyen mari cikin fushi tace” fulani na miki mgn kin yi shiru sbd baki gaji arziki ba” cikin sauri fulani ta daga mata hannu sannan ta juya tana kallon  rumana tace” sam bazan dauki wannan rashin da’ar naki ba kuma ki gaugauta neman afuwa ga gimbiya” kallon gimbiya bilkisu tayi tace” tuba nake ranki ya dade” harararta tayi sannan ta cilla mata handbag dinta dake riqe a hannunta ta cafe da sauri tabi bayanta suka fice……


Littafi na biyu na kudi ne…..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like