WANDA BAIJI BARI BA 3-4

Advertisement

               3&4

          Jigum tayu ita kaɗai tana nazari da tunani mabanbanta, tashi tayi jiki a sanyaye ta fice daga ɗakin ta ɗauki buta kai tsaye cikin banɗaki ta faɗa babu ko Addua, shigar ta toilet ba wuya taji wata irin juya na ɗibanta da sauri takai hannu da niyyar dafa bango, wata irin iska mai sanyin ce ke ratsa cikin jikinta sai da tai da gaske ta iya furta, ” A’uzubillahi minnashshaɗainirrajim ” take taji iska ta ɗauke a hankali juwar ta fara sakinta.


       Sai da ta ɗan samu nutsuwa sannan ta yi abinda zatayi ta fito ta gabatar da alwala ta wuce cen ɗakinta, bayan idar da sallarta ta jima a zaune tana nazarin abubuwan da suke faruwa cikin rayuwarta.


     Tana nan zaune taji shigowar saƙo cikin wayarta da sauri ta janyo ta fara dubawa, kamar yanda yake bisa ɗabi’arsa ce kullin duk kimanin ƙarfe shida na safe zai turo mata saƙon barka da safiya, sai dai aduk saƙon da zai turo mata tafe yake ta ɗai-ɗaikun kalmomi masu wuyar fahimta.


      Murmushi tayi ta fara karanta sakon cikin zuciyarta kamar haka.


Advertisements

       ” Zuciya da Ruhi na tare da ke kamar yanda na fahimci haka a tattare da ke, Da’irata na kara marhabun lale da samun gamayyar jinsin kyakykyawar hallita kamar ke, dauwammarki tare dani na ƙara kusantowa hakan ne yasa bazan daina ƙawataki ba tare da miƙa miki saƙon barka da safiya da fatan kin wayi gari lafiya. “


       Girgiza kai Yusra tayi cikin jindaɗi a fili ta furta, ” Shiyasa kake ƙara shiga cikin zuciyata MARWAN, kulawarka gareni tana ƙara birgeni ” tashi tayi ta koma kan gado ta kwanta tayi masa reply da kalaman soyayya.


         Tashi tayi ta fice tsakar gida lokacin Umma ta fara hada-hadar haɗa musu kayan break fast, hannu ta sa ta fara taya mahaifiyarta aiki tana ƴan waƙe-waƙenta.


      Umma da mamaki ta kalli Yusra ta ce, ” Oh su Yusra kunci da ɓacin rai ya ƙare tunda kk samu Abaya ni har mamaki kike bani, da agidannan haka kika dinga shuka wulaƙanci da rashin mutumci ” 


       Tura baki gaba Yusra tayi ta ce, ” Yo haka kawai kowa ya shiga yayi banda ni ƙarshen lalacewa ace wai har Zalihar gidan masu awara ta sai abaya ni banda ita ai da sake, so kike idan na fita su dinga mun dariya dama ta cikin group ɗinmu karkiji yanda kowa yaci burin wankan ta ” 


     Guntun tsaki Umma tayi ta ce, ” Ai shikenan nidai abinda nake gaya miki ki tsaya iya matsayinki, ki daina hangen na sama da ke ” 


Advertisements

    Shiru Yusra tayi tana zumɓurar baki daga baya ta hau ƙananan maganganu ƙasa-ƙasa.


       Tana nan zaune taga kamar giftawa mutum daga wajen ɗakinta, ƙurawa gurin ido tayi tana kallo a hankali iska ta fara kaɗa labulen ƙofar ɗakinta, daga ɗan cikin ɗakin ta hango abaya tsaye har zuwa lokacin iska na ƙara kaɗawa har abayar, gabanta ne ya yanke ya faɗi musamman da abayar tayi mata shigen kama da abayar jikin mutumin da ta taɓa gani cikin mafarkinta.


      Da sauri ta ce wa Mahaifiyarta, ” Umma dan Allah kalli gurin cen kamar wata irin abaya nake gani? ” Umma ɗagowa tayi ta ƙurawa ƙofar ɗakin Yusra kallo amma bata ga komai, haushi ne ya kamata ta cewa wa Yusra, ” Yusra ki fita idona na rufe wallahi ki kiyaye ni da zancen abayar  nan ya isheni inba haka ba ranki zai ɓaci “


       A fakaice Yusra ta watsawa Umma kallo sannan ta tashi ta nufi ƙofar ɗakin nata, tana ɗaga labulen ta ji faɗowar Abayarta har sai da ta tsorata tana ja da baya, Abayar da ta cire kwanaki huɗu da suke wuce ta gani wacce ta saƙalet jikin ƙusa, da mamaki ta ɗauko ta saboda ada ta ga kamar ba wannan abayar ta gani ba.


     Kaɗeta tayi sannan ta maidata jikin ƙusar ta ajiye, magensu ta hango tsugunne a gefe ta kafet da manyan idanunta suna haɗa ido haka kawai taji gabanta ya faɗi, hijabinta dake gefe ta ɗauko da niyyar dukanta tana faɗin.

   

      ”  Fita dan ubanki da ƙwalaƙwalan idanunki kin sani a gaba ubanki zan baki mage sai….” Maganarta ce ta maƙale lokacin da taga magennan tayi wata girgiza take wasu fukafukai suka fito a gadon bayanta sannan ta nitsa ƙarƙashin ƙasa ta ɓace._UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like