SHINE SILAH 6-10

Advertisement

 *PAGE* 6-10

……………………📖”Yau Yaya Najma da Adaidaita sahu taje yana tsaye mukafito yakawomu gida”  ajiyar Heart ta sauke sannan tashige daki tanajin Ummi nacewa “shiyasa kukayi saurin dawowa”

idai bata dawoba

Tana shiga bedroom ta kulu kofa ta zauna akan bed ta ciro wayarta tayiwa Najib message tasan na ajiye phone din tafita kitchen ta dora musu abinci 
After one week 


Advertisements


anfara shirye shiryen bikin Najma dan saura three weeks yanzu ko fita ba’a barin Najma tayi tana zaune a daki kulum a kule a daki tana aikin danna waya
Najib ne yashiga room din Mami da salama ta amsa sama-sama ya zauna ya gaida ita ta amsa tana kauda kai yace “Mamee dama zuwa nayi na fada miki yau za’akai lefan in zaki gani”   cikin fushi tace “cemaka akayi ina son ganin tsinanen lefan da za’a kaiwa wannan ‘yar iskar yarinyar”  ajiyar zuciya ya sauke yace “ayyah Mamee kiyi hakuri ki daina aibata Najma nibanga laifin Najma ba kuma Allah yari yatsara itace matata ba Khairat ba”  tsaki Mamee taja tace “mtsss dala karufemun baki ubanwa yace ka nanewa yarinya kace ita zaka aura kilama asiri sukamaka ka nane mata” 
magana zaiyi ta ‘data mishi hannu tace “bana son jin komai tashi ka bani guri”  “kiyi hakuri Mamee wallahi inason khairat akwai abunda yasa nace Najma zan aura sabuda Najma sonda takemun yafi nawa sosai”  harararshi tayi tace “naji tashi ka bani guri”  mikewa yayi sum sum yafita daga dakin Mamee tayi tsaki kawai tacigaba da abunda takeyiAdvertisements


Najib na fita ya ‘dauki waya yakira yayarshi Binta wace ita ta hada masa laifan yace kawai tabaya su Jibirin sukai lefan gobe da safe Mamee tace bazuwa zatayiba da to ta amsa mishi yaimata godiya ya kashe wayar 
washe gari aka kai lefe gidan su Najma ba laifi kaya sunyi kyau kuma duk da haka Mamee tasa an rage wasu kayan ankai mata
‘Yan uwa da abokan arzki duk sunzo ganin kefan kowa sai san barka


Najma na ‘daki dadin duniya ya isheta burinta na malakar Najib yakusa cika yau jinta take kamar a wata sabuwar duniya message ne ya shigo wayata taduba taga Najib ne 
Sarauniyar matan duniya ina kifar gida kifito inason ganin kyakykyawar fuskarki da kyakykyawan……….! 
Murmushi tayi ta mike tashafa powder tasa wata dokuwar riga pink ta ‘dau hijab tafito 


dakin Ummi taje tasanar da ita zuwan Najib Ummi tace “dawo lafiya” cikin farin ciki tafito dan yau Yaya Nura maisa mata ido baya nan dan haka tafito ta bude dakin Yaya Nura  tayiwa Najib magana yashigo 
zama yayi yana kalonta itakuma sai murmushi take yace “my Wife yau ina cikin farin ciki nakusa malakarki”  ido ta ‘dan zaro tace ”waya fada maka bayan baka biya abunda yazama tilas a aure ba kuma shine me wuya sadaki”  dariya tayi yace “ai yanzu auren mu na Malam ba Haushe ka gama laife to kagama babban aiki sauran duk shakafce” 

