YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 38-39

Advertisement

 *NUSAIBA*

     *’YAR AMANA*☘️☘️

       *PAGE 38-39*

_____ Mum kuwa cikin tashin hankali tace “kiyi shirunki FINAH wlh ABUDULJABBAR bai isa ba mudin inono na yasha bai isa ya sakeki ba! Inkuma yaqi tabbas sai ya biyani nono na da yasha”

Cikin kuka FINAH tace ” ki barshi kawai MUM ni nahaqura da ABUDULJABBAR duk danasan sonsa shine zai zamo ajalina amma ba yanda na iya tinda baya buqatata arayuwarsa na haqura zankar’bi qadarata zanyi nisa daku Mum sai wata rana”

Rungume FINAH Mum tayi cikin ‘bacin rai tace “A’a FINAH banyarda ba tabbas inkibar ABUDULJABBAR lalle kuwa sai de yamutu ba mata domin kuwa ni Murjanatu bazan ta’ba kar’bar wata mace da banba amatsayin sirikata! Kece FINAH kece za’bina kece naga kindace da d’ana ABUDULJABBAR shi yasa namasa sha’awar auranki domin kuwa ked’in mace ce ta nunawa sa’a shine shi d’an zamani zai bad’amin qasa a ido to wlh yayi kad’an, sbd haka ki zauna ba inda zaki auranki kuwa kamar yamayar dashi”


Cikin kuka FINAH tace “amma Mum yanzufa igiya daya tarage tsakani na da ABUDULJABBAR ina tsoran ranar da zai tsinka d’ayar igiyar”.


Advertisements

“A’a FINAH qaryane wlh zan gindaya masa sharud’a qarfafa akanki my FINAH sbd haka ki kwantar da hankalinki kudin ina raye kece kawai sirikata”

Rungume MUM FINAH tayi cikin farin ciki tace ” tabbas nayi dacen uwar miji lalle da ana samun iyayen miji irinku tabbas da matsololin aure sunqare kuma tabbas Mum yanda kika riqeni da AMANA nima zan soki so na AMANA har qarshen rayuwata”


‘YAR AMANA kuwa sosai suka miyar da hankalinsu akan karatunsu ita da IKIRAM inda Mus’af shima ya dage akan shifa da gaske yake yana son IKIRAM dan kuwa yaje ya fad’awa dad d’insa, shine dad d’insa yace to yaji zefad’awa iyayenta asan da maganar zuwa yarinyar tagama karatunta, ko da dad d’insu Mus’af yasamu daddy da maganar sai daddy yace Shikenan dama shi idan tagama secondary aurar da ita zaiyi.


Mum kuwa sosai take fishi da daddy domin gani takeyi shi yaziga ABUDULJABBAR ya saki FINAH dan haka taje tasamu daddy ta tsaya akan daddy yana hira shida Anti Amarya a parlour d’insa, cikin masifa MUM Tace ” wlh Alhaji kaji kunya da har ka iya zuga d’anga ya saki matarsa sbd baka qaunarta dan kana baqin cikin mahaifinta ya fika kud’i to wlh bara kaji sirikata bata saku ba, dan dolenshi inyanaso inci gaba da zama amatsayin uwarsa yadawo da matarsa d’akinta inkuma ba haka ba to wlh yanemi wata uwar bani ba, tinda yafi qarfina shi adole yagirma dan munafurci harwata qasar yatafi batare da sani naba sbd haka yasan tayi ni Murjanatu na yafe sh……

“Haba Hajiya waike wata irin wawiyar uwace da batasan abunda ya dace da d’antaba arayuwarshi! Anti Amarya tace cikin masifa sanan taci gaba da cewa to wlh bara kaji ina akan wacar marar mutunci surukartaki kike nema kiyiwa d’anki baki kidawo kina da nasani marar AMFANI to ki rubuta ki ajiye ni Rahama nafad’amiki sai taci amanarki sbd irin soyayar da kike nuna mata, soyayar ma bata da amfani wlh tinda harkinfi sonta da d’an da kika haifa”

Tas!Tas!! Mum ta sauqewa Anti Amarya tagwayen maruka zafafa sanan cikin huci tace “ke harkin isa kibani shawara wacece ke banza ‘yar baqin cik……..

