YAR AMANA 21-22

Advertisement

 *NUSAIBA*

        *’YAR AMANA*☘️☘️

        *Page 21-22*

____ Ya na isa makarantar su IKIRAM ya samu sunyi close, dan haka ya d’aukota suka nufo gida tin amota yayi mata bayanin komai akan ‘YAR AMANA, amma bai ga ya mata cewa matar saba ce, kawai de yace mata daddy ya kawo mata qawa dan haka ta kula da ita kuma ta ringa ko ya mata abubuwa ita kam IKIRAM da murnarta ta shiga gida domin dama tana son abokiyar hira, kai tsaye d’akinta ta nufa tayi Sallama ‘YAR AMANA na kallonta ta miqe tsaye tana neman hanyar guduwa, itako IKIRAM matsawa kusa tayi da ita tace “Sister lafiya ina kuma zaki, ina kece qawata da yaya ABUDULJABBAR yace Daddy ya ka min”


Cikin tsoro ‘YAR AMANA tace ” nima bansan me kike cewa ba, ke d’in mutum ce ko Aljan?”

IKIRAM kuwa cewa tayi “banji me kika ceba ”  qara maimai ta mata ‘YAR AMANA tayi, ABUDULJABBAR  ne ya shigo  ja yayi ya tsaya yace “lafiya na ganku a tsatsaye?”

“Yaya wai tambaya ta takeyi nid’in mutum ce ko aljan, amma Yaya qawarta wa bata jin hausa sosai danni na d’auka ma filatanci take min ashe hausa tamin”


Advertisements

Wani mugun kallo ABUDULJABBAR yayi wa ‘YAR AMANA yace ”  wato ke bakyajin magana ko bance karki qira kowa da aljani ba? Ke wacce irin baqauyiya ce bakidahuma ‘yar daji kawai”

Cikin muryar kuka ‘YAR AMANA tace ”  ka gafa irin kayan da ke jikinta, ai wanan ba irin kayan mutane bane”

IKIRAM kuwa duba jikinta tayi sosai taga de rigar yunufon d’inta take sanye da shi iya gwiwa, sai qaramin hijab dake kanta iya wuyanta sai kuma takalminta kambos da baqar safa da ta saka, sai qatuwar jakar makarantarta da ta goya.

ABUDULJABBAR kuwa cikin fushi yace villager kawai kayan makaranta ne ajikinta kuma kema kin kusa sa irinsu kuma wlh mudin naji kin sake kiran wani da aljani tabbas sai na miyar dake rugarku su hard’o suyi miki duk abunda za suyi miki”

Ai kuwa ‘YAR AMANA ta ‘barke da kuka wai wayyo baffanta, Shi kuwa ABUDULJABBAR sbd da takaici d’akinsa ya nufa ya watsa ruwa yayi kwanciyar sa”


Itako IKIRAM kama ‘YAR AMANA tayi tace “habba ‘yar uwata kukan me kuma kike yi ki haquri dan Allah?”

Cikin kuka ‘YAR AMANA tace “Baffa na na tuna ina son sa sosai”

“To kiyi haquri kinji sister ai zaki sake ganin Baffa naki domin kuwa Ya ABUDULJABBAR yace min karatu Baffanki yakeso kiyi shi yasa dadyna ya kawo ki anan, kinga inkingama karatun naki sai ki koma wajen Baffanki”

A’a ni bazan koma ba domin su hard’o kasheni za suyi, sai de ina so inga Baffana domin shine kad’ai yake sona duk da shima Gwaggo ta hana shi ya soni”

To naji kiyi shiru amma ki roqi YA ABUDULJABBAR domin zai iya zuwa qauyenku ya kawo miki Baffanki ki ganshi”

‘YAR AMANA kuwa kallon IKIRAM tayi tace “dan Allah ku mutane ne ko Aljannu?

Advertisements

“Meyasa kika min irin wanan tambayar me kika gani a dangane damu?”

“Sbd naga ku din ba irin mutanen rugarmu bane kuma kayanmu da naku ba iri d’aya bane, dan ko kad’d’on da suke yankinmu ma, ba irin kayanku suke sawa ba domin ni banta’ba ganin mutane irinku ba, da abinci irin naku haka ma gidajenku da komai naku dan Allah suwaye kud’in?”


“Mu mutane irinku sai de matsalar ku aqauye kuke mu kuma abirni kuma qila baki ta’ba zuwa birni ba shi yasa sanan bakiyi karatu ba ko”?