dariya tayi tace “kumafa hakane tu kaima kagama Babban aiki ko?”  “Sosaima saura kiriss” ya fada a daidai kunan ta hijab tasa tarufe fuskarta tana dariya ya b’ata rai yace
“Wai sonawa zan miki magana akan sa wannan k’aton hijab din kinsan banaso ko”  bai bata damar tayi magana ba yasa hannu zai cire hijab ‘din tai saurin rike hannushi tace “ayyah dan Allah kayi hakuri karka cire Allah bazan kara sakowa ba” bai saurare taba ya ciga da abunda yakeyi mikewa tayi taza fita yace “Najma na rantse da Allah kika fita zakiga abunda zanyi” tsayawa tayi batare da tajuyota ya mike yana cewa “nizaki kora bake zaki fita ba aini najawa kaina koma me kikai mun dan ninakawo kaina” ganin da gaske fita zaiyi ta riko Hannuta idonta cike da kwala tace “kayi hakuri zan cire amma kabari na cire da kaina”  murmushi yayi sannan ya ha’de fuska ya juyo yace “to cire da kanki”  cire hijab ‘din tayi ta nike ta ajiyeshi veil din rigar ta yafa Najib ya lumshe ido yace “Wallahi kinfi kyau a haka Matata”  dariya kawai tayi ta zauna tace “wai message din da kayi dazu bayan kyakykyawar fuska saikuma kace da kyakykyawan……!  baka ‘karasa ba”  dariya yayi yace “baki manta ba ashe”  “Eh ban manta ba”  “to ina nifin da kyakyawan halinki” ”hmm” kawai Najma tace badan ta yarda da maganar Najib ba haka suka sha LOVE dinsu sai 9:30pm Najib ya tafi gida 
da dare Yaya Nura ya dawo Ummi ta dakomishi lefe yagani yasa albarka sannan yakali Najma yace ”yanzu kinga aurenki kulum k’ara kusan tuwa yakeyi iyayemu ba ‘karfi gare suba gara Ummi tana hida ma damu amma shi Baba wata nawa mukeyi bamu sa shi a ido ba dan haka kiyiwa mijiki biyayya kiyi hakuri shi zaman aure dan hakurine ki zauna da iyayen mijinki da ‘yan uwansa lafiya ki rike mutuncin ki dan Allah Najma” kanta a ‘kasa tace “insha Allah Yaya Nura zankiyaye nagode sosai”  nan suka cigaba da hirarsu ta duniyaWacece NajmaMalam Yakubu shine mahai finta ‘dan asalin garin jigawane neman kudi yasa yake zuwa Legas yana dawo wa time to time harya auri Ummi ya ajiyeta a burnewa yana Neman  kudinsa yana kula da iyalisa haka har Allah ya azirtasu da samun yaro namiji ranar suna yaro yaci suna Nura haka suka cigaba da zamansu lafiya bayan shekara Biyar tasake samun yarinya wace mesuna Najma tana rainon yaranta cike da kulawa  
Bayan shekara 13 a yawon Legas ‘din Baba ya hadu da wata mata ‘yar duniya me suna atune nan hankalishi gaba ‘daya ya koma kanta tasa ya debo iyalisa tabashi gida a Dutse yadebo Su Ummi ya dawo dasu aka daura aurensa da Atine tunda akayi auren su da atune Ummi ta daina ganin Baba lokacin tana da cikin harta haihu yara biyu Annur da Noor harta yayesu Baba bai dawo ba saidaga baya yazo yabasu hakuri yashirya musu karya da gaskiya kuma yana kara komawa yaki dawowa tun yana karya suna yarda harsuka saba da idan yatafi sai sun ganshi Yaya Nura shiyake musu komai a gidan dayake Allah yasa yanada sana’a harda abun hawanshi 
lokacin da Najma ta hadu da Najib koda zancen yazo gun Baba baiyi wani bikice ba ya bashi auren NajmaShikuma Najib Mahai fisa Alhaji Ahmad shine mahai finshi yanada runfin asiri sosai gashida alhari da son mutane sab’anin matarshi Hajiya Fidausi wace batason ganin wani talaka ya rabesu Sunda yara 4 

Binta itace Babba sai Najib yana da Kane mata biyu Aysha da Ameenah 

Kuma duk cikin yaransu bawanda yayo halin Hajiya Fidausi sai Najib bayaso yaga kowa yarabesu shi mutum ne da bayason mutane ko kadan 
Najib irin mazan nane ‘yan yaudara amma tunda yaga Najma yace yaga matar aure kuma abunda ya sa yake kara sonta ko huta ya rura yace tafad’a saita fad’a shikuma irin wannan matar yakeso 
duk da Mamee batason Najma amma haka yaringa rarrashinta amma tace ‘yar ‘kanwarta Khairat takeso ya aura amma Alhaji Ahmad ya dage yace abarshi ya auri choice ‘dinsa

Shiyasa tun ba’ayi auren ba Mamee ta ‘dorawa Najma karan tsanaCIGABAN   LABARIgaskiya yau inbanga comments da yawa ba bazanyi wani Page din ba zan karkata ne kawai a TAURARI BIYU incigaba da Typing dinsa shi kadai 
COMMENT

AND

SHARE
by

 *XAHRA*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like