WANDA BAIJI BARI BA 1-2

Advertisement

 

               1&2


       Ilahirin jikinta banda karkarwa ba abinda yakeyi, gumi daga sassan ɓangarorin jikinta ta ko’ina tsiyaya yake, atakure take cen jikin kusurwar bishiyoyin dake cikin harabar dajin da babu abinda yake tashin cikin ƙungurmin dajin banda gurnanin waɗansu irin hallitu da kukan tsuntsaye marasa daɗin sauraro.


      Gabanta banda faɗuwa ba abinda yake idanunta sunyi zuru-zuru sai waige take tana dube-dube, daga cen gabanta ta fara jiyo motsin tafiya mai kama da takun dawakai, da sauri ta ƙara maƙurewa jikin bishiyar jikinta na cigaba da karkarwa, wata irin dariya taji an ƙyaƙyace da ita na ɗan wani lokaci sannan dariya ta tsagaita.


      Iska ce ta fara kaɗawa ahankali ta fara hango waɗansu irin manyan ƙwari masu kama a fasalin maguna sai dai kowanne su maƙale yake da fukafuki a gadon bayansa, sautin tafiyar Dokin ce ta ƙara kusantota hakan ne yasa ta maida kallonta ga inda tafi jin sautin na matsowa.


Advertisements

         Kamar yanda ya bayyanar mata a karan farko wannan karan ma wata zabgegiyar Abaya ta hango baƙa, tsawon abayar ya kece tsawon bishiyoyin dake cikin dokar Dajin sai da ta ɗaga kanta sama sosai sannan ta hango dai-dai kansa sai dai kansa ne amma babu alamar fuska ajikinsa.


        Ƙarasowa yayi gabanta ya tsugunna cikin murya mara daɗin sauraro ya fara magana, ” Bingirsima baguar kinbasu wakisfatminar, kisasu biragu kilbasu tattarakimbas wajihagar, farafafus bintigad gurmanas YUSRA? harbaskila mindadu bar washbasbismas shizas kima bu warsa? ” ( A karo na biyu ina ƙara miki barka da zuwa cikin daularmu nida ahalina, da sannu zan gabatar da ke ga sauran iyalaina domin kusan juna keda su ina fatan kina jina YUSRA? Ga ƴaƴana nan sun fara zuwa gaisheki ina fatan zaki basu kulawa ? ) Wannan zabgegen Aljanin ya ƙarasa maganar yana nuna mata waɗannan hallittun masu fasalin Maguna da fukafukai.


       Yusra da tuni hawaye yake wankewa fuska ta ƙara durƙushewa ƙasa cikin sigar magiya tana faɗin, ” Ka dubi girman Allah da Annabi ba dan ni ba, ba dan halina ba kayi haƙuri ka maidani cikin mutane dan Allah, wallahi bazan iya rayuwa cikinku ba na tuba dan Allah kamun rai ” 


        Miƙewa tsaye yayi sannan yayi taku biyu zuwa uku sannan ya waigo ya ce mata, ” Hargigas markusa bayas tinga ” ( Tashi tsaye kije jikin waccen bishiyar kukar )


    Yusra har tuntuɓe take da sauri ta miƙe tsaye saura kaɗan Abayar jikinta ta kayar da ita, jikin bishiyar taje ta tsaya tana  sauraron abinda zai sake faɗa, batayi aune ba ta tsinkayi muryarsa yana faɗin.


     ” YUSRA Lilbas faragaras binsafa walgibas zalzulfat kinari ” ( YUSRA kalli Abayar jikinki da kyau, idan har kin iya cireta daga jikinki to tabbas zaki koma cikin jinsinki ” yana rufe baki Yusra ta hau kiciniyar cire Abayar jikinta amma ga mamakinta sai ji tai ta mata wani irin nauyi ga santsi, duk yanda taso cireta ta kasa ta jima a haka tana abu ɗaya amma ba mafuta har ta fara galabaita.


Advertisements

      Kecewa yayi da dariya ya jima yanayi sannan ya kalli halittun nan yace, ” Kalarbirar hasas kiba farisdaf ” ( Ku wuce gurin iyayenku ku bamu guri ) bai ƙarasa rufe baki ba gaba ɗaya suka watse daga gurin ta hanyar nutsewa cikin ƙarƙashin ƙasa, juyowa yayi da kallansa gurin Yusra sannan ya ce.


     ” firibar yaukinsat kirigiri marbiskat gilfat binasi warƙatkinsa ” ( Kibar wahalar da kanki domin bazata fita daga jikinki ba, wannan Abayar dana baki itace sadakin aurenki ) yana ƙarasa faɗa ya juya yayi gaba taku uku yayi shima ya shige ƙarƙashin ƙasa ya ɓace.


     Yusra kuka ta rushe da shi mai tsanani nadama da dana sani lokaci guda suka shigeta, wani tunani tayi cikin zuciyarta aikuwa da sauri ta zabura ta miƙe ta fara falfala gudu tun iya ƙarfinta.


       ” Ke Yusra, Ke Yusra tashi mana har gari ya fara wayewa baki tashi kinyi sallar asuba ba ” firgigit Yusra ta miƙe zaune tana murza idanu, kanta taji yayi nauyi wani abu take san tunawa amma ta kasa, gani take kamar mafarkinsa tayi kamar kuma acikin film ta kalla, gabanta ne ya yanke ya faɗi lokacin da ta ƙarewa rigar  dake jikin Ummanta kallo, baki sake ta ce.


    ” Umma wannan Abayar ta jikinki fa? ” 


      Umma ƙarewa doguwar rigar baccinta kallo tayi ta ce, ” Yusra wacce irin tambaya ce wannan? rigar tawa baki ganeta bane ko gizau take miki? kodan kin ƙwallafawa ranki masifar Abaya dole kiga komai yana rikiɗa, banasan sakarci wuce kije kiyi sallah ” Umma na gama faɗa ta fice waje ta bar Yusra zaune.


MORE COMMENTS MORE TYPING👹


_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

Leave your vote

-3 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like