“Nayi karatu amma na addini, Akwai wani karatu da akeyi wanda Baffa na yace min karatun nasara ne wai za’a bud’e arigarmu shine Baffa yace ze kaini amma Gwaggo tazo ta rabamu ‘YAR AMANA taqare maganar tana kwalla”


IKIRAM kuwa cewa tayi Shikenan NUSAIBA kiyi haquri duk dani bana gane hausarki sosai domin kamar fulatanci kikeyi, amma ba damuwa domin Yaya na ya fad’amin komai akanki sbd haka karki damu insha Allah kema zaki zama ‘Yar birni kuma zakiyi karatun da baffanki yace ze kaiki” rungme IKIRAM ‘YAR AMANA tayi tace ” nagode sosai, amma wa  ya fad’a miki sunana NUSAIBA?”

“Yayana ne ya fad’amin” 

“Waye yayanki?”

Wanda ya fita yanzu Ya ABUDULJABBAR”

“Au kad’d’o”

“A’a ba haka bane sunansa sunansa ABUDULJABBAR, amma ki kirasa da Yaya”

“Sunan yamin dad’i , Shikenan zan kirashi da Hamma”

“Menene kuma Hamma?”

“Bakisan Hamma ba amma naga kuma kamar fulani ne sbd Hammaki yana kama da fulani sosai”

“Eh mu fulani ne amma na birni domin bama ma jin yaren, kawai de daddynmu ne yake ji danko Mum bata ji”

“Wacece kuma Mum”

Mum mama na ce ni Ya ABUDULJABBAR amma yanzu hardake, sai kuma Antynmu wato Matar Ya ABUDULJABBAR”

Zare ido ‘YAR AMANA tayi tace “au dama  Hamma yana da mata?”

“Eh yana da ita tana asibiti zaki ganta anjima” shiru ‘YAR AMANA tayi, 

“Menene?” IKIRAM tace, 

“Dama Hammanki yana da mata amma yabari su Hard’o…… Sai kuma tayi shiru ta rufe bakin ta domin ta tuna alqawarinsu da ABUDULJABBAR akan baza tafa d’a kowa anyi musu aure ba.

Kallon IKIRAM tayi tace “ya sunanki?”

“Sunana IKIRAM amma ki ringa kirana da Sister” to ” sunan ki da dad’i wlh haka ma sunan Hammanki harma yafi na kowa dad’i sai de shi mungune ba ya dariya”

Dariya IKIRAM tayi sanan tace ” Ya ABUDULJABBAR ba mugubane Sister kawai de shi ba yason raini ne shi yasa ba ya dariya”

“To naji menene kuma Sister?”

“Sister yana nufin ‘yar uwa, dan haka zan ringa kiranki da Sister nima haka zaki ringa kirana kinjiko Sister?”

Dariya ‘YAR AMANA tayi tace ” sunan Akwai dad’i  amma ni nafison sunana  ‘YAR AMANA”

IKIRAM kuwa cewa tayi ” to Shikenan bara nayi wanka muci abinci sai na nuna miki wasu abubuwan ki sansu”


Haka de IKIRAM tashiga wanka, ita kuwa ‘YAR AMANA tsohon buhun da Baffa ya bata ta d’auko ta bud’e shi kayane acikin leda aqulle, since ledar tayi,  ta ciro kayan ciki, kayan jariraine set guda harda towel d’insu da safar hannu da ta qafa, acikin safar qafar kuwa sarqane da d’an kunne da sarqar qafa ta yara masu shegen kyau da kyalli ruwan makuba dan har d’auke ido sukeyi, juya kayan ‘YAR AMANA taitayi tana kallo tana tambayar zuciyarta kayan miye wanan? Ga wani uban qamshi da sukeyi wanda tunda take bata ta’ba jin qamshi irin wanan ba, koda taji motsin IKIRAM zata fito sai ta mayar da kayan cikin buhun ta turasu qarqashin gadon IKIRAM.


Bayan IKIRAM ta shirya abinci taje ta kawo musu,  shinkafa da miyar kaza da hadin salat,  inda ‘YAR AMANA taita zabga qauya

nci da kuma santi,  dan ita kam acikin abincin kaza kawai ta sani kazarma dan Baffa yana gasa musu ne shi yasa.

Tin aranar IKIRAM ta fara ko yawa ‘YAR AMANA abubuwa, hatta cikin gidan sai da ta nunawa ‘YAR AMANA ko ina, inda cikin IKIRAM sai da yayi ciwo sbd da dariyar qauyancin ‘YAR AMANA domin kuwa aganin IKIRAM gaskiya qauyanci da jahilci babban ciwo ne, dan haka ta yiwa kanta alkawarin zata taimaki rayuwar ‘YAR AMANA.


