YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 36-37

Advertisement

 *NUSAIBA*

       *”YAR AMANA*☘️☘️

    *PAGE 36-37*

——- Ana cikin haka sai ga dr Musa nan Suka d’au daddy suka kaishi d’akinsa dr Musa yamasa allurai kuma ya d’aura masa drip,  Anti Amarya ce ta kalli dr Musa cikin tashin hankali tace ” yaya de dr me yasamu Alhaji”?

Mum kuwa dake tsaye tana ta harare – harare karaf tayi tace ” kaji munafuka ina ruwanki da abunda ke damunsa in ba iya yiyi ba”

Wani matsiyacin kallo Anti Amarya tayi mata sanan tace ” ni yanzu bana tataki ta lafiyar mijina nakeyi qila ma bazai wuce baqin cikin da kike qunsa masa ba yasa ya fad’i”.

Nan fa Mum tahau zagin Anti Amarya,ai kuwa dr Musa yace ” dan Allah Mum da Anti kufita domin kuwa hayaniyarku zai qara jefashi cikin wani hali, gaskiya kuyi haquri amma hakan da kukeyi ba girmanku bane ai”

Mum ce tafara ficewa cikin fushi tamkar zata tashi sama itako Anti Amarya guri tasamu ta zauna tana cewa ” ba in da zani dr domin kuwa zantsaya na kula da mijina.

Haka kuwa Akayi Anti Amarya ce taita jinyar daddy ita dr Musa har daddy yafara samun sauqi itako MUM fushi takeyi sosai bugu da qari ga rashin FINAH akusa da ita ga kuma ABUDULJABBAR har yanzu bata san inda yakeba tana so taje tayi bikon FINAH amma tana jin kunyar iyayen FINAH domin kuwa tayaya zatayo bikon mata ba miji dan haka MUM taci gaba da saqawa da kuncewa inda tafara binkicen Abokanan ABUDULJABBAR ko sunsan inda yake, hatta dr Musa sai da tabincika akan wa yaqira shi lokacin da daddy yafad’i, shiko dr Musa yace mata IKIRAM ce taqirashi ta wayar daddy, nan MUM tashiga yimasa tamboyoyi ko zai san inda d’anta yake amma ba nasara dan haka dolenta ta haqura tasa ido tana jira taga dawowarsa.

Advertisements


*Bayan sati biyu*

A yanzu jikin daddy Alhamdulillah domin ya warke garas tamkar baiyi jinya ba inda ya had’a MUM da Anti Amarya yayi musu fad’a sosai tare da nasiha kuma yace duk wacce ta sake tayarmar da hankali tabbas sai tabar masa gidan sa, dan haka Anti Amarya ta dena shiga huld’ar Mum, itako Mum dagangan take takalarta dan Anti Amarya tabiyeta inyaso daddy ya koreta, itako Anti Amarya tini ta ganota dan haka ko me MUM zata mata bata kulata nan fa MUM tashiga mata gori iri iri wai Anti Amarya tana tsoro takoma wa shan baqar miya.

JALALULDEEN kuwa ganin daddy ya samu sauqi sai yace zai tafi amma Daddy yace ya zauna a gidan kawai tinda ayanzu ma ba wani namiji babba a gidan dan haka JALALULDEEN ya zauna yaci gaba da karatunsa, hakan kuwa baqaramin baqin ciki yasa Mum dan har sai da tasamu daddy taita masifa wai yacika musu gida da tarkace, Shiko Daddy yace ai de gidana ne dan haka dole in ajiye wanda naso.


FINAH kuwa tini fa zaman gidan nasu yafara isarta, gashi gani takeyi kamar zaman da takeyi zata iya rasa ABUDULJABBAR nanfa tacewa Mum d’inta zata koma gidan ta, ai kuwa Mum d’inta tahau ta da fad’a tana cewa ” haba FINAH nifa banaso ki koma wanan qadararen gidan auranaki haba dafa quriciyarki kuma ba masoya kika rasa ba sbd haka tsinke wacan auren zamuyi ki samu miji maisonki bacan d’an wahalar ba”

“A’a Mum bazaki gane bane nifa ba namijin da yake burgeni inba Mijina ABUDULJABBAR ba dashine kawai zan iya rayuwar aure domin kuwa maza duk mata nake kallon su mijina shine kawai namiji”

Cikin ‘bacin rai Mum tace ” lalle kuwa iska tana wahalar da me kayan kara dan haka saiki shirya ki koma amma daga zarar yadawo daga yawon abaibad’ancin da yatafi zansa amiki wani aiki akan sa da zai manta kowa ya soki ke kad’ai ke hatta uwarsa sai ya mata tabbas wanan wahalar dake d’in da yakeyi bashine akan sa sai yabiya dan kuwa sai yasoki kamar zaiyi hauka”

Cikin farin ciki FINAH tarungume Mum d’inta tana mata godiya domin kuwa har tafara hangowa tana juya ABUDULJABBAR son ranta.

Haka de FINAH tashirya takoma gidan Mum inda MUM taji dad’in komawarta sosai akaci gaba da gwari’bawa.


*Bayan shekara daya*

Advertisements

Ayanzu ABUDULJABBAR yacika shekara d’aya da tafiya kenan Mum da FINAH sunshiga tashin hankali sosai akan rashinsa inda MUM kullum fad’a takeyi da daddy akan sai yafad’a ina d’anta yake, shiko yaqi sanar da ita, haryanzu da ABUDULJABBAR yayi shekara daya harda wata biyu, dan haka daddy yafara yi masa zancen dawowa, amma ABUDULJABBAR ya bashi haquri akan zai dawo kwananan.