Tas!Tas!!! Kafin Mum taqarasa daddy ya sauqe mata maruka biyu lafiyayyu, dafe kuncinta Mum tayi tana zubar da hawaye tadubi daddy tace ” yanzu Alhaji ni kamara sbd namari wanan makirar matartaka?”

“Yes” daddy  yace sanan yaci gaba dacewa ai ita makirar gaskiya take fad’amiki amma da yake daqoqiyace mai qwaqwalwar kifi kika kasa fahimta sbd haka kome zakiyi kije kiyi keki kasani sbd kinga Allah yabaki d’a mai biyayya shine kike abunda kike so”

Jan hanun Anti Amarya daddy yayi sukabar d’akin sukabar MUM atsaye dafe da qunci.

Shiko daddy bai sake Anti Amarya ba harsai da yakaita shashinta sanan yararasheta da kalamai masu dad’i,  kuma yacewa Anti Amarya duk abunda MUM zatayi ita da FINAH karta kuma sa bakinta ba ruwanta tabisu da ido kawai.

Advertisements

Haka kuwa rayuwa taci gaba da tafiya Anti Amarya ba ruwanta da sabgar su Mum, harkokin gabanta kawai takeyi, ‘YAR AMANA kuwa sosai tamai da hankalinta akaratunsa ita da IKIRAM ba kama hanun yaro, sanan Anti Amarya sai sake wayar da ita takeyi dan kuwa ‘YAR AMANA  kuwa har tamanta da rayuwar qauye.


__________________________


*Bayan shekaru uku*

Rayuwa kenan Abubuwa da dama sunfaru anyi samu anyi rashi sai de muce Allah yasa mudace ayanzu ‘YAR AMANA da IKIRAM suna ss2 inda suka zama cikkakun ‘yan mata ba yama ‘YAR AMANA tana cikin shekara18 kenan amma kamar ‘yar shekaru25 domin kuwa tazama wata cikakkiyar budurwa mai class da ilimin zamani da na addini wanda ma magana da qar take iya yi sbd jan aji ga kyawunta da dirinta komai ya qara baiyana ko mace sai tasara da kyawun ‘YAR AMANA balle maza domin kuwa ‘YAR AMANA batama fita sbd yanda ‘yanmaza suke rubibin sonta sai de duk wanda yazo in daddy yafad’a masa wata magana to baidawowa amma JALALULDEEN ya nace sosai akan NUSAIBA inda bai haqura ba harsai da ya tusa mata sonsa, sosai ‘YAR AMANA takeson JALALULDEEN duk dashi d’in sai ahankali domin kuwa yana shaye-shaye amma Nusaiba tace taji tagani domin kuwa ya kamata tasoshi sbd karamcin yarsa agareta dan haka sosai suke soyayya ba kama hanun yaro, inda duk abunda akeyi daddy bai sani ba, daga Anti Amarya sai IKIRAM kawai suka sani.


         *ITALY*


A Italy kuwa shiko ABUDULJABBAR tini yatara dukiya mai uban yawa wanda yake ta aikowa daddy ake aikin alkairi dashi, ayanzu kam ABUDULJABBAR yazama wani big MAN dashi wanda yake juya Naira son ranshi kyawunsa ya qara fitowa sosai yayi jajir dashi har wani d’an saje ya ajiye afuskarsa wanda yake tarud’ar ‘yan mata, domin kuwa da dama ‘yan mata sunsha kawo masa tallar kansa amma shi kuma ko kulasu baiyi domin kuwa ayanzu yacire ‘ya mace aransa azumi kawai yakeyi duk sati dan haka sha’awa taragu masa sosai saide abunda ba arasa ba, ayanzu kam yayi yaqi da zuciyarsa yabar tinanin ‘YAR AMANA sai de zuwa – zuwa Ψ¬Ψ¬aikin sa yasa agabansa.