Wanan kenan.________________________A guest house d’in Abban FINAH kuwa shine da Alhaji Biliyaminu da kuma Alhaji  Qasimu, Alhaji Halliru ne wato Abban FINAH ya kalli abokanasa yana huce gefe kuma matasan da suka bawa qwangilar kashe ABUDULJABBAR ne atsatsaye daka gansu kasan ba imani atare dasu,  Abban FINAH yace “Alhaji Biliyaminu! Alhaji Qasimu! Zaune fa bata ganmu ba domin kuwa shegen yaronan bai mutu ba dan da ida nuna naganshi a Teaching hospital, ya kuma ya ‘bamin maganganu domin kuwa ya gano mune mutanen da muka tura a kawar da shi sbd haka dolene musan abunyi tunkafin yayi ciki damu”

Alhaji Biliyaminu ne ya dubin Matasan cikin daka tsawa yace “ku marasa mutunci haka mukayi da ku kunsan ba kuka sheshi ba kuka kar’bi maqudan kud’ad’enmu to yazama dole kudawo da kud’ad’anan mu bawa wa’yanda suka san aikinsu ba kuba shashashu sakarkaru”

Acikin sune d’aya yace “kayi haquri Alhaji tabbas munbi wanan gayen domin kuwa da nufi zamu kashe shi amma sai ya fad’a cikin wani qaton rami mai duhu wanda ba’a kallon komai na ciki, shi yasa muka qaleshi domin kuwa ba muyi zaton zaifita awanan raminba, amma maganar kud’i kam babu munci bilis”

“You are very stupid, ku har kun isa musa ku aiki kuqiyi sanan ku ci mana kud’i? Qaryane yara ya zama dole kubiya ko kuma ku biya da rayukanku”

“Qarya kakeyi Alhaji Halliru ‘barawon gwamnati, Babban matasan yayi magana sanan ya dubesu dukkansu uku yace ” ku tsaya kuji ni  Jagwa bana tsoronku kud’i kuma munci munci kuma halak domin kuwa kud’ad’enmu ne mu tallakawa dan haka sai kusan tayi kuma kubi wani tsuntsun amma ba jagwa ba”

Abban FINAH ne ya ciro bindiga Aljihunsa ya harbi d’aya daga cikin matasan aqirji sai toch toch kawai Suka ji, Shi ko wanda aka harba tini ya zube agurin, sanan Abban FINAH ya nuna su da bindigar hanunsa yace ” ni d’inan da kuke ganina nafi ku rashin mutunci da tashanci sbd haka 24 a hours na baku kudawo da kud’ad’anan ko kuma dukkanku iyi muku abunda nayi wanan banzan” ya fad’a yana nuna wanda ya harbe.


Shi kuwa Jagwa gawar d’an uwansu suka d’auka suka fice agurin sai da suka fita a parlour d’in sanan yace ” ku kiyayi had’uwata daku domin sai na d’au fansa zaku san kun ta’bo jagwa”.


Zubewa Abban FINAH yayi akan d’aya daga cikin kujerun dake parlour di’n sanan yace ” lalle rayuwarmu tana cikin hatsari mudin ba musan yanda zamuyi da wanan yaron ABUDULJABBAR ba domin kuwa ya zame mana karan tsaye”

Alhaji Biliyaminu yace ” ni duk nafiku shiga tashin hankali domin kuwa, wasu maqudan biliyoyi ne nake so nayi wuf dasu kwanan wanda gwamnati zata sake su domin gyaran titin dake qasar nan kaga kuwa idan na saci na sata bai zama lalle dole gyara ko ina ba sai de gurin da ya samu kawai, sbd haka dolene muhad’a kai da gwiwa domin sace wa ‘yanan arnan kud’ad’en dan naga ma mana binkicen komai akansu”

Cikin ‘bacin rai Abban FINAH yace ” tayaya bayan wanan yaron ya sama na ido tabbas nasan yanzu tar yake kallonmu kuma yana da record d’in komai akanmu sbd haka sai munyi dagaske, sanan haqarmu zata cimma ruwa”

Alhaji Qasimu ne yace ” Shikenan ku bani nan da sati d’aya zan samo mana mafita”

Haka de suka gama qulle qullen sharinsu taron nasu ya watse.


Niko nace ya Allah ka mana tsari da mugayen mutane irinsu Alhaji Halliru.Yau kam da gyare gyare escort d’in ABUDULJABBAR da masu aikin gidan suka tashi dashi domin kuwa yau ne su Mum za su dawo, ‘YAR AMANA na tsaka da baccinta bayan sunyi Sallah sai ta koma bacci, IKIRAM ne ta d’aka mata dukka tace. ” ke tashi yau Mum d’inmu zasu dawo ita da Anti FINAH.

Tashi ‘YAR AMANA tayi ta zauna tace oho Gwaggon kice zata dawo yau domin baji Baffanki yace suna zaman jinya?”