A’bangaren ABUDULJABBAR kuwa har yanzu bai manta da Nusaiba ba domin kuwa tana nan daram acikin zuciyarsa da ita yake kwana yake tashi, yayin da ‘bangare d’aya kuma ya mayar da hankali akaratunsa, amma tunanin ‘YAR AMANA yafi yawa gashi haryanzu yanan da sha’awar yarinyar a zuciyarsa kuma yanan akan batunsa na sakinta domin kuwa a ganin sa tausayinta yakeji shi yasa ya kasa dena tunaninta sai de sha’arwata fa baisan ta menene bace ta zaunamar daram aransa.

‘YAR AMANA kuwa ayanzu tama manta da wani ABUDULJABBAR dan ita bata tunoshi sai IKIRAM tayi maganarsa sanan take tuno shi amma sam tama manta da auransa dake kanta kwata-kwata tinanin baffanta kawai shine wanda takeyi dan wataran zata ‘boye tasha kukanta taqoshi dan tana son ganin baffanta amma batasan ya zatayi taganshi ba balle inta tuna da sharrin da akamata dan haka sai tasake karaya, amma ita tini tamanta da wani batun aure dake kanta shi kanshi kad’onma tafara manta shi domin kuwa tinda tasamu Anti Amarya Shikenan damuwarta tatafi.

FINAH kuwa tananan tana jiran zaman ABUDULJABBAR inda MUM take tausaya mata sosai domin tasan FINAH sirikar kirkice baza a ta’ba samun irinta ba, awanan zamanin dan haka tad’au fishi sosai da ABUDULJABBAR.

Ayanzu kam ABUDULJABBAR ya cika shekara biyu da tafiya dan har yagama karatunsa yafara aiki dasu akan binkicen qasa, kuma har lokacin FINAH nanan zaman jiransa, ‘YAR AMANA da IKIRAM kuwa tini har sunshiga JSS one, inda suke da shekaru 15 kenan ‘YAR AMANA sosai tazama cikakiyar budurwa mai kyau da sura da aji ga kuma ilimi dan yanayin jikinta kamar mai shekaru 18 ayanzu kam tasaba sosai da JALALULDEEN qanin Anti Amarya dan shi yake koya mata assignment sosai shaquwa mai qarfi tashiga tsakanin su inda JALALULDEEN yakamu da tsananin sonta har yakasa ‘boyewa wata rana suna hira yafirta mata abunda ke ransa aikuwa ‘YAR AMANA tarufe ido tatashi ta gudu, tindaga ranar kuma ta shiga kunyar JALALULDEEN.


Yau fa MUM takai maqura dan rabonta da d’anta shekaru buyu kenan harda kwanaki dan haka tasamu daddy a parlour yana wani lissafi cikin ‘bacin rai Mum tace ” wlh Alhaji kasan inda yaronan yake domin kuwa na lura kuna waya dashi to kasanar dashi mudin bai dawo gida ba acikin kwanakinan bani bashi yanemi wata uwar”

Mum taqarasa zancen tana kuka tabar wajen. Kawai sai daddy yaji ta bashi tausayi dan haka ya d’aga wayarsa yaqira ABUDULJABBAR ai kuwa ABUDULJABBAR yana d’auka daddy ya shiga yimasa fad’a sanan ya fad’a masa abunda Mum tace. Kashe wayar yayi ya qira Mum da take dakinta tana kuka ringing biyu ta daga da mamaki taji muryar da batayi zaton ita bace tashi tayi tsaye tace ” ABUDULJABBAR kaine Inayinki kashiga?

Dasaurinta tayo d’akin FINAH.

“Eh Mum nine dan Allah Mumy na kijanye sharadin da kikayi aikaina”

“Ba sharadin da zanjanye wato ni nazama banza agareka ni ka guja har tsawon shekarunan, sanan ka ajiye Matarka kayi tafiyarka anya ABUDULJABBAR kana tsoron Allah kuwa? ina zaka kai haqqin ‘yar mutane ? to wlh bara kaji maza kazo gida asatinan na fadamaka”.

“Haba Mum mezanmuku inazo tinda naga bakwa buqatata daga ke har ita FINAH dan haka gwara nayi nisa daku ina ganin zaifi sbd haka tinda ita FINAH tagaji kawai taje na saketa saki day…….. “ABUDULJABBAR!!!!!!!!!!!!!!

Mum takirasa tace” wlh bara kaji FINAH bata saku ba kuma wlh idan ka qara kuskuren sakinta anan gaba banyafe maka ba”

ABUDULJABBAR kuwa qittt. Yakashe wayarsa 

FINAH kuwa dake jin komai nan tasa kuka tana cewa ” yanzu da abunda zaka sakamin kenan ABUDULJABBAR wanan itace ribar soyayyar da nake maka katafi kabarni tsawon kwanaki amma qarshe kibiyoni da ladan saki……………


Hhmm muje de zuwaNo comments

No TypingDan Allah inkinkaranta kiyi min shere asauran groups
*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

YAR AMANA 11-12

Advertisement  ðŸ‘©â€ðŸ¦°ðŸ‘©â€ðŸ¦°ðŸ‘©â€ðŸ¦°ðŸ‘©â€ðŸ¦°ðŸ‘©â€ðŸ¦°ðŸ‘©â€ðŸ¦°ðŸ‘©â€ðŸ¦°ðŸ‘©â€ðŸ¦° *NUSAIBA ‘YAR AMANA* Page 11&12 __Shi kuwa ABUDULJABBAR baima tsaya sauraransu ba ya shiga motar sa…