Domin ko MUM baya qiranta FINAH kuwa tini ya maidata dan dolansa domin kuwa Daddy yayi masa magana duk abunda MUM tafad’a ya sanarmasa.


IKIRAM kuwa ita da Mus’af soyayya sukeyi sosai domin kuwa jira ake IKIRAM tagama karatunta asha biki inda MUM take ta jiji da kai sbd ‘yarta zata auri d’an gidan Alhaji Usman dala, dan a ganin ta Shikenan ta haye, surukarta ‘YAR masu kud’i kuma ‘yarta ma zata auri d’an masu kud’i, inda takeyiwa Anti Amarya habaici iri iri wai wasu ma duk kyawun yatafi abanza tinda anrasa mashin shini, itako Anti Amarya ko kallon ta batayi, ayanzu Anti Amarya haihuwarta daya da daddy inda ta haifi ‘yarta Yasmin, ‘YAR AMANA naji da yarinyar kamar me Yasmin shekarunan ta biyu, kuma itace kawai mace acikin yaran Anti Amarya dan haka sukeji da ita, inda yaran Anti Amarya yanzu duk sunzama ‘yan samari.IKIRAM ce da ‘YAR AMANA suna dawowa daga Isilamiya IKIRAM ta kalli ‘YAR AMANA tace ” NUSAIBA kinga dakinfitar da miji ai saide asha bikinmu tare”

Murmushi ‘YAR AMANA tayi sanan tace ” miji kuma nanawa aini JALALULDEEN shine za’bina”

“Amma de NUSAIBA kinsan JALALULDEEN yana shaye-shaye ko? Tinda munsha kamashi yana shan taba, ni wlh bansan me kika ganiba ajikin JALALULDEEN har kika mato akan sa haka dan Allah kisanja shawara”

“Hmm IKIRAM kenan baza kigane bane shifa so ba ruwansa da kudi ko asali ko kuma kyau, kinga kuma aibun JALALULDEEN Shaye- shaye ne kawai kuma daga zaran munyi aure zanitsar dashi”

“A’a NUSAIBA baki dace da JALALULDEEN ba agaskiya inayiwa yayana ABUDULJABBAR kamu”

Yayanki ABUDULJABBAR aini bansanshiba”

“Mijin Anti FINAH ne baki saniba Nusaiba? Wanda har amanarki yabani yace inkula dake tamkar kaina”

“Hmm IKIRAM kenan inaga haryanzu da Sauran ki a so ni JALALULDEEN shi nakeso shine rayuwata domin kuwa ni shine yayimin acikin maza……..


Hhmm muje de zuwa my pans

Agaskiya zakujini off domin kuwa naga comments d’inku yana kadan aha.
Dan Allah inkinkaranta kiyi min shere asauran groups


Kullum ina roqonku yin shere

Amma banga kunayimin ba

Abubuwa ne suna yimin yawa.

*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

YAR AMANA 9-10

Advertisement  πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦° *NUSAIBA ‘YAR AMANA*πŸ’§πŸ’§ Page 9&10 ABUDULJABBAR ne kwance a gadonsa FINAH tana rungume dashi tamkar zata…

YAR AMANA 3-4

Advertisement  πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°        *’YAR AMANA Page  3&4 Wata Mota ce qatuwar gaske fara tas mai shegen…

YAR AMANA 11-12

Advertisement  πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦°πŸ‘©β€πŸ¦° *NUSAIBA ‘YAR AMANA* Page 11&12 __Shi kuwa ABUDULJABBAR baima tsaya sauraransu ba ya shiga motar sa…