IKIRAM tace ” eh ai kema Gwaggonki ce, kuma ba Gwaggo ake cewa ba anan Momi zaki ce, Baffa kuma Daddy”

“To naji muje ki had’amin ruwa nayi wanka kinsan har yanzu ban gama iya amfani da komai ba”

Kama hanun ‘YAR AMANA IKIRAM tayi suka shiga bayin ta had’a mata komai sanan ta fito tasa kaya, ta kuma fitowa ‘YAR AMANA wanda zata saka”

‘YAR AMANA na fitowa daga bayin IKIRAM tace bari naje gurin daddy mugaisa kafin ki gama, ga kayan kwalliya nan akan dressing mirow, maza kiyi kwalliya mai kyau ina zuwa”


Ita ko ‘YAR AMANA tinda take arayuwarta ko kwalli bata dashi balle ta saka dan haka dad’i ya kamata domin tana son kwalliya dan kuwa ‘yan matan rugarsu nayi harma na rugar su Kad’d’o amma ita bata ta’ba yiba dan haka ta sauqo da dukka kayan kwalliyar qasa daga ita sai qaramin towel d’aurin qirji ajikinta, ta zauna dirshan tafara kwa’be-kwa’be afuskarta,  ABUDULJABBAR ne ya shigo d’akin bakinsa d’auke da sallama amma bata jiba shi kuwa tsayawa ma yayi yana kallon ikon Allah, da kuma jikin girma da yarinyar take dashi domin ‘YAR AMANA irin yaranan ne masu ga’ba tana da jiki ga diri mai kyau amma bata da tsayi sosai gata fara tas gashinta kuwa harya mata yawa domin kuwa duk gashin ya barbazu aqasa ta bayanta,  ga fatar jikinta amurje mai d’aukan ido, wani irin yarrrr yakejin tsigar jikinsa na tashi can kuma ya hango alkamakashi akan dressing mirow d’in, ta kawa yayi yaje ya miqa hannu ya d’auka ‘YAR AMANA kuwa na ganinsa ta miqe tsaye tana riqe da towel d’inta baki ta murgud’a tace “kad’d’o miye haka zaka shigo bako sallama hannu yakai zai kamata amma ta zille binta yayi ai kuwa ta haye saman gadon binta shima yayi ya kamata ya had’e ta da bango yace “ke villager  bana ce karki qara qira na kad’d’oba?” 

“Dan Allah kayi haquri Hamma na”

“Waye Hamma naki?” 

“Kai mana”  ta fad’a tana murgud’a baki”

Shi kuwa ABUDULJABBAR baisan lokacin da yad’e bakinsu ba ya shiga kissing d’in ‘YAR AMANA baji ba gani duk ya danneta ko kallonta ba’ayi shi sam yama mance da wa yake tare sosai yake sarrafa ‘YAR AMANA domin dama ahannu yake,   gashi bakinsa yana cikin nata balle tasamu dama tayi ihu, sai da ya fitar da bakinsa anata yana neman hanyar tafiya garinsu domin yama d’auka FINAH ce, ita kuwa ‘YAR AMANA dantsen hanunsa ta samu ta gasa masa cizo har sai da gurin yayi jini wata qaramar qara yasaka tare da tureta gefe alokacin ne yaga ashe NUSAIBA ce kansa ya dafe yace ” ya ilahi,  oh ni ABUDULJABBAR me zansamu ajikin wanan jinjirar”

Itako ‘YAR AMANA cewa tayi cikin kuka “oho maka mugu kawai kuma sai na fad’awa baffanka”  kafin ta ankara tini ABUDULJABBAR ya cafkota ya matseta aqirjinsa yace ” wlh inaji zancanan abakin wani sai kinkoma rigarku wajen su hard’o VILLAGER kawai, sanan yasa alkamakashi ya kama rabin jelar gashinta ya yanke dai-dai lokacin IKIRAM ta bud’e qofa ta shigo tana cewa Sister daddy fa yatafi d’auk…………… Maganar tace ta maqale ganin ‘YAR AMANA kwance aqurjin yayanta, shi ko ABUDULJABBAR cika ‘YAR AMANA yayi yana cewa banza kanna kima wari yakeyi” sanan ya wullawa IKIRAM mugun kallo yasa kai ya fice a d’akin…………Hhmm muje zuwa dan yanzu aka samo wasanDan Allah in kinkaranta kiyi shere shere asauran groups Ngd

*ASSTAGAFIRILLAH, WA ‘A TUBU ILAIKA*🀲

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

YAR AMANA 9-10

Advertisement  πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦° *NUSAIBA ‘YAR AMANA*πŸ’§πŸ’§ Page 9&10 ABUDULJABBAR ne kwance a gadonsa FINAH tana rungume dashi tamkar zata…

YAR AMANA 3-4

Advertisement  πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°        *’YAR AMANA Page  3&4 Wata Mota ce qatuwar gaske fara tas mai shegen…