Advertisement
*PAGE* 11-15
……………………📖Kwanci tashi ba wuya kulum biki dada matsowa yakeyi yau ya rage saura 4days Najma tayi rabon IV da duk abuda ya dace danma Mamee tace bazai ‘bata kudinshi akan wata ‘yar matsiya taba
Shirye shirye yayi nisa haryau Friday akayi kamu a Majid na Juma’a a uguwar su bayan an gama kamune ta dawo gida Najib yazo gidan kiranta yayi a waya tafito yana jiranta
Duk da gidan na mutane saida taje ta sanarwa Ummee sannan ta fito acikin mota tasameshi ta bu’de tashiga ta gaidashi kanta a ‘kasa tana wasa da yatsunta
Advertisements
kafeta yayi da ido kafin yayi ajiyar zuciya ya kamo hannuta yace “wow gaskiya wannan lalen yayi kyau my wife wayamiki shi” murmushi tayi tazame hannuta a hankali tace “nagode amma bakasan ta ba koda na fa’dama” ”okay naji daman zuwa nayi muyi wata muhimiyar magana da ke”
Hankalin ta tamayar gurinsa ya juyo yana fuskan tarta yace
“Yanzu lokacin boye boye yahuce a tsakaninmu kinsan da haka ko?” kai ta gyada masa ya ‘kara da cewa “to dama inaso na sanar dake nifa banaso daga kinje gidana ki haihu” atsorace ta ‘dago ta kaleshi ya gyada mata kai yace “dan haka nayi magana da Doctor na yace gobe muje musameshi yasamiki in plan” cikin mamaki take kalonshi ya sauke nunfashi yace “plx Najma ki fahim ceni banason ki haihu da huri ki saurin tsufa kuma kinga ba dad’i nace zan ‘kara aure kuma ni mutum ne meson macen da bata mufaba kindai gane abunda nake nufi ko”
ahankali Najma tace “amma daka bari ko haihuwar fari nayi sai………!” katseta yayi da cewa “aji tunda bazaki yi abunda nace ba ni tafiya zanyi zaki iyafita”
Advertisements
kwalace ta tarar mata a ido tace “bawai naki abunda kace ba……..!” tsawar da ya buga matace tasata saurin yin shiru yanuna mata hanyar waje yace “zaki iya fita banason jinkomai” ganin yadda ya had’e raine yasa ta bude motar tafita
afusace yaja motar yabar gurin
kuka Najma tasaka agurin taja ‘yammatan kafafunta ta koma cikin gida tashiga ‘daki ta kule kanta a ‘daki taringa kuka kiranshi ta ringayi a waya amma yaki ‘dauka saga bayama ya kashe wayar gaba daya
Ranar yadda Najma taga rana haka taga dare ga kuka datasha kamar ranta zai fita
Washe Gari
Najma ko bearkfast bata iyayiba ta rimga kiran Najib takiya yayi sau 20 bata shigaba harta hakura ta ajiye sai kuma ta kasa hakuri ta ‘doko wayar ta ‘kara kiranshi cikin sa’a tashiga
Najma batasan sanda tasaki wani murmushi ba batayi tsamani ba taji ya ‘dauka amma baice komai ba
ta sauke ajiyar zuciya tace “plz kayi hakuri insha Allah bazan ‘karama musuba nayarda kazo muje Hospital din”
Najib nadaga kwance ya mike zaune yace “to naji kishirya zuwa 10 zanzo muje amma koda wasa banason wani yaji wannan maganar wannan Sirimune” “insha Allah bawanda zaiji”
Cike da farin ciki yace ” owk nagode my wife”
Nan suka bude shafin LOVE
Sunjiya muna waya kafin suyi salama
tashi Najma tayi tai wanka tayi bearkfast tashirya cikin atafa Yellow ne flower green ta dauko veil green tasa tashi ga ‘dakin Ummi Allah ya taimaketa bakowa daga Ummee sai kanwarta ta gaida su Ummee ta kaleta tace ”Najma meya sameki haka idonki duk ya kubura?” “Ayyah Ummee cikina ne yake ciwo jiyama kwana nayi banyi bacci ba” “sannu Allah ya sawake, kinsha magani?”
“A’a yanzu zanje Hospital na fada musu matsalata su rubutamin magani nasiyo saiyafi kyau” “hakanma zaifi yanzu Bara nabaki kudin muta” “A’a Ummee kibarshi inada kudi a guna” “to ko akira Yaya Nura ya kaiki” da sauri tace “A’a sauri nakeyi naje na dawo da wuri sabuda shirin Mother’s night da zasuyi a gidan Su Najib kisan zanje” “hakane Allah ya kiyaye” “ameen” tace ta mike tafito
tana fitowa ‘kofar gida takirashi a waya ta sanar dashi tafito yace shima yakusa ‘kara suwa toyo gaba
can bakin titi tafita bata jimaba yazo suka huce Hospital ‘din
Suna zuwa basu wani jiran layiba Doctor ya basu izinin shiga ciki
zama sukayi dayake Doctor yasan dalilin zuwansu bai wani jira ba yasawa Najma in plan din ya rubuta mata magunguna Najib yamasa godiya suka taho gida
tun a Hanya gaban Najma ke faduwa yanzu wane irin gangaci tayi haka ta yarda da buk’atar Najib yanzu bata sani ba tana haihuwarma ko batayi amma aka ‘kara mata da wani abun na hana ‘daukan ciki shi Najib namijine yanada damar da zai iya haihu amma itafa?
Ta tanbayi kanta
Ai batasan sanda wasu hawaye masu zafi suka zubo mataba
Kalonta Najib yayi yace “yadai meya faru” saurin goge hawayen tayi ta ‘ka’kalo murmushi tace “bakomai” kafad’a ya ‘daga alamar ko ajikisa
gida ya kaita sannan shima ya Huce
*NIGHT*
Tunda yamma Najib yanemo me kwaliya tazo ta tsara Najma sosai tayi kyau cikin doguwar rigar less Red aka mata komai red tayi kyau sosai abun sai wanda yagani shima a ‘bangaren Najib Red din yadi yasa ba ‘kamun haduwa yayiba
dakanshi yazo ya ‘dauketa suna tafe suna nunawa Juna tsantsar SO
A harabar gidan su Najib aka shirya ida za’ayi Mother’s night din gurin ya hadu sosai komai na gurin red ne da white
Najma da gani take ba ya ita amma suna zuwa gidan su Najib ta raina kanta
Koda suka shiga mutane suna ta daukansu pic amma saitaga kamar kalon baza akemata tunda ga nan tasha jinin jikinta duk saita jita a takure
Mamee ce tashigo da ‘kawayenta da ankonsu taringa likawa Najib 1k amma ko kalon Najma batayiba MC ne yayi magana wai yayaga Hajiya iya ango takewa liki murmushi tayi tace mishi “ai shine ‘dan gidan masu arziki kuma ya gaji arziki kaga dole shi ya dace da naiwa liki” aikuwa gurin ya ‘dau shewa da tafi mutane wasu suce “sai Hajiya wannan haka yake” wasu kuma “hakane Hajiyar mu Allah ya ‘kara arziki”
Najma dake zaune wasu irin hawaye masu ciwo suka zubo mata
Yinkura tayi zata tashi Najib ya riketa ya girgiza mata kai
Ta kauda kai kawai badan tasoba tazauna har aka gama taron aka watse masu mata Habaici nayi
Koda Najib ya maida ita gida ko sauraronshi batayi ba tashige gida ta rabu dashi shima bai damuba yai tafiyarshi gida
Washe gari
Yau Sunday yauta kama za ayi daurin aure tun Najib bai tashiba Mamee taketa kiranshi a waya gajiya yayi da kiran yamike yaje yaji dalilin takura masa da akayi………………!
COMMENT
AND
SHARE
by
*XAHRA*
GIPHY App Key not set. Please